Maɓallan rigar shi ta makaranta yake ɓallewa, ya saka hannu a aljihu ya ciro links ɗinshi, kasancewar rigar mai dogon hannu ce. Hajja ce ta fito daga ɗaki tana kallon shi.
"Dogo ɗan baban shi, Sojan gidan Bugaje..."
Ta faɗa da alamun zolaya, ƙayataccen murmushin da ba ko yaushe ake gani ba Abdulƙadir ya yi mata. 'Yan gidan Bugaje suna da tsayi babu laifi daga mazan har matan, don gajerun cikin gidan ba su wuce su huɗu ba, amma tsayin da Abdulƙadir yake da shi har mamaki yake basu, duk manyan yayyen shi tsayinsu ɗaya. . .