Skip to content
Part 1 of 2 in the Series Al-Mustapha by Asmau Abubakar Musa

Dare ya tsala sosai, babu sauran hayaniyar jama’a sai na dabbobin da dare ne lokacin shawagin su. Kamar yadda Bahaushe ke faɗi, ‘Dare mahutar bawa idan lokacin ka ya yi dole a tare ka, idan kazo dole komai ya samu akasi.‘ A wannan lokacin akasarin mutane sun yi nisa a cikin bacci, sai ƙalilan da wani uzurin ya hana su runtsawa, a cikin wanɗanda ba su samu damar runtsawa a wannan dare ba har da Al-Mustapha.

Yana kwance a kan tsohuwar tabarmarsa, ɗakin da ya ke ciki babu girma sosai, babu wasu tarkace a ciki illa wannan tabarma da wani ƙaramin buhu da ke ɗauke da tsirarun suturunsa, sai dai kuma ɗakin a tsabtace yake kasancewar sa mai tsabta sosai.

Yaro ne ƙaramin da shekarunsa na haihuwa za su kai goma sha ɗaya, yana da haske mai sheƙi sannan kyakkyawa ne sosai, don a lokaci guda mutum ba zai iya hasashen tsatson da ya fito ba, kamar yadda aka saba wasu lokutan daga kallo ɗaya ake iya hasasho tsatson mutum.

Hannunsa dafe da ciki yana runtse ido jin yadda hanjin cikinsa ke murɗawa tamkar za su tsinke, gefe guda kuma ga zafin dake ziyartar sa daga ƙirjinsa ta hagu. A hankali bakinsa ke motsawa yana ambaton sunan Allah tare da addu’ar Allah Ya sassauta masa wannan ciwon, don ya san ko ya nemi agaji a wannan gidan ba zai samu ba.

Cikin sa’a kuwa bayan shuɗewar wani lokaci ya ji ciwon ya fara lafawa, zufa ta fara tsattsafo masa. Hamdala ya yi tare da miƙewa zaune a hankali yana sake nazarin shawarar da ya yanke tun kafin lafawar ciwon, don ya san zai yi wuya ciwon ya ƙi sake tasowa musamman cikinsa da har yanzu yana iya jiyo sautin da yake bayarwa na tsananin buƙatar abinci.

Cike da sanɗa ya fita a ɗakin yana dafe bango saboda jirin da ke barazanar kayar da shi, kamar yadda ya yi tsammani babu kowa a tsakar gidan, don haka ya yi dabarar buɗe ƙofa ya fita a gidan ba tare da ya bada damar da za a ji motsi a ankara da shi ba.

Garin ya yi tsit babu sautin komai sai na tsuntsaye da sauran ƙananun dabbobin da ke shawagi da dare, yanayin damina da ake ciki ne yasa garin ya yi sanyi sosai saboda ruwan da aka yi sosai a wunin ranar, hasken farin wata kuwa ya mamaye ko’ina. 

Kai tsaye hanyar da za ta sada shi da gidan mahaifiyarsa ya nufa, yana tafe a hankali tamkar mai jin tausayin ƙasar da ya ke takawa. Hannayensa ya naɗe a ƙirji tare da matse su sosai jin yadda ciwon ƙirjin ke barazanar dawowa.

A haka ya cigaba da tafiya har ya iso ƙofara wani madaidaicin gida da aka yi wa ginin zamani mai ɗan kyau, tsayawa ya yi tare da ƙurawa ƙofar ido cike da tunanin yadda zai ƙwanƙwasa ƙofar kuma a ji har a zo a buɗe a wannan daren, har ya juya da niyyar komawa inda ya fito, wani sashi na zuciyarsa ya dakatar da shi tare da ba shi ƙwarin gwiwar buga ƙofar, hannu ɗaya ya ciro tare da ƙwanƙwasa ƙofar a hankali.

Da mamaki sosai yake kallon ƙofar saboda alamun da ya ji na buɗe ƙofar da ake yi, ido ware ya ke kallon fara kuma kyakkyawar bafulatanar da ta buɗe ƙofar jikinta sanye da dogon hijabi, babu alamar magagi a idonta. A hankali ya furta “Umma!”, Murmushi tayi tare da jan hannunsa suka shiga gidan, ta mayar da ƙofar ta rufe sannan ta sake kama hannunsa suka nufi wata ƙaramar baranda. 

“Sannu Baɗɗo!.” Ta furta tana miƙa masa ruwan da ta ɗebo a randar ƙasar da ke gefe, sai da ya gyara zama a kan tabarmar da ya gani shimfiɗe a wajen kafin ya karɓi kofin daga hannunta, bai sha ruwan ba ya ajiye kofin a gefe.

