Skip to content
Part 30 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

ASMA’U

Ba su yi wani taron suna ba, amma yaro ya ci sunan Abdallah wanda Alhaji Abdullahi ne ya yi mishi huduba da kanshi ya kuma zabi sunan.

Zuwa yanzu kam ya yarda wannan din ƙaddararsu ce, kuma tilas ne karɓarta.

Asma’u kam na ta shan jego, ba ta ƙara waiwayar Mk ba, kamar yadda shi ma bai sake waiwayarta ba. Kawai dai ya kara turo mata kudi masu ɗan kauri.

AG ma ya turo da mata da kudi wai ta yi hidimar suna kafin ya zo.

Sosai take son yakice AG a lamarinta amma hakan ya ci tura, komin ta sai ya kutsa kai ciki ya shiga.

Hidimar da ya yi wa Abdallah ko mahaifinshi bai yi mishi ita ba.

Abdallah da bai san komai da ya wuce ya ji ya ci abinci, girmanshi kawai yake cike da kuzari.

Irin girman nan da duk wanda ya kalle shi sai yaron ya ba shi sha’awa duk kasancewar yana da duhun fata.

Yanzu misalin karfe biyar na yamma da ya kama satinta uku da haihuwa. Zaune take a gefen katuwar katifarta tana cirewa Abdallah dattin kunne.

Wayarta da ke gefe ta shiga vibration alamun kira.

Ganin AG sai ta daga bayan sun gaisa ne ya ce “Mai jego gani a kofar gida”.

Cike da mamaki ta waro ido kamar tana gabanshi ta ce “wane kofar gidan”

“Kofar gidan Aunty” ya amsata.

Wayar ta sauke hade da kallon jikinta, ko dazu da safe sun yi waya bai fada mata zai zo ba. Abdallah ta kwantar hade da mikewa ta zira dogon hijab dinta

A falo ta cimma Aunty tana kallo.

Hannun kujerar da take zaune ta dafa tare da fadin “Abubakar Garba ne ya zo Aunty”

Cike da mamaki Auntyn ta ce “Da yammar nan?”

“Wlh!” cewar Asma’u a hankali.

“To ki bude sitroom din nan sai ya shiga ciki, tun da ko dazu na gyara shi, a can ma na yi baccin rana”

Da kai Asma’u ta amsa sannan ta juya zuwa wajen gate

Bude kofar tata ke da wuya fuskokinsu suka hadu. Lallausan murmushi AG ya sakar mata, ita ma ba ta san lokacin da ta mayar mishi da murmushin ba.

Ya matso sosai wurin kofar yana amsa gaisuwar da take mika mishi sannan ya ce “Ina Baban?” haka yake kiran Abdallah

“Yana bacci” ta amsa cike da jin dadin yadda yake damuwa da yaron kamar na shi. Kila don bai san ta hanyar da ya zo duniya ba ne.

“Shi na zo gani, ko yana fushi ne?”

Cikin murmushi ta girgiza kai tana fadin “Baya fushi. Bismillah mu je ciki” ta kai karshen maganar hade da mika hannu ta karbi wasu daga cikin ledojin da ke hannun shi

Tare suka isa sitroom din, bayan ya zauna ne ya ce “Kawo min little, I’m eager to see him”

Wani murmushin ta mika mishi kafin ta juya.

Ya lumshe ido a kokarinshi na danne abin da ke yi mishi yawo. Asma’u ta ƙara cika, ta yi wani fresh da ita. Kila ko don tana tsakiyar danyen jego ne, amma sosai ta tafi da duk wani kuzarinshi.

Yana a haka ta kuma shigowa bakinta dauke da sallama, ya amsa tare da bude idanunshi ya sauke a kanta.

Saman cinyarshi ta dora mishi Abdallah lokaci daya kuma ta koma kan kujerar da ke fuskantar shi ta zauna

Ya zubawa Abdallah ido cike da mamakin ganin fuskar Mk, saboda duk wanda ya san Mk ya kuma kalli Abdallah ya san jininshi ce

Take ya rikice, da kanshi yake tambayar kanshi ko dai da gaske Asma’u matar Mk ce, kamar yadda Mk din ya fada mishi a rana ta farko da ya nuna mishi bukatar shi a kan Asma’un

Amma kuma lokacin da yake tsare da shi ya fada mishi bai taɓa zuwa gidansu Asma’u ba

“To kodai ya boye min ne don kar in zo?” shi da kanshi ya tambayi kanshi.

