Skip to content
Part 18 of 18 in the Series Abbakar by Fadimafayau

 

Gidan da Ummu take.

Inna, ce ta shigo. Ummu na gyara musu kaya, ta ja ta zauna a gefen katifar su. Ummu ta ce, with a calm but firm tone,”Ummul Khairi, zuwa nai mu yi magana.” Ta fahimta da ke, jin haka, yasa Ummu ta jiye kayan ta zo ta zauna dab da Inna.

Inna ta dafa, ta ummu ada na yadda da abinda diyata. Ummi ta fada, leaning forward with a serious expression, “Ke ɗin uwaddakinta ce, wani abu mai mahimmancin ya baro daku da gida. Sai dai ina ganin kudin da kike kashewa, hankali kwance. Yasa na fara tunani wani abu daban. Ummu, dan Allah ki faɗan gaskiya. Ke wace Me ne alaqarki da yarinyata? Ina ji ajikina kamar baki da gaskiya.”

Ummu ta sa kuka, wiping tears from her eyes,”Wallahi, Inna, abinda kike zato ba haka bane. Gaskiya muka fada miki. Ni ban yarda ba dan zuciya na fada. Kodai satowa kikai ko kuma ke din karuwa ce ganinki danai da yaro karami ko yaye bai isa ba yasa na kuma gazgazata zato na” Kuka ta kuma fashewa dashi, raising her voice slightly, tace, “Inna, zan fada miki. Ko ni wace, wallahi, ni ba barauniya bace, ba kuma karuwa bace. kudi na wane na gado , ban taba dauka ba sai yanzu.”

Tashare hawaye kafin ta maida hankalinta sosai ga Inna, tace, with a deep sigh, “Kamar yadda na fada miki, ban kuma miki karya ba. Sunana Ummul Khairi, Yasir Mahmud. Tarihina ya fara kamar haka.”

Mahaifina haifaffen garin Kano ne. Su tara mahaifinsu ya haifa. Mahaifina shine na taran, wato autansu Bashir shine babba. Sai Muktar, Muhammad, ukunsu Dahiru na hudu, Salisu da Salman sune na biyar, wato yan biyu ne. Sai Kamal na bakwai, Aliyu na takwas.

Lokacin da aka haifi Aliyu, sai da ya yi shekara goma sha hudu aka haifi mahaifina. Lokacin ma mahaifinsu ya tsufa, hakan yasa duk suka dauki san duniya suka dorawa Yasir yayyensa gabaki daya. Maza ne suma, duk soyayyarsu sun dorata akan Yasir ne. Ko wanne ya samu abu, to Yasir zai kawowa.

Lokacin da aka yaye Yasir ne, mahaifinsu ya dauki gidan da suke ciki ya bai wa Yasir. Dan yanzu baya wani aiki. Yayyensa basu ji komi ba, dan samadin kowanne da irin abinda aka bashi azahiri na Yasir dinne. Ya samu abu mafi qanqanta.

Shekarun Yasir uku, Allah ya yi ma mahaifinsu rasu. Babban yayansa wanda ya dade da kammala Masters dinsa, yana kasuwanci, shi ya ci gaba da kula da kannensa da mahaifiyarsu azahiri. Yasir shi, Yaya Bashir yake dauka matsayin mahaifinsa. Dan kuwa komi shi yake masa, duda kuwa sauran yayyunsa ma ba abarsu abaya ba azahiri. Yasir dan gata ne, nagaba da baya danshi, besan wani abu waishi maraicin uba ba.

Yasir ya na JS 1, yayansa ya yi aure. Aikuwa mahaifiyarsu ta tubure. Ita danta bazai barta ba. Dole agidansu ya yanki guri ya yi bangarensa, duda cewar sunsan da gida bana gado bane. Gidan Yasir ne.

Yasir yana SS 2, sannan matar yayansa ta haihu. Dan qin yadda tai ta haihu, lokacin farkon auren dan tace karatu zatai ta haifi danta namiji. Ya ci sunan kakansa, wato Mahmud, suke kiransa da Mu’allim.

Shekarunsa biyu, takuma haifar danta namiji. Ya ci sunansa Yasir. Alokacin qannen mijin hudu, duk sun yi aure suma, agidan suke zaune. Wasu cikinsu ciki ke garesu daya, harda danta mai suna Abul Fathi.

