Skip to content

A Daren Farko | Babi Na Uku

1.5
(2)

<< Previous

“Na samota Jiddo! Mahaifiyar ki ta bayyana,kin san me? A shekaru takwas da wata tara da ‘yan kwanaki da na ɗauka ina neman ta Allah ya amsa addu’ata dota,tabbas na kusa tabbata mijin Jidda Abban Jidda! Zuciya da ruhi sun kusa samun abun da su ke so my little Jiddo.”

Dr Sani ya ƙarasa maganar sa yana shafa screen ɗin wayarsa da hoton ƴarsa Jiddo mai shekaru hudu a duniya ya mamaye fuskar wayar. A tsayin shekarun nan zai iya rantsewa sauyin da bugun zuciyar sa ta samu sabida girman soyayyar Jidda da yake kwana yake da tashi da ita.

Jiya yana ɗaya daga cikin ranakun da ba zai taɓa mantawa da ita ba. Sai ga shi yau har yafi jiya. Lallai jumma’ar za tai kyau,tinda ga dukkan alamu larabar jiya ta sa ce shi kaɗai da abar ƙaunar sa

“Amma Allah ya kwashewa direbar babbar motar nan albarka!”

Dr Sani ya faɗi haka yana mik’ewa tare da ajiye wayar a gefen gadon sa.

Wani ƙaton hoton da wani kwararren mai zane ya zana masa Jidda ya ɗauko

“Don Allah ki bayyana mani kan ki! Ke ce rayuwata,na tabbata
zuciya da ruhina da na ki suna tare a ko yaushe! Ki ƙara so gare ni,ni da Jiddo muna jira,mun yi kewar ki,kewar da baki ba zai taɓa misaltata ba! I love u Jidda,i love u with all my heart Sweatheart matar Dr”

Ya ƙarasa maganar yana dunkule hannayen sa tare da sakin ƙara kamar mai shirin yin dambe.

Wayar sa ya ƙara ɗauka Dr Ahmad,sunan daya bayyana a fuskar wayar sa kenan. Har ya kai hannu da azama zai kira lambar ya ji zuciyar sa ta buga da ƙarfi

“So ka ke Dr Ahmad ya ɓata maka rai? Jiya da yau rana ku ne da suka bambamta da sauran ranakun da suka wanzu cikin rayuwar ka! Me yasa ka zaɓi Dr Ahmad matsayin wanda zai taya ka raya fararen ranaku biyun nan?”

Dr Sani yai saurin ajiye wayar bayan dogon zancen zucin daya ɗauki lokaci yana saƙa da warwara.

“Ni dai Jiddan da na sani marainiyar Allah ce! Bata da gata ko galihu,saɓanin wannan Jiddan,mai aji da kwalliya,har mota fa ka faɗimin ka ga tana ja! Anya kuwa ba karuwanci…!”

“Ya isa haka Ahmad!!”

Dr Sani ya ƙarasa maganar cike da karaji yana huci,jikinsa na rawa tamkar wanda a ka jona ma shokin. Yana shirin shaƙe kwalar Ahmad yai saurin rintse idanunsa.

Wani dogon tsaki ya ja daya fahimci cewar kogin tunani ne kawai ke hasasho masa Dr Ahmad. Manzon Allah ya yi gaskiya,da yace mu faɗi alkhairi ko mu yi shiru! Duk da Dr Ahmad ya gane kuren sa na k’in Jidda da yai a farko hakan bai sa Dr Sani ya mance ba. Tare da shi su kai ta zaga gari,police station,mutuwari da asibitoci neman Jidda! Ko a lokacin daya k’i Jidda tausayin rayuwar abokinsa ne ya rinjayi zuciyarsa,daga baya ya gane “SO” babbar cuta ce,ba shiri ya zubda makaman yak’in. Ya rungumi abokinsa,suka haɗa karfi da karfe don ceto rayuwar Jidda a duk in da take amma kamar an shuka dussa! Sai ga shi a yau yai tozali da Jidda cikin shiga ta alfarma da jin dadin rayuwa. Don kallo ɗaya zaka mata ka gane sauye-sauye da dama tsakaninta da Jiddan da ya ma mahaukacin so shekarun baya da suka wuce. Soyayyar da yake mata ba zai taɓa mance surar ta da kyawun fuskarta ba ko da a buge yake cikin maye bare kuma yana cikin hankalin sa. Wannan tunanin yasa ya ƙara ɗaukar wayarsa a karo na biyu,ba tare da tunanin komai ba ya danna lambar Dr Ahmad

“Wayar ma sai an min yanga za’a ɗaga?”

