Skip to content
Part 1 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

Coffee dinta take hadawa hankalinta a kwance tana kallon NTA don tana son shirin da MTN suke yi na tabo rayuwar mutane.

Yarinyar data fi burgeta “Yusra fari” ta karbe show din da fadin.

“Yau mun samu wata wasika ne da tai matukar bamu mamaki ta kuma taba zuciyarmu. Bamu taba cin karo da abin mamaki ba irin wannan.”

Hankalinta sofi ta mayar kan t.v din tana cakuda coffee dinta da cokali. Aka soma karanta wasikar kamar haka:

Neman Moh da Gaggawa

Kai babana ne!!!

Ban san abubuwa da yawa ba akan ka. Nadai san sunanka Fu’ad. Kuma kai dan wasan kwallon kafa ne sai dai bansan ko wanne club ba.

Sannan da jimawa kana sha’awar wasannin mota na stunts. Mutane suna kiran ka Moh.

An gaya mun bakasan dani ba. Ance mun zan fahimta wata rana.

Ni nawa mai sauki ne.

Wannan shine: Shekarata goma sha biyu. Mutuwa zan.

Nasan mamata ba zata taba jin dadi ba. Ina so inganka kamun in mutu.

Wata rana zata gane. Har yanzun tana sonka sosai.

Moh idan ka karanta wannan dan Allah ka dawo. Ba ma saika zama babana ba. Ba sai kace kana so na ba ko kabani hakuri.

Kawai kazo kaganni.

Ina jira amman bani da lokaci sosai.

Nana

*****

Ana gama karanto wasikar mug din coffeen dake hannunta ya subuce ya fadi ya ko tarwatse ko ina na kitchen din.

“Nanaaaa!”

Sofi ta kwala mata kira cikin tashin hankali.

Ji tayi kafafunta basu da kwarin daukarta.

Tsugunnawa tai ta jingina da locker din kitchen din tana maida numfashi.

“Ya Allah! Me Nana ta je ta yi ne?”

Ta furta a fili.

“Mumy!”

Ta juya ta sauke idanuwanta cikin na Nana data kira sunanta da yanayin tambaya da shakku.

Kallonta ta ke sosai. Jeans ne a jikinta blue sai riga itama blue mai haske. Kanta sanye da hular data lillibe askakken kanta.

Duk da ramar da ta yi sosai. Bai hana kyawun nan nata fitowa ba. Hawayen dake cike da idanuwan ta ya zubo.

Lokaci daya sofi taji zuciyarta ta karye. Hannu ta mika ma Nana alamar ta je.

A hankali ta karasa ta rike hannunta sannan ta zauna kusa da ita.

“Nana zaki bata kayanki. Tashi kigani na zubda coffee a wajen.”

Kaman bata ji mai tace ba ma ta riko hannunta.

“Mumy kiyi hakuri. Kawai ina so ingan shi ne ko sau daya.”

Sauke ajiyar zuciya Sofi tai tana kokarin tarbe hawayen dake zubo mata.

Ta ina zata fara ce ma Nana tun wata biyu da haihuwarta tai kokarin nemo Moh amman a banza.

Ta gaji ta hakura. Haka ma da yanzun shi ne karshen zatonta akan samun saukin Nana din.

Bata san duniyar da yake ba. Bakuma tasan inda zata nemo shi ba. Haka ta yanda zata soma gaya ma Nana.

“Nana bana son ki daga zatonki akan nemo shi ne. Karkizo ba a ganshi ba.”

Hawayenta Nana ta goge sannan tai mata wannan murmushin da ke siye zuciyar mutane.

“Ko ba a ganshi ba. Bazanji kaman banyi kokarin nemo shi ba.”

Murmushin sofi ta mayar mata hadi da fadin.

“Badai naso ki kwallafa rai. Oya tashi daga cikin coffee din nan. Ki wuce ki sake kaya ki kwanta.”

