Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Abinda Babba Ya Hango by Ummu Adam

Muryarta a sanyaye ta yi masa sallama amma ko kansa bai ɗaga ba ballantana ya san ta shigo, a hankali take tafiya saboda rashin ƙarfin jiki data ke ji; ta aje kofin shayin zata koma falo sai ya juyo yace mata, “Kenan ni zanje na ɗauka ko?”

A tsorace ta koma ta ɗauko kofin shayin ta miƙa masa. “Subahanallahi!” Muryar Okasha Aisha da Zahra suka jiyo mai cike da razani wanda ya sa suka miƙe tsaye suna tunanin mai yake faruwa. “Wayyo Allah na” suka sake jiyo wata ƙarar mai ɗauke da sautin mari, nan fa suka garzaya ɗakin a firgice dan ganewa idanunsu abunda ke faruwa.

“Na shiga uku anty Jameela me zamu gani haka!?” Aisha ta faɗa yayinda ta kama ‘yar uwarta da take ƙoƙarin faɗuwa ƙasa. “Yaya Okasha mai ya faru ne?” ko kula Zahran bai yi ba ya yi ficewarsa a ɗakin.

A hankali suka ja Jameela zuwa bakin gadonta, bayan ta dawo hayyacinta take sai suke tambayarta abunda ya faru, zazzafar hawayene suka fara zubowa daga idanunta. Zahra ta miƙo mata ruwa ta bata a baki ta sha sannan ta yi wani irin ajiyan zuciya tamkar wacce aka shaƙe da niyar ɗaukan ranta.

Halinda Jameela ke cike tabbas abun tausayi ne domin ko maƙiyinta ba zai mata fatan kasancewa cikin irin wannan hali ba. “Idan za kuyi aure kada ku yi mummunar zaɓi irin nawa.”

Da ƙyar Jameela ke magana saboda nauyin da laɓɓanta suka yi, hankalin Aisha da Zahra ya yi matukar tashi!

“Anty wai me kike nufi ne?” Aisha ta faɗa.

Cikin ƙarfin hali Jameela ta dafa jikin ƙannenta kana ta yunƙura dan ta tashi amma sai wani irin jiri ya ɗebeta ta koma kan gadon da sauri.

“Sannu anty, ko dai muje asibiti ne?” Aisha da Zahra suka faɗa cikin alamun damuwa.

“Kada ku damu, lafiyata ƙalau domin kuwa na saba da dukansa zuwa anjima zan war-ware.” Jameela ta faɗa.

Aisha ta ce, “To wai dan Allah me kika yiwa yaya Okasha ya mareki ne?”

“Ruwan shayin dana haɗa ne ya ɗan zuba a jikinsa, kuma wallahi ba da gan-gan nayi ba” Kafun ta ƙara cewa komai ta fashe da matsanancin kuka mai tada hankali!

“Dan Allah anty Jameela ki daina kuka haka” Aisha da Zahra suka faɗa yayinda su ma kansu kukan suke yi.

*****

Jameela kyakkyawar mace ce wacce ta haɗa dukkanin farillan kyau da ‘ya mace ke buƙata, ta kasance yarinya mai cike da nutsuwa, hankali da kuma ladabi kafun ta haɗu da Okasha. Iyayenta dattawa ne na gaske ga kuma rufin asiri dai-dai gwargwado. Aisha da Zahra sune tagwayen da suka biyo bayanta tsakaninsu shekaru biyar cif; amma sun fita girman jiki kai ka ce ma sune yayunta.

Suna makarantar kwana ta sakandire suka ji labarin aurenta, hankalinsu ya tashi da jin yadda abun ya zo a gaggauce bugu da ƙari ko zuwa gurin bikinta ba su yi ba bisa ga umarnin mahaifinsu.

Dawowarsu gida kenan bayan wata uku suka garzayo gidan antinsu anti Jameela da yaya Okasha dan su yi musu fatan alkairi game da aurensu, shigarsu gidan kenan suka zauna a falonta yayinda ta haɗowa Okasha shayin coffee ta kai nasa ɗaki.

