Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Akwai Ciwo by Rasheedat Usman

Kiran da aka yi mini a waya ya sa jikina karkarwa. Na ƙurawa wayar na mujiya. Na kasa ɗagawa har ta tsinke sakamakon zuciyata da ke famar harbawa da ƙarfi tamkar za ta hudo ƙirjina ta faɗi ƙasa. A karo na barkatai kukan wayar tawa ya ci gaba da kuwwar neman ɗauki. Ina tsaka da wasiwasin amsawa ko akasin haka sautin muryar Goggo ya doki ruɗaɗɗiyar ƙwaƙwalwata kalamanta suka dinga kai kawo a masarrafar jina. Hankalina ya yi matuƙar tashi take jikina ya ɗauki raɗaɗi tamkar an sheƙa mini ruwan zafi a dukkan sassan jikina, zuciyata ta yi nauyi tamkar an danne da ƙaton dutse, lallai ne masifar da ke bin rayuwata tsakanin waɗannan kwanaki biyun ya tabbatar mini da cewa an yanka ta tashi. duk abin da ya samu Shamuwa dai ta dalilin watan bakwai ne. A zatona duk marayan da ya rasa iyayensa dangin uwa ko na uba kan zamo masa jigo su tallafi rayuwarsa ko da ba su yi tamkar yadda iyayen suke ba za su kwatanta saɓanin ni da suka zama tsanin karya alkadarin rayuwata, a sanadin riƙon sakainar kashin da kore batun naka ba koyaushe ke zama naka ba.

A karo na biyu Goggo ta kuma jefo mini da kalamanta da a iya kiran su gaskiya mai ɗaci, sai dai ina ruwa ya ƙarewa ɗan kada sai a taya shi jaje kawai.

“Laifinki ne. Ke ki ka jawowa kanki. Masifa yanzu kika fara gani! Ki ɗaga wayar munafuka.” Kaina na sunkuyar hawaye ya keto daga kwarmin idanuna na kasa ce mata komai, hannuna yana karkarwa tamkar mazari na ɗaga wayar da ke ƙara ruri. Kalaman da na ji ya sanya ni sakin wayar a firgice zuciyata ta matuƙar karaya, numfashina ya sarƙe. ina ma ace mutuwa ta zo ta ɗauke ni ko na samu salama na huta da baƙin kallon da mutanen unguwa suke mini. Ina cikin wannan yanayin na fara tariyo yanayin da ya jefa rayuwata cikin wannan baƙar masifar da na tsinci kaina a yanzu.

Gidanmu babban gida ne da gaba ɗaya ‘yan’uwan mahaifina da suke uba ɗaya suke haɗe waje guda. Sai dai kowa da sashinsa, mahaifina malam Shehu talaka ne mai ƙaramar sana’a. Ya rasu tun ina da shekara goma sha shida a duniya. Ya bar ‘ya’ya uku a hannun mahaifiyarmu. Tun da mahaifinmu ya rasu ƙuncin babu ya sa mahaifiyarmu a gaba, da ƙyar take samu ta ciyar da mu, da ‘yar ƙaramar sana’ar wanki da surfen da take yi wanda hatta kuɗin makarantar ƙannena ita ta ke biya. Ni kuwa tun da na gama secondary ban ci gaba ba kasancewar ba mu da sukuni. A kaf cikin ‘yan’uwan Babanmu zuwa na mahaifiyarmu ba wanda yake kallon mu da abin naira biyar. Kowa ya samu daga shi sai ‘ya’yansa da jikokinsa.

Haka muke ta fama da rayuwar babu, a da sana’ar mahaifiyarmu ta wanki da surfe na iya riƙe mu. Sai dai juyawar zamani da tsadar rayuwa da kuma ƙarancin kuɗi da ya karaɗe gidan kowa ya kuma cilla rayuwarmu a cikin tashin hankali. Abinci ya yi tsada kuɗi ya yi ƙarancin da rayuwar talaka ke fuskantar barazana. Koyaushe na zauna nazari nake me ya jawo wannan bala’in da muke ciki? Shin laifinmu ne ko kuma na shugabanni? Koda yake kowa na da nasa laifin idan ɓera da sata daddawa ma na da wari. Ina jin takaicin ganin abin da za mu ci yana neman ya gagare mu. Nauyi ya yi wa mahaifiyata yawa ta yadda ba ta iya ɗauke mana komai na rayuwa. Kwatsam rana tsaka mutuwa ta yi mana yankar kauna tsakaninmu da mahaifiyarmu.

Sati guda da mutuwar ta, kowa ya watse aka bar mu a ɗaki mu kaɗai da sahalewar yayan Babanmu babba zai dinga kula da mu. Sai dai ina! Ba a je ko’ina ba ya yi fatali da rayuwarmu. A matsayina ta budurwa mai buƙatar kayan ƙyale-ƙyale an bar ni da ɗawainiyar kaina da ta ƙannena, ta kai ta kawo makarantar ma sun jingine ta tun da suka kammala firamare. Baffanmu da ya ce zai riƙe mu ko abinci ba ya ba mu bare kuma a yi tunanin omo da sabulu. Mun zamo tamkar mujiya a idanun matayensu, ba mu da kataɓus a gidan sai zagi da hantara. Babu kuma wanda ya taɓa tambaya ta ina nake samo mana abinci mu ci.