Babu musu Nana ta mike. Matsawa tai sosai kusa da Sofi ta manna mata sumba a kunci hadi da fadin.

“I love you mumy.”

Mayar mata da sumbar ta yi ta ce,

“I love you too princess. Maza ki wuce.”

Har nana tazo fita daga kitchen din Sofi ta kirata da cewar.

“Ya akai kika kai gidan TV?”

Wani murmushi tai ta ce,

“Mumy a school ne fa muke maganar da fa’iza shine ta ce mun muje gidan radio can ake kai cigiyar mutum.”

Shine na rubuta a takarda da aka tashi bamu tsaya lesson ba muka je.

Suka hana mu shiga ma. Saida inata kuka ne wani mutum yazo ya tambaya na ce ina neman babana ne kuma ni mutuwa zan yi.

Inaso ingan shi. Shi ne fa yaje damu har ciki ya biya kudi muka bayar da wasikar.

Wallahi mumy bance su sa a TV ba.”

Tunda ta fara bayanin Sofi kallonta kawai take. Tama rasa me za tace dan haka ta daga mata kai kawai.

Kallonta take harta bar kitchen din. Sai lokacin tabar hawayen da take kokarin tarbewa suka zubo.

Tana jin muryar Fu’ad cikin kanta tamkar yanzun abin ya faru.

“I don’t do happily ever after. Daga randa ki ka yarda da soyayyata ya kamata kisan banyi kalar wanda zai dinga zarya da yara da pampers ba.

Ban kama da wanda zai asarar lokaci da soyayyar shi akan yara ba. Ina da su Haneef. Ina da su Pha’iza. A duk sanda naji marmarin ganin yara zanje gidansu inga nasu.”

Mikewa Sofi tayi ta dauki wayarta ta kira Ansar kamun tunani ya haye mata bugu daya ya daga.

“Sofi lafiya dai ko?”

Shine tambayar farko da Ansar yai mata da wata damuwa a muryarshi.

“Nana tana lafiya. Tana dakinta…”

Ta amsa shi. Jin yanda ya sauke numfashi yasa ta murmushi.

Ansar kenan badon ita ta haifi Nana ba saita rantse ya fita sonta.

Jin yayi shiru ta ce.

“Ansar Nana ta ballo aiki.”

Cike da damuwa ya ce,

“Me ta yi?”

Cikin nutsuwa ta soma bashi labari iya abinda tasani.

“Good. Ni banma san yanda akai wannan tunanin bai zo mun ba.”

Ansar din ya fadi.

“Ni fa bana jin za a ganshi Ansar. Bana son Nana ta saka ranta akan abinda ba zai taba yiwuwa ba. Nafi so ta samu duk wani farin ciki dazan iya bata kamun ta…”

Katse ta Ansar yai da fadin.

“No sofi. Please No karki karasa. Za a ganshi and he is going to be a match.”

Dafe kai tayi dan ya soma mata ciwo da yanayin tunanin data cika shi dashi.

“Zamuyi magana anjima dai.”

Ta fadi muryarta a gajiye. Sallama sukai da Ansar din ta fita daga kitchen din zuwa bedroom dinta.

*****

Tana shigowa office ringing din wayarta yai mata maraba. Kamun ta karasa inda wayar take harta yanke.

Ta dauka ta duba. Missed calls har biyar. Ta bude ta lumshe idanuwanta ganin Jabir ne. A ranta tana fatan Allah dai ya sa lafiya.

Tana shirin kira kenan. Ya sake kiranta ta dauka da fadin,

“Honey J…”

Kaman yanda take kiranshi. Muryarshi dauke da yanayi na bacin rai ya ce,

“Sai yanzun ki ka ga damar daukar wayar kenan?”

Glass din dake manne a fuskarta ta cire ta ajiye kan table sannan ta ce,

“Wallahi wayar na bari a office munata fama da marassa lafiya.”