“To mutum na gida cikin iyalansa sai a bi a dame shi ina dalili ? Gani ga rabin raina” Dr Ahmad ya ƙarasa zancen sa cike da shak’iyanci

Dr Sani ya haɗiye wani yawu mai ɗaci kafin ya samu damar ba ma Dr Ahmad amsar tambayarsa

“Uhmmm lokaci yayi gorin gurubar ka zata tsaya a kanka..”

“Bani in sha kawai”

Dr Ahmad ya faɗi yana cike da zakuwar jin abinda amininsa zai zo ma sa da shi

“Na samota Dr”

“Wa kenan?”

“Zuciya da ruhi jiya gani ga Jidda Dr..”

“Da gaske?”

Dr Ahmad yai saurin katse ma amininsa hanzarinsa.

“Na taɓa yi maka irin wannan wasar?”

“A ina ka ganta? Shin tana da aure ko kuma…”

Cike da zakuwa wannan karan Ahmad ke jehowa Dr Sani tagwayen tambayoyinsa

“Kar ka ƙarasa don Allah Dr!”

Dr Sani ya ƙarasa maganar cike da karaya. Zuciyarsa tayi zurfi a ƙaunar Jidda. A tunaninsa haduwarsa da ita shi ne zai tabbatar da duk wata rayuwa daya dade yana hango musu. Ashe sam ba haka ba ne. Zuciyarsa tayi zurfi,idanunsa sun makance ta yadda bai iya gane fari bare bak’i a kan Jidda!

Ashe aure zai iya masa katanga tsakaninsa da Jidda? Tsayin shekarun daya ɗauka yana dakon jiranta bai taɓa hasashen haka ba.

Da sauri ya katse kiran,zuciyarsa na bugawa da sauri-sauri. Layin Hajiya ya shiga nema. Bugu ɗaya yaji an ɗauka,muryar yarinyar ya katse masa hanzarinsa

“Hello Daddy za ka zo mu tafi ne? Daddy Hajiya bata bani wayarta in yi game,daddy har yau ba ka kai ni wajen momma ba”

Yarinyar ta ƙarasa maganar cike da yarinta da shagwaba

“Kina so ki je wajen momma ko my Jiddo?”

“Eh mana daddy”

“To ki dinga yin addu’a sosai. Banda rashin ji,very soon momma ɗinki zata dawo kin ji,ki gaishe da Hajiya take care,bye-bye”

“Bye daddy…”

Tun kafin ta ƙarasa yai saurin katse wayar cike da k’warin gwiwa.

Kullum zancen Jiddo ɗaya ne..Momma momma,hakan ba ƙaramin ƙara masa kwarin gwiwar neman Jidda yai ba,zai shiga zai fita,faɗin Garin Katsina da kewaye,in har Jidda na rayuwa a cikinta dole ta ƙaraso gare shi. Wannan alƙawari ne yai ma kanshi,domin ba zai sake yarda ta kubuce mi shi ba a karo na biyu”

(To Dr Sani ai komai sai Allah ya amince! Ina laifin ka ce in Allah ya yarda) Kuskuren da muke yi kenan a duk lokacin da soyayyar wani abu ya rufe mana idanu,babu neman zaɓin Allah tun daga mafari. Sai akasi ya gifta a zo a na dana sani. Don Allah mu kula. Komai nufi ne na Allah. Duk da an ce so…Babbar cuta ce mai tsaida numfashi.

“Ta ina zan fara?” Dr Sani ya faɗi haka yana mai shirin faɗawa toilet bayan ya rage kayan jikin sa.
*****
“Sannu Mama ya ƙarfin jikin na ki?” Allah ya ba ki lafiya”

“Jiki da sauki Habiba, Allah yai muku albarka ke da ɗan uwan na ki, ya raya ma ku zuri’a.”

