Skip to content
Part 45 of 45 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

Tafiya ce ta kusan awanni sha’uku tsakanin Jama’a zuwa Nasara, shi ya sa ana kiran sallah magriba suka shiga garin, amma basu isa cikin gidanta ba, Sai ana sallame sallahr isha’i.

Tun daga waje yan kawo amarya ke yaba gida, har zuwa lokacin da suka zaunar da amarya gefen gadonta bakinsu bai yi shiru ba.

Tsarin gidan ba karamin burgesu ya yi ba. Ga shi ita kadai bai hada ta da Maman Nawwara ba.

Ƴan’uwan AG suka shiga hidima da su har zuwa lokacin da suka kwanta baccin huce gajiya.

Lahadi kuma AG ya ce ai sai sun yi dinner, haka su Aunty Hajara suka zauna, karfe biyar aka tafi dinner, dinnern da ta warwarewa Asma’u damuwa da kuma kewar gida, saboda an yi nishadi sosai, yayin da AG ya nunawa duniya cewa shi din yana sonta.

Safiyar Monday su Aunty Hajara suka dauki hanya, bayan da AG ya yi musu sha tara ta arziki.

Zamu dawo mu ga zaman amarya da ango. Yanzu bari mu leka su Aunty Safiya, ya suka koma gida.

*****

Sai 6:00pm su Aunty Safiya suka bar Maƙera cike da farin ciki, saboda yadda aka tarbesu a kauyen, da abubuwan da aka yi, ba karamin sanya su nishadi ya yi ba.

Shi ya sa a cikin motar ba ka jin komai sai labarin yadda abubuwa suka faru a ranar suke yi. Su yi ma wasu dariya, wasu su basu mamaki, wasu kuma sai su ji lamarin ya taba zuciyarsu.

Ana kiran sallahr magriba suka iso gida, kai tsaye kuma bangaren Hajiya suka nufa, inda suka shiga ba ta labarin abubuwan da suka faru na al’adar garin, da yadda aka tarbesu hakan sai ya yi wa Hajiya dadi, ta rika jin wani farin ciki sosai.

Su Goggo B dai suna yin sallah suka wuce, haka ma Maman Zarah, wacce Asad ya zo daukarta.

Sai dakin ya rage daga Aunty Safiyya sai Aunty Ummi. Ummi kuma ita ce suke uwa daya uba daya da Ahmad, Aunty Safiya kuma uba suka hada kuma duk ita ce babba a gidan.

Hajiya ta gyara zama sosai tana fuskantar Aunty Safiya sannan ta ce “Fada (Haka wani lokaci suke kiranta Fada, saboda ranar da aka ba Hakimi Galadima a ranar aka haife ta) ya batun yarinyar kuma fa, ko ba ku ganta ba?”

Ummi ta yi zaram hade da mikewa zaune daga kwanciyar da ta yi tana fadin “Ai Hajiya a wannan karon ma dai Ya Ahmad ya darje. Don nesa ba kusa ba, wannan ta fi Aunty Ma’u kyau, ga ta yarinya sharaf. Sai dai mu yi fatan Allah Ya sa zuciyarta ma ta kasance kyakkyawa”

“Ummi!” cewar Hajiya cikin alamun mamakin yadda ta zuzuta abun

“Allah da gaske Hajiya, bari ki ga hoton ta, ai na dakko shi a wayata, sosai yarinyar na da kyau.”

Ta kai karshen maganar hade da nuna mata hoton Hafsat.

Sosai Hajiya ta zubawa hoton ido, kafin ta ce “Tubarakhallah Ma Sha Allah! Gaskiya kam tana da kyau, kuma da gaske yarinya ce. Amma shi Ahmad da ya ce bai son karamar yarinya to don gidansu wannan Zaitun ma a ta girme ta”

“Gaskiya ta girme ta, wannan fa ba ta fi 16-17 ba” cewar Ummi

“Bari ya dawo in ji canja ra’ayi ya yi. Kuma ga shi sun ce ba za su sanya bikin da nisa ba. Bare mu ce ko zai jira ne”

“Hajiya! Kar ƙi ga laifinshi, ya zauna jiran wannan yarinyar ta girma, wlh kila ɗan shugaban ƙasa ko shugaban ƙasar ne zai zo ya aure ta. Ko wani babban ɗan siyasar.”Cewar Ummi

Cikin dariya Aunty Safiya ta ce” Kai Ummi wato kyan yarinyar nan fa ya tsorata ki, a ina shugaban ƙasa zai ganta? “

” Aunty kin san manyan nan kuwa? Ai suna zaune ake kawo masu kyawawan mata su aura. To har fadar shi za a kai mishi hoton ta. Sai dai ki ji kwatsam “

Dariya Hajiya ta yi hade da mikawa Aunty Safiya wayarta da ake kira

Cikin salon gulma ta ce” “Angon ne, yana son tambayar ko ba mu je ba.” Duk suka yi dariya kasa-kasa

Ita kuma cikin salon tsokana ta ce “Ango ka sha kamshi. Da kusa kake kanena ai dana rangaɗa maka guɗa”

Sautin murmushinshi ya fita kadan kafin ya ce “Aunty kun dawo?”