Tanajin yanda yake jan numfashi ta cikin wayar. Tasan halin shi sarai. Ranshi a bace yake.

“Idan kina da lokacin mu kizo gida. Ikram bata da lafiya, aka mun waya na je na daukota a school.”

Cikin damuwa ta ce,

“Ya Salam aida ka kawomun ita nan asibitin mana Honey J kasan…”

Katse ta Jabir yai da fadin,

“Idan ba zaki dawo ba Jana ki fadamun kawai. Insan yanda zan da yarinyata.”

Shiru tai hakan yasa jabir kashe wayarshi. Ta sauke wayar daga kunnenta hadi da maida numfashi.

Sai da ta kira Dr. Farida ta fada mata zata je gida akwai wani abu daya taso ko da an nemeta sannan ta dauki duk abinda take bukata ta fita.

*****

Da sallama ta shiga. Ba kowa a falon dan haka ta taka zuwa dakin baccin su. Nan ma da sallamarta ta shiga. Bataga kowa ba.

Jakarta ta ajiye. Ta cire lab suit din dake jikinta ta rataye sannan ta fita zuwa bangaren yara.

Saida ta tura kofar sannan tai sallama. Yana zaune gefen gadon Ikram yana danna wayarshi.

“Honey J…”

Hannu ya daga mata tare da fadin.

“Shhhhh…….”

A hankali. Shirun tai ta karasa inda yake. Ikram tana kwance da alama bacci take.

Tashi Jabir yai ya nufi hanyar kofa ya bude ya wuce. Jana ta sauke wani wahaltaccen numfashi.

Sam sam bata son rikici. Ciwon kai ya ke saka mata. Ta kuma kula yau Jabir rikice ne fal a cikin shi.

Taba jikin Ikram ta yi taji shi zafi rau. Musamman kanta. Ta kula da wata leda da take gefe.

Ta dauka ta duba. Magunguna ne da katin asibiti. Da alama Jabir asibiti ya kai Ikram.

Gyara mata lulluba tai sannan ta fita daga dakin ta samu Jabir a dakinsu a tsaye.

Karasawa tai inda yake. Ta dora hannunta akan kafadarshi tana kallon idanuwanshi da suke cike da rigima.

“Da kinyi zamanki ma. Na riga da na kaita asibiti.”

Hannunta tasa ta shafi fuskarshi. Yana wani kauda idanuwanshi daga cikin nata.

“Sai da nai handing over ne fa na taho. Ya jikin nata?”

Hannuwanta ya cire cak daga jikin shi ya wuce ya zauna. Bata dai gaji ba. Dole ta lallaba shi.

Dan haka ta bishi kan gadon ta zauna gefe.

Hannunta ta dora kan cikinshi.

“Kaci abinci?”

Ta bukata. Muryarshi a dake ya ce,

“Karki samu damuwa. Indai patients dinki sun samu yanda suke so. Meye matsalarki damu?”

Da gaske yau Jabir rikici yake ji. Tashi tai ta shiga toilet dan ta watsa ruwa. Inya gama fushin sunyi magana.

Jabir gyara kwanciyarshi yai kan gadon. Jana ta gama kai shi bango tana daukar rigimar nan karama ce.

Tazo tana wani lallabashi da soyayyarta din nan zata wargaza mishi plan.

Europe

20 Feberuary 2017

Kwance ya ke abinshi yanayin yammacin ya saukar mishi da kasala. Yau bayajin zuwa ko ina.

Sunyi da Logan za su fita sai dai baya jin zai iya zuwa ko ina.

Wayarshi ya ji tana ruri ya dauko ta gefenshi ya daga. Logan ne.

“Hello logan. I am sorry…”

Kamun ya karasa Logan ya katse shi da fadin,

“You are not in the mood huh?”

Dafe kai yayi. Yanajin logan ya kashe wayar. Ya ajiye ta gefe.