“Ameeen mama”

Habiba ta faɗi haka fuskarta cike da tsantsan farin ciki

“Mu kuma ya tsine mana ko? Wallahi mutum yai kaɗan! Ramatu ba ki isa ba! Wallahi sai na ga bayan ki ke da waɗan nan tsinannun yaran na ki,Malam nawa ne ni kaɗai! Kina tunanin har zan gaji in kyale ki ne? Barci na yi..Na yi dogon baccin da na so in makaro,amma kar ki manta sunana Samira ungonzoma yar Nijar! Kin manta inkiyata? Tsantsi ce ni,na kada giwa bare mai ƙafa biyu,dole ki tafi ki bar ni na wataya,sauran kiris…”

A zafafe Habiba ta mike tana shirin fita daga ɗakin,muryar mahaifiyarta Ramatu yasa ta tsaya cak

“Dawo Habiba,ku barta da halinta,mai hali bai fasa halinsa,kin san an ce mahaukaci bai taɓa warkewa,maza dawo ki zauna ki ji da abinda yake jikin ki tashin hankali ba na ki ba ne kin ji ko”

“Shi ke nan mama! Ta ci albarkacin ki.”

Habiba ta faɗi tana haki sabida tsohon cikin data ke ɗauke da shi. Hakan yai daidai da shigowar Malam,Ungon zoma na jin sallamar shi tai saurin rik’e kunci tare da sakin ƙara

“Yanzun Habiba ni zaki mara? Daga abin arziki sai ya zama na tsiya Allah ya baki hakuri,ki gafarta min idan na ɓata maki…”

“Habiba! Habiba!! Habiba”

Malam ya shiga kwalama ƴarsa Habiba kira tamkar sabon makahon daya tsira daga ciwon makanta

“Sannu da zuwa Abba”

“Ba na hana ki zuwa gidan nan ba? Ko ban ja ma ki kunne a kan hakan ba? So ki ke in yi fushi in tsine ma ki ki bi uwa duniya? Maza ki ba ma Samira hakuri ki ta shi ki fi ce min daga gida,shashasha mara tarbiyya kawai.”

Tuni fuskan Habiba ya gama jik’ewa da hawaye. Bata da mafita daya wuce na bin umarnin mahaifinta,da kyar ta iya tsugunnawa a gefen ungon zoma zuciyarta na suya.

“Ki yi hakuri.”

Tana faɗin haka ta mike ta fi ce daga gidan ko hanya bata iya gani sosai.

Ramatu da ke cikin ɗaki bata san lokacin da ta fashe da kuka ba

“Kin cuce ni! Kaico na da tun farko na amince miki yar Nijar,Allah ba zai bar ki ba,kin raba ni da mijina,kin raba uba da ‘ya’yan sa,kin tarwatsa farin ciki da kwanciyar hankalin dake cikin gidan aure na,kin tsangwami rayuwar marainiyar Allah,da sannu Allah zai min sakayya! Babu yafiya tsakanina da ke Ungon zoma.”

Ramatu dake kwance ta ƙarasa faɗin haka tana fashewa da kuka mai cin rai! Tsanar ungon zoma da tarin dana sanin haɗuwa da ungon zoma ya ƙara dabaibaye mata kwanya.

*****
Ki gafartamin Samy tawa! Idan ba ki yafe ma mijinki a wannan daren ba ya samu natsuwa ina zai sa ransa? Don Allah kar ki min wannan horon kin ji yar aljanna”

Ya ƙarasa maganar kamar mai shirin yin kuka. Wani sanyi ne ya mamaye zuciyar ungon zoma. Ta saki wata shu’umar murmushi tana girgiza ko ina na jikinta cikin kissa da jan hankali. Ba tare da ɓata lokaci ba ta janye kudurinta na k’in hana Malam hakkinsa.

