Da wani irin gudu Haura ta fito daga cikin motar ganin kamar Amminta ce a kwance cikin jini. Ai kuwa ta na ƙarasowa taga ita ɗin ce. Hakan yasa ta kurma ihu tana ja da baya tana kallonta, sai kuma take mata gizo kamar ita kamar ba ita ba. Sai Kuma ta dawo da gudu ta faɗa kanta tana kiran sunanta tana jijjigata. Mutane suka rirriƙeta ganin dai kamar ta na da alaƙa da gawar da ta buge ɗin. Duk yadda suka kai da tayi shiru taƙi sai ihu take yi tana kiran sunan Amminta. Wani. . .