Jameela tana matuƙar tsoron Okasha domin kuwa ko kallonta ya yi sai tsikar jikinta ya tashi ballantana idan ya yi mata tsawa. A tsorace take komai kusa da shi tamkar baiwarda take taka tsan-tsan da mai gidanta.

Rawar da hannayenta ke yi saboda tsoro da kuma zazzaɓi dake damunta ga kuma laulayin ciki, shi ya zama silar kwaɓar da shayin coffee da tayi a jikin Okasha; cikin fushi da zarani na zafin da Okasha yaji na ruwan zafin ta ke ya miƙe tsaye ya sharara mata mari a kyakkyawar fuskarta da ko tabo babu saboda tsananin kyau.

Marin da Okasha ya yi mata shine amo na biyu da su Aisha suka jiwo yayinda suke zauna a falonta.

To wai shin Jameela da Okasha ba auren soyayya suka yi bane? Shin menene dalilin da yasa yake mata wannan wulaƙancin? Mai yasa Jameela take matuƙar tsoron mijinta haka?

Wa’ennan tambayoyi ba ga zuƙatanku kaɗai suke yawo ba, hatta ga zuƙatan Aisha da Zahra ma abunda suke tambayar kansu kenan.

A hankali ta kama hannun ƙannenta tace musu “Aisha da Zahra yau zan baku labarin abunda kuke san ji daga gareni, dan ya zama izina gare ku wajen zaɓen mijinda zaku miƙawa ragamar rayuwarku.

Ranar alhamis da misalin ƙarfe bakwai na dare ina tsaye cikin yanayi na ɗar-ɗar, kwatsam na ji sautin murya mai ratsa kunnuwar mai sauraro, cikin tsoro na juya dan ganin wanene yayinda nayi tozali da kekkewar idanunsa masu ɗaukar hankali.

“Wa alaikumus-salam”
Na amsa sallamar da ya yi mun, ta ke ya saki wani irin murmushi wanda ya ƙara bayyana kyansa a fili, na yi daɗika biyar ina kallonsa ba tare da na motsa ba har sai da ya sake yi mun magana a karo na biyu.

“Baiwar Allah, ko zan iya sanin sunan ki?”

A lokacinne na motsa kana na fahimci ba mafarki nake yi ba, daddaɗan ƙamshin turarensa yana ratsa zuciyata tare da isar da sako mai cike da shauƙi.

“Suna na Jameela”
Na amsa masa yayinda na yi ƙoƙarin juyawa dan barin inda yake, tattausan fata na ji ya kama hannu na wanda ya sanya bugun zuciyata harbawar da ban san sanda na juya cikin hanzari ba na kai kallona izuwa ga hannu na. Na shi hannun na gani cikin nawa yana kai komo da babbar yatsarsa a kan fata ta.

A hanzarce na janye hannuna na ce masa haba bawan Allah, shin baka san haramunne taɓa jikin matar da ba muharramarka ba?

“Zube gwiwarsa ƙasa ya yi ba tare da la’akari da fararen kayan da ke jikinsa ba, sai ga hawaye na zuba daga idanunsa wanda ganin hakan ya sanya jikina sanyi kuma hankalina ya tashi matuƙa ganin yadda babban mutum a gabana yana zubda hawaye.

“Dan Allah ka tashi” Na faɗa muryata a sanyaye.

A lokacinne Khadija ta fito daga gidansu muka wuce gurin dinar auren Halima, har muka daina ganin juna da shi babu wanda ya kara cewa kowa komai.

Duk da hayaniyar gurin dinar amma hankalina, nutsuwata da kuma tunanina duk suna kan mutumin da ko sunansa ban sani ba.

“Sunana Okasha”
Na sake jin wannan muryar a karo na biyu, haka na juyo na sake yin tozali da shi a karo na biyu; abunda ya bani mamaki shine ɗan lokaci da muka rabu da shi har ya koma gida ya sauya tufafin dake jikinsa.

Wai dan Allah malam me kake buƙata a gurina ne kake ta bibiyata? Da kakkausar murya na yi masa magana.

“Idan kina ɗagamun murya zuciyata kaɗawa take yi bebi, ko zaki iya bani lambar wayarki?”

