Fu’ad ne ya yi kanta. Zama ya yi ya kamata yana jijjigawa.
"Sofi. No please. Sofi ki tashi..."
Gaba ɗaya ya wani gigice. Momma ce kawai ta ƙarasa kusa da shi. Ta janyo Sofi jikinta ta ce,
"Fa'iza miƙo min ruwa ga shi can..."
Jiki babu ƙwari Fa'iza ta miƙo mata ruwan. Zubawa ta ɗan yi a hannunta ta murza sannan ta shafa wa Sofi a fuska har sau biyu.
Fu’ad kam ya tattara gaba ɗaya hankalin shi ya mayar kanta.
Wani dogon numfashi ta ja ta buɗe idanuwanta a firgice. Janye. . .