Skip to content
Part 49 of 54 in the Series Abinda Ka Shuka by Khadija S. Moh'd (Matar J)

MK, RUMA & ALARAMMA

Alaramma dai sunayen wadanda suka yi interview ya fito, Sai dai babu sunanshi, Sai daga baya aka yi mishi cuku-cuku ya samu wani position, position din da bai kai wanda ya yi requesting a farko ba, wannan din ma sai da ya bi dare ya yi aiki sosai, sannan aka samu.

Wannan abu kuwa ba karamin ɓata mishi rai ya yi ba., shi ya sa ba tare da shawarar kowa ba, ya shirya zuwa Ɓurma, a wata makaranta, wacce ake yin karatu juma’a, Asabar da kuma Lahadi, ya sayi form ya cike inda yake neman certificate na diploma.

Don haka lecture ba ta wuce shi, tun da ya samu admission, sosai yake mayar da hankali akan abinda ake koyawa, amma Sam baya fahimta, saboda da turanci ake koya komai, ga kuma matsalar iya rubutu, bai sare ba, haka yake zuwa makarantar koda yaushe, duk da ranshi yana matukar ɓaci, wani lokaci sai ya ji me ya sa tun can baya bai yi ba. Yanzu ga shi yana ji gani, da shekarunshi yana bin hanya.

Bangaren Ruma kuma ta samu lafiya, har an kara samun wani cikin, Sai dai fatan Allah Ya raba lafiya, wannan ma kamar wancan haka Alaramma yake yo rubutu yana kawo mata, yayin da duk wani aiki na karfi ba ta yi, kuma ba ta tafiya mai nisa. Duk yadda ta so da zuwa Dawuri hakan bai samu ba, saboda jinin haihuwa na dauke mata, wani cikin ya samu, dole ta hak’ura, Sai dai waya da suke yi da Goggon nata.

Mk ma dai yanzu hankalinshi da duk wani burin shi yana a kan cikin Ruman ne, sosai yake son gani yaro a tsakaninsu yana dabdala, duk lokacin da ya ga Asma’u ta dora videon Abdallah da su Nawwara suna kiriniya sai ya ji son yaron ya kara shiga kirjinshi, Sai dai ya san kuma ya fi karfinshi, bai ƙi ba ace Asma’u ta rike yaron har a tashi duniya, tabbas zai yi farin ciki da hakan.

Yanzu ma zaune yake a falo yana shafar wayar shi, yayin da Ruma ke baccinta na al’ada.

Kamar ko wane lokaci da baya missing din status din Asma’u yanzu ma ga ni ya yi ta dora status din, kamar guda biyar.

Da gudu ya shiga budewa, na farko videon Abdallah ne da ya tashi cikin magagin bacci, Sai kuma ga shi nade cikin farin towel alamun an yi mishi wanka, Sai kuma ga shi sanye da boxer da vest, Sai videon ya kare, na biyu kuma ga shi nan ana sanya mishi uniform,, na gaba kuma hotuna ne, daya yana shirye tsab cikin uniform din, dayan Kuma yana zaune cikin mota alamun za a kai shi school, Sai kuma ga shi a cikin school din.

Duk caption din status din yana nuna ranar shi ce ta farko a zuwa makaranta.

Idanunshi ya lumshe, wannan shi ne ga koshi ga kuma kwanan yunwa, yaro lafiyayye kuma mai kama da shi, amma ya fi karfinshi, kamar ko wane lokaci haka ya koma hade da yin savings din hotunan, kafin ya mike zuwa kitchen, saboda Ruma abinci take yi Amma bacci ya dauke ta, wannan cikin mai bacci ne.

*****

HAFSAT

Monday tun misalin karfe bakwai da rabi ta shirya, saboda tun 6am Ahmad ya kira ta, wai ta shirya da wuri, kar Asad ya zo ba ta shirya ba.

