Bai ko jira an amsa masa sallamar ba ya shigo cikin palon da sauri ya na kiran sunanta. Ya na zuwa kusa da ita ya tsaya ya na kallonta, itama shi take kallo idanunta ƙur a kansa babu alamar tsiro ko nadama akan abun da tayi. Kafin yayi magana ta ce "I'm sorry Daddy please kayi hakuri" Ta faɗa ta na marairaicewa alamun abun tausayi. Adam da gaba daya jin daɗin ganinta ya kawar da ɓacin ran da yake ciki. Ya ce "Ina kika je?" Ta ce "Daddy ina makaranta fa, cen na koma da kwana amma. . .