Fu’ad ne ya yi kanta. Zama ya yi ya kamata yana jijjigawa.
“Sofi. No please. Sofi ki tashi…”
Gaba ɗaya ya wani gigice. Momma ce kawai ta ƙarasa kusa da shi. Ta janyo Sofi jikinta ta ce,
“Fa’iza miƙo min ruwa ga shi can…”
Jiki babu ƙwari Fa’iza ta miƙo mata ruwan. Zubawa ta ɗan yi a hannunta ta murza sannan ta shafa wa Sofi a fuska har sau biyu.
Fu’ad kam ya tattara gaba ɗaya hankalin shi ya mayar kanta.
Wani dogon numfashi ta ja ta buɗe idanuwanta a firgice. Janye jikinta ta yi daga na Momma ta matsa ta haɗe da bangon wurin.
Wani irin kuka ta saki. Ƙarasawa Fu’ad ya yi kusa da ita ya kai hannunshi. Yadda ta janye jikinta da hanzari kamar wadda ta ga miciji ya sa shi fasa taɓa ta.
Muryarshi can ƙasa yace,
“Hey look at me. Sofi ni ne. Muna tare fa. Komai zaiyi dai-dai.”
Kamar daga sama suka ji muryar Abba yace,
“Ko wani zai min bayanin abinda ke faruwa a wajen nan? Na kasa ganewa.”
Fu’ad ya ɗauke idanuwanshi daga kan Sofi ya sauke su kan Momma yana roƙonta da ta fahimce shi.
Sai dai ita ta ma rasa me take ji a lokacin. Mamaki? Ɓacin rai ko me? Gaba ɗaya kanta ya wani ɗaure.
Haneef da ke tsaye yace,
“Kai muke jira Fu’ad.”
Kallon Haneef ya yi tare da faɗin,
“Wace kalma ce ba ka gane ba cikin maganata ta ɗazun?”
Girgiza kai kawai Haneef ya yi. Rashin kunyar ta dawo kenan. Da magana cikin gatsali da isa.
“Wace maganar banza ce kake yi haka Fu’ad. Me ka faɗa da za mu gane?”
Abba ne ke faɗar hakan rai a ɓace.
Tausasa murya Fu’ad ya yi.
“Ya zan yi ne Abba? Ɗaukota na yi muka je aka ɗaura mana aure.”
Ƙarasawa inda yake Abba ya yi ya ɗauke shi da wani mari da ya sa har iskar ɗakin ta daina motsi na wani lokaci.
“Sake maimaitawa mu ji!”
Hannunshi riƙe da kunci yace,
“Abba aure muka yi. Wallahi ba ƙarya nake ba.”
Wani marin ya sake ɗauke shi da shi da ya sa Safiyya dake gefe ƙara riƙe jikinta tana kallon Abba.
Nadama akan kuskuren da suka yi ɗin na mata yawo a duk jikinta. Balle da ta ga Abba ya juyo da hankalinshi kanta.
Ta sake takurewa da bango kamar za ta shige ciki. A fusace Abba yace mata,
“Idan shi ba shi da hankali ina kika kai naki? Kin san darajar da Allah ya yi miki kuwa? Kin san halin da kika bar iyayenki a ciki kika bi namiji aka ɗaura muku aure? Ya Rabb. Wannan wane irin hauka ne kuka yi? Kina da tabbacin zai daraja ki? Zai zauna da ke har abada? Zai soki fiye da yadda iyayenki suke sonki?
Wane tabbaci kike dashi na ba zai gujeki ba…?”
Da sauri Fu’ad ya katse Abba da faɗin,
“Wallahi zan riƙe ta Abba. Ba zan wula…”
Momma Abba ya kalla yace,
“Idan yaron nan bai fita min daga gida ba zan ji masa ciwo. Ku fita da shi ba na son ganin shi.”
