Kiran da aka yi mini a waya ya sa jikina karkarwa. Na ƙurawa wayar na mujiya. Na kasa ɗagawa har ta tsinke sakamakon zuciyata da ke famar harbawa da ƙarfi tamkar za ta hudo ƙirjina ta faɗi ƙasa. A karo na barkatai kukan wayar tawa ya ci gaba da kuwwar neman ɗauki. Ina tsaka da wasiwasin amsawa ko akasin haka sautin muryar Goggo ya doki ruɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwata kalamanta suka dinga kai kawo a masarrafar jina. Hankalina ya yi matuƙar tashi take jikina ya ɗauki raɗaɗi tamkar an sheƙa mini ruwan zafi a. . .