Fu’ad ya kaisu gida da kanshi. Nana ma bacci take, don haka ya saɓeta a kafaɗa ya kaita har ɗakin Sofi ya kwantar da ita.
Yana fitowa ya samu Sofi tsaye bakin ƙofar. Idanuwanshi ya ke yawatawa kan fuskarta ba tare da yasan abinda yake son gani akai ba. Kallon nata na nutsar da shi ta fannoni da ya ke kasa fahimta. Da duk wani abu da ke jikinshi yake son sake jin ɗuminta ko na minti biyu ne.
Baya son takura mata. Yarda da aurenshi da ta yi bayan ta san bashi da abinda zai bata. . .