Ban san meye dalili ba amma idan yana magana ji nake kamar kada ya daina saboda kyan laɓɓansa suna motsawa gwanin ban sha’awa, ko musawa ban yi ba na amshi wayar da ke hannunsa na sanya lambar wayata a ciki. “Dan Allah ka tafi daga kusa dani, kuma ka daina bibiyata.” Na faɗa yayinda na kau da kaina daga gare shi.

A ɓoye na koma gida saboda babanmu bai san na fita ba, tunda na dawo gida nake jin zuciyata na bugawa kuma nake jin wata kifiya na sukar zuciyata, ƙamshin turarensa ya kasa barin hancina kyakkyawar fuskarsa nake gani a duk sand na lumshe fatar idanuna “me yake shirin faruwa da ni ne?” na tambayi kaina yayinda ni kaina banda amsar tambayar.

Watanni biyu da haɗuwarmu, Okasha ya mamaye ko ina a cikin zuciyata banda mararin kasancewa tare da shi babu abunda nake so; duk da Hajiya ta ƙi bani damar na iso da shi gurin Baba.

Okasha ne ya hure mun kunne na isar da maganarsa gurin baba ba tare da izinin Hajiya ba, Babanmu ya amince da maganar bisa sharaɗin zai yi bincike a kansa.

Na amince da sharaɗin cikin farin ciki dan a tunani na babu wani hali marar kyau da za’a samu daga Okasha.

Shuɗewar wata ɗaya kenan da maganarmu da Baba, ina zaune a ɗaki na sai Hajiya ta shigo tace mun Baba yana san gani na a falonsa, da hanzari na isa zuwa gare shi amma sai na fahimci akwai alamun ɓacin rai tattare da shi. Mun ɗauki kimanin sa’a ɗaya muna tattaunawa game da lamarin Okasha amma sam ya ƙi fahimta ta.

“Okasha mutum ne da Allah ya horewa arziki da kuma dukiya sannan gashi da ƙuruciya, matashi ne mai kyawun halitta kuma ɗan gidan manya; to amma ba su ne kaɗai abunda ake nema daga gurin miji ba, saboda wasu daga cikin halayensa da na tabbatar akwai saurin fushi, girman kai da kuma ƙarancin addini.

Jameela ni mahaifinki ne kuma ba zan so abunda zai cutar da ke ba, dan haka ki yi haƙuri da auren Okasha hakan zai fi miki alkhairi kuma zaki samu miji na gari da yardan Allah.

Tamkar fitar tabar sigari haka nake jin maganganun Baba suna fita daga kaina, hakan yasa ina fitowa na kira Okasha na faɗa masa komai kamar yadda na saba duk sanda akai maganarsa to sai na faɗa masa dan har yake mun faɗa akan na riƙa haƙuri.

Tun Baba yana lallaɓani yana bina a sannu har muka fara samun matsala, har sai da ta kai Baba ya kwace wayata kuma ya hana ni zuwa ko ina sannan ba wacce za ta zo gurina; tamkar marainiya haka na koma.

Na ƙauracewa abinci har sai da ciwon olsa ta kama ni, na rame na ƙanjame, ganin haka Baba ya kira Okasha ya tambaye shi ko da gaske yake san aure na? Okasha ya amsawa Baba tare da yi masa alƙawarin zai riƙe ni amana babu musgunawa ballantana cin fuska.

Ina gadon asibiti amma na ƙi yarda na sha magani kuma bana cin abinci. Hajiya ta yi tsammanin mutuwa zanyi, kwatsam Baba ya zo ya ce mana magabatan Okasha sun zo kuma ya bada aurena ga Okasha an ɗaura aurena da Okasha a falonsa ɗazu da safe kan sadaki naira miliyan ɗaya.

“Alhamdulillahi” na faɗa cikin tsananin farin ciki da murna! Hajiya ranta ya ɓaci matuƙa da faruwan hakan amma ni hankali na a kwance, bayan kwana uku a aka yi min jere tare da shirya biki matsakaici kamar yadda Baba yace.

