Skip to content
Part 3 of 48 in the Series Akan So by Lubna Sufyan

19 February 2017

Farar suit ɗinta ta ɗora a saman kayan jikinta sannan ta sanya ƙaramin hijab, shi ma fari. Ta yi matuƙar kyau. Ta ɗauki ƙatuwar jakarta sannan ta manna glass fari mai ratsin zaiba.

“Honey J, za mu fita tare ne?” Ta buƙata.

Tun jiya yake sha mata ƙamshi. Ta yi lallashin duniya amma ya ƙi kula ta. Yau ma da ta tashi ta gama haɗa komai. Ta bar Atika ta ƙarasa shirya mata Umar don Yasir ya iya komai da kanshi. Bai jira ta ba, ya yi breakfast ɗin shi. Gaisuwarta ma da ƙyar ya amsa. Idanuwansa da suke dagula mata lissafi ya kafa mata.

A daburce tace;

“Alright, bari na wuce kawai maybe….”

Katseta ya yi da faɗin;

“Jana, wato rayuwar wasu ta fi miki muhimmanci akan tamu ko?”

Ta lumshe idanuwanta ta buɗesu sannan tace;

“Na ɗauka mun gama maganar nan fa.”

Saukowa ya yi daga kan gadon ya zo inda take ya tsaya suka fuskanci juna. Idanuwansa ta kalla sosai, yau ma rikici yake ji. Ita kam ba za ta biye masa ba. Juyawa ta yi da niyyar tafiya ya janyo hannunta tare da faɗin;

“Jana kina da hankali kuwa?”

Zuciyarta ke wani irin dokawa duk da hakan ba baƙon abu bane in har jikinsu zai haɗu ita da shi.

“Ikram ce kwance a ɗaki.”

Ya furta a dake. Sai da ta haɗiye miyau, don bakinta ya bushe sannan tace masa;

“Na yi mata komai da take buƙata, bacci ma take and Honey J, Ikram ba ƙaramar yarinya bace, ɗan ƙaramin zazzaɓi duk ka wani damu.” Kallon da yake mata ya sa ta yin shiru. Har wani huci yake yi, muryarsa da ƙyar take fita yace;

“Ƙaramin zazzaɓi? Jana kin daina damuwa da mu ko? Aikinki ya fi miki muhimmanci ko? Good!”

Kafin ta ce wani abu ya fice ya bugo ƙofar da ƙarfi. Wasu siraran hawaye suka zubo mata. Ta cire glass ɗinta ta sa hannu ta goge su.

Ji take zuciyarta duk ba ta mata daɗi. Ta san yanzun haka patients na can suna ta jiranta. Fitowa ta yi zuwa falo. Ta samu Jabir zaune akan kujera. Ta zo wucewa ta kalle shi ya watsa mata wani kallo.

Har takai ƙofa ta ji Ikram ta ce mata;

“Mami, yau ma fita za ki yi?”

“Ya Allah!”

Ta furta a cikin ranta, ta buɗe baki za ta yi magana Jabir yace;

“Ikram da kin koma kin kwanta, ni zan zauna tare dake.”

“Thank you, Papa.”

Ikram ta faɗi tana wucewa. Jana ta kalli Jabir da ya ɗauke fuska yana ta ɗacin rai. Addu’a ta yi kawai sannan ta fita daga cikin gidan zuwa inda motarta take.

*****

Ƙafa ya sa ya ture table ɗin ɗakin yana faɗin “Damn it.” Wayar shi ta soma vibrating cikin aljihu. Ya ɗauko ya duba. Aina ce. Ya ɗaga tare da faɗin;

“Hello.”

Cikin sanyin muryarta da ke burge shi tace;

“Assalamu Alaikum.”

A hankali ya amsa sallamar. Ɗabi’ar Aina ce ba ta amsa hello. Ta fi gane ka yi mata sallama.

“Zan ji ya jikin Ikram ne. Na ga ba ka shigo office ba.”

Murmushi ya ƙwace masa. Zai iya karantar kunyar da take ji daga muryarta.

“Ta ji sauƙi. Aiki ya yi wa Jana yawa a office shi ne na ce zan ɗan zauna da Ikram ɗin.” Ya amsa cike da jin daɗin kulawar da ta nuna.

“Allah ya bata lafiya. Sai anjima.”

Ba ta ma jira amsarshi ba ta yanke wayar. Ya cire wayar daga kunnenshi ya zuba mata idanuwa.

Ya sani. Kallon Jana kawai na saukar mishi da kwanciyar hankali. Babu ƙarya a soyayyarta da take zuciyar shi. Abin da ya fi rikita mishi kai shine yadda yake jin matsayin Aina a zuciyarshi.

Gani yake kamar yinin da Jana take yi a wajen aiki. Shi ya bada gap ɗin shigar wata zuciyarshi.

Shi kanshi ya san a satin nan, dalilin faɗa kawai yake nema da Jana. Don hakan ne kawai zai sa ya ji kamar bai ci amanarta ba da ya bari son wata ya shigar mishi zuciya. Kwanciya ya yi, ya lumshe idanuwanshi.

*****

Kwance yake akan kujera. Kanshi na kan cinyar Zainab da ke ta danne-danne a cikin wayarshi.

“Zee sai kin cinye min caji ko?”

Lukman ya faɗi yana miƙa hannu zai karɓi wayarshi. Hannunshi Zainab ta ture tace;

“Ɗaga min cinya nima. Sai in baka wayarka.”

Gyara kwanciyarshi ma ya yi. Ta ture masa kai cikin sigar wasa.

“Maza, karya min cinya.”

Dariya ya yi.

“Ni kam kin buɗe min data, Saƙonni na ta shigowa ko?”

Dariya Zainab ta yi. Neman rigima ne kawai ya sa ta ɗaukar mishi waya. Whatsapp ɗin shi ta shiga.

“Bari na dinga karanto maka saƙonnin, sai ka faɗi reply ɗin da kake so in rubuta.”

Zaro idanuwa ya yi ya ce:

“Idan kuma baby na ce ta min n saƙo fa?  Sai kin ga sirrinmu?”

Murmushi Zainab ta yi . Tana jin daɗin yadda akwai yarda da fahimta mai ƙarfi tsakaninta da mijinta. Shekarunsu na biyar kenan da aure. Da yaronsu guda ɗaya ga na biyu nan a cikinta.

Amman kullum soyayyarsu da yarda ƙaruwa take yi. Sam ba ta da shamaki da wayar shi. Ta san Lukman ko da wata tace tana son shi sai ya faɗa mata. Tun tana kishi, har ta haƙura. Don ta san in ya tashi ƙara auren shi, ba ta isa ta hana ba. Kuma ba ɓoye mata zai yi ba.

Wani saƙo ne ya ja hankalinta. Da wani yanayi a muryarta tace;

“Dee, Fu’ad ba abokinku bane?”

Jin sunan Fu’ad a bakinta ya sa shi miƙewa babu shiri. Wayar ya karɓe daga hannunta yana faɗin

“Fu’ad?”

Da mamaki ƙarara a muryarshi. Hamza ne ya turo masa wata wasiƙa ta wata yarinya.

Daga ƙasa ya ce;

“Lukman anya wannan ba ‘yar Moh bace?”

Kanshi ya ji ya wani bala’in sarawa. Zainab ta taɓa hannunshi a tsorace ganin yadda fuskarshi take ɗauke da tashin hankali.

“Dee?  Lafiya kuwa?  Me ke faruwa?”

A iya saninta, Fu’ad wani ɓangare ne na rayuwar Lukman da ba ya so a faɗa. Ta rasa gane alaƙarsu. Ta san cewar abokinshi ne da daɗewa. Hakanma wani hotonsu ne da ta gani ta tambaya. Ko da ta buƙaci ko sanin Fu’ad ɗin na ina yanzu, ce mata ya yi ta bar maganar. Saboda bai taɓa ɓoye mata komai ba sai Fu’ad, hakan ya sa ta girmama roƙon shi. Banda yau, ba ta sake maganar ba, kamar yadda shima bai ƙara ba.

