Shiru Alaramma ya yi kafin ya ce "Rufin bakin na gabadaya, ko mutum ne kwara daya?"
Khalid ya juya kan Mk wannan ya sa Mk ya ce "Eh to kamar dai duk wanda yake da hannu a lamarin"
"Akwai sunansu ai ko?" Alaramma ya kuma tambaya
Mk ya jinjina kai alamar eh
Littafi Alaramman ya mikawa Mk yana fadin "Rubuta min sunansu a nan" saboda shi idan ban sunan shi, to ba ko wane suna yake iya rubutawa ba farat da garaje. Sai idan da ajmi, da boko kam, ba lallai ya iya rubutawa Shi ma rubutun sai ka. . .