Momma ta miƙe tana girgiza kai wa Abba. Ƙarasowa ta yi inda yake a tausashe ta ce,
“Don Allah alhaji ka kwantar da hankalinka a bi a tsanake…”
Safiyya kam wani irin kuka take yi mai sauti. Abba ya kalle ta yace,
“Kukan me za ki yi? Namiji ne ga ki ga shi nan.”
Har wani ɗaci yake ji. Zuciyarshi na masa wani irin raɗaɗi. Ganin Safiyya yake kamar Fa’iza.
Ji yake kamar ya ɓatar da Fu’ad ya daina ganinsa. Yaushe Fu’ad ɗin ya yi hankali? Har da zai rabo ‘yar mutane daga gidansu ba da sanin iyayenta ba. Sam ba ya son ganin Fu’ad. Muryarshi na rawa yake kallon su Haneef.
“Ya fita bana son ganin shi.”
Fu’ad da ke zaune ya miƙe. Don bai ga amfanin zaman da yake yi ba. Akan me Abba ba zai fahimce shi ba. Laifin shi ɗaya bai gaya musu zai yi aure ba. Yau Abba ya ɗaga hannu ya mare shi har sau biyu. Ya ɗauka shi kaɗai ya isa hukuncin laifinshi a wajensu. Abba bai yarda da shi ba yana ganin zai ci amanar Sofi ne.
Kuma ma ai ba cewa ya yi ya rabata da iyayenta ba. Zai kaita su yi musu bayani ba su da wani zaɓi.
Safiyya ya kalla. Kukanta na ƙara mishi zafin da yake ji kanshi na yi. Don tun ɗazu yake jin har wani jiri-jiri ke ɗibarsa.
“Taso mu tafi.”
Yace mata. Ware idanuwa ta yi cike da hawaye. Tana roƙon Allah ya sa komai ya juye ya zama mafarki. Miƙewa ta yi da sauri. Ƙila in suka fita daga gidan nan hankalinta ya dawo jikinta.
Kowa kamar an dasa shi a wajen. Lukman mamaki ya hana shi tunanin komai.
Kallon su kawai yake yi. Haka ‘yan biyu ma. Sun fi maida hankalinsu kan Safiyya. Kayan da ke jikin ta da komai nata suna mamakin wannan abu.
“Ina kake nufin za ku tafi?”
Cewar Momma da a yanzun take jin kamar ta rufe su da duka don takaici. Ba ta san banbancin halayyar Fu’ad ɗin da sauran ‘ya’yanta na da yawa ba sai yau. Kanshi a ƙasa yace,
“Idan Abba ya huce sai mu dawo.”
Numfashi Momma ke fitarwa tana jan wani a hankali. Don gab take da losing ɗan sauran control ɗinta. Wanda take da buƙatarshi don ta kwantar wa da Abba hankali. Kallon Abban ta yi da ke tsaye dafe da goshi ta ce,
“Mu je mu yi magana don Allah…”
Bai yi mata musu ba ya wuce. Ta juya ta kalli Fu’ad.
“Ka tsaya a inda kake. Wallahi za ka ga ɓacin ran da ba ka taɓa zato ba in na fito na samu ba ka nan.”
Kai kawai ya ɗaga mata. Ta bi bayan Abba. Sai a lokacin Haneef yace,
“Why?”
Ya buɗe baki zai amsa Haneef Lukman yace,
“Haka ake zaman tare? Yanke hukunci babu shawara da kowa?”
Toshe kunnuwa Fu’ad ya yi yana wani rintse ido. Ya saki hannuwanshi yana faɗin,
“Ya isa! Ku ƙyale ni please. Akan me kowa zai dinga ɗiga min ayar tambaya ne wai?”
Kallon shi Safiyya ke yi wasu hawayen na sake wanke mata fuska. Duk da ba hayaniya yake ba yanayin yadda yake maganar ya mata wani iri. Oh Allah na take faɗi a ranta tana tambayar kanta. Me ta yi haka? Wace wauta ta bari zuciyarta ta aikata mata.
*****
“Don Allah Alhaji karkai haka. Wallahi har da rashin hankali yake damun Fu’ad.