Busassun laɓɓansa y lasa hade da dago kai yana kallon Asma’u wacce kanta ke duke tana wasa da hannayenta

“Fine boy” ya fada idanunshi a kanta. Daga cikin zuciyarshi ya fadi wannan kalmar don da gaske yaron kyakkyawa ne.

Komai Asma’u ba ta ce ba

Zama ya gyara tare da fadin “Sai kika ganni kwatsam”

“Ya kwatsam kam. Fatan lafiya?”

“Na yi kokari sosai da na kwashe tsawon wata biyar ba tare da na kara sanya ki a cikin idona ba. Amma ba abu ne mai sauki ba”

Dole ta dauke idanunta a kanshi, saboda kallon da yake yi mata

Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce “Da ace za ki amince kina yin arba’in da an daura mana aure”

Ido ta waro sosai ba tare da ta ce komai ba

Murmushi ya yi kadan kafin ya ce “Me kike tsoro? Zan kula da ku ku dukan ku”

Shiru ta yi komai ba ta ce ba, wannan ya sa dora

“Ban san ko sai yaushe ne za ki yarda da ni Asma’u, bayan na fada miki dukkan gaskiya ta. Sonki nake yi, kuma da aure ba wai don in ci mutunci ko zarafinki ba”

Nan ma shiru ta yi sai wasa da take yi da yatsunta, yayin da wani bangare na zuciyarta ke  kokarin yarda da maganganunshi, wani kuma bangaren yana kin aminta. Har yanzu tana mamakin yadda za ace namiji ya ga mace a hotel kuma ya dauki tsawon lokaci yana neman ta, har ya lalubo ta ya kuma ce zai aure ta. Wannan abu akwai mamaki a ciki

“Me kike so in aikata wanda za ki gasgata ni?”

“Ni fa ba wai ban yarda da maganar za ka aure ni ba ne. Amma ina tsaro ne.”

“Tsoron me?” ya tambaye ta da sauri

Idanunta ta dago, ganin na shi yana kanta sai ta yi saurin janye natan.

“Ina jin ki”

“Ni kawai ba na son auran ne yanzu”

Shiru ya yi ba tare da ya ce komai ba, saboda ko wane lokaci abin da take fada mishi kenan, ita dai ba ta son aure yanzu. Bai san wane irin treating mijinta ya yi mata, da take gudun auran kowa yanzu.

“Asma’u!” ya kira sunanta a hankali.

Duk da ba ta amsa ba hakan bai hana shi fadin abin da ya yi niyya ba “Mijinki na baya ya cutar da ke ne, da har ya dasa miki tsoron aure haka?”

Tun da ya fara maganar take girgiza kai alamar a’a. Sai kuma siraran hawaye suka shiga gangaro mata, a haka ta ce “Bai taɓa cutar da ni ba wlh”

“Kina son komawa gidan shi ne?”

Shiru ta yi kamar ba za ta ce komai ba, Sai kuma ta girgiza kai a hankali alamar a’a

Shiru ya yi yana kallonta, yayin da wani abu yake yi mishi yawo a zuciya, kamar ya share sai kuma ya gagara yin hakan ya ce “Kina son komawa dai kenan idan na fahimce ki.

Cikin dauke hawayenta ta ce” A’a. Ni ba zan koma ba”

Wannan kuma shi ne gaskiyar zan ce, ko Ahmad zai juyo gare ta, akwai matukar kunya ta kara daga ido ta kalle shi, har ma ta iya zama da shi irin na aure da shi.

