Skip to content
Part 6 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

Jiyai kamar an tsikareshi lokaci guda hankalinsa ya dawo jikin sa wanda ya bashi nasarar yaƙi da zuciyar sa, yai saurin cewa ” muje waje ko,” tai saurin buɗewa dan gabaki daya jikinta rawa yake “Time in sallah yayi, so u come back leter.”
Ta yi saurin cewa” ok Sir”

Bai ce komai ba ya yi C.mosque.

Acan masallaci yai sallarsa ya roƙi Allah gafara na yunƙurin saɓa masa dayai ya kuma gode masa da yasa bai saba masan ba.

Tabbas yanasan Ummulkhairi so bana wasaba, saidai yasan tai masa nisa ya rasa me yasa duk yadda yaso cireta aransa ke zama wahala, yarasa wane irin so yake mata,

Wayarsa ce tai ƙara hakan ya dawo dashi daga dogon tunanin da ya fad’a ya kai duba kan screen din wayar ƙanwata yagani yai murmushi khairiyya ce frnd dinsa ta facebook ya kai hannu zaidauka kiran ya tsinke yabi bayan kiran.

Da sallamarta ta Amsa shima ya amsa mata ƙorafunta ya biyo baya “yanzu yah na ka kyauta kenan kanaji ina kiranka kaƙi ɗauka?”

Murmushi ya yi kamar tana gaban sa ” to sarkin ƙorafi nazo ɗauka ta katse ayimin afuwa” tai dariya har yana jin sautin ta ” No bakamin komi ba.”

“Yanzu abunda kike kina kyautawa kenan? duk kin barni da tunaninki, ta zaro ido kamar tana gabansa “menayi?”

“Kyace me kika yi mana, saiki kashe wayarki inneme ki ” in rasa yau wajen sati uku fa kenan ko a online bana ganinki,”

Tai dan murmushi “amin afuwa”

” Haka kullin kike cewa” ya faɗa

Hmm ” wallahi ba ina sane na kasheba wayarce ta sami matsala ne “

“Aishikenan ya wuce” suka dan taba fira kafin suyi sallama.

Ya kashe yana murmushi yasani yanasan Ummulkhairi wanda be taɓa yima wata mace shiba sedai yasani ya yi trusting din khairiyya fiye da kowacce mace, yasani aduniya in aka dauke ummansa sai ƙannensa babu wata mace da yake sakewa yayi fira da wasa da dariya kamar khairiyya duda kuwa bai taɓa ganinta ba.

Asannu a hankali tunaninsa ya fara sauyawa kanasan Ummulkhairi anman ka yadda da khairiyya har kana iya sakewa da ita, why not ka mata tayin soyayya inyaso kayi aure ko ka rabu da san Ummu ya aminta da zuciyarsa but dole se yaga khairiyya before ya iya gabatar mata da abunda ke ransa, yasan duk duniya babu abinda ta ƙijini kamar ya nemi su hadu anman yanzu dole ta yadda if not zai yanke alaƙarsu.

Ummu ke zaune tana kallo ya shigo da baby a hannunsa “ungoshi kuka yake” ta karba tana dariya “Allah yaya kana shagwabashi infa ka tafi ya dinga kuka kenan, sai Farida ta ɗaukeshi tai masa rawa kasan ni ba iyawa naiba ace kaita jijjiga yaro sai kace wata yar tsana.”

Yai dariya “to banda abinki inban jijjigashi ba wa kikeso injijjga kinsan kuwa yadda nake sansa,” tai dariya “ai basai ka faɗa ba kowa yasan Dad loves his one”

Murmushi ya yi “to ni nawa san da nakema nawa d’an yafi na kowanne Baba harke mamarsa” suka saka dariya gabaki daya.

Zaune suke suna hira Mahfouz ya ce “Mutumina ya kaji shawarar tawa kuwa tayi ko?,”

Abbakar ” yai tsaki wace shawara kuma?”

Kallon sa Mahfuz ya yi da mamaki ” au har kamance”

” eh tunamin” Abbakar ya faɗa a taƙaice.

“kan yarinyar da kake so mana,”

Abbakar yaja tsaki “shawara ko cuta Allah mahfuz baka sona inda kana sona bazaka bani shawarar indauki ƙafata da kaina inkai jahannama ba”

Ɗaga masa hannu Mahfuz ya yi “Kagani tunda kaga zaka iya jurewa aishikenan, ni kaban shawara wallahi bana iya bacci kullun da tunanin cousin dinnan tawa dashi nake tashi kai ko ni ɗaya na zauna ita kawai nake hangowa.”