Don Allah ka zo muje da ni da kai, da su gaba ɗaya mu samu iyayen yarinyar nan.”
A gajiye Abba yace,
“Da wane ido zan kalle su? In Fa’iza ce a matsayin waccan yarinyar bansan me zan yi ba wallahi…”
Ita kanta ta san abinda Fu’ad ya yi babba ne. Su dukkansu ya taɓa mutuncinsu. Duk da ta kula maganar ba ta ma gama zama daidai wa Abba ba.
Tunda bai fara hango maganganun mutane in maganar ta fita ba. A tausashe ta ce,
“Hakan na lura, shi ya sa nace muje. Na san duk inda hankalinsu ya yi dubu a tashe yake wallahi…”
Jinjina kai Abba ya yi. Saboda yarinyar kawai.
“Ɗauko mayafinki mu tafi. Amma Fu’ad ya bar falon nan kafin in fita.”
Da hanzari Momma ta wuce ta ɗauko hijabinta. Ta fita falo wajen su Fu’ad.
“Haneef, Lukman ku tafi a mota ɗaya kai da su Fu’ad ɗin. Gamu nan za mu biyo bayanku yanzu.”
Wani ɗan sanyi Fu’ad ya ji. Yana god wa Allah. Gara ma suje a yi komai yau a ƙare. Tunda dai Sofi ta zama tashi ba shi da matsala da ko me zai biyo baya.
*****
Motar shiru banda kuka da ajiyar zuciyar da Safiyya ke faman yi. Ta wani haɗe jikinta da kujerar. Ta sa kanta cikin hijab tana kuka.
Kallonta kawai yake yi. Zai barta ta yi kukanta iya yau. Zai ba ta iya yau kawai ta yi abinda take so.
Duk yadda kukan yake damunshi. Daga yau ba za ta yi kukan nan ita kaɗai ba. Ba ma ya jin zai barta ta yi komai ita kaɗai.
Wannan shine tabbacin da ya dinga ba wa kanshi da mafarkai da yawa. A hanyarsu ta zuwa Bichi yake tsara yadda za su yi rayuwarsu shi da Sofi. Daga ita sai shi. Zai nuna mata yadda zai yi komai Akan sonta.
*****
Inna ce tsaye tana kallon ƙofa tana sharar ƙwalla. So take ta ga ta ina Baba zai ɓullo.
Ya ma za a ce an nemi Safiyya an rasa? Ina za ta je haka? Kuma wani abin takaicin shi ne ko wanda ya ga giccinta babu cikin gidan. Maganganun Safiyya ke ta dawo ma Inna. Addu’a ta shiga yi kar abinda take zato ya zama gaskiya. Ko wani ya yi wa Safiyya asiri. Don tun yaushe take kula kamar ba ta cikin hayyacinta.
Yin komai take kamar wadda aka saka wa batiri. Shi ya sa ta matsa da tambayarta ko lafiya sai ta ce bakomai. Duk gidan anyi jugum-jugum ana jimamin wannan ikon Allah. Tun suna fama da Inna ta zauna har suka haƙura suka ƙyale ta.
Ita ina ta ga zama ba ta san halin da ‘yarta take ciki ba. Ganin shigowar Baba ya sa Inna tarbarsa da hanzari tana cewa,
“An ganta?”
Girgiza mata kai ya yi. Ta rushe da wani kuka tana kiran Allah da ya kawo musu ɗauki.
Shi kanshi Baba kallo ɗaya za kai masa ka gane tashin hankalin da yake ciki. Ya san yanzu kam ya kamata ya je ya sanar gidansu Ado. Kasa ce wa Inna komai ya yi. Ya sa kai ya fice daga gidan.
Daidai ƙofar gidansu Safiyya suka yi parking. Gaba ɗayansu suka fito. Safiyya ta ji wani sabon tashin hankali. Jikinta ya ɗauki ɓari. Ba ta san da wace ƙafa ma za ta shiga gida ba. Fu’ad hankalinsa na kanta. Ganin yada ta sake rikicewa ta na neman shiɗewa ya sa shi kallonta cikin idanuwa.