“Umma ba ki yi bacci ba har wannan lokacin?.” 

“Na farka ne.” Ta amsa a taƙaice sannan ta miƙe ta nufi kicin, ba jimawa ta dawo riƙe da kula da kuma kwano. Zama tayi tare da buɗe kular da fara zuba masa abin da ke ciki a kwanon, tuwon dawa ne da miyar kuɓewa ɗanya ga tsokar nama manya-manya a ciki, sai tashin ƙamshin man shanu abincin yake yi. 

“Baɗɗo! Tun safe nake zuba ido ko za ka zo amma shiru har dare, hankalina ya tashi sosai saboda na san a wahale za ka wuni a wannan gidan. Na kwanta amma zuciyata ta gaza samun sukuni, shi ya sa na farka ina nafiloli.” 

Cike da tausayawa ya sa hannu ya share mata guntun hawayen da ke ƙoƙarin sauka a kuncinta, yana son Ummansa sosai, yana so su rayu tare, kullum da safe idan ya tashi ya gan ta, haka da daddare kafin ya kwanta su yi hira. Sai dai ƙaddara tayi masa shamaki da abubuwa da dama na rayuwarsa da yake son ya gudanar tare da ita.

“Tunanin me kake yi haka Baɗɗo?” Muryarta ta katse shi daga tunanin da yake yi, murmushi ya yi mata kawai tare da buɗe baki ya karɓi abincin da tana ba shi. A hankali ta cigaba da ba shi har ya ci sosai, sai da ta ba shi ruwa kafin ta tattara kwanukan ta nufi kicin da su. 

“Yau ka sha magani?” Tambayar da tayi masa kenan bayan ta dawo ta zauna a gefen shi.

“Maganina ya ƙare tun jiya da dare.”

“Me ya sa ba ka zo ka karɓi wani ba? Ba na so kana wasa da shan maganin nan. Koda sun hana ka fita ai sai ka saci jiki ko wani yaron ka nema ka aiko shi ya karɓa.”

“Zan kiyaye Umma.”

“Yawwa, Allah ya yi maka albarka. Tashi mu je nayi maka rakiya, asuba ta gabato.”

“Zan iya komawa Umma, ki yi min addu’a kawai.”

Murmushi kawai tayi tare da shafa kansa sannan ta shige ɗaki, ba jimawa ta dawo da kwalin magani a hannunta ta ba shi.

“Ya batun alkawarin da ka yi min?.”

“Ban karya ba fa Umma, ko kaɗan bana saka damuwa a raina. Idan ba na yin komai karatu nake yi kamar yadda kika umarce ni.”

“Yaron kirki. Allah ya kula min da rayuwarka.”

“Amin Umma.”

Har ƙofar gida ta raka shi, sai da ta daina hangen shi kafin ta shige gidan tana sauke ajiyar zuciya tare da share hawayen da ya zubo mata.

Ba kamar lokacin da ya bar gida ba, wannan karon yana jin ƙarfi sosai a jikinsa sai dai ciwon da ƙirjinsa ke yi kaɗan-kaɗan.

A hankali ya maida ƙofar ya rufe bayan ya shiga, yana ƙoƙarin barin zauren zuwa cikin gida ya tsinkayo muryar mahaifinsa, cike da tsoro ya dafe kirji saboda wani sauti na dam da zuciyarsa ta bada.

“Al-Mustapha! Kar ka bari na iso ɗakin nan na riske ka, na san kana jina sarai ka yi biris.”

Shiru yayi bayan ya mannu da bangon zauren cike da fargabar abin da zai biyo baya idan mahaifinsa ya fahimci fita yayi a gida, cikin sa’a ya jiyo muryar Inna Larai na faɗin, “Malam ka bar shi sai da safe, ita ma ba ta san tayi kashin ba, yanzu idan aka katse mata bacci damun mutane za ta yi kafin ta koma.”

Shiru ya ratsa na wani lokaci kafin ya jiyo alamun kulle ƙofa, da alama mahaifinsa ya ji maganar Inna Larai ya koma. Ajiyar zuciya ya sake mai ƙarfi kafin ya lallaɓa ya shige ɗakinsa.

Hamdala ya yi tare da sakin ajiyar zuciya sannan ya ɓalli maganin ya sha, gyara makwancinsa ya yi sannan ya kwanta, ba jimawa kuwa bacci ya yi awon gaba da shi.

