Bai bi ta kan kowa ba ya shige bangaren su na ƴan mazan gidan, kai tsaye toilet ya shige, ruwa me dumi ya haɗa yai wanka ya wanke jikin sa, yakai sau goma still bedana jin wani iri ajinkinsa ba, haƙuri yai ya ɗaura towel ya hau shaving din gemun da ya yi wanni iri a fuskar sa, ya rarrage sumar kansa sannan ya sake wanka, aƙalla yadanji daɗi.
Ya fito yana saka kaya ne Hajiya ta shigo riƙe da kofi, Ummi na biye da ita taƙe da flask gabaki ɗaya sunyi mamakin Mahfuz. . .