Duda cewar yayun Yasir sun yi yaransu, saidai fa har yanzu suna ji da qanin nasu. Komi ya ke so ake masa, har sun fi kulawa dashi fiye ma da iyalansu. Hakan ya sa duk matansu jin haushin Yasir din. Karma matar Yah Bashir, tsanar duniya ta dauka ta dora kan Yasir, dan yadda take ganin wani abun intace amata. Yasir ya ce, Ina buqatar wani abin shi mijinta Kema ya ce, Ita ta yi haquri sai ya samu kudi.” Abinda bata sani ba, shi Yasir da kudin gadonsa ake masa komi, tunda sun yanke sai ya kammala degree zasu bashi gadonsa.

Shekarun Yasir goma sha biyar, ya yi candy, yana murna zai tafi jami’a. Dan ya ci JAMB, saidai akace sai ya je 16 years. Aikuwa ya tashi hankalinsa danshi, bai so ace yau wani cikin dan ajinsu ya riga shi tafiya jami’a.

Yadda ya bi ya rame ya tsangwami kansa, yasa dole badan yayyensa sun so ba suka aikashi India. Dan yin karatun da ya fi so, wato karatun hada magunguna. Aiko ya yi murna sosai, saida zai tafi ne ma. Ya yi kukan rabuwa da hajiyarsu da yayyensa. Dan yanzu yasan duk yayyensa ne, sai dai har yanzu bai daina kiran Yaya Bashir da Dady ba. Hakan nama yayan nasa dadi.

Shekarar da ya tafi ne, matar Bashir ta kuma haihuwar namiji. Ya ci sunansa Mansur. Ashekarar yan biyu da sauran yayyen Yasir suka yi aure. Yasir bai samu zuwa ba, saidai an tura masa da hotuna. Ya yi murna sosai, ya kuma so ya zo din.

Shekarun ashirin, cif ya kammala degree dinsa. Baibi shawarar kowa ba, ya cike komi nayin Masters dinsa. Ya bai samu wata matsala ba, haka ya cigaba da karatunsa. Dan bashi da wata matsala, yakan zo hutu gida a hankula. Ya fiskanci tsanar da matan yayyensa suka masa, saidai ko ajikinsa.

Koda ya kammala Masters dinsa, ya fara aiki da jami’ar da ya kammala. Dan result ya yi kyau sosai, a nan yake lecturing. Ya kuma aiki a wani babban kamfani na sarrafa magunguna.

Lokacin da ya cika shekaru ashirin da biyar, mamaki yayyensa suka bashi har India suka zo dan tayashi murna. Ya ji dadi sosai, harda Hajiyarsa.

Dakyar ta yadda ta koma Nigeria da cewa ta yi kodai ta zauna gurinsu ko kuma ta yi bita su tafi. Dan ita ta gaji so take yi aure. Dakyar ya lallasheta kan zai yi aure bada jimawa ba. Tai tamasa addu’a kawai.

Tun bayan haihuwar Mansur da Rabi, matar ta yi yau shekaru bakwai bata kuma haihuwa ba. Yaranta hudu, hakan ya sa ta tashi hankalinta dan matar Mahmood ma yaranta shida, kuma ta riga ta shiga gidan aure.

Cikin ikon Allah, ta sami wani cikin murna kam ba kama hannun yaro. Cikin ikon Allah, ta haifi danta namiji. Shima taso mace ce, saidai yadda mahaifinsa, wato mijinta, ya yi murna, yasa itama ta yi sosai cewa ya yi ta zabi sunan da takeso. Asama yaron, ta ce, “Mahfuz.” San duniya ta dauka ta dorawa Mahfuz. Ko yayyesa ne suka masa abu, to yanzu zasuga bacun ranta.

Lokacin da Yasir ya kammala PhD dinsa, ya cika shekaru talatin. Cif lokacin ma harda mahaifiyarsu aka zo dan tayashi murnar karbar doctorate degree dinsa a pharmacist. Bayan an gama bikin karbar, Hajiyarsu tasa kuka, ita dole ya yi aure in ba so yake ta mutu bata ga jininsa ba.

Ya tabbatar mata kwanan nan zai yi aure. Tai murna sosai.

Wani aiki ne ya kai su Malaysia, wata university da ake kira University of Malay. Acan ne cikin daliban da yake koyarwa, ya hadu da wata yarinya yar Jordan ce. Sun shaqu sosai, har soyayya ta shiga tsakaninsu.

Ba su wani dade tare ba, maganar aure ta shiga tsakani. Dakyar iyayanta suka bashi shima darajar yayansa Bashir. Danshi ya yi ta kai kawo harsika yadda dan qanin nasa cewa ya yi, ba zai yi aure ba in ba ita ba.