Kiran sallar asuba ne ya katse masa daddaɗan baccin da yake yi, _sabo da yi_, kowani irin bacci ya ke yi da zarar an kirayi sallar asuba ya ke tashi ko da kuwa bai jima da kwanciya ba. Sa’arsa guda mutanen gidan ba su tashi sai gari ya yi haske sosai, hakan ke ba shi damar gabatar da salla a nutse.

Fita tsakar gida ya yi tare da ɗaukar buta ya zaga banɗaki, yana fitowa ya ɗaura al’wala ya wuce masallacin da ke kusa sosai da gidansu.

Bai dawo gidan ba sai da gari ya ɗan yi haske don yana tsayawa a yi karatun da ake koyawa yara maza a masallacin tare da shi.

Cikin nutsuwa ya fara gabatar da ayyukan da suka wajabta a kansa a kowace safiya, gidan ya fara tsabtacewa kafin ya ja ruwa a rijiya ya cika abubuwan da suke adana ruwa a ciki. Sai da ya kammala da tsakar gidan kafin ya nufi kicin, nan ma sai da ya fara tsabtacewa kafin ya kunna wutar gawayi ya ɗora ruwan zafi. Bai bar kicin ɗin ba sai da ruwan ya tafasa ya juye a fulas ya sake maida wani. 

Bokiti ya ɗauka ya ɗebi ruwa ya nufi banɗaki, ba jimawa ya yo wanka. Shiryawa ya yi cikin kayan makarantarsa sannan ya koma kicin ɗin ya tsiyayi ruwan zafi a kofi ya sha.

Dakinsa ya koma ya sanya kayan makaranta sannan ya koma kicin din ya tsiyayi ruwan zafi a kofi ya sha.

Ganin lokaci zai ƙure ne ba su fito ba ya sa shi miƙewa don tafiya makaranta.

Alamun buɗe ƙofar da ya ke ji ne ya sa shi dakatawa, mahaifinsa ne ya fito yana mika alamun tashinsa daga bacci kenan, kauda kai ya yi daga kallon shi gudun kar ya yi laifi, ya isa kusa da ƙofar ya durƙusa ya ce, “Ina kwana Baba.”

Ido ya zurawa yaron yana kallon shi ba tare da ya amsa gaisuwar ba, wani sashi na ƙwaƙwalwarsa ke son tariyo masa wani lokaci da yake matuƙar so da ji da ɗansa Al-Mustapha, da kuma yanayin da a yanzu yake ji game da yaron tamkar ba ɗansa bane, shi dai ya san Larai ba ita ta haifi Al-Mustapha ba, haka kuma ya san bai auri wata mace kafin ita ba. Sai dai akwai abubuwa da dama tattare da yaron da duk wanda ya san su zai bada tabbacin yaron jininsa ne. Shi ma a ransa wasu lokuta ya kan ji cewa lallai Al-Mustapha jininsa ne, sai dai ya kasa samu dalilin da ya sa a duk lokacin da ya yi niyyar sauke haƙƙin yaron da ke kansa wani abu ke tasowa ya danne wannan niyyar, tare da dasa masa tsanar yaron a zuciyarsa.

Muryar Al-Mustapha ta fargar da shi kogin tunanin da ya tsunduma.

“Baba, na gama komai zan iya tafiya makaranta ko akwai wani abu da ya saura.?”

Tausayin yaron yake ji na tasowa daga ƙasan ransa, amma kamar kullum take wani abu ya fara ƙoƙarin kawar da abin da yake ji, don haka ya girgiza kai da sauri tare da sa hannu a aljihu ya zaro Naira goma ya miƙa masa yana faɗin, “Ka tafi kawai, ga wannan ka siya ƙosai.” 

Cike da mamaki Al-mustapha ya miƙa hannu ya karɓa, a tsayin rayuwarsa wannan ne karo na farko da mahaifinsa ya ɗauki kyauta ya ba shi.

“Allah ya saka da alheri.” ya faɗa, daga haka ya miƙe tare da ficewa daga gidan.

Cike da mamaki Malam Jibrin ke alwala, abin yana yi masa gizo tamkar a mafarki, yau shi ne ya cire kuɗi daga aljihunsa ya ba wa Al-Mustapha kyauta. Gefe guda kuma zuciyarsa cike take da damuwar sakaci da ibada da yake yi, ya sani wannan ba ɗabi’arsa bace sam, idan zan yi sallah gari ya yi haske haka to dama walha ce amma yanzu sallar asuba ce ya maida yin ta a wannan irin wannan lokacin.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

Al-Mustapha 2 >>

2 thoughts on “Al-Mustapha 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×