*****

“Haba Habibaty tunda na dawo na same ki kina aikin abu ɗaya,don girman Allah ki faɗiman abinda yake damun ki,baby’n ne ki ka ji ba ya motsi? Ko haihuwar ce ta zo? Ko kuma sauran kayan da ban ƙarasa saya ba ne ki ke kuka? Faɗimin don Allah maman Baba,kar ki ɓoye min kin ji ko!”

Auwal mijin Habiba ya ƙarasa maganar sa cike da magiya. Tun da ya shigo gidan ya sameta tana kuka hankalinsa yai kololuwar tashi,ya tsani ya ga matarsa cikin kunci da bacin rai ko ba ciki,bare kuma yanzun data ke ɗauke da tsohon ciki na wata takwas! Dole ya shiga tashin hankali.

Ganin yadda hankalin Auwal ya tashi yasa ta tattaro dukkan natsuwarta.

“Ka yafemin! Yau na aikata laifin da ban taɓa aikata ma ka shi ba a tsawon zaman mu! Fita na yi ba tare da izinin ka ba! Sai ga shi fitar bata amfane ni da komai ba ban da jinina dake shirin hauhawa…”

“Ya isa haka.”

Auwal ya faɗi haka a ɗan tsawace.

“Kul na ƙara jin kin ce jinin ki na shirin hauhawa Habibty,na san Umma ki ka je dubawa ko?”

“Ehhh can na je! Shi ne wancan mai kama da aladen..”

“Wai ba na hana ki kiranta da wannan sunan ba

“To ai ballagazar mace irinta tamkar zoben zinari ne a hancin alade,ko ka manta wacece Samira ungon zoma? Ita ce fa wacce ta tarwatsa duk wani farin-ciki da wadata dake cikin gidanmu! Sanadin ta mama ta kamu da ciwon zuciyar da kullum yake farautar ranta! Ka manta ita ce fa Samira ungon zoma wanda mama ta sha ikirarin tsine mana a baya idan bamu gaisheta ba ni da yaya. Ita ce silar da Aunty…”

“Ya isa haka Habibtyna kwanatar da hankalin ki,da yardar Allah mun kusa kawo ƙarshenta. Ki yi min alƙawarin baza ki ƙara shiga harkarta ba,in ba haka ba zaki ga bacin raina.”

Auwal ya ƙarasa zancensa yana riko hannun Habiba.

“Na yi maka alƙawari Habibi,in sha Allah zan yi yadda ka ce,Allah ya cika mana burin mu.”

“Ameeen maman Baby.”

Auwal ya faɗi haka yana lakatan hancin Habiba.

“To maza taho ga wainar fulawar kofar gidan Malam Ado da ki ka ce in siyo miki,da zafinta karta huce..”

Ai tun kafin ya ƙarasa sai gata a ƙasa.

*****

“Hmmmm! Ya tafi da imani na Aliyah…”

Ɗaya daga cikin ƴan matan da ke cikin bus ɗin ta faɗi haka bayan zungurin da ƙawarta tai mata.

“Me ki ka ce?”

Sai a lokacin Airah ta gane katoɓarar da tayi,ashe zancen zucinta ya fito fili,tai koƙarin kanne hakan ta hanyar kawar da zancen.

“In tayi wari ma ji”

Aliyah ta faɗi tana ƙarasa kwankwaɗar ruwan gorar dake hannunta.

Daidai nan Bus ɗin data taso daga Ajman zuwa Abu Dhabi ta tashar bus ɗin union square ta tsaya a Al Ghubaiba Metro Station.

Al ƙaseem Adam Alƙali ne ya sauka a natse rataye da yar madaidaiciyar jakar dake sagale a bayansa.

Sanye yake cikin wani black jeans da farar r T.shirt. Idanunsa ɓoye cikin bak’in gilashin daya ƙara ƙawata fuskarsa. Kyakyawan matashi ne da kwarjininsa ke haska idanun duk wanda ya kalli kwayar idonsa.

Sannu a hankali ya fara tafiya hankalinsa kwance.

“Al ƙaseem A Alƙali right?”

Wani kakkauran balarabe ya tambaye shi haka cikin harshen larabci fuskarsa cike da murmushin ganin Jikan Alƙali.

