Skip to content
Part 1 of 13 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Mk tsaye a kofar hotel, yayin da kunnensa yake manne da earpiece, lokaci zuwa lokaci ya kan duba agogon hannunsa, ko na wayarsa, hakan kuma bai dauke mishi hankali daga  kallon keke napep  da suke wucewa a titin da ke gaban shi ba.

Har zuwa lokacin da wani keke ya yi parking  daidai kofar hotel din.

Ya zubawa keken ido har  lokacin da matar da ke ciki ta ziro dogayen kafafunta zuwa waje, daga bisani kuma ta bayyana gabadaya, cikin wani leshe mai  kalar ruwan madara, wanda aka yi wa kwalliya da kananan duwatsu masu kyalli da daukar ido.

Dinkin riga da siket ne na zamani, da ya zauna jinkinta das, hakan ya kara bayyana kyawun dirinta, fuskarta fayau ba wata kwalliya mai nauyi, amma hakan bai hana kyawunta bayyana ba, musamman bakin gilashin da ta yi amfani da shi ya kara kawata kwalliyar tata.

Daurin dan kwalinta ya zauna das a saman goshinta. Yayin da ta yi amfani da gyale mai shaka-shaka  a kan kafadarta.

Duk da basu taba haduwa da juna ba tsawon shekara shida hakan bai hana shi  gane wannan ita ce bakuwar da yake zaune a nan domin ta.

Ko a cikin bacci ya tashi ya ganta tsaye a gabansa, kuma a cikin duhu tabbas zai shaidata.

Saboda   shakuwar  da ke tsakaninsu, tun kafin zuwan hanyoyi ma fi sauki, da kan iya bayar da damar tura hotuna, da kuma kira na video.

 Hanyoyi da suka kara taimakawa Mk wajen  kara sanin bakuwar ta shi sosai. ko alkalami da  takarda aka ba shi, zai iya zana ta, ta fita radau.

Ya  karasa wurin da keken ya tsaya, tare da  karbar madaidaiciyar ledar da ke hannunta, sannan ya mikawa mai keken kudinsa.

A karon farko suka zubawa juna ido fuskarsu dauke da murmushi mai nuna zallar farin cikin da suke ciki.

Asma’u  ce ta fara dauke kanta gefe guda, har yanzu da yanayin murmushi a kan fuskarta.

“Ranki-ya-daɗe! ” Mk ya fada  yana kallon ta fuskarsa dauke da murmushi

Ta kara fadada murmushinta, kafin ya katse da fadin “mu je ciki.”

 bayansa ta bi kamar mai tausayin ƙasa, har zuwa reception

Shi ne ya cike wani dan littafi.

Yayin da Asma’u ke gefe tana kallon sa.

Duk da dai ta takura saboda yadda wani babban mutum da ke gefensu ya kafe da idanuwa, kamar yana kokarin gano wani kuskure da aka yi yayin halittarta.

“Mu je” Mk ya kuma fada bayan ya karbi key din.

Ba musu ta kuma bin bayansa, amma hakan bai hanata juyowa don kara kallon mutumin can na tsaye ba.

Har lokacin kuma shi ma ita yake kallo,  ta kasa  dauke idonta a kansa, kamar yadda shi ma ya kasa janye na shi idanunn a kanta, har zuwa lokacin da ta ɓacewa ganin shi

Lokacin da suka isa dakin  tsaye ta yi a tsakar dakin tare da kare mishi kallo, kamar tana son gano wani kuskure da maginin ya yi, yayin gina shi.

“Kin hadu fa, fiye da yadda nake kallonki a hoto da video call”

Mk ya fada yana kallon fuskarta cikin lallausan murmushi.

Knocking kofar da ake  yi ne ya dakatar da ita ba shi amsa.

Suka kalli juna a tare, kallon da ke nuna alamun mamaki.