Ga shi har 8am bai zo ba, yanzu ma zaune take tana game da wayarta, don bayan game din ba ta iya komai ba sai amsa kira, tun da aka sayi wayar kuma ba ta taba kira ba sai dai a kira ta, su Juwairiyya, Nabila sune suka fi kiran wayar, don Ahmad tun da ya ba ta wayar bai taba kiran ta ba sai yau, da ya ce ta shirya za a zo daukar ta.

Tajuddeen shi ne ma ya dan koya mata  mata wasu abubuwan jiya kafin ya koma Tunga wajen aikinshi.

Kuma shi ne ya sanar mata kudin wayar ya tasar ma 150k,ta ji ne kawai amma ba ta yarda ba, ta ya za a cire 150k a sayi waya.

Tana tsaka da game din ne kiran Ahmad ya shigo, duk da ba ta yi saving lambar ba saboda ba ta iya ba, hakan bai hana ta gane shi din ba ne

“Ki fita yana jiran ki” abin da ya fada kenan bayan ta daga kiran.

Milk hijab din ta da ke gefe ta dora saman riga da siket din atamfar da ke jikin

Jakar baka ta sagala mai igiya hade da baƙin takalmi, duk na Nabila ne ta sanya kasancewar takalma kala daya kawai ta zo dasu.

Dakin Mama ta shiga, ganin tana bacci, Sai ta yi saɗaf, ta fita zuwa dakin Goggo, a lokacin ita kuma mopping take yi, ganin Hafsat din ya sanya ta dakatawa. “Zan je makaranta, koda Mama ta tashi”

“To!” Goggo ta amsa cike da fara’a

Hafsat ta juya zuwa gate, zuciyarta cike da mamakin mijin Mama Halima da ya auro Goggo, a yadda ya sha boko ta ƙoshi, ba ta taba tunanin zai kalli Goggo da sunan so ba, bare har ya kai ga aure. Kai maza wani lokaci harawa ba ta kayar dasu sai yaryadi.

Duk da dai Goggon tana da kirki, haka bin Mama Halima take yi sau da kafa, har abun ba Hafsat mamaki yake yi, kamar ba kishiya ba

Da wannan tunanin ta bude gate, kai tsaye kuma ta nufi motar da Asad ya fito ya bude mata back seat

“Ina kwana?”

Ta fada lokacin da ta karaso wurin na shi.

“Lafiya kalau amarya ba kya laifi”

Murmushi ta yi cike da kunya ba tare da ta ce komai ba, shi kuma ya shiga motar, yana kara tsokanarta

Abin da ta fahimta Asad yana da faram-faram, sannan kallo daya za ka yi mishi ka fahimci yana saurin sabo

Tun daga gate din makarantar Hafsat ke kare mata kallo, har zuwa lokacin da suka shiga ciki, duk daliban suna aji, idan ka dauke kalilan da suke yawo a gaban classes din su.

Karon farko uniform din su ne ya fara tafiya da ita.

Mata baƙin siket irin tummy din nan, wasu kuma su kan yi shi iya kugun amma budadde mai kama da kasan yar kantin yara, Sai farar riga long sleeve. Mata musulmai da farin hijab wanda ya tsaya kan cikinsu, Christian kuma hula. Kaf mata farin cambas ne ko cover

Maza kuma farar shirt bakin wando da baƙin cover shoe.

Yadda suke cikin tsabta ya kara burge Hafsat sosai. Haka ta yi zaune cikin motar tana kallon su, har zuwa lokacin da Asad ya fito daga office din principal ya ce ta zo.

“Good morning sir!” Hafsat ta fada cike girmamawa lokacin da ta shiga office din

“Morning, how are you?” ya amsa hade da tambayarta

“I’m fine, thank you sir”

“You’re welcome” ya yi maganar hade da nuna mata wurin zama

Gaban Asad faduwa yake yi, saboda yadda ya ga principal din da wuya idan yana jin Hausa, ga shi kuma Hafsat din da wuya idan tana jin turanci.