“Breath in…”
Yace mata ganin kamar ta manta yanda ake jan iska. Kula ya yi ba ma ta gane me yake nufi ba.
“Sofi. Kin ga ki kwantar da hankalinki. Ki yi numfashi. Ki ja iska…”
Can sama take jin muryar Fu’ad. Sai da ya yi mata magana sannan ta tuna numfashinta ne take riƙe dashi. Shi ya sa take jin duniyar ta yi tsaye. Haka ya dinga mata sai da ya ga numfashinta ya daidaita tukunna. Hankalinshi ya maida kan Abba da ke tsaye shi da Momma a ƙofar gidan su Safiyya. Suna yanke shawarar Momma ta shiga.
*****
Yana fitowa ya ga mutane tsaye a ƙofar gidanshi da motoci guda biyu. Gabanshi ya sake faɗuwa.
A mutunce suka gaisa da Abba. Ya ɗora da faɗin,
“Mai gidan nan muke nema.”
A daddage Baba yace,
“Ni ne, Allah dai ya sa lafiya.”
Don sam bai ma kula da Safiyya da ke can gefe tana ɓoyewa bayan Fu’ad da ta hango shi ba.
“Alhamdulillah dai. Magana za mu yi.”
Sauke numfashi Baba ya yi.
“To amma dai ina sauri ne. Saboda hankalina ba a kwance yake ba…”
Da hanzari Abba yace,
“Na san yana da alaƙa ne da ‘yar wajenka ko?”
Cike da mamaki Baba ke kallonshi. Abba ya dora da faɗin,
“Maganar da ta kawo mu kenan.”
Juyawa ya yi. Ya yi wa Haneef nuni da su ƙaraso. Shi kam Baba ya tsaya ne kawai yana kallon ikon Allah. Su Haneef da ke tahowa yake kallo. Safiyya na bayansu don haka bai ma hangota ba. Su ukun dai ya gane su. Musamman Fu’ad da ya san fuskarshi ba za ta mantu a wajenshi ba.
Yaron nan ne da ya mare shi. Wanda suka yi rikici da Iro. Yaron nan marar tarbiya da akanshi ya soma sanin menene tsanar mutum. Haneef kuwa sai yanzun ya tuna shi. Tun ranar da suka zo neman auren Safiyya yake masa kallon sani. Mamaki ya sake cika Baba. Ko wani sabon neman auren Safiyyar suka zo? Yake tambayar kanshi.
Mamakin shi ya ƙaru da suka ƙaraso ya ga Safiyya a bayansu kamar wadda aka koro.
Gaba ɗaya ta wani firgice. Wani abu ya ji na neman tsayawa cikin kanshi. Saboda baya so ya haɗa abinda yake son ya yi tunani.
Ba zai taɓa ma yiwuwa ba.
Momma ya kalla.
“Ku shiga ciki da ita ko.”
Hannun Safiyya Momma ta kamo, ta ja ta suka rakuɓe Baba da ke binsu da ido suka wuce ciki.
Da sallama Momma ta shiga gidan da yake cike da mutane ga mamakinta. Da gudu Inna ta ƙaraso ta rungume Safiyya tana sakin wani irin kuka tare da yi wa Allah godiya. ‘Yan gidan ma hamdala kowa yake yi. Wasu kuma na tofa albarkacin bakinsu.
Sakin Safiyya Inna ta ɗan yi tana kallonta don ta tabbatar da ita ɗin ce. Ita ma kuka take yi sosai.
Innar ma haka, tana faɗin,
“Oh ni, Allah mun gode maka!”
Hankalinta ta maida kan Momma da ke tsaye kawai. Tana tunanin ta inda za ta fara gaya wa Inna maganar da ta kawo su.
*****
A nutse Abba ke wa Baba bayanin abinda ya kawo su. Da kuma iya abinda ya sani. Ai yana ƙarasa faɗin cewar an ɗaura musu aure da Fu’ad kamar ya ma Baba wata allura ne. Da hanzarin gaske ya nufi cikin gida…!
