Haka ta shiga gyara gidan tana hawaye, ta shiga tuno lokacin da take da ciki da suka je supermarket yin sayayya har faɗa ya haɗa ta da yarinyar soja, karshe Adam ne ya sha dukan. Ta sake tunowa da mai sayar da kwai inyamuri na ƙasan layin su da shima rigama ya haɗa, a ranar idan bata manta ba Adam ya mareta, amma itama ta rama. Bata manta lokacin da tace masa ya tashi ya tafi aiki ƙarfe shida na safe ba. Bata manta lokacin da ta hana shi zuwa gidan Khadijah ƙanwarsa ba, bata manta lokacin. . .