Ga mamakinsa duk wata tambaya da ko magana zai yi wa Hafsat din da turanci kai tsaye take amsawa, babu wani in-ina. Wannan ya sa hankalin shi ya ɗan fara kwanciya.

Hankalin na shi ya kara tashi ne lokacin da principal din ya fada mishi za su yi wa Hafsat ƴan tambayoyi a bangaren darasin lissafi, English, Math’s, Biology, physics da Kuma Chemistry Tun da ta ce science class take.

Kai ya dago yana kallon Hafsat, ita din ma shi take kallo, ya mayar da kallon na shi kan principal din yana fadin “Amma thumbprint kawai aka ce za mu yi, ban ji batun interview ba”

Zama principal din ya gyara Kafin ya ce “Yadda mu ka yi da yallaboi din shi ne, next term za ta ci gaba da karatu a nan, kuma a ka’ida muna yin interview don tantancewa, kar ka damu tambayoyin kadan ne, kuma masu sauki”

Time da principal yake wannan jawabin tuni Asad ya turawa da Ahmad sakon batun interview. Ahmad din ya yo mishi reply dai kada ya damu, ko ba ta ci ba, zasu dauke ta.

Wannan ya sa Asad ya dan rage damuwa, har ma ya amsawa principal din da ya amince.

Yanzu kam gaban Hafsat ne ya shiga faduwa jin Asad ya amince da a gwada ta. Idan ba ta amsa ba lallai akwai kunya, ba karama ba kuwa, Sai rika jin kamar ta gudu, tun ba yadda principal din ya shiga kiran Malaman ba.

Ta yi tsu! Kamar dantsakon da ruwa ya jika, shi kan shi Asad sai ya ji babu dadi, musamman yadda Hafsat din ta yi la’asar

Malamai biyar sun tasa ta gaba kamar ta yi karya an kamo ta.

Malamai biyu mata ne, na biology da kuma English, physics, Chemistry da Kuma Math duk maza ne.

Tana jin principal din na fada masu simple questions za su yi mata, daga makarantar kauye ta zo.

Yadda kuma ya fadi daga makarantar kauye ta zo, sai abun ya ɓata mata rai sosai, shi ya sa ta kuduri niyyar sha Allah sai ta kare makaranta lr kauyen nan, ko iya wadannan mutanen kawai ta canja musu tunaninsu a kan makarantar kauye.

Ba za to ba tsammani ta ji mai English ta ce

“Mention 5 part of speech you know?

” Noun, pronoun, verb, adverb and preposition “

” What is a noun? “

” Noun is name of person, place animal and things”

“example?”

“Hindatu, Nasir, Najib, Hafsat and Ahmad”

Karon farko da ta juya ta kalli Asad, Sai ya yi murmushi hade da ci gaba da videon da yake mata

“Give me 2t examples of pronoun?”

“She & He”

“Make a sentence?”

“She is sleeping, He is going to work”

“Good” cewar Malamar

“Do you know direct and indirect speech?”

“Yes!” Hafsat ta amsa

“Give me one  example of each one?”

“Ahmad is my friend” said our  teacher(direct)Hafsat said that Nasir was her choice “

Ido Hafsat ta lumshe cike da jin dadi, jin principal ya ce a bar ta haka, fatan Allah Ya sa sauran ma ta tsallake.

“What do you understand by word of Bio?” Malamar Biology ta yi tambayar

“Bio means life”

“And logy?”

“Means study” Hafsat ta amsa, saboda wannan din ma waka suka mayar da shi.

“What is Biology?”

“Is the study of all living things and non living things. So biology is the study of life”

Kai malamar ta jinjina alamar gamsuwa kafin ta ce

“What are the characteristics of living things”

“Respiration, Movement, growth, irritability, reproduction…” shiru ta yi alamar ta kakare, wannan ya sa Malamar ta tafi next question

“What are the examples of living things and non living things”

“Animals and plant are living, stone, chalk, table and chairs are non living things”

“What are the reasons make plants as a living things?”