Mk ya nufi kofar

“Muhammad KB “

Mutumin ya tambaya, bayan da Mk ya bude kofar hade da zira kansa waje, don ganin waye.

“Eh” Mk  ya amsa

“Minti  biyu don Allah, Oganmu na son magana da kai”

  Bai amsa ba, sai da ya juyo ya kalli Asma’u, wacce ba ta san ma me aka fadawa mishi ba, yadda yake kallon ta, kamar yana jiran ta ba shi umarni,  Ita ma sai ta zuba mishi nata idanun

Ya mayar da kallon shi a kan ɗan aiken tare da fadin

“Ok”  kafin ya  juyo  a karo na biyu yana kallon Asma’u

“Ina zuwa”

Ya ce tare da ficewa ya bi bayan dan aiken.

Ajiyar zuciya Asma’u ta sauke, kafin ta zauna a gefen gadon tana kallon kofar.

Tafiya kadan ta kaisu wani daki matsakaici, wanda kallo daya za ka yi wa dakin ka gane office ne.

Wani mutum ne fari tas, wanda yanayin jikinsa kawai zai nuna ma yana cikin yanayi na jin dadi, sanye yake cikin fara tas din  shadda,  wacce ta sha aikin hannu, dinkin kuma ya karbi jikinsa.

Hatta hula, takalmi da agogon dake hannunsa farare ne tas. Yanayin kwalliyarsa kawai za ta nuna maka ya wadatu da ilmin zamani.

Sanyi ac mai hade da kamshin air fresheners  ke fita mai dadi a cikin office din.

Bayan dan aiken ya fita

Mutumin ya yi ƙaramin juyi a kan kujerarsa, yana kallon Mk da ke tsaye bakin kofa, saboda bai shigo cikin office din sosai ba  ya ce “Bismillah” tare da nuna mishi wata kujera da ke gefe.

Ba musu Mk ya zauna.

Mutumin ya nisa, hade da hada hannayensa du biyun  ya matsa suka yi kara, daga bisani kuma  ya ja lokar da ke jikin teburin da yake zaune hade da jawo kudi bandir daya, ya aje a gaban Mk

Su duka suka zubawa kudin ido.

“Dubu dari ne cif! Ka dauka naka ne, amma so nake ka ba ni yarinyar da naga kun wuce da ita yanzu”  ya fada yana kallon Mk cikin ido, ba tare da nuna shakka ko fargabar abin da ya fada a kan fuskarsa ba.

   Ido Mk ya waro  hade da dorasu a kan mutumin. Lokaci daya kuma fuskarshi na nuna tsantsar mamakin maganar.

Da farko da ya shigo kallon mai hankali yake mashi, amma yanzu kam ya rasa wane irin kallo zai yi mishi.  Zararre ? To idan ba zararre  ba yaushe zai gan shi da mace, sannan kuma ya ce ya ba shi ita. Ina aka taɓa yin haka?

Mutumin ya kara nisawa tare da ture laptop din shi gefe daya, sannan ya aje duk hannayensa a kan tebur din, wannan ya ba shi damar kusantar da fuskarshi a kan ta Kb

“Waccan yarinyar ba sa’arka ba ce, ba ta dace da kai ba, ka kalle ta ka kalle ka ina mamakin abin da ya sa ma ta biyo ka.”

Har zuwa lokacin Mk bai yi magana ba, illa ido da yake ta bin mutumin dasu.

Ya ɗan murmusa kaɗan, murmushi da Mk ya kasa sanin dalilin shi” Ina sonta ne, a kallo daya da na yi mata, na ji ta kwanta min, kuma Ina son mallakarta ta ko wace hanya, ko ta hanyar da kake son mallakarta a yanzu, ko kuma ta hanyar aure.”

A wannan karon Mk mikewa ya yi da niyyar barin office din, baya da lokacin ci gaba da sauraron wadannan maganganun banzan da kuma rainin hankali.