Tun daga ranar da aka ɗauramun aure Baba bai ƙara ɗaga idanunsa ya kalle ni ba ballantana maganar arziki ya shiga tsakaninmu. Har ranar da aka kawo ni gidana Hajiya bata ce mun komai game da bikin ba hasalima ni da ƙawayena mukai komai na shagalin.

Daren juma’a Baba ya ɗauko ni a mota ya kawo ni gidan mijina, bayan ya yi sallama Okasha ya buɗe kofa sai Baba ya damƙa hannu na a hannunsa yace masa ga amar Jmaeela ka tabbatar ka cika alƙawarinka.

Ban taɓa ganin hawaye a idanunsa ba sai a wannan ranar amma ko kaɗan hawayen Baba bai taɓa zuciyata ba. Baba yana tafiya na rungume mijina cikin farin ciki inata jin daɗi shima haka.

Tun a satin farko na aurena na fara ganin alamun akwai matsala domin kuwa ban taɓa ganinsa ya tashi yayi sallar asuba akan lokaci ba ko da na tashe shi ba zai tashi ba har sai ƙarfe takwas zuwa goma na safe.

Bai damu da kulawa da ni sosai ba ko da na yi kwalliya baya yabawa sannan bai damu da cin abinci na ba. Abun ya dame ni amma sai na ɗauka ko bai da lafiya ne daga baya na fahimci sam ba haka bane.

Watanmu ɗaya da aure na samu juna biyu, na yi tunanin zai yi farin cikin jin haka amma sai ya hauni da faɗa yana zagina wai ashe ni “yar ƙyauye ce daga aure sai nayi ciki ko jin daɗin auren bai gama yi ba! Haka ya dinga wulaƙantani yana kyamata saboda laulayin ciki kullum amai da zubda miyau.

A lokacinne ya ƙauracemun ya daina hulɗa da ni, hatta kwana a gidan sai ya ga dama yake yi. Na yi kuka harna gaji kuma na rasa wanda zan faɗawa abunda ke damuna ga shi Baba yace duk abunda ya faru kada na zo gidansa.

Ina ji, ina gani ‘yammata ke kiransa a waya yana ɗagawa a gabana yana firar soyayya kamar yadda muke yi da shi a baya, abun har ta kai Okasha zai shigo da mace gidana ya kai ta ɗakinsa su yi abunda zasu yi yayinda nake jin muryarsu.

Satin baya da ya wuce ya kawo wata mace mai suna Mira, a gabana yake sumbatarta ba kunya ba tsoron Allah hakan ya sa na kira Mamansa dan na faɗa mata a waya amma sai take faɗamun cewar ita ba mahaifiyarsa bace Okasha hayarta ya ɗauka da wani mutum ya biya su naira miliyan biyar suka nemo mutane dan su zo gidanmu a matsayin iyayensa.

Ƙarar faɗuwar wayata naji yayinda na rusa wani irin ihu ina cewa na shiga uku na lalace Okasha ka cuce ni!.

“Hahaha” na jiyo sautin muryarsa a bayana yana mun dariya.

“To ke dama kin yi zaton da gaske nake son ki harda da zan haɗaki da iyaye na?”

Tsayawa na yi ina ƙarewa maci amanar kallo cikin tsananin baƙin ciki, a lokacinne Okasha ya dinga faɗamun wasu maganganu da bazan taɓa mantawa da su ba.

“Ni fa da kike gani tamkar hula nake kallon ‘ya mace, zan sa wacce na ga dama kuma na cire a lokacinda naga dama, zan iya yiwa mace komai kuma na jure komai har sai na samu abunda nake so daga gareta.
Ke ce mace ta farko da ki ka ƙi bani haɗin kai har sai da na aure ki, haka ki ka sani asarar maƙudan kuɗi kuma ga shi ko fanshewa ban yi ba kika kwaso ciki to wallahi cikin nan zubda shi zan yi ko zaki mutu.

A tsorace nace “Na shiga uku haba Okasha mutuwa kuma sai kace ka daina so na!”