Inna ta kalli Momma da ke tsaye. Ta buɗe ba ki za ta yi magana Baba ya shigo a fusace.
Safiyya da ke riƙe hannun Inna ya kama ya wurgar gefe ɗaya ta yi wani irin ihu. Gaba ɗaya gidan mamaki suke yi kawai. Safiyya ya kalla yana faɗin,
“Wallahi na yafe ki Safiyya. Ko ke kaɗai nake da ita yau na haƙura da ke ballantana ina da wasu..!”
Da rarrafe Safiyya ta taso ta riƙe ƙafafun Baba tana wani irin kuka mai taɓa zuciya.
“Baba…!”
Tureta ya yi. Inna da ke gefe ta kamata tana kallon Baba. Riƙe ta Safiyya ta yi tana wani irin kuka kamar ranta zai fita.
“Ki sake ta kawai. Kin san me yarinyar nan ta yi mana kuwa?
Kin san guduwa ta yi da wani suka ɗaura aure? Safiyya wai. Safiyya fa!”
Baba ke faɗi yana jin kamar ya haɗiye zuciya ya mutu ya huta da fuskantar wannan abin kunyar.
Ture Safiyya Inna ta yi daga jikinta tana jero innalillahi… Tare da wasu cikin ‘yan gidan.
Sulalewa Inna ta yi ta faɗi. Da sauri Safiyya da wasu suka yi kanta. Safiyya ta riƙe ta tana ihun,
“Inna….Inna ki tashi. Don Allah ku yafe min …”
Janye Safiyya Baba ya yi daga kan Inna. Tana ƙoƙarin ƙwacewa tare da ihun kuka.
Ya jefar da ita gefe.
“Ai baki damu da halin da za ki saka mu ba kika biye son zuciyarki. Ki ƙyale ta. Ki ƙyale mu ki bi wanda kika zaɓa a kanmu.”
Tare da Momma aka yayyafa wa Inna ruwa ta farfaɗo. Tana kallon Safiyya ta rushe da kuka.
“Safiyya wane abin kunya kika ja mana? Gobe ɗaurin aurenki. Ina ma kika san yaron da kika bi?
Waye shi?”
Ta kasa magana sai kuka da take yi. Baba ne ya amsa ta da faɗin,
“Yaron da ya ɗaga hannu ya mare ni ne. Yaron da ya sa aka kulle mu gaba ɗayanmu. Shi ne ta zaɓa a kanmu.”
Girgiza kai Inna take yi tana kallonsu. Tana so su ƙaryata maganar da Baba ya faɗi.
Ture mutanen da ke kusa da ita ta yi ta ƙarasa inda Safiyya take ta kamata ta jijjiga.
“Ki ce min hakan bai faru ba Safiyya. Ki ce min baki gudu kin auri wani ba. Don Allah ki ce min baki auri yaron da ya wulaƙanta mu ba.”
Kuka kawai Safiyya ke yi. Sai da Inna ta sake girgiza ta sannan da ƙyar ta ce,
“Na yi Inna…Wallahi na yi babban kuskuren rayuwata. Akan so…”
Ba ta rufe baki ba Inna ta ture ta. Tsaye ta miƙe tana zubda wasu hawayen takaici.
“Ki fitar mana daga gida. Wallahi ni ba zan miki baki ba. Zan barki da ɓacin ran da kika saka mu kawai…”
Miƙewa ta yi ta nufi Inna. Da sauri ta ja baya.
“Zan miki baki in kika ƙaraso inda nake wallahi. Ki je gurin wanda ki ka zaɓa. Na haƙura da ke. Malam ka fitar min da ita…”
Momma ta ƙarasa wajen Inna ta kamata tana faɗin,
“Don Allah da Annabinsa ki tsaya a bi abin nan a hankali. Na san ta yi kuskure. Karku ɗora laifin nan akanta kawai. Har da ɗanmu.
Mu zauna a gyara kuskuren nan.”