” Kawai daga ganina  da mace, sai ka ce in  bar ma ita, wai bamu dace ba, ka san wacece ita a wurina?” ya rufe maganar zucin na shi da jan dogon tsoki. , bai taɓa jin abun takaici irin wannan ba, ko barkar shege ba ta kai wannan abun haushi ba.

Ganin Mk na niyyar fita ya sa mutumin saurin dakatar da shi ta hanyar fadin

“Na kara ma dubu dari”

Mk ya juyo zuciyarsa na kara cika da bacin rai gami mamakin maganganun mutumin, karon farko da ya bude baki da niyyar datse wannan haramtaccen kasuwancin a tsakanin su.

“Ko miliyan dari za ka ba ni, ba za ka samu abin da kake so ba. Saboda ba ta siyarwa ba ce.”

Yana gama fadar haka ya bude kofar tare da ficewa cikin wani irin takaicin da bai taba tunanin zai  riskesa  , a wannan rana ba, ranar da suka kwashe tsawon shekaru shida suna jiran ta.

Yanayin fuskarsa kawai ta kalla ta fahimci ransa a bace yake, hakan ya sa ta mike da sauri, lokaci daya kuma tana jeho mishi tambayar

“Dear me ya faru?”

“Ba komai” ya fada hade da zaunawa a gefen gadon, kokarin danne bacin ransa yake  yi, amma zuciyarsa ta ƙi yi mishi biyayya.

Jiki a mace ta zauna gefensa, hade da kafesa da ido kamar suna kallon ƙuda.

“Da komai Dear, na fa sanka sosai ko ka manta, a waya ma ina gane halin da kake ciki ta sautin muryarka bare yanzun da nake kallonka cikin ido.”

Ya ja tsokin da bai san ma ya fito ba, sannan ya shiga shafa kansa, yayin da kwakwalwarsa ke kara tuna mishi maganganun mutumin, zuciyarsa na ƙara tunzura.

” Shi kenan tun da ba za ka fada min ba” cewar Asma’u tare da mikewa ta  shige toilet ba dan tana da wata bukatar da za ta biya ba. Haka nan ta ji tana son shiga.

Ya bi bayanta da kallo hade da lumshe idanu. Gaskiya ne Asma’u cikakkar mace ce, wacce ba namiji lafiyayye da zai kalle ta ba tare da ya ji ina ma ace ita din mallakinsa ba ce

Duk da kasancewarta baka, amma bakin bai hana mata kyan ko wane diri na jikinta fita ba

Doguwa sambal, mai wadataccen kwankwaso mai jan hankali, haka ma kirjinta yake, doguwar fuskarta me dauke da manyan idanu masu lumshewa, siririn gashin gira da yalwar gashin kai.

Yanayin fatarta smooth wacce shafe-shafen zamani bai bata ba.Ban da media shi kansa ya san bai kai matsayin da zai tsayar da ita, kuma ta saurare shi ba, da gaske ita ba a jinsa ba ce, amma media ta kawo mai nesa kusa, yau ga shi har yana shirin mallakarta.

Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya a daidai lokacin da ta fito daga toilet din.

“Zo ki dauki mayafinki mu tafi”

“Ina za mu je kuma?” mamaki sosai ya bayyana a kan fuskarta

Bai amsa ta ba, illa idanunsa da suke a kanta, yayin da zuciyarsa ke wani wurin daban.

Ta yi amfani da hannunta a saitin fuskarshi, dalilin da ya maido da hankalinsa wajen ta.

Idanunta ta saka sosai cikin na shi, kallon da a badini ma idan ta ce ta yi mishi shi, yana kashe mishi jiki, bare yanzu a zahiri.

Dalilin da ya sa kenan ya janye na shi idanun,  lokaci daya kuma ya dauki mayafin nata ya dora mata a kan kafada.

Har yanzu kallonsa take cike da mamaki.

Ya sagala mata ƙaramar jakarta, shi ma ya sagala ta shi jakar tare da daukar  ledar da ta zo da ita.

