Skip to content
Part 7 of 13 in the Series Abbakar by Fadimafayau

A tsorace Abbakar ya yi mota tare da ɗauko ruwa ya shafa masa a fuska, wanda yasa ya farfaɗo, ahanzarce ya miƙe yai cikin gidan da yaga ta shiga yana ƙwala mata kira.

Farida ce ta dakatar dashi ” haba Malam mene hakan zaka shigo mana gida”

Ɗaga mata hannu ya yi ” kinga ni ba gurinki nazo ba masoyi yata kawai zan ɗauka.”

Ita ko khairiyya tana shiga ɗaki ta faɗa cikin kuka ta rufo ƙofa ta hau kiran mijinta zance ko wane oho mata.

Cikin kuka da tashin hankali take masa bayani ”  Yah Mahfuz ne wallahi shine yazo yakuma ƙi tafiya.”

Hankalinsa atashe ya kashe wayar yayo gidan.

Tun a ƙofar gida ya yadda da abinda ta ce ɗin dan ganin Aminin ƙanin nasa, basar wa ya yi kamar be sanshi ba yace “Malam lafiya kuwa daman kai kashigar min gida?”

Girgiza Kai Abubakar ya yi ” bani bane Mahfuz ne” bai tsaya jin bayanin Abbakar ba kawai yai ciki abinsa.

Mahfuz yagani yana faman bugun ƙofar kan yana so ta buɗe ƙofar, da sauri yai gunsa ya kamo hannunsa ya kwaɗa masa mari, ” kai mahaukacin ina ne zaka shigo min gida haka.”

Jin muryar Nasir yasata fitowa ta ɓuya bayansa yayin da shi kuma yaja Mahfuz ɗin zuwa bakin gate.

Tankaɗa shi waje yai yana faɗin “karka kuma kuskuren zuwar min gida inba haka ba zakai danasani me yawa ka kiyaye.”

Bai kula da ciwon da Mahfuz din yaji ba ya banko ƙofarsu.

Da sauri Abbakar ya zo ya ɗaga Mahfuz ɗin ransa cike fal da tambayoyi.

Ganin bashi da amsar tambayarsa yasa shi katse musu shirun nasu da faɗin “bari muje asibiti amaka dressing in ciwon da kaji naga kamar ma yana buƙatar dunki.”

“Ok” kawai mahfuz yace dan yasan yanzu magana kadan zata iya sa shi fashe wa da kuka.

Adedai gurin Parker motoci na emergency na asibitin nasarawa Abbakar ya ajiye motar dan dare yayi yasan OPD yanzu ba doctor, muje ko yace da Mahfuz wanda ya fito yana dingishi sukai ciki.

Kamar yadda Abbakar yaje har gida ya tawo da Mahfuz haka ya rakashi suka rabu kowa da abinda ke damunsa a rai.

Bacci ya ƙi zuwarwa idanun Mahfuz gabaki ɗaya tunaninsa yaushe ne yayansa yai aure shi be saniba.

Zumbur ya miqe yai area ɗin da ɗakin yayyansu yake, ahankula ya tura ƙofar kamar yadda ya zata baya ɗakin, bedroom ɗinsa ya shiga anman ga mamakinsa kwance yake kan gadon yana baccinsa cikin kwanciyar hankali to me hakan ke nufi.

Gabaki ɗaya kansa ya kulle rasa me zaiyi yai abinda be saba ba ya mike ya ɗauro alwala ya hau nafilfilu.

Shima dai Abbakar kusan abu guda ne da Mahfuz ɗin, ya kasa bacci saidai abu guda ke daminsa wato tausayin kansa yasani ayanzu san Ummu ya gama kassarashi, yasani santa bazai barshi ba duniyar yaji gabaki ɗaya ta masa zafi kamar ya kashe kansa ya huta.

Hawayene kawai kebin idansa ya rasa shi kuwa wannan wace irin ƙaddara ce ta afka masa, shi yasani yana kuma faɗe So be masa adalci ba ya miƙe yai toilet dan dauro alwala.

Washe gari da safe kamar yadda yake al’adar gidansu Mahfuz, an hadu a babban falo ana breakfast wasu na kan dinning tsoffi na kasa dansu sunfi san ci a ƙas juya cokali kawai Mahfuz yake gami da baza idanu so yake kawai yaga ta ina yah Nasir zai billo.

Baikai ga dire tunaninsa ba yaji muryar Nasir ɗin na fadin “kai Hajiya se kace wani yaro” beji farkon maganar ba dan haka be fahinci abinda suke maganar akaiba.

Kamar yadda yake al’adar gidan koda da kwana mutun ya girmeka zaka gaidashi, hakan yasa Mahfuz fadin “Yah Nasir ina kwana” ya amsa “lafiya ƙalau ƙanina” yahau zubama kansa abincin.

Kusa da Mahfuz ɗin ya zauna yanaci yana nazarinsa saida yakai lomar ƙarshe kafin yace “wai ƙanina meke damunka ne naga duk ka rame gashi ka rigani fitowa anman har na cinye na barka”

“Bakomi yaya kawai banajin dadi ne.” Mahfuz ya faɗa

“Ayya anman ai daurewa zakai kaci abincin, seka sha maganin cuta da yunwa ai sai abin yai yawa”

A kagare Mahfuz ya ce ” to yaya zanci”

“Yawwa ko kaifa” ya faɗa tare da miƙewa zai bar wajen.