Falon ya dauki tsawon lokaci shiru kamar babu kowa, sai Abdallah da ke ɗan korafe-korafenshi alamun yana bukatar abinci

Da kanshi ya mike zuwa inda take zaune ya dora mata Abdallahn, kasancewar a kan 2 sitter take Sai ya yi zaman shi a gefen ta, wannan ya ba sansanyan turarenshi shiga ko wace kofar hanci tata a hankali. Yayin da kusancinsu ya haifar mata da abubuwa masu yawa. Sai ta rike Abdallahn kawai ba tare da ta yi yunkurin ba shi abin da yake nema ba. Yayin da AG ya yi kamar bai san me ke faruwa ba. Tun Abdallah na kuka kasa-kasa har ta bude baki sosai cikin azzakar muryarshi y shiga rera kuku.

Duk da kukan na damunta amma ta rasa yadda za ta yi wurin lallashi ko ba shi nono.

Cikin murmushin tsokana AG ya tashi hade da komawa wurin zamanshi na farko yana fadin “Ki ji da shi.”

Cikin sauri ta dage hijabinta, hade da tura Abdallah ciki. Saboda kuka yake yi sosai.

*****

Mk

Kamar yadda Alaramma ya shaida mishi hakan ne ya faru, after 2dz suka kuma dawowa Malamawa. Yanzu ma kamar waccan ranar basu samu ganin Alaramma ba sai bayan da aka fito sallahr azhur

Dakin waccan ranar a nan ya sauke su, bayan sun gaisa kai tsaye ya shiga ciro musu layun tare da bayanin yadda za su yi amfani da su.

Yadda suka nutsu kamar tuwo a kula ya isa ya nuna maka yadda suka dauki abin da yake fada musu da matukar muhimmanci.

Bayan ya gama duk bayaninshi suka dire mishi hakkinshi, kafin suka fito a tare zuwa zauren gidan. Inda suka yi kicibis da Ruma tana shigowa.

Cikin sauri kuma a nutse ta kai kasa tana fadin “ina wuninku?”

Su Mk ne suka amsa, idanun Mk din a kanta, har ta mike zuwa cikin gidan Alaramman.

Suna a kofar gidan kuma ta kuma fitowa ta wuce su.

Daidai lokacin kuma Alaramma ya koma cik gida daga rakiyar da ya yi musu.

“Gaskiya ba zan bari kaina ya yi murfi ba.” Cewar Mk yana kallon Khalid

“Me ya faru?”

“Komawa za mu yi ciki in nemi aure”

Baki bude Khalid ke kallon shi, Sai kuma ya yi guntuwar dariya tare da fadin “Aure kuma, a ina za ka nemi auran?”

“Ina muka fito mana”

“Ba ka da hankali to, ta ya kake tunanin wannan gidan za su bamu aure, ba ka ga yanayinsu da tsarinsu ba ne. Ka zo wurinsu neman taimakon binne aika-aikar da ka yi. Kuma ka ce kana son ƴarsu. Ka yi hauka ne?”

Shiru Mk ya yi yana ta ce maganganun Khalid kafin ya ce” amma ai bamu fada musu ainihin abin da ya sa muke son daurin bakin ba. Ka san Allah ina son yarinyar Khalid, tun da na ganta take min gizo a idanuna”

“Wai wace yarinya ce?”

“Yarinyar nan da ta shigo muna cikin zaure”

Wani kallo Khalid ke yi wa Mk irin na ka yi haukan nan, Sai kuma ya juya zuwa hanyar komawa inda suka fito yana fadin “To zo mu je”

Da gayya ya yi wa Mk haka, amma ga mamakinshi sai ya ga ya biyo bayan shi har zuwa lokacin da suka yi wata sabuwar sallama a kofar dakin bayar da maganin.

Alaramma da ke waya ya yanke wayar hade da amsa sallamar yana fadin “Kun yi mantuwa ne”

“A’a Malam, magana yake son yi da kai” cewar Khalid, cikin dabara yan janye kanshi daga batun.

Umurnin shiga ya basu, hakan ya sa suka shiga hade da zama inda suka tashi tun farko.

“Me ya faru?” ya tambaya idanunshi a kansu

Khalid ya saci kallon Mk, don da gaske ba zai ce komai ba a wannan gaɓar.

Dalilin da ya sanya Mk shiga kame-kame, musamman yadda ya ga Alaramma ya kara cika mishi ido. Dakyar ya samu ya ce “Dama yarinyar da ta shigo dazu muna a cikin zaure an yi mata miji ne?”

