Skip to content
Part 1 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

LITTAFI NA DAYA

Zaune take a gaban mudubin, jikinta sanye da doguwar riga ta material mai fari da purple mai haske a jiki. Hannunta riƙe da ɗankwali purple da take ɗaurawa akanta. Turaruka ta ɗauko kala biyu tana feshe jikinta da su. Duk da kyan da ta yi bai hana damuwa bayyana a fuskarta ba. Idan aka ce ta faɗi yadda ta yi rayuwa a wata ɗayan nan a cikin gidan Rafiq ba zata iya faɗa ba. Komai zuwa yake yana wuce mata, hannu ta sa tana dafe ƙirjinta, wajen zuciyarta da yake mata zafi kamar zai kama da wuta. Kanta ta kwantar a jikin mudubin tana maida numfashi ta bakinta saboda azabar ciwon da take ji.

Ba don ba ta tsammaci kauce wa abinda yake faruwa yanzun ba, ba dai ta ɗauka zai yi ciwo irin na yanzun ba, hukuncin da ta tsammaci Rafiq zai mata daban da wanda ya ɗauka. Duk da banbancin ƙalilan ne, da igiyar auren shi har ukku akanta. Wannan ma wani abu ne, zuciyarta ta faɗa mata. Runts idanuwanta ta yi, daren ta na farko a gidan Rafiq ɗin na dawo mata, kamar a lokacin yake faruwa.

*****

Kuka take da yake jin shi har kasan zuciyarshi yana ƙara mishi ciwon da take yi, kafin ya janye jikinshi daga nata yana jin dauɗar da bai kamata ace yana jinta ba. Hannunshi ya sa yana goge bakin shi cikin son cire yanayinta daga jikin laɓɓanshi. Runtse idanuwa yayi yana ƙirga ɗaya zuwa goma cikin kanshi, nutsuwa yake buƙata ko yaya take kafin ya yi abinda su dukansu za su yi da na sani.

“Ni ya kamata in yi kuka Neem…ni ya kamata in zubda hawaye bake ba…”

Kamar maganganun shi take jira, don ƙara wa kukan da ta ke yi gudu ta yi. Muryarta na sarƙewa ta soma Magana,

“Sugar…ka fa…ka fahimce ni don Allah…”

Wata irin dariya Rafiq yayi da ba ta da alaƙa da nishaɗi, yana dafe kanshi dake juyawa da duka hannuwanshi biyu, kafin ya miƙe ya nufi  bandakin dake cikin ɗakin ya tura ya shiga ya doko ƙofar. Ƙarar da ta yi ya gauraye ɗakin kasancewar dare ne. Miƙewa zaune Tasneem ta yi ta jingina bayanta da kan gadon tare da janyo ƙafafuwanta ta haɗe jikinta waje ɗaya. Kuka take yi har numfashinta na barazanar ɗaukewa, idan ta ce ga yanayin da take ji ƙarya take, sai yanzun ta san in tashin hankali ya yi girma ba shi da yanayi sam. Hannuwa take sawa tana goge fuskarta da wasu sabbin hawayen ke sake ɓatawa, jikinta ko ina ɓari yake yi, da ƙyar takai hannunta ta lalubo wayarta dake ajiye kan drawer ɗin gefen gadon. Dannawa ta yi tana swiping key ɗin da ke jiki. Ƙarfe uku da rabi na dare. Hakan bai hanata lalubo lambar Samha ba. Ba ta jin za ta iya magana, don haka ta tura mata text,

‘Ya gane Samha… Wallahi ba zan iya rasa shi ba. Shi kaɗai ne dai-daito dana samu a rayuwata na tsayin lokaci, ba zan iya rasa shi ba… Bazan iya ba.’

Ko wayar bata ajiye ba kiran Samha ya shigo, sai da Tasneem ta share hawayen da ya zubo mata tukunna ta ɗaga ta kara a kunnenta, muryar samha ya sa sabon kuka ƙwace mata.

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un… Tasneem…. Ya Allah. Wallahi na kasa bacci tun ɗazun gabana sai faɗuwa yake yi…. Yana ina yanzun?”

Cikin kuka Tasneem ta amsata,

“Yana banɗaki…na shiga ukuna samha…”

Ta ƙarasa tana kokawa da numfashin ta da baya kaiwa inda ya kamata yakai.