Lukman wani juyi ya ji kanshi na yi. Babu yadda za a yi ace Fu’ad na da yarinya.

Ta ina?  Ta yaya?  Wacece ita? Ya ɗauka Sofi ta bar garin da jimawa saboda ya gwada nemanta bai ganta ba. Zainab ya riƙo jikinshi ya rungumeta sosai. Riƙe shi ta yi itama. Sannan ta sumbaci gefen wuyar shi. Ta janye jikinta daga nashi tana haɗa bakinta da nashi da wani salo na ƙoƙarin mantar da shi koma menene. A hankali take aika mishi da saƙonni har sai da ta ga ya ɗan nutsu tukunna tace

“Dee, me ke faruwane wai?”

Numfashi ya sauke. A nutse yace,

“Zan faɗa miki. Right now, zan je inyi wani abu tukunna.”

Tare suka miƙe, ta rakashi har bakin ƙofa. Sai da ta sake tallabo fuskarshi ta sumbace shi sannan tace,

“Allah ya dawomin da kai lafiya. Ka kula sosai Dee.”

Kai ya ɗaga mata. Ya tsugunna ya sumbaci cikinta sannan yace,

“In shaa Allah. Ki kulamin da kanku. Zan kira ki.”

*****

Address ɗin makarantarsu Nana ya sake dubawa da Hamza ya aiko mishi da shi. Makarantar Crescent ba ta mishi wuyar ganowa ba. Kasancewar ba ta shiga lungu ba.

Kai tsaye office ɗin Principal ya wuce. Suka gaisa sannan ta tambaye shi ko ta wace hanya za ta iya taimaka mishi.

“Wata yarinya nake nema. Nana. ban san ko da wanne suna take amfani ba dai. But, anan makarantar take.” Kallon shi Principal ɗin take yi. Yanayin nutsuwarshi da kamalar shi ya sa ta cewa;

“Eh, a nan makarantar take. Amma gaskiya ka yi haƙuri. Saboda mamanta ta mana kashedin cewar kada mu bar ɗan jarida ko ɗaya ya yi magana da ita.”

Sauke numfashi Lukman ya yi, zuciyar shi na wani bugawa.

“Ba Ɗan Jarida bane ni. Abokin babanta ne. Kuma ba sai na yi magana da ita ba. Ko daga nesa ne ki taimakamin in ganta.” Sai da ta ɗauki mintina tana tauna maganar tukunna ta miƙe ta ce ya biyo ta zuwa cikin makarantar. Ƙafafuwanshi har rawa suke yi. Bai ma san kalar addu’ar da yake yi ba. Bai kuma san yanayin da yake ji ba. Ta window ɗin ajin suka tsaya. Ta ce masa ka ganta can a front sit. Kamar Nana ta san ita suke son gani, dai-dai ɗagowar fuskarta tana dariya akan wani abu da ƙawarta ta ce. Ƙafafuwanshi kasa ɗaukar shi suka yi. Bangon wajen ya dafa ya tsugunna yana karanto

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un!”

Babu adadi.

Idanuwanta. Idanuwanta sak irin na Fu’ad ne. Yanayin dariyarta.

‘Yar shi ce. Fu’ad yana da yarinya. Ko ina na jikinshi kyarma yake yi.

Wayarshi ya ɗauko. Lambobin Fu’ad da a duk tsayin shekarun nan ko saving ɗin su bai yi ba don kar tsautsayi ya sa ya gwada kira ya shiga sakawa. Don zaune suke daram cikin kanshi. Ta London ya fara gwadawa, ba ta zuwa.

Ta Europe ya saka. Bugu daya ta shiga…!