An yi biki komi anan Malaysia. Suka ci gaba da zama. Dan ita Fatiha tana shekarar karshe ne, shi kuma zai yi shekara biyu ne kafin ya koma India.

Ta kammala karatunta tas anan, ta fara aikinta temporary kafin ya kammala abinda ya kawoshi. Suka koma India.

Shekararsu biyar da aure, ba su samu haihuwa ba. Abinka da yan boko kwata kwata, ba su damu ba.

Sai da Hajiya ta tada hankali sosai, sannan suma suka fara damuwa. Suna shekara ta bakwai, sika samu haihuwa. Aiko ramyar da Fatiha ta ce masa tana da ciki. Murna kamar me harda dagata yana rawa. Ya godewa Allah sosai. Aranar yasanar da Hajiya itama ta yi murna sosai.

Wata tara cif ta haife diyarta mace mai kama da ita, saidai ba ta yi farin larabawanta ba, sai ta yi baqin yan Nigeria kamar babanta kenan.

A Nigeria suka sauka bayan kwana uku da haihuwar dakyar Fatiha. Ta yadda akan suna gama kwanakinsu zasu tafi Jordan gidansu. Yasir ya yadda da hakan.

Ranar suna yarinya ta ci sunanta Ummul Khair. Sunan Hajiya ne ta ci, hakan yasa suke kiranta da Ummu. Mace ta farko a cikin jikokin gidan. Aikuwa yayyen Yasir sun nuna farin cikinsu sosai. Ji suke kamar diyarsu ce. Yayin da Hajiya ta fi kowa farinci, dan tanasan mace sosai, saidai kawai Allah ne ba bata ba.

Watansu guda a Nigeria, suka Jordan.

Watana goma sha daya a duniya, mahaifina ya hau cuta, wato ciwon qoda ne mai tsanani. Ya kamashi ciwo ne sosai, bana wasa ba. Hakan yasa dole suka dawo Nigeria, ba wai dan babu magani a Indian ba, sedai kawai dan Hajiya ta takura.

Ganin ciwon gaskene, yasa Hajiya ta yadda suka dawo India harda ita dan jinyarsu.

Watansu uku da dawowa, an masa dashen qoda. Ya dan koma normal har ya zo gida hutu. Sai daime satin da zasu koma ciwo ya dawo sabo baiko kwana ba. Allah ya masa rasuwa.

Kowa mutuwar ta girgizashi, dan ba wanda ya bashi mutuwa. Ganin cewar Hajiyarsu nada rai, ga kuma yayyensa duk araye, saidai kash ita mutuwa ba ruwanta da shekaru girma ko yarinta.

Lokacin da Ummana ta gama takaba, taso tafiya dani. Sai dai me Hajiya ta tubure ita abar mata. Ni ta dauki zugar mamar Mahfuz.

Haka mamata ta cireni a Nono, ban isa yaye ba. Ina da wata goma sha hudu tabarni, tana kuka ni in ba a hoto ba, ban san Ummana ba, balle Abbana.

Ummu ta kuma share hawaye, gami da goge majinar da ta tawo mata ta dora.

Lokacin Hajiya nada rai, banyi wani maraici ba. Abu daya ne damuwata shine Mahfuz. Dan ko a hanya muka hadu, sai ya maujeni. Wataran ya kaimin duka, gami da zagina, dan haushina yakeji sosai kan kakarmu tafi sona. Inka dauke matsalar Mahfuz, banda ta komi dan komi, tanai min lokacin da babana ya cika shekaru biyar da rasuwa. Ina shekara shida da watanni, Hajiya ba lafiya ta tara yaranta. Ta ce kamar yadda kuka sani, gida na Yasir ne, sedai ya rasu yana diya mace daya tal.

Kenan, kuna da gado a dukiyarsa. Ni nawa gadon na gidannan na yafe harga. Allah nabarma Ummu, diyarsa budar bakin Yaya Bashir. Shima ya ce ya barmin duk sun barmin gadonsu na gidan.

Sauran dukiyar mahaifina aka raba, aka bai wa Baba Bashir. Nawa na Ummana aka tura mata tumunin takabarta can Jordan. Dakyar ta amsa.

Ina JSS one, Hajiya ta rasu. Alokacin na fara wayo, na san mutuwa. Gashi duniya da ita na saba. Aikuwa na ji mutuwar sosai, nai kuka har na haqura.

Tun mutuwar Hajiya, ba irin wahalar da bn sha agurin mutanen gidan nan babu. Me tausayina ko kadan. Musanman Mahfuz, dan ko kadan baida mutunci. Gashi hajiyarsa ta yi ta bin bayansa. In ya shigo na sake muka haɗu ina cikin masifa wannan yasa duk wata hanya ko abu da zai haɗa mu nake guje masa.

Lokacin da Baba Bashir ya rasu, nan komi ya kuma cakudemin, dan banda sakat inba dare ne ya yi. Ko sauran yayun babana sun dawo. Duda akwai yanxu sakonnina mata jikokin gidan da yawa. Anman duk wata wahala nice.

Mahfux bashi da kirki, baya hulda da kowa. Wanda yake na gari, inka dauke abokinsa daya da yake so sosai tun suna yara, wato Abubakar wanda ban taɓa gani ba sabida ƙoƙarin gujewa wulaƙancin Mahfuz gare ni. Hausawa nacewa se hali yazo daya ake abota, sai dai shi nasu ba haka bane. Dan kuwa Abubakar ba halinsu daya ba, danshi miskiline vaikuma shiga shirgin iskancin Mahfuz kawai. Soyayyarsu da abotarsu daga Allah take.

Lokacin suna yara, kullin se Abubakar ya daki Mahfuz. Hajiyarsu Mahfouz intai ma Abubakar fada Mahfouz Yasa kuka ya ce, with a smirk, “Ai abokinsa ne.” Duk yadda taso rabasu, Mahfuz ya qi duda shi Abubakar ke jibga. Se Mahfux ya tafi wani gurin hajiyar mahfuz. Ta kama kunnen Abubakar, ta matse. Ta ce, with a stern voice, “Kar ya kuma dukar mata da.” Sedai abinda bata sani ba, shi Mahfux dinne ke fara tsokanar Abubakar Dun saidai shi ba qarfi gareshi ba, shi kuma Abubakar zuciya gareshi. In ya bashi haushi kawai, sai ya rufeshi da duka.

Sannu a hankali, Abubakar ya dena dukan Mahfuz. Koda ya tsokaneshi, saidai kawai ya yi kamar bai ganshi ba. Shaquwarsu ta qaru sosai ajinsu daya. Lokacin suna SS2, Ina primary 4. Abubakar ya zo yasanar da hajiya kan ta tsawatarma Mahfuz. Dan ya fara shaye shaye, ta ce, with a raised eyebrow, “Ina qaryane tama haishi da fada.”

Hajiyarsu ya fadawa dan haka, ta je ta samu hajiyar Mahfuz. Aikuwa ta rufe ido, ta ci mutuncin hajiyar Abubakar. Wai sunma danta sharri. Dan ita da kowa ma ta bata kan Mahfux. Dan ba wanda ya isa ya fadi lefin Mahfuz agabanta. Yanxu ta ce, with a firm tone, “Yama danta sharri.”

Hajiyar Abubakar ce ta kira Mahfux, ta mai nasiha. Ya ji sosai, hakan yasa ya dena shaye shayensa a gaban Abubakar. Yawanci ma sai dare.

Lokacin da suka yi candy, sun fara karatun likitanci a ABU. Sai aka tafi yajin aiki. Abubakar ya ce, “Shi waje zai tafi.” can ya tafi Japan, ya fara karatun qere qere, wato engineering. Yayin da Mahfuz ya ce, “Ina ba inda zai je.” Danshi mutunne da kullin yana manne da Hajiyarsu. Shiya shaquwarsu da ita, kullin qaruwa take.

Lokacin da aka koma sch qin komawa, ya yi dan damashi. Dan Abubakar yake science, anman art yake so. Hajiya tai tai ya cigaba da MBBS dinsa. Ya ce, “Ya qi dole tanaji tana kallo.” Ya kuma yin JAMB ya dauko necon sa. Dan daman ita ya dade da biyan kudi aka masa. Ita a art bai samu matsala ba. Suka bashi abinda ya nema, watk mass communication. Ya fara karatunsa anan Bayero. Saidai rashin mutuncinsa kullin se abinda ya qaru.

Bayan shekaru biyar, zaune nake ina maida numfashi. Dan kam na gaji da yawa, ba kowa a gida. Duk sun tafi BUK wajen taya Mahfuz kammala degree dinsa. Ayau ni kadai ce a gidan. Ya shigo, na kalleshi da mamaki.