A tsawon shekarun nan Logan ne kadai abokin da ya rage mishi.

Yana da abokai amman a gaisane kawai sama sama. Saboda babu wanda zai iya jure halayyar shi.

Shi da kanshi da ya samu dama daya guje ma halayyarshi. A da can ma mutum biyu da ko da wasa bazai bar tunaninshi ya kai gare su bane suke jure ma halayyarshi.

Wayarshi ta sake daukar kara. Dauka yai ya duba. Mamaki bayyane a fuskarshi.

Number din Nigeria ne. Yasan ba mamanshi bama daya daga cikin yan gidansu bane tunda yana da number dinsu.

Banda mamanshi ba da kowa ya ke magana ba. Yanda basa kiranshi haka shima baya kiransu.

Shekaru goma sha daya da dori yake rayuwarshi lafiya kalau. Batare da kulawar daya daga cikinsu ba.

Yana kallo har tai ringing ta tsinke. Ta sake daukar wani rurin. Dagawa yai da alamar takura a muryarshi, ya ce,

“Hello!”

Shiru akai na dan wani lokaci kamun ace.

“Fu’ad!”

Wata irin dokawa zuciyarshi tai da saida ya tashi zaune.  Shekaru goma sha daya. Muryarshi na nan daram. Kuma zai gane ta a duk inda ya ji ta.

Lokaci daya komai ya soma mishi yawo a idanuwanshi kamar a lokacin ya ke faruwa.

12 February 2006

“It is my life saboda me kowa zai kasa fahimtata.”

Fu’ad ya ke fadi cikin hargowa.

Girgiza kai Lukman yake yi cikin ganin wauta da rashin hankalin abinda Fu’ad din ya aikata.

“Wallahi duk yanda kake fadar rashin son haihuwa ban taba kawo wa yai kamari haka ba Fu’ad. Ban kuma taba zaton cewa a zamanmu zaka yanke hukunci irin haka ba tare daka shawarce ni ba.”

Saima kaji abinda na sake yi za kai mamaki tunda rayuwa tace bata wani ba. Fadar Fu’ad din cikin ranshi a fili kuma ya ce,

“Na saki Sofi!”

Lukman bai san sanda ya dauke Fu’ad da wani irin mari ba. Fuskarshi dauke da wani yanayi daya girmi tsana da kyamata ya ce,

“Fu’ad anya baka haukace ba? Ko dai makiya sun maka asiri? Na dauka akan auren Sofi kawai Allah ya gama jarabtarka. Na dauka ka gama girbar mugayen halayenka.”

Wata irin dariyar takaici Fu’ad yai hadi da fadin.

“Zan bar muku kasar gabaki daya. I have set her free. Ta auri wanda zai iya bata yara. Kaima bankwana nazo inyi maka.”

20 February 2017

“Fu’ad!”

Kiran da Lukman yai masa da alamar yana son tabbatarwa ko shi din ne ya dawo dashi hayyacinsa.

Ji yai makoshin shi ya bushe kaman wanda yai kwanaki bai sha ruwa ba.

Da kyar ya tattaro wani yawu ya hadiye sannan ya ce,

“Lukman!”

Wani numfashi Lukman ya ja da saida Fu’ad ya ji shi ta cikin wayar kamun ya ce,

“Ka tattara ko me kake yi ka ajiye shi. Ka biyo first jirgin daka samu available zuwa gida.”

Shekaru sha daya wannan ne maganar farko da Lukman zai gaya masa. Cikin rashin fahimta, ya ce.

“Meke faruwa Lukman? Bangane ba.”

“Wallahi za kai kuskuren daya fi na barin Sofi inhar baka dawo ba.”

Bai jira amsar shi ba ya kashe wayar.

Cikin tashin hankali Fu’ad ya sake dialing amman a kashe kaman ba yanzun suka gama magana ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.8 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Akan So 2 >>

4 thoughts on “Akan So 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×