“Ni ba shawarar da zan baka, haƙur zakai matarma da wanda ya san inda take balle, kawai kaita addu’a Allah ya yaye maka.” Abbakar ya faɗa

Hawaye suka biyo kuncinsa Mahfuz ” kafadamin taya zan iya haqurin, wallahi ni asan khairat bansan wani abu waishi haquriba kafaɗan yazanyi inba haka ba wallahi santa zai iya hallakani a kwanannan.”

Uhum “Mahfuz kenan ka dunga saka dangana a’al’amranka wallahi nasan abinda kakeji aranka bekai nawa ba, kawai nafika haƙurine kadena sama ranka komai kake so zaka samu in kuma mutuwa taifa. Kadinga sama ranka ta mutune bakuma zata dawoba zakaji sassauci.”

A ƙagare Mahfuz ya ce ” to Habu nagode zan gwada insha Allah”

Dafa shi Abbakar ya yi ” yawwa nawan be a Man dan Allah.”
Bayan ya dawo gida ne, Wayarsa ya ɗauka ya kira Khairiyya sun gaisa kamar koyaushe be bari ta fara surutunnanta ba yace “magana nakesan muyi me mahinmanci”

” to yayah na inajinka.”

“Wallahi ina cikin matsala inasan kiban shawara kamar yadda kika saba, sai dai ba ta online ko through phone call ba a’a inasan ganinki face to face”

Tace “what!”

“eh”

sai ta kashe wayar.

Saƙo ya tura mata “khairiyya nagaji da kullin sedai mudinga magana a waya ko through chat, if baki yadda mun haɗu ba wallahi wannan shine ƙarshen alaƙarmu bazan kuma kiranki ba and kuma bazan kuma ɗaga kiranki ba and in facebook u will be out of my frnd list and I will soon block u in WhatsApp.”

Har safe ba reply be kuma yi abinda yace ba.

Yashirya zashi aiki saƙo ya shigo wayarsa yana dubawa nata ne, ayi haƙuri abin be kai ga haka ba, ƙasa kuma ta rubuta kwatancen gidansu ne ta ƙara da kazo ran Friday ko lahadi sauran ranaku inada sch, yai murmushi yau talata Allah ya kaimu juma’ar. Ya fada a ransa.

Bayan ya dawo yaje gidansu Mahfuz, sunsha fira Mahfuz din duk yai baqi sai dai ba kamar randa yazo gunsaba ya dan ciko.

“Kasan me ya kawoni zuwa nai infadama zaka rakani gidansu khairiyyar nan frnd dita ta Facebook” Abubakar ya faɗa

“ok yaushe?”

“Gobe” inji Abbakar

” Allah ya kaimu” Mahfouz ya faɗa

Abbakar yace “amin.”

Baisan me yasa yaketa rawar ƙafa zuwa ganin khairiyyanba ji yake kamar zashi ganin Ummu ne rasa kayanma da zaisa sai ƙarshe ya nemo milk shadda dinsa mai dunkin coffee sai yasa hularsa ita kalar dunki da ratsi ratsin milk takalminsa coffee yai kyau sosai kai kace wani sabon ango ne.

Kamar sun haɗa baki shigar da Mahfuz yai kenan dan yawancin kayansu iri ɗayane tun suna yara komai tare suke halinsu ne kawai ya ban banta.

Hajiya na ganinsu ta baro inda take “ah kace yau in sadaka kenan nayi suruka” suka hau sosa qeya bata tambayi ko ta wayeba ta musu fatan alkairi suka fice.

A qofar gidan suka faka motar suka fito Abbakar ya kirata tace gatanan.

Tai kyau sosai dan kaya ma na ƙasan kwaba tasa ko mace yar uwarta ce ta ganta saita yaba balle kuma namiji.

Alamar bude ƙofar gidan da suka ji yasasu gabaki daya maida hankalunsu kan ƙofar kowa da tunanin yadda zai ganta.

Gabaki ɗaya sukai mutuwar tsaye daga su har ita da gudu ta koma cikin gidan tana kuka Mahfuz na faɗin Abbakar khairi ce yayin da Abbakar yarasa abinyi, bakowa shi kuma idansa ya gane masa face kuma Ummu khair ɗalibarsa ya riƙe Mahfuz “wace khairin?” Yake tambaya a ruɗe.

“Causin ɗi ta mana, masoyiyata fa”

A firgice Abbakar ya ce ” kasan me kake faɗe”

No Mahfuz khairiyya ce fa da nace ka rakoni gunta”

Mahfuz ya zube agun, inda Abbakar yahau faɗin “inna lillahi wa’inna ilaihirraji’un” kawai Abbakar yake fade…..

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abbakar 5Abbakar 7 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×