Mk tsaye a kofar hotel, yayin da kunnensa yake manne da earpiece, lokaci zuwa lokaci ya kan duba agogon hannunsa, ko na wayarsa, hakan kuma bai dauke mishi hankali daga kallon keke napep da suke wucewa a titin da ke gaban shi ba.
Har zuwa lokacin da wani keke ya yi parking daidai kofar hotel din.
Ya zubawa keken ido har lokacin da matar da ke ciki ta ziro dogayen kafafunta zuwa waje, daga bisani kuma ta bayyana gabadaya, cikin wani leshe mai kalar ruwan madara, wanda aka yi wa kwalliya da kananan duwatsu masu kyalli da. . .