*****

Ai kam ta san ba ƙaramin taimako Allah ya yi mata ba da ta taho da Ansar. ‘Yan Jarida ne cike a bakin ƙofar makarantarsu Nana. Da ƙyar ya ture su suka shiga ciki. Ba ƙaramar godiya ta yi wa Principal ɗin ba da bata ko bari Nana ta san da zuwansu ba. Ba ta kuma nemi wani ƙarin bayani ba. Ta dai ba wa Sofi tabbacin cewar in dai babu yardarta, ba za ta ma bar kowa ya ga Nana ba. Fitowa suka yi. Cikin ‘Yan Jaridun har da Yusra Fari. Tana zaune a gefe, hakan ya sa Sofi ce wa Ansar ya ba ta mintina biyu.

Sallama ta yi mata. Cikin fara’arta ɗin nan da ke burge Sofi ta amsa suka gaisa. Ta faɗa mata ita ce mahaifiyar Nana. Yusra ta ji daɗi sosai. Don a yanzun babu labarin da ya ja hankalin mutane da social media gaba ɗaya irin na Nana.

Kowa so yake yi ya ga yarinyar.

“Da za ki taimaka mana ko da mintina biyar ne. Mu yi magana da ita, kila hakan zai taimaka wajen gano babanta. Abin ya ƙara jan hankalin mutane jin cewar baban Nana dan wasan ƙwallon kafa ne.” Cewar Yusra. Wani

murmushin takaici Sofi ta yi sannan ta amsa da cewan;

“Hakan ne ya sa ba na son Nana ta yi magana da ku. Kema don kina burgeni ne shi ya sa na yi miki magana.” Cike da tausayawa Yusra ta ce; “Nagode sosai. Ba lallai ki yarda da cewar akwai mutane da dama da ƙaunar ‘yarki ne ya sa su son ganinta ba. Ba wai son jin labarinta ba.” Jakarta Yusra ta buɗe ta ɗauko katinta tace; “Please, ki kirani idan kin canza shawara. Na gode sosai.”

Karba Sofi ta yi suka yi sallama ta koma wajen Ansar. Shi ya sauke ta a asibiti don da motarshi ma suka fito.

*****

Tun da Doctor Jana ta soma bayaninta babu inda ba ya rawa a jikin Sofi. Tama kasa tambayarta wani abu. Ansar ne ma da ke zaune ya yi ƙarfin halin cewa;

“Options nawa muke da shi Dr.?”

A nutse, Dr. Jana tace; “Option ɗaya ne kawai Ansar. Shi ne transplant idan an samu match.” Cikin rawar murya Sofi tace, “Idan ba a samu match ba fa?”

Shiru Dr. Jana ta yi. Cikin aikinta babu abinda ta fi tsana sama da wannan ɓangaren. Kallon mutane a kullum lokacin da za ka faɗa musu mutuwar wani nasu. Ko lokacin da za ka tarwatsa musu burinsu da magana ɗaya. Cikin wani ƙarfin hali Sofi ta sake cewa;

“Wata nawa muke da shi da ita in ba a samu match ba?”

Muryar Jana can ƙasa ta ce; “Rayuwa a hannun Allah take Safiyya. Zan iya cewa ƙasa da wata shida. Idan Allah ya yi ƙarfin ikon shi, shekara ɗaya.”

Miƙewa Sofi ta yi. Gaba ɗaya kanta ta ji wani abu ya yi shiru. Ba ta jin duk kiran da Ansar yake yi mata. Tafiya kawai take yi ba don tana gane inda take saka ƙafafuwanta ba, har ta fita daga asibitin. Ita kanta ba za ta ce ga yadda aka yi ta gane motar Ansar ba. Ta buɗe ne kawai ta shiga ta zauna. Gida Ansar ya sauke ta. Sai da ya tabbatar ta buɗe ta shiga tukunna ya koma office da wani nauyi a cikin zuciyarshi.

<< Akan So 2Akan So 4 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×