“Because plant can grow, can reproduce…” sai ta kuma yin shiru.

“What are the five scientific method you know?”

“Observation, analysis, data, interference…”

Sai ta kuma yin shiru, wannan ya sa aka mika ragamar tambayoyin ga malamin Chemistry

Haka Shi ma ya rika jefo tambayoyin Hafsat na cafewa, yayin da Asad ke ta daukar ta video cike da mamaki yarinya kamar wannan a makarantar kauye, amma sai kai, ina ga a makaranta mai kyau ta kudi ta tashi. Yadda take amsa tambayoyi ba karamin burge shi ta yi ba. Shi ya sa ana gama interview ya turawa Ahmad video.

Hafsat da har lokacin take dariya, jakar ta karba hade da gangarawa zuwa inda shanun suke. Ahmad kuma ya biyo ta, yana yi yana waigen Tukuro.

Yayin da zuciyarsa ke ta mamakin abun, kowa da baiwar da Allah Ya yi mishi, amma shi kam ba ya son irin wannan. Ba a wasa da rayuwa.

Kusan a tare suka sauka daga saman dutsen, shi ya sa suka tsaya a jere.

Fuskarta ya leka da take ta faman boyewa, lekawar tashi ya sa ta saki dariyar da take boyewa, wannan ya sa saka hannayenta biyu hade da rufe fuskarta.

Siririyar dariya ya yi kafin ya ce “Ni fa ba rago ba ne, kawai dai ba na son wasa da rayuwa, amma ke kin san zan iya zubar da katti goma kamar Tukur”

Sautin dariyar tata ya kara fita, ganin yadda yake kokarin kare kanshi. Shi ma dariyar ya yi, sosai yake cikin nishadin abin da ya faru din.

Ya kuma san ta samu abun tsokana, kila sai ya yi wani abun jarumtar zai rage mishi wannan abun da ya yi.

Dakyar ta samu damar tsayar da dariya, kafin ta kira sunan wata Saniyar.

Bai yi tsammanin Saniya ta kira ba, Sai da ya ga Saniyar ta waro kanta cikin dabbobin ta nufo su tinkis-tinkis.

Idanu ya zuba yana kallon yadda take tatsar nonon cike da ƙwarewa, bayan ta wanke kan nonon.

Kamar 10mns haka, Sai ta kuma kiran sunan wata.

A haka ta rika kiran sunayen Saniyoyin tana tatsar nono har ta cika galoon din hade da wata gora, wacce suke kada nonon a samu manshanu, yayin da Ahmad ke cike da mamaki. Idan da ace labari aka ba shi zai ce karya ne.

Galoon din ta ajiye gaban shi, kafin ta ce” kana shan man shanu? “

Kai ya cira alamar eh. Har zuwa lokacin mamaki bai sake shi ba.

Ita ma komai ba ta ce ba, ta shiga kada nonon da ke cikin gorar, yayin da Ahmad ke ta kallon ta cike da sha’awa, kasa jurewa ya yi ya ce” Kawo in kada ni ma”

Ba musu ta mika mishi, ya shiga yin kamar yadda ya ga tana yi, Hafsat dai kokarin kunshe dariyarta kawai take yi. Shi da kanshi ya mika mata.

Bayan ta karba, bude gorar ta yi hade da lekawa, har man ya ya tattaru waje daya.

Gorar ta ajiye tana fadin ina zuwa.

Ya bi bayan ta da kallo har ta haye saman dutsen. Ta sakko hannunta rike da koko.

Nonon cikin gorar ta juye a ciki, sai ga manshanun dunkule-dunkule ya taso

Dukawa Ahmad ya yi yana kallo, wannan ya sa numfashinshi ya rika haduwa saboda kusancin da suka samu.

Wani abu ya rika yi wa Hafsat yawo a jiki, dalilin da ya sanyata mikewa tsaye, duk da ba ta gama tattara manshanun ba

“Ikon Allah! Dama haka ake fitar da manshanu?” Ya yi tambayar lokaci daya kuma yana tattaɓawa

Sai kuma ya mike yana fadin “Duk waye ya koya miki wannan? Ya aka yi shanun nan suka san sunansu?”

Lokacin da yake fadan Hafsat hankalinta yana a kan wasu raguna da suke fada, don haka kafin ta ba shi amsa ta kuma ba shi wani mamakin, saboda cikin daga murya ta ce “Commander!” take ragon ya dakata daga shirin kai dukan da yake yi wa dan’uwanshi yana kallon ta.

Hannunta daya ta bude a kanshi alamun dakuwa sannan ta dora da “Zo nan”

“Ka zo na ce” ta kuma fada ganin yana ta kallon ta.

Sai ga ragon ya tako zuwa inda take tsaye. Da hannu ta rike dogon kunnen shi ta ce “Ba an ce ka daina fada ba, shi ne ba za ka bari ba?”

Kan ragon a kasa bai dago ba”Wuce ka tafi”ta yi maganar hade da sakin kunnen. Ya wuce tinkis-tinkis

“Yaya Tukuro” ta kira shi

Ya amsa daga saman dutsen yana fadin “Miɗonwara Hafsat” rufe bakin nashi ya yi daidai da fara gangarowarshi daga saman dutsen.

Tare suka jera su ukun zuwa bakin hanyar da za ta sada sa ruga, inda Ahmad ya Parker motarshi, a duk tafiyar tasu Ahmad ya fi mayar da hankali ne a kan duk abubuwan al’ajabin da ya gani. Hafsat dai murmushi ne nata, surutun duk da Tukuro suke yin shi. “

*****

RUMASA’U

Ranar Litinin Alaramma ya kwaso duk wanda ya kamata zuwa duba Ruma, shi kuma ya wuce interview a zonal office

Ya dauka samun takardar haihuwa da kuma primary certificate gami da na secondary shi ne interview, Sai da ya isa wurin, ya rika cin karon da mutanen da kallo ɗaya za ka yi musu ka fahimci sun sha boko sun koshi, har da wadanda ko Hausa bassa ji. Sai duk gwiwarshi ta yi sanyi.

Bai ƙara yankewa da al’amarin ba, Sai da ya shiga ciki, ya ci karo da mutanen da kwarjininsu ya sanya shi daburcewa, ya ji kamar ya koma baya ya ce ya fasa.

Haka nan ya daure ya shiga ya zauna, Sai ya rasa me zai ce kuma, har sai da daya daga cikinsu ya ce “You don’t know how to greet people?”

Kara daburcewa ya yi, ya shiga raba idanu a tsakaninsu.

Sai kawai daya ya karbi takardun hannunshi ya duba, suka dan yi mishi tambayoyi, duk kam babu wacce ya amsa, saboda da turanci suka yi mishi. Shi ko idan ban da Yes, go, no, what is your name? Come. Ba ya jin yana jin wani abu.

Haka ya fito jiki ba ƙwari, tun daga lokacin ya fahimci akwai bukatar tafiya da zamani, muddin hakan bai sabawa addini ba. Yau kam ji yake duk ya muzanta.

Fatanshi Kar ya rasa damar, saboda shi da kanshi ya fahimci akwai wadanda suka fi shi cancanta. Amma zai yi aiki a kan hakan, Sai ya nuna musu Alkur’ani ya fi karfin wasa. Kuma sha Allah da zarar ya samu aikin, zai yi kokarin shiga makaranta shi ma ta yadda zai iya gogayya da kowa, ta ko wane fanni.

Ya fahimci hada biyun sai ya fi yi wa mutane kwarjini, fiye da ace a bangare daya yake.

Da wannan tunanin ya wuce gidan Ruma ya ɗauki su Yaya zuwa gida.

<< Abinda Ka Shuka 48Abinda Ka Shuka 50 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.