Wani irin tsawa ya yi mun har sai da na razana sannan yace mun “ku fa mata matsakarku kenan bakwa gane bam-bancin soyayya da kuma sha’awa, Jameela bana son ki ballantana na ƙaunace ki, da ina sonki da bazan taba yin kuskuren kusantarki ko taɓa fatar jikin ki kafun aure ba, da ina sonki da bazan taɓa zama silar ɓatawarki da iyayenki ba, da ina son ki ba zan nemo iyayen goge dan na aure ki ba.

Saboda nauyin maganar Okasha sai da ƙafafuna suka kasa ɗaukata, daɓas na faɗi kan kujera yayinda hawaye suke zuba daga idanuna. Ko kaɗan halinda nake ciki bai damu Okasha ba saboda rashin imani.

“Jameela shi namiji so daban sha’awa daban a zuciyarsa amma ita mace duka abu ɗaya ne, na san kina so na kuma kina tsananin sha’awata amma ni kuma sha’awa kawai ki ke bani amma sam ba kya cikin zuciyata ballantana na ji tausayinki, dan haka baki da maraba da dabbar da na siyo dan yi mun hidima.”

Okasha ke mun magana cikin ƙasaita da ji da kansa babu tausayi babu imani tamkar fir’auna. Tun daga wannan ranar na koma tamkar baiwa a gurinsa kuma nake nadama ina dana sanin mummunar zaɓin da nayiwa kaina, ga shi ba zan iya zuwa gida ba ballantana na nemi yafiyar iyayena.

Hajiya taja mun kunne game da shi harma take faɗamun muddin na auri Okasha to ba zata yafe mun ba kuma ba zata taɓa zuwa gidana ba ko mai zai sameni.

Maganar Hajiya ta ɗaga mun hankali amma kuma sai nake ganin zata sauƙo daga fushin da tayi ta yafe mun amma ba zan iya rayuwa ba Okasha ba; yanzu ga shi ina girban abunda na shuka dan haka nake baku shawarin kada ku gabatar da son ranku kafin na iyayenku sannan ku san waye zaku so dan ku san wa zaku aura.

Garaf suka ji ƙarar bugun ƙofar ɗakin Okasha ya bankano cikin fushi sannan ya jefo musu wata takarda ya faɗa kan cinyar Jameela.

“Na gajiya dake dan haka ki koma gidanku na sake ki saki uku.”

“Inna lillahi wa inna lillahi raji’un, subahanallahi meye haka yaya Okasha!?” Aisha ta faɗa cikin fushi.

Lalle abunda babba ya hango yaro ko ya hau dala bai zai hango ba.

Wata uku da faruwan hakan, Jameela tayi ɓarin cikin da ke jikinta saboda damuwa da zullumi da take ciki, ga rashin cima yanda ya kamata kullum sai kuka.

Ƙarfe biyun dare Jameela da ɗauko wayarta dan ta duba shafinta na kafar sadarwa, kwatsam ta yi kiciɓis da labarin wani matashi da wata budurwarsa ta watsa masa ruwan batir a fuska.

A tsorace ta zabura ta zauna kana ta jawo hoton kusa taga alamun Okasha ne tsohon mijinta, tayi ƙokarin karyata idanunta duk da ta tabbatar amma sai idanunta suka kai ga sunansa a saman hoton Okasha Sani Sa’id.

Rayuwa kenan idan ka san mai za ka yi, to baka san mai za’a yi maka ba.

Alhamdulillahi nan na kawo ƙarshen labarin, ina fata mu amfana da darasin da ke ciki.

Ina muku godiya da kuka bada lokacinku dan karanata labarina.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.3 / 5. Rating: 27

As you found it interesting...

Follow us to see more!

28 thoughts on “Abinda Babba Ya Hango”

  1. Masha Allah
    Allah ya kara basira as always littafi yayi ma’ana sosai kuma ya wa’azantar you did a great job 👍

    1. Fatanmu a kullum mu farka kuma mu farkar da ‘yan uwa musamman mata game da sha’anin soyayya da rayuwar aure. Amma hakan ba maai yiwu bane har sai mun samu goyan baya daga makaranta kamar ku. Na gode.

  2. Masha Allah
    Allah ya kara basira
    Ya kamata yan uwa mata su rinka bin shawarwarin iyayensu
    Gunga darasin Da yake cikin wannan lbrn.
    Allah ya karemu

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×