Shiru Alaramma ya yi a kokarin shi na tuno yarinyar, can kuma sai ya ce “Rumasa’u ce ko?”

Jin sun yi shiru basu amsa ba ya tuna ashe fa basu santa ba. Ya dora da “Rumasa’u ce. Me ya faru?”

Mk ya dago idanu a hankali yana kallon Khalid. Harara Khalid ya aika mishi da ita, alamun ba fa zai magantu ba.

Cikin dakewa Mk ya ce “Idan ba a yi mata miji ba. Ni dai Allah Ya gafarta Malam ina sonta”

Bayan wasu ƴan mintuna Alaramma ya ce “Waye kai?”

“Sunana Muhammad Kabir Bashir, Ni yaro ne ga Alhaji Bashir Ɓurma.”

“Alhaji Bashir Ɓurm wanda yake  takarar ɗan majalisa?” Alaramma ya katse Mk

“Eh shi”

“Allah sarki, ai na san shi sosai, ya sha zuwa nan da kan shi ko ya yo aike.”

“Allah sarki” karon farko Khalid ya sa baki a maganar

“Amma kai ka taɓa aure ne?”

Kai Mk ya girgiza alamar a’a

Zama Alaramma ya gyara tare da fadin “To ita harka ta aure babu ɓoye-ɓoye ko kumbiya-kumbiya. Yarinyar nan ƴata ce, saboda ƴar Yayana ce. Ni ne nan nake aurar dasu. Idan na ce a yanzu a daura ma aure da Ruma babu wanda zai ce a’a. Kuma zan iya ba ka Rumasa’u in biya ma sadaki ma, saboda mahaifinka muna huldar arziki da shi. Amma maganar gaskiya yarinyar nan bazawara ce, bara muka aurar dasu ita da ƴan’uwanta. Sai dai ita ba ta yi dacen miji ba. Yanzu haka dai ta shiga wata na biyu da rabuwarsu da mijin.”

Ta kasan ido Khalid ya saci kallon Mk, shi ma Mk din ta kasan idon ya kalli Khalid.

Dakin ya kasance shiru ku san mintuna goma. Kafin Mk ya ce” Ina sonta haka”don da gaske son nata yake yi, ko karuwanci aka ce ta dawo zai iya auranta

Da hanzari Khalid ya dago kai yana kallon Mk kamar ya aikata wani babban zunubi.

Alaramma kuma ya yi shiru kamar ba zai ce komai ba sai kuma ya ce “Mu fa ɗan rukunin nan ba ma daukar maganar aure da wasa, idan muka ce eh to eh din ne. Don haka ka je ka kara nazari daga nan zuwa lokacin da za ta kammala idda”

Cikin girmamawa Mk ya ce “To mun gode sosai”

Daga haka suka fito daga dakin, Sai da suka kusa isa wurin mashin dinsu ne Khalid ya ce “Anya kuwa wajen barbara dan bunsuru ba zai dawo da ciki ba”

“Mtswww!” Mk ya ja tsoki, saboda haka kawai yake jin ba dadi, kamar ya daure kanshi da kanshi.

“Kai yanzu da bazawarar za ka fara? Don Allah jibe ka, kalli matsayinka ta ya za ace karasa diyar aure sai yar kauye bazawara wacce ba ta ko iya rubuta sunanta ba.”

“Haka nan nake sonta”

“kuma wai da gaske auranta za ka yi?”

“In Sha Allah” Mk ya amsa da dukkan zuciyarshi.

Cikin dariya Khalid ya ce”Anya kuwa ba hakkin Asma’u ne yake bin ka ba. “

Ambaton Asma’u da Khalid ya yi sai gaban shi ya shiga faduwa, saboda rabon da su yi waya ko chat an dade.

Baiwar Allah tana can tana fama da yaro, ko wane hali take ciki oho.

Yana sonta, da ace ta zubar da cikin nan zai iya yin komai don ya aure ta. Yana gudun ta ne kawai saboda yaron da ke tare da ita.

Bayyanar yaron babbar matsala ce a wurin shi.

<< Abinda Ka Shuka 29Abinda Ka Shuka 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×