Yai saurin dawowa ” subhanallahi ciwon mene haka a kafarka?” Mahfuz ya kalleshi da mamaki kamar bashine jiya ya ji masa shi ba.

“Ina tambayarka ciwon me ne haka ta yaya ka jishi?” ya hau sosa ƙeya ganin yadda mutanen falon suka zuba masa na mujiya kowa nasan jin yadda akai “faɗuwa nai jiya munje unguwa da Aminin” sunan da mutanen gidan ke fadawa Abbakar “Ayya to Allah ya kiyaye” ya faɗa tare da fucewa.

Sama sama Abbakar yaci Abincin karinsa sauran ya faki Hajiyarsu yaje ya kaiwa kaji, yana yo kwana daga gurin kajin nasu yaji dariyar Ummi “Allah ya kamaka wato kaji kake kawowa, to abakin Hajiya” tai saurin juyawa zatai cikin gida.

Yabita da sauri yana roƙonta “haba yar ƙanwata ki tsaya kiji mana” tai masa banza ganin tai falon hajiyar yasashi kai kwanon kitchen ya bita da sauri.

“Haba ƙanwis bafa ma haka dake” karaf kunnen Hajiya “zonan autana me yayi?, faɗamin” ta kalleshi duk yai wani kalar tausayi “bashi bane nace ya temaka yaje yamin test yace ba inda zashi” ya saukar da ajiyar zuciya dan yasan indai Hajiya taji yaƙi cin abinci ya gama yawo.

Hajiya tasa dariya ” kyaleshi kije kiyi abinki da kanki zaki ci fiye dashi kinji autana,” turo baki Ummi ta yi ” anman hajiya..” dakatar ta Hajiya ta yi “kedai kawai ki yadda dani zakici, zan miki addu’a” “to hajiya ai shi kenan,”

“yawwa ko kefa” inji Hajiya

“Hajiya ni na tafi” yace mata.

“Ok seka dawo Allah bada sa’a”

“Amin” ya ce ya fice.

Yakai bakin gate a cikin motars,a yana shirin fita Ummi ta fito da gudunta, yaja ya tsaya, ta tsaya bakin tagar me zaman banza, to sarkin rigima lafiya zaki tsaidani what do you want?

“Eh kace haka mana, I save u today dole kabani tukwici, ko in Faɗa mata”

Girgiza kai yayi this thief woo “ai daman nasan da biyu” ya ciro kuɗi ya miƙa mata, ta karɓa tana dariya shima ya kaɗa kai yana dariya.

Inba dan dole ba da ba’abinda zai hanashi dena zuwa BUK koyarwa tun da ya fara tuƙin abinda ke faman kai kawo a ransa kenan, har ya isa yai parking yai ƙofar office insa.

Kamar ance kalli gefe ya hango Ummu riƙe da babyn ta a hannu Fatima na gefenta suna ta dariyarsu, cikin nishadi wani ƙululun takaici yazo masa wuya, lallaima yarinyar nan ta rainashi wato shi ta gama raina masa hankali, ita tana cikin farinciki da aurenta tana chat dashi tasa ya shaƙu da ita rasa abinda ma zaiyi yai.

Ji yai Fatima na faɗin “lah Aminiyar yafazo”

“Ɗan bari ya dan jima da shiga kar yaga daga zuwansa min takura masa” yaji ta bata amsa.

Da sallama suka shiga office din, ita da Fatima suka gaisheshi a ciki ya amsa kafin yace lafiya me ya kawo ku “Daman make up ɗin dakace zakamin kullin in nazo bakanan” ta faɗa cikin rawar murya.

A wulaƙance ya ce ” oh shine daga zuwana zakuzo ku takuran?” basu ce komi ba sai ido da suka zuba masa, “well I don’t think I have any time for wani abu wai shi make up test but tinda nace I will do it for you zan baki assignment kiyi submitting jibi, but ki baima captain inku sai ya kawon,” ya faɗa tare da miƙo mata question ɗin da ya rubuta. ta amshi question in tana godiya suka fice.

Binsu yai da ido zuciyarsa na ayyana masa abu buwa da dama masu kyau da akasunsu, yaja tsaki gami da ɗiban kayan sa zuwa inda yake da  lecture.

Koda yaje ma ajin be iya tabuka komi ba, ya rasa wannan wace irin masifa ce ya kawo lecture insa asabar dan duk sanin yan ajinsu Ummu basa karatu week end, akalla bazai ganta ba anman se ace yana shigowa ita zai fara gani.

“Abu daya zakai zuciyarsa ke faɗa masa Nigeria da fadi take kawai ka nemi aiki a wani state in ka koma can wataqil ka huta da wannan takaicin,” jiyai yayi na’am da shawarar ya miƙe dan ɗauko paper a daya 6arin dan fara rubuta takardar neman aikin in ya tashi yakai amasa printing dan bezo da system inshi ba, bama yasan se yaje gida ya sauya ra’ayi…

Zan cigaba insha Allah

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Abbakar 6Abbakar 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×