Girgiza kai Baba yake yi.
“Ki je da ita. Zuwan da kuka yi ya tabbatar min da ɗanku bai biyo halayyarku ba. Kamar yadda tamu ta sa ƙafa ta yi fatali da duk wani mutuncinmu. Da duk wata ƙauna da muka taɓa nuna mata.”
Safiyya ya kamo da ke tsaye ya miƙa wa Momma yana faɗin,
“Na bar muku ita kyauta. Wallahi na yafe muku ita. Kamar yadda mahaifiyarta ta faɗa. Ba za mu yi mata baki ba. Sai dai zan tsine mata duk ranar da ta zo min gida.”
Kamo Safiyya Momma ta yi tana jin wasu hawayen tausayi wa yarinyar na zubo mata.
Wannan wane irin bala’i ne Fu’ad ya ja wa ‘yar mutane. Ƙanƙame Momma Safiyya ta yi tana wani irin kuka numfashinta har sama-sama yake yi.
Haƙuri Momma ke ƙoƙarin ba su amma kamar ma tunzura su take ƙara yi.
Dole haka ta ja Safiyya tana tirjewa suka fita. Don ta ga alamar sam ba za su ji wata maganar fahimta ba.
Wani irin kallo Abba ke wa Fu’ad da ke cike da fassarori kala-kala.
Balle da ya ga Momma ta fito riƙe da Safiyya da ke wani irin kuka. Ita ma hawaye take yi, ta kalli Abba ta ce,
“Gobe ɗaurin aurenta…Fu’ad…”
Kasa ƙarasawa ta yi saboda kukan da ya ci ƙarfinta. Wannan wane irin abu ne. Girgiza kai Abba yake yi kawai yana faɗin,
“Innalillahi wa ina ilaihir raji’un!”
Me Fu’ad ya yi haka. Me waɗannan yaran suka yi haka. Kallon shi ya mayar kan Fu’ad da ke tsaye can gefe.
Sannan ya kalli Momma.
“Ki saketa ta tafi wajen shi. Bana son ganin shi a gidana. Kar su zo min gidana..”
Fuskarta ta goge tana sake riƙe Safiyya.
“Ina kake so suje? Don Allah ka bari mu je gida. Karka yanke hukunci cikin fushi.”
Cikin idanuwa ya kalleta sannan yace,
“In har na ga Fu’ad a cikin gidan nan zan iya yanke kowane hukunci cikin ɓacin rai.
Su tafi gidana na Hotoro…”
Ba ta son yi masa musu. Da kanta ta kama safiyya ta je ta buɗe mota ta sakata. Ta dawo ta kalli Haneef.
“Ka sauke su gidan Abbanku na Hotoro. Idan na lallaɓe shi…”
Fu’ad da ke gefe ya katse ta da faɗin,
“Ki bar shi kawai Momma. Ina da wajen da za mu zauna.”
Cike da wani takaici ta kalli Fu’ad.
“Ɓacin ran da muke ciki bai isheka ba ko?”
Wani ɗaci yake ji ga kanshi na ciwo.
“Shi ya sa na ce ina da wajen da za mu zauna. Abba ba ya son ganina.
Saboda me zan zauna masa a gida?”
Wucewa kawai Momma ta yi ba ta ce komai ba. Ba ta son ya ƙara ɓata mata rai. Addu’ar shiriya take wa Fu’ad ɗin. Haneef ma wucewa ya yi don ya tabbata in ya tsaya za su kwashi ‘yan kallo ne da Fu’ad ɗin.
Lukman ya kalle shi.
“Really?”
Lumshe idanuwanshi ya yi ya buɗe su yana saukewa kan Lukman.
“Banda kai ma please. Abin zai min yawa.”
“Banda kana da concussion babu abinda zai hanani naushinka.”
Wani gajeren murmushi kawai ya yi da ya tsaya iya fuskarshi ya wuce ya buɗe motar ya zauna kusa da Safiyya da ke kwance luf jikin kujera. Yasan Lukman sarai. Ya yi fushi da shi sosai, amma za su shirya. Kamar yadda ya san za su shirya da su Abba. Komai na buƙatar lokaci.