“Tun dazu”

“Amma babu wata matsala ko?”

“Babu komai, an tarbemu tarba ta mutumci, an karammamu an yi nishadi Ahmad, fatanmu Allah Ya sanya alkairi gami da albarka a, wannan lamari, amma tabbas iyayenta mutanen kirki ne.”

Idanunshi ya lumshe cikin jin dadin yabon da Aunty Safiya ta yi wa surukanshi. A hankali ya furta” Ma Sha Allah! “

Ita kuma ta dora da” Sun ce sha Allah daurin auran ba zai wuce watanni biyu ba, don haka a cikin satin nan sai a samu su Baba Magajin Gari su kai kudin auran. “

” In Sha Allah! “ya fada cike da nutsuwa

Daga inda Ummi take kwance ta daga murya tana fadin” Ya mun ga kyau da na zuba a jikin amaryarka”

Murmushi ya yi ba tare da ya ce komai ba ya yanke kiran.

Duk suka yi dariya. Hajiya ta ce “Saboda surutunku ya sa ya gudu yau ai, kuna tafiya ba jimawa shi ma ya tafi”

Suka kuma yin dariya a tare. Kamar kullum Hafsat kam sai magariba ta shigo gidan, alwala ta yi hade da yin sallah, sannan ta yi wanka. Sai da aka yi sallahr isha’i ne ta nufi wurin Inna Kuluwa saboda ita ce da girki, a ɗan tsorace ta ce “Akwai abinci”

Dunguna mata tuwon kawai ta yi, ita kuma ta je ta nemi miya.

Tun da ta shigo take jin kamar kamshin dakinta ya canja zuwa wani daban, yanzu ma da take cin tuwon haka ta rika shakar kamshi, da ta rasa daga ina ya zo.

Bayan ta gama gadonta ta haye hade da dakko sannu littafin English dinta tana dubawa.

Kamar daga sama ta rika jin muryar Babanta yana fadin “Ke Hafsat! Kina ina?”

“Ga ni nan Baba” ta amsa hade da durowa daga saman gadon, zuwa lokacin har ya kai kofar dakin amarya, wannan ya tabbatar mata a can yake so ta same shi.

Daga kofar dakin, hade da gaishe su, bayan sun amsa ne Malam Ayuba ya ce “Amarya dakko mata kayan nan”

Cikin ƴan daƙiƙi Amarya ta zube tarin kayan a gaban Hafsat, kamar za a bude shago.

“Kin ga kaya ko Hafsat? ” kai ta jinjina alamar eh, tana kallon mahaifin nata, zuciyarta na fada mata, to kodai yar ragowar gonar ya sayar zai bude shago.

Zamanshi gyara hade da tattare hankalinshi a kanta ya ce

“Kin san Ahmad ne ɗan Dawuri?”

Kai ta girgiza alamar a’a

“Ba ki san shi ba? Kwata-kwata ba ki san shi ba?” cike da mamaki ya yi tambayar

Kan ta kuma dagawa alamar eh

Malam Ayuba ya juya kan Amarya da take sauraronsu, Sai kuma ya dawo da kallon na shi a kan Hafsat ya ce

 “Ikon Allah! To kin ga kayan nan? (bai jira ta amsa ba ya ci gaba) to wadannan kayan duka na ki ne Asma’u, daga jiya zuwa yau abubuwa sun faru kamar mafarki. (ya shiga ba ta labarin abin da ya faru daga jiya zuwa yau din) a yanzu haka dai na bayar da auranki ga Ahmad.”

Abun bai wani tayar mata da hankali ba, sai dai kawai ya zo mata da mamaki. Ba ta taba kawo ma kanta aure ba, kenan dai da gaske Ya Tukuro yake tun da ga shi maganar da ya yi mata ta tabbata.

Daga duƙen da take, ta saci kallon tulun kayan da ke gabanta, wai duka duk nata ne, to shi waye wannan Ahmad din? A ina ya santa? Me ya sa kai tsaye ya tunkari iyayenta?

Wadannan duk tambayoyi ne da ba ta da amsarsu. Ba ta da matsala da luluben amsar me ya Babanta ya bayar da ita haka ziƙau ga mutumin da ba ta sani ba?

Ta san zai iya yin fiye da haka ma, musamman idan ya kudi. Rokon ta da fatanta Allah Ya mutumin kirki ne. Idan har ya kasance mutumin kirki ita ba ruwanta, za ta yi zaman ta, saboda ta san idan ma ta ƙi amincewa to ba lallai wani kuma ya kara zuwa da irin wannan bukatar ba

Sai kuma ta tuna karatunta, da nan da watanni bakwai ta kammala.

A wannan gaɓar ne ta shiga tashin hankali, lallai aka yanke mata karatunta a wannan gaɓar an ƙware ta. Ta sha wahala sosai, sai da abu ya zo karshe ace ba za ta rike sakamakon wahalarta ba. Ita da take son har gaba ta ci, duk dai nan ma ba ta dora ranta ba. Don ma kar ta ƙi samu ranta ya ɓaci.

“To Baba karatun fa?” ta yi maganar a hankali, tana kallon shi da idannunta da suka yi wani narai-narai kamar an zuba musu mangyada

“Wane karatu Hafsat? Ai aje maganar karatu gefe a yi wannan, saboda ya fi muhimmanci. Kuma ba za mu bari wannan damar ta wuce mu ba. Yaron nan mutumin kirki ne ga shi ɗan manyan mutane. Ya ce zuwa Laraba iyayenshi za su kawo kudi. Kuma ya ce baya son bikin ya wuce wata biyu.”

Kamar za ta yi kuka ta ce” Don Allah Baba a bar ni in karasa makarantata, na fa kusa gamawa, ni ba canja ra’ayi zan yi ba”

“To dama ai ba ke ce damuwar ba shi. Hafsat don dai kin ce ba ki san Ahmad ba, da ba ki tsaya jayayya ba”

Mayar da kallon ta ta yi kan Amarya, alamun dai tana neman agajinta, Sai ko Amaryar ta gane me Hafsat din ke nufi.

Cikin kwantar da murya ta ce “Malam a fa duba maganar yarinyar nan, tun da dai shi da kanshi ya ganta ya ce yana sonta, ko shekara ne ai ba zai canja ra’ayi ba. Saboda haka a nemi alfarmar ko jarabawa fita ne a bar ta ta zo ta rubuta. Karatun nan fa yana da rana.”

Malam Ayuba baya gardama da Amarya, bayan shirun da ya yi alamun nazari ya ce” To zan yi mishi magana in ji me zai ce tun da shi ma na G dan bokon ne”

Wani dadi ya ratsa Hafsat, a zuciyarta take addu’ar Allah Ya amince ko jarabawar ce ta zo ta rubuta idan lokaci ya yi

“Yaya Halima ta zo, ta so ganinki amma ba lokaci, Sai dai ta ce a fada miki, ban da wannan jamu’ar waccan ta sama za ki je Dawurin, mijinta zai yi aure, dn haka za ki je biki, ni kaina zan je daurin aure in Sha Allah”

“Allah Ya kai mu” cewar Hafsat, cike da mamaki wai mijin Mama Halima zai yi aure. Kai lamarin maza, ita tana mamaki namiji yana da yara manya, kuma ya ce zai yi aure.

“Ta shi ki je”

A sanyaye ta mike hade da ficewa daga dakin zuwa dakinta.

Tsaye ta yi a tsakiyar dakin bayan ta shiga, wani iri take ji, kamar ba ita ba, kamar kuma tana mafarki wai ita za a yi wa aure.

Aure dai irin wanda ta san ana yi wa mutane.

“Waye wannan Ahmad?” ta kuma tambayar kanta a karo na ba adadi.

Tana son ganinshi, ta ga waye shi? A ina ya santa?

Ta jima kwance bacci bai dauke ta, Sai can cikin dare ya dauke ta, a’a kiran sallahr asuba kuma ta tashi,l. Sallah ta yi hade da shirin zuwa makaranta.

Yau kam dole ta zauna jiran abincin safe, haka Inna Luba ta gama shauninta ta dora musu dumamen tuwo. Ɓalli daya aka sanya mata, ta ci sannan ta tafi school, dalilin da ya haddasa mata makara, don ma tana aji shidda ne da ta sha bulala.

Tana shiga ajin suka dau ihu “Amarya! Amarya!! Amarya!!!”

Su Farida kam har da makale ta, dakyar ta samu ta je wurin zamanta, Sai ko suka rufe da tsokana. Kai kawai ta kifa saman desk tana sauraron duk surutansu. Basu kyale ta ba sai da Malam ya shigo, ana yin break kuma suka kuma dorawa, a nan ne ma ta ji wai Ahmad ɗanɗan Galadima ne. Wai kuma Galadiman ne da kanshi da a aurawa ɗan nashi Hafsat. Wai tun da ya zo wajen graduation ya ganta ya yi wa yaronshi kamu.

Wannan magana sosai ta kama hankalin Hafsat ɗari bisa ɗari, saboda dai ta san ita ba ta san wani Ahmad ba, amma ta san Galadima kuma Galidiman ma ya santa.

Yau kam har aka tashi shan tsokana take yi, sai dai yaƙe kawai take yi musu, sam zuciyarta babu dadi, kuma ba za ta ce ga abin da ke yi mata rashin dadin ba.

<< Abinda Ka Shuka 43Abinda Ka Shuka 45 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×