“Ke! Ki nutsu! Ki saurareni…. Babu abinda zai faru In shaa Allah…

Shi ya sa na so ki faɗa mishi gaskiy sanda ya tambaya…”

Har lokacin numfashinta bai koma yadda ya kamata ba, hakan bai hana maganganun da Samha ta yi su ɗauki tunaninta su watsa wani lokaci can baya ba.

*****

A zaune ta same shi cikin motarshi, direban shi na ɗayan gefen. Sanin ko gaisuwa ba zata haɗa su ba ya sa ba ta bi ta kan shi ba. Hankalinta na kan Rafiq da ƙafafuwan shi na daga waje, ya dafe goshin shi da hannuwanshi duka biyun. Ba ta san dalilin da yasa zuciyarta bugawa ba. Cike da shakku ta kira shi.

“Sugar…”

Ɗago fuskar shi ya yi yana sauke mata idanuwan shi da suka canza launi saboda ɓacin rai.

“Waye Alhaji Mando?”

Gyara tsayuwarta ta yi, don za ta iya rantsewa tana jin bugun zuciyarta har cikin tafukan ƙafarta. Ta buɗe bakinta ya kai sau huɗu tana rufewa saboda babu kalma ko ɗaya da ta iya fitowa.

“Neem tambayar ki nake yi. Waye Alhaji Mando?”

Gudu tunaninta yake yi cikin ƙwaƙwalwarta da haɗa ƙaryar kafin ta ɗora ta akan harshenta da faɗin,

“Kamar na taɓa jin sunan, ina tunanin ko a ina ne?”

Tayi mamakin muryarta da ba ta rawa ba, da dukkan ƙarfin halin da take da shi take jure idanuwan Rafiq da suke cikin nata da wani yanayi.

“Na gaya miki abu na farko da zai iya wargaza alaƙar mu shi ne ƙarya, ni da ƙarya muna da tarihi marar daɗin ji…”

Muryarta a karye, zuciyarta cike da wani irin tsoro da take addu’ar bai nuna akan fuskarta ba tace,

“Ehen…Nasan na taɓa jin sunan, wani mutum ne da yasha zuwa kofar gidan nan wai yana sona. Sugar kallo ɗaya za ka yi mishi kasan ba mutumin kirki bane ba…saida na daina fitowa in ya aiko tukunna ya haƙura ya daina zuwa…”

Kallon ta Rafiq yake yi, kallon ta yake yana son fahimtar gaskiyar maganganun da ta yi ta cikin idanuwanta.

“Ba koda yaushe nake yarda da shaidar mutane akan ‘yan uwan su mutane ba… Allah ya sa kar in yi da na sanin yarda dake.”

Kai take ɗaga mishi da sauri tana ƙoƙarin ɗora murmushi akan fuskarta.

“In shaa Allah ba za ka yi ba…ka shigo mana.”

Girgiza mata kai ya yi ya ja ƙafafuwanshi ya mayar cikin motar, sannan ya ɗan ja murfin ya rufe kafin ya ce mata,

“Akwai inda zanje… Abin da na zo tambayarki kenan dama.”

Matsawa ta yi daf da motar sosai tana yawata idanuwanta kan fuskarshi tare da sauke muryarta,

“Ranka a ɓace yake har yanzun… Zuciyata ba za ta samu nutsuwa ba.”

Numfashi ya ja yana saukewa a hankali. Ranshi a ɓace ya ke ba ta yi ƙarya ba, maganganun da ya ji sun tsaya mishi, duniyarshi a birkice take, wajenta kaɗai yake samun nutsuwa, in ya rasata bai san abinda zai kama ba. Kallon ta ya ɗan yi.

“Abubuwa ne suka yi min yawa…”

“Are we okay? Ni da kai?”

Kai ya ɗan ɗaga mata. Yana jita sauke wani dogon numfashi da ita kanta ba ta san tana riƙe da shi ba. Tana kallon shi ya yi wa driver ɗin nuni da hannu alamar su tafi. Ba tare da ya sake ce mata komai ba har driver ɗin ya tayar da motar suka wuce. Sai a lokacin ƙafafuwanta da suka yi sanyi suke barazