Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Abnur by Maimoona Abdallah

Bismillahi ar-rahmani ar-raheem

Hasken farin watan da ya haske illarin garin shi yake bata daman ganin inda take sanya ƙafafuwanta. Gaba ɗaya ba ta cikin hayyacinta, tafiya kawai take yi ba tare da tasan inda ta nufa ba.

Tafin hannunta ta sanya ta share hawayen da ya zubo mata a karo na ba adadi she really wish all dis was a dream cigaba da tafiyan kawai takeyi a ƙauyen da ko sunansa ma bata saniba Ita dai kawai burinta tayi nesa da inda ta fito. 

A daidai kofar wani gida ta ja ta tsaya saboda batajin xata iya cigaba da tafiyan saboda galabaitan da take sake yi rabonta da abinci tun breakfast shima ba wani sosai taci ba gashi a yanda xata ƙiyasta saboda yanayin shirun garin da kuma duhun dare aƙalla ƙarfe 11:00 zai iya yi.

Guri ta samu ta zauna a ɗan dakalin dayake ƙofar gidan tare da kifa kanta tana cigaba da kukan da har takejin zuciyarta kamar ba’a jikinta yakeba batasan iya lokacin data share a zaune a wajen ba kawai dai taji idanunta na lumshewa alamar bacci takeji.

Miƙewa tayi a hankali akan dakalin tana jin zuciyarta na mata zafi batason tuno abinda ya rabo ta da gida a cikin wannan tunanin bacci ɓarawo yy nasaran fizgarta duk da ba ɗaɗin baccin takejiba sam 

Sanyin asuba tare da kiraye kirayen sallah a masallatan da suke ƙauyen yasata ɓuɗe idanunta a hankali waɗanɗa suka kumbura Sukayi jajir saboda tsananin kukan ta sha zaunawa tayi akan dakalin tana jin duk jikinta na mata wani irin ciwo ta shiga ƙare ma ƙauyen kallo tanason tuno inda take dafe kanta da ke tsananin ciwo tayi tana jingina da bango wasu hawaye Masu ɗumi suka sake gangaro mata. 

Hannunta tasa da sauri da kare fuskarta saboda hasken fitilar daya haske mata fuska. 

“Subhanallahi mutum ko aljan” mutumin ya tambaya da alamar tsoro a tare dashi yana tsaye daga ƙofar gidan da take zaune kasa cewa komai tayi sai hawayenta da ya ƙara ƙarfin gudu juyawa mutumin yy da sauri ya koma cikin gidan sai gashi ya ƙara fitowa tare da wani ɗan saurayi da alama shima alwala yayi na tafiya masallacin. 

“Kaganta nan wlhy nidai har na tsorata” tsohon ya faɗa yana nunama saurayin ita da alama ɗansa ne ƙarasowa kusa da ita yy ya tsaya ɗan nesa kaɗan da ita yana faɗin ” baiwar Allah ” ɗago kanta tayi a hankali tana kallonsa hawayen idanunta na cigaba da kwarara tsura mata ido kawai yy sai kuma ya juya ya kalli babannasa yace “baba ko xata shiga ciki kafin mu dawo daga masallaci lokaci na ƙurewa “wani kallo babannasa yy masa yana nuna ta yace “ta shiga ina wai, kasan wacece ita xakace ta shiga ciki “miƙewa yy yana sake kallonta sai kuma kawai yy wucewarsa baban ma ya bisa a baya suka nufi masallaci. 

Har aka idar da Sallah gari ya soma haske tukun suka nufo gida tun daga nesa suka hangota still tananan zaune inda suka barta baba ya kalli kamal yace “anya wannan yarinyar mutum ce kuwa “murmushi kamal yy yace muƙarasa mugani “daidai kusa da ita ya durƙusa ya sake cewa “baiwar Allah” a karo na uku sannan ta ɗago kai ta kallesa murmushi yy mata yace “me ya sameki haka kike zaune anan da alama ma anan kika kwana ki faɗa min ko akwai taimakon da xan iya baki “nan ma shiru tayi ta sake miyar da kanta shiru yy kamar mai tunani sai kuma yace to ki tashi mu shiga ciki kiyi sallah nasan bakiyi ba ko kallonsa kawai takeyi kamar statue sai da ya sake maimaita abinda ya faɗa tukun ta miƙe a hankali jiri na ɗibarta saboda gaskiya tana buƙatar tayi sallolin da ake bin ta. 

Kallonta yy tayi saboda baiga alaman yar ƙauyen bace ko duba da irin suturar da ke jikinta kaɗai to itakuwa me ya kawota ƙauyennan haka har suka shiga ciki ta tsaya a zaure tana raba ido baba da tunda yaga kamal ya tsaya wajenta ya shige cikin gida ya samu a tsakar gida zauren ya nuna masa yace “wannan yarinyar baba nace ta shigo ko xatayi sallah “saída baba yy shiru sai kuma yace “kamal mutum fah yanxu abin tsorone kuma kwata kwata batayi kamar yar nan ba bawai bana son taimaka mata bane” kamal yy murmushi yana komawa zauren tare da faɗin “karka damu baba banji ajikina mai cutarwa ce kuma mu ai dan Allah mukayi da kyakkyawar nufi idan ma ta cucemu Allah baxai barta ba. 

A zauren ya sameta a rakuɓe yace baiwar Allah shigo yayi gaba tana binsa a baya har ƙofar ɗakin mahaifiyarsa sallama yy ta amsa sannan ya shiga itama ta bishi a zaune suka tarar da ita har lokacin akan abin sallan ta gaisheta yy ta amsa da fara’a tana kallon baƙuwar sai kuma tace ” kamal wannan Fah a Ina ka samo ta” murmushi yy yana miƙewa yace” to muma dai a ƙofar gida muka ganta da alama ma anan ta kwana kuma taƙi magana shine nace mata ta shigo ko xatayi sallah” kallonta kawai umma takeyi sai kuma tace “to badamuwa bari tayi sallan idan mun karya sai muji daga ina take haka dan sam batayi kalar yan ƙauyennan ba” yauwa umma kamal ya faɗa yana ficewa daga ɗakin dan tafiya gona tare da baba dake jiransa a waje. 

Abuja, Nigeria

A haukace yake sauƙowa daga matakalan da yake haɗesu uku uku hurhuɗu hankalinsa a matuƙar tashe ƙofa ya nufa da azama yana sake dialling din number a wayarsa ɗaya daga cikin securities ɗinsa ne ya ƙaraso da sauri yana faɗin “morning sir” wani kallo da yy masa ya sashi shiga hankalinsa ya sake faɗin “sorry sir” juyowa yy gabaki ɗaya yana kallonsa yace “ina take” a tsorace guard ɗin yace “sorry sir we have tried our level best but still we are not able to reach to her” cakumo wuyansa yy a zafafe Yana faɗin “what the heck do you mean baku ganta ba wata sani ,ina xata je she has no one but me so na baku nan da awa ɗaya ku nemo min NOOR duk inda ta shiga a garin Abuja” hankaɗasa yy baya tare da sake faɗin “sorry sir” sake kallonsa yy sannan yace “don’t u dare, keep ur fucking sorry to yourself, just make sure lokacin da na baku kundawo min da noor gidannan “sai kuma ya juya a fusace ya nufi motarsa ya fice a gidan a guje. 

To ABNUR has just started the story is yet to begin.

Maimoona

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×