LITTAFI NA DAYA
Zaune take a gaban mudubin, jikinta sanye da doguwar riga ta material mai fari da purple mai haske a jiki. Hannunta riƙe da ɗankwali purple da take ɗaurawa akanta. Turaruka ta ɗauko kala biyu tana feshe jikinta da su. Duk da kyan da ta yi bai hana damuwa bayyana a fuskarta ba. Idan aka ce ta faɗi yadda ta yi rayuwa a wata ɗayan nan a cikin gidan Rafiq ba zata iya faɗa ba. Komai zuwa yake yana wuce mata, hannu ta sa tana dafe ƙirjinta, wajen zuciyarta da yake mata zafi kamar zai. . .
Masha Allah.
Masha Allaah
Da alama tafiyar za tai dadi kamar yadda ko wane littafi Lubnah ke da ma’ana. Allah ya kara basira amin.
Allah bamu ikon gyara halayenmu,bantaba samun novel maidadi kamansa.