“Yah Mahfuz, kai da aka tafi taya murna. Kuma seka riga kowa dawowa ya galla min harara ke dan ubanki. Ni sa’anki ne, zaki dinga min wannan tambayoyin eyye?” Dan shima ya ya tsaneni sosai, dan yadda mahaifinsu kan ya rasu yake nunamin soyayya.

Na murguda baki, badai ubana ba. Sedai nawa nace ai babanka babana ne. Anman danace sedai naka. “What to me zakiyi?” Inna kuma zaginki ka kuma dinmana ka gani. Lallai yarinyar han ko yau zanci kutmar……. Saukar marin da ya ji afuskarsa ya shi dafe gurin tabdi. Kin jawoma kanki bala’i. Ni kikia mara anmare kan danmene zaka zagar min uba bacun ya dade da mutuwa.

Caraf ya daukeni, ya yi dakina dani. Ina kuka, ina ihuuu. Zatona dukana zai yi. Tunda na ga dakina ya yi dani, saidaime abinda yamin yafi duka baqinci ya gama wulaqanta min rayuwa. Kafin ya miqe, ya ce, with a calm but firm tone,”Kinga gobe in akace ki mari wani mai suna Mahfux kan ya zageki kya Kuma kallon yadda nake kuka ne yasa shi kwashewa da dariya kadan. Kika gani cikin shika shikan rashin mutunci.

Yadda marin da kika min, bazan tava mancewa ba. Haka abinda namiki nasan bazaki taba mancewa ba. Allah ya isa mugu azzalumi kawai nake fade. Ke kimin shiru ko yanzu ki kuma shan mamakina gum nai da bakina ya fice daga dakin.

Yana fita ya hadu da yayansa Nasir, wanda hai cika magana be bai cika shiga sabgar yan gidanba koni baya sani abu. Ko gaisheshi nayi, amsawa kasa kasa yake. Ya wuce gurin ko a bangarensu ya ganni ina shara kirana yake. Yamin fada kan kar insake shigowa seda hajiyarsu ta mai fada. Sannan ta haqura ya kyalene sedai hijabai da ya siyon inxani. Ya ce, “Indinga sawa sautari.” Ina kula dashi ko fita zai yi. Inyaga na shigo barinsu zama yake. Ya ce “Insauri in gama badon komi ba.” Sedan kowane irin namiji ke shiga barin yake masu mutunci da marasa shi.

Mahfux me yakaika dakin yarinyar nan, ya fada hankali atashe. Ya watsa masa wani kallo hankanli naje na koya mata “What me kayi mata?” Ya fada yana firgizashi. “Kaje ka tambaye ta mana” Ya yi cilli da hannunsa da ya riqeshi.

Kuka kawai nake tausayinna. Fal ran Nasir, kasantuwarsa likita kuma malami mai koyarda yara masu san zama likitoci ne. Ya sa temaka min ya ban magunguna, ya hada min ruwa. Ya ce, with a reassuring tone,”naje nai wanka komi da ya cancanta.” Shi ya fadan yadda zan yi.

Bayan na fitone, naita roqarsa kan yabar maganar. Ya rufemin sirrina daqyar ya amince. Ya haqura saidai gabaki daya ya sauyawa Mahfuz ko magana ma sun dena yi.

Wata daya da faruwar al’amarin, ciki ya bayyanarmin. Alokacin mun kusa fara lectures, dan har Nasir ya amson komi. Aikuwa hajiya ta gane nan, ta tara jama’a maza da mata kan sena fadi. Uban da yaimin nace ai Mahfuz ne yahau ya tubure shi. Bashi bane qarya nake masa. Hajiyama haka ta yadda ina ita ba danta bane.

Nan kowa ya yi Allah wadai dani. Yah Nasir bainan ya yi tafiya haka. Suka ce, with a stern voices “Inbar gidan ko hijabi balle takalmi.” Suka turani waje nan. Na fadi na kukkurje.

Kuka nake sosai. Baba mai gadi ya zo ya dagoni, yana cewa, with a comforting tone,”Inzo muje gidansa.” Hajiyar Mahfuz ta fito cikin fada take fadin Sale. Indai koda wasa na ji ka temakawa yarinyar nan, Allah kabar aiki kenan. Jin haka yasa na miqe kafin ma ya je ya gama roqota. Kan ta yi haquri, ya kaini gidansa. Tuni nai gudu nabar lokon tafiya kawai nake. Banma san a tsakiyar kwalta nake ba. Dan kaina wani irin ciwo yake min daga idon da zanyi ne. Na hangi mota ta yo kaina. Duk yadda nai in kauce mata ina………….

<< Abbakar 17

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×