Cikin wa ta siririyar murya ta ce "Sir i miss you, ina ta tunaninka ko barci na kasa yi ina ta son na zo school kawai saboda na ganka, kaima ka yi kewa na?" Ta ƙarasa ta na zama a kan cinyarsa. Kasa magana Habib ya yi sai binta da kallo kawai ya ke yi, ga shi duk ta cika masa ofis ɗin da wani almurin turare mai shegen ƙamshi. Tambayoyi ne da ya wa a bakinsa da yake so yayi mata amma ya kasa samun damar yin ko guda ɗaya. Bai san mai ya sa idan baya tare da. . .