Da sauri ya fito daga motar ya ɓude masa gidan baya. Sai da ya tabbatar ya zauna ya rufe motar ya koma mazaunin shi ya cilla hancin motar kan titi ba tare shakkar komi a ransa ba.

“Gaskiya Airah baki kyautamin ba,ni fa shisshigin ki ke haɗani dake wani lokacin. Ina ruwan ki don na je na miƙa masa tayin soyayyata? Mutuncin ki ko nawa ne ya zube? Zuciyata ta haɗu da irin namijin data dade tana mafarkin samu amma kin zama silar daya subucemin,to an yi walƙiya na ganki,watau dukan mu biyu mu rasa ko? Ko an ce miki banga lokacin da ki ke kallonsa kina murmushi ba ne..”

“Haba Airah! Mutuncin ki nake son kare miki,baki ganshi ɗan gayu ajin farko ba,daga ganinsa irin samarin nan ne masu wulakanta ƴan mata da yaudararsu…”

“Babu abinda zaki gayamin in yarda da ke,enough is enough.”

Airah ta ƙarasa zancenta cikin harshen larabci haɗe da sirkin turanci a ƙarshen maganar. Duk yadda Aliyah ta so ta fitar da kanta wajen Airah abin ya gagara. Cikin zuciyarta tace yau fa na taɓo Airah yar Daddy.

*****

Abu Dhabi babban birnin hadadiyar daular larabawa. Sannan birne na biyu mafi girma. Majiyoyi da dama sun yi kiyasin cewa Abu Dhabi shi ne birni mafi arziki a duniya,kasancewarsa cibiyar hada-hadar kudi,banki al’adau da sauran su. Shi ne masarauta mafi girma a cikin UEA.

Direban Balaraben ya faka motar a wani kayataccen lodge dake birnin MBZ. Muhammad bin Zayed City.

Tun kafin ya fito daga motar ya hango Hamdee Al Hassan tafe fuskarsa cike murmushi. Hannunsa rike da ƙaramar ɗiyarshi mai watanni takwas a duniya.

“Allah yayi yau Dr AA Alƙali ne da kansa a cikin gidana..barka da zuwa mu ƙarasa ciki”

Balaraben ya ƙarasa maganarsa cikin harshen larabci fuskarsa cike da farin cikin ganin bakuncin AA Alƙali a muhallinsa. Tare suka ƙarasa shiga cikin gidan. Falon daya fi kowani falo kyau da tsari A Hamdee Al Hassan ya sauke aminin na shi. Cikin yan mintuna kaɗan a ka jere duk wasu kayan ciye-ciye a ɗan ƙaton teburin cin abinci dake falon.

Bayan matar gidan ta fito sun gaisa da Al’ƙaseem ne. Take ƙara labarta masa yadda mijinta ke yawan ba ta labarin shi.

“Lokacin da kayi ma Ammi fiɗa bana nan,na tafi Morocco shi yasa ban san ka ba sai yau,kasan ni balarabiyar Morocco ce,daga zuwa Abu Dhabi wajen Aunty na Hamdee ya ce in ba Aƙilah ba sai rijiya”

Aƙilah ta ƙarasa maganarta cikin gurbatacciyar Hausarta data fara koya a bakin Ammi. 

Tuni maganganunta suka gundiri Alƙaseem. Fahimtar haka da Hamdee yayi yasa yai ma Aƙilah ido. Ba shiri ta mike ta fice daga falon.

“Nasan komai nufi ne na Allah! Amma kaine sila,silar daya hana wani babban bangon da rushewarsa zai zama tamkar rushewar rayuwata ne baki ɗayanta,wannan da sauran kyawawan dabi’unka AA Alƙali su suke ƙara min son ka a cikin zuciyata. Na ƙaru da abubuwa masu yawa daga cikin dabi’unka. Ka ci abinci sai in kai ka ɗakin Ammi ku gaisa,in ya so sai mu tattauna kan abinda yasa na nemi ka zo nan in da nake.”

A Hamdee ya ƙarasa maganar yana bin bayan matarsa Akilah.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

6 thoughts on “A Daren Farko | Babi Na Uku”

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×