*****
Ƙofar gidan Haneef ya yi parking. Budewa ya yi ya fita yace wa Safiyya ta fito. Babu musu ta fito saboda jinta take wani sama-sama. Ga wani zazzaɓi da ya saukar mata. Ko ya ta rufe idanuwanta sai ta ga yadda Baba ya ɓanɓareta daga jikinshi ya cillar. Yadda Inna ta tureta take faɗin ba ta son sake ganinta
Wani irin raɗaɗi take ji. Ga ƙirjinta na mugun zafi.
Zagayawa ya yi yace wa Haneef,
“Motata please. Credit cards ɗina and….”
Wani mugun kallo Haneef ya yi masa. Bai ce komai ba ya fizgi motar ya yi reverse. Sauke numfashi ya yi.
Zai kira Lukman. Ya san ba zai ƙi kawo masa ba. Beside ba zama zai yi a gidan nan ba. Ba ya son komai na Abba sai ya huce.
Hannun Safiyya ya kama. Yana jin yadda take kiciniyar ƙwacewa ya ja ya tsaya. Cikin idanuwanta da har sun ƙanƙnace saboda kuka ya kalla yace,
“Ki kalle ni sofi. Zan daidaita komai. Ban miki alƙawari zuwa yaushe ba. Amma na miki alƙawari komai zai wuce.
Ni da ke ne cikin wannan abin. Akan son da muke wa juna ne komai yake faruwa.
Ke kaɗai nake da ita a yanzu. Ni kaɗai kike da shi. In baki taya ni ba ta yaya kike so mu gyara komai?”
Yanayin sanyin muryarshi ta ji yana mata wani tasiri na daban. Ta gasgata kalamansa. Ta karɓi alƙawarinsa. Hawaye suka zubo mata. Kai ta ɗaga masa. Ya sa hannu ya goge mata hawayen da ke fuskarta. Wani sanyi ya ji ya ratsa shi na daban. Kama hannunta ya yi zuwa cikin gidan. Wajen mai kula da gidan ya karɓi keys. Ba wani girma gare shi ba. 3 bedroom flat ne. Buɗewa ya yi. Ya tsaya a bakin ƙofar yana addu’a.
Kallo Safiyya ta bi shi da shi. Sai da ya gama sannan ya ja hannunta suka shiga ciki. A falo ya zaunar da ita da kanshi ya shiga kitchen ya ɗauko kofi. Fridge ɗin da ke kitchen ɗin ya buɗe. Bakomai a ciki. Numfashi ya sauke yana faɗin,
“Great…!”
Fanfon kitchen ɗin ya buɗe ya ɗibo ruwa ya kawo mata. Ta girgiza masa kai. Ba ta son shan komai. Lukman ya kira. Wajen sau biyar ya ƙi ɗauka. Text ya yi masa ya roƙe shi da ya kawo masa motarshi da wasu abubuwa.
Text ɗin na shiga da ‘yan mintina ya sake kiran Lukman. Picking ya yi da faɗin,
“Karka dame ni. Nake jin abinda ka ga dama kake yi? Tam nima sai na ga dama.”
Sauke numfashi ya yi.
“Lukman please. Gidan ba komai fa. Ba don ni ba. Ko don Sofi…”
“Na ji…”
Ya amsa sannan ya katse wayar. Murmushi ya yi ya maida kallonsa kan Sofi da ta ja jiki ta kwanta akan kujerar. Zazzaɓi take ji sosai a jikinta. Kula ya yi jikinta kamar yana rawa. Da sauri ya ƙarasa inda take.
“Sofi… Mene ne?”
Da ƙyar ta iya ce masa,
“Kaina ciwo…”
Hannunshi ya sa a fuskarta ya ji wani zafi. Ya ɗauka ɗazun da ya riƙe hannunta zafin da ya ji wani abun ne daban.
“Damn….”