Mama ta ce "To kuwa sai dai ka mutu ɗin, domin ba za a bar wa ran abun da yake so ɗin ba dan ubanka" Ta na faɗa ta na ƙaraso wa gurin da yake, ta ci gaba da daɗin "Sakar mata hannu ta bar gidan nan na ce ko na saɓa maka mutumin banza mutumin hofi kawai?" Habib ya ce "Dan Allah Mama kar ki..." Kafin ya ƙarasa ta ɗauke shi da mari wanda sai da Haura ta rintse ido domin ji tayi kamar ita aka mara. Tun da su Mama suka shigo take ta ƙo. . .