Har zuwa lokacin a tsaye take tana kallon shi.

“Mu tafi to”

Ba ta ce komai ba, ta nufi kofar fita.

“Kin zo da hijab ne?”

Maganarsa ta katse mata tafiyar da take yi.

Kai ta jijjiga alamar Eh.

“Yauwa cire gyalen, ki sanya hijabin, idan ma akwai nikabi duk ki sanya.”

Ta motsa baki da niyyar magana, amma yadda ya dora yatsansa a saman labbansa, ya sanyata dakatawa.

Aiwatar da abin ya bukata ta yi, duk da dai ba ta da nikabin, amma hijab din ya sauka har kasa.

Ita ya ba key din ta rufe kofar, sannan ta mika shi key din, ya wuce gaba ita kuma ta take masa baya, suka rika sauka   daga matakalar bene ba tare kuzari ba.

A reception suka hadu da mutumin dazu, tsaye da wasu ma’aikata da alama yana fada masu wata magana ne mai muhimmanci, saboda yadda suka natsu.

Cikin hikima yake satar kallonsu, yayin da Mk ke  jifanshi da wani kallo wanda daga shi sai Mkn ne suka san ma’anarshi.

Har Mk ya mika key din dakin, zuwa lokacin da ya tasa keyar Asma’u suka fice daga da reception  din mutumin bai daina satar kallon su ba.

Mk bai samu nutsuwa ba, sai da ya ji shi a sabon masauki.

Duk da  jefi-jefi ya kan ji maganar mutumin na kartar masa zuciya.

Har sai yake jin ina ma  ya  wanke shi da kyakkyawan mari, duk da shekarunsu ba  daya ba, amma Hausawa sun ce babba bai ji kunyar hawan jaki ba, jaki ba zai ji kunyar tutsu da shi ba.

Ba mamaki marin ya dawo da shi cikin hankalinsa idan ma hankalin nasa ya yi nisa da shi ne.

“Ina jin yunwa” Muryar Asma’u ta katse mishi tunani

Sai yanzu ya tuna ashe tun ta iso ko ruwa ba ta sha ba, kuma a kalla ta yi awa biyu da zuwa, saboda yana jin kiraye-kirayen sallahr magriba.

Ya zuba mata ido, kwance take rigingine ta kara yin filo da hannayenta du biyun ta hanyar dorasu a kan filon.

A cikin zuciyarsa ya yi murmushi saboda ganin yanayin fuskarta, wanda ke nuna mishi zuciyarta a lalace take.

“Me za ki ci?” Ya tambayeta fuskarsa dauke da murmushin da  ya subuce mishi.

Shiru ba ta amsa ba, har sai da ya kara maimaita tambayar

“Komai ma” ta amsa a hankali hade da zumbura baki.

Ya mike tsaye yana kallonta, yayin da sautin murmushinsa ke fita

“Ke fa damuwata da ke rikici”

Tabe baki ta yi, ba tare da niyyar magana ba

Hijabin ya tattaro ya cire mata, yana fadin “Cire to ki sha iska.”

Ba ta yi kokarin hanashi ba, sai ma ta gyara mishi yadda zai ji dadin cirewar.  ya ninke hijabin tare da  aje ta gefen gadon.

“Fada min me za ki ci?”

“Na ce ma komai”

“Wai fushi kike?”

Mikewa ta yi, hade da rabashi ta shige toilet don dauro alwallar magriba

Ya kuma yin murmushi, a zuciyarshi ya ce “Asma’u sarkin rikici.”

Idan dai rikici ne ko kan mota ya san da zaman ta.

A kaf soyayyarsu fada shi ya fi yawa, bai taɓa tsammanin soyayyar tasu za ta yi tsawon rai zuwa wadannan shekarun ba.

Sai da ya ga ta kabbara sallah, sannan ya fice daga dakin, don nemo musu abinci.

Abinda Ka Shuka 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×