Ƙawata Zainab ta so ta ɗora ni a keken ɓera ina ƙin hawa. Sai dai lokacin da miji ya fito mini ya sa na fara tunanin ta yaya zan samu kuɗin kayan ɗaki don na san daga dangin uwata har na uba babu wanda zai iya mini kayan ɗaki. Mutanen da suka kasa ciyar da ni ma sai na bi gidajen ƙawaye nake nema mana abinda za mu kai bakin salati. shawarar da Zainab ke ba ni yau da gobe ya fara shiga na zomayena, sau da yawa idan ina zaune da ƙawayena ina jin suna hirar maza sun fi son macen da aka kai ta da kayan ɗaki wai har abokansu suke gayyatowa ganin kayan ɗakin amarya. Idan kuma ba a mi ki kayan ɗaki ba an dinga zunɗen ki kenan ana miki kallon hadarin kaji. Ni kuwa ga shi gidan kishiya za a kai ni.

Wannan dalilin na son ganin na wuce rainin kishiya da abokan miji ya sa na yi tsalle na haye saman keken ɓeran da Zainab ta ɗora ni na zauna daram. Duk daren duniya sai na je dakin Audu ya yi lalata da ni ya ba ni kuɗi. Kasancewarsa matashi da ke tashen kuɗi a unguwar mu. Cikin ƙanƙanin lokaci na fara tara kuɗaɗe hakan ya sa ni ƙara ba da himma da zuwa ɗakin Audu tun da ni ina ganin kakata ta yanke saƙa.

Bansani ba ashe Hankalin mutanen unguwa ya dawo kaina, suka fara saka mini na mujiya. Ni sam ban kula da hakan ba. Kwatsam rana tsaka samarin unguwa suka kama ni a ɗakin Audu. Nan take suka rangaɗa mini ihun kwartuwa, jama’ar unguwa suka yi ca a kaina suna zagi na da Allah wadarai har kofar gidanmu suka rako ni. Na samu yayan Babanmu yana tsaye a ƙofar gida har labari ya isa kunnensa. A wajen ya taka mini birki ya ce nasan inda dare ya mini ba dai na shiga wannan gidan ba. Ina kallon ƙannena na ihu tamkar an aiko musu da saƙon mutuwa. Takaici da kunyar duniya ya sa naji tamkar na tsaga ƙasa na shiga. Ganin Baffa ya hana ni shiga gida suka yi kaina za su dake ni. Ina ji wani dattijo ya hana su yana ce musu su bar ni da duniya ma ta ishe ni. Kuka nake tamkar raina zai bar gangar jikina, na nufi gidan Gwoggo, yara na biye da ni suna mini ihu. Ita ma da ƙyar ta karɓe ni.

Kwanana uku a gidan Su ma ƙannena suka biyo ni. Fita ƙofar gida ya gagare mu muna fita sai an mana gori. Takaici da baƙincikin rayuwa ya dame ni, ba ni da wani sukuni a gidan sai kishiyoyin Gwoggo sun goranta mini abin da na aikata. Masoyina Kamilu ya daina kiran wayata. Duk da fargaba da tsoron kiransa nake saboda ban san abin da zan ji daga bakinsa ba.

Ina cikin wannan tashin hankalin sautin kiran wayar masoyina Kamilu ya daki kunnena. Na razana matuƙa da jin kalamansa a kaina. Wannan dalilin ne yayi sanadiyar sarƙewar numfashina,kuma ya jefa rayuwata cikin masifar da nake fuskanta a rayuwa. Har ya sa a yanzu na fi ƙaunar mutuwa sama da rayuwa “Meya faɗa miki?” Sautin muryar Gwoggo ta dawo da ni daga duniyar waiwayen halin da ya jefa ni cikin wannan masifar. Jikina na karkarwa na ce mata, “Kamilu ya sanar da ni ya fasa aurena, iyayensa sun ce ba su yarda ya auri karuwa ba, ko sun yarda shi ma ba zai yarda ya haɗa zuri’a da ni ba, gudun janyowa ‘ya’yansa abin gori.”

“Lallai Jidda! Kin fara ganin hisabin rayuwar ki tun a duniya.”

Hawayen idanuna na sharce ina jin takaici da baƙin cikin babu wanda ya damu da dalilin da ya jefa rayuwata duniyar zina kowa laifina yake gani. Na yi tunanin Gwoggo za ta bibiyi silar shigata cikin wannan ƙazamar rayuwar, sai dai ba ta yi hakan ba. Haka dangin mahaifiyata babu wanda ya biyo bayana domin ya ji ba’asin abin da ke faruwa da ni. Kowa gani yake son zuciyata ne ya sa na aikata hakan duk da kaso mafi yawa riƙon sakainar kashi da aka mini ne ya sa ni afkawa tafkin nadama. Tare da Zallar yunwa da ɗawainiyar kaina da aka bar ni da shi a matsayina ta mace mai raunin tunani shi ya jefa rayuwata cikin wannan masifar.

Anya kuwa bakin jama’ar unguwa zai bar ni na samu mijin aure? Na san shakka babu duk saurayin da ya zo sai sun ƙyanƙyasa masa abin da ya faru da ni. Kodayaushe laifin dangin mahaifina nake kallo domin duk su ne silar jefa ni a cikin komar danasani ta har abada, Akwai ciwo a raina da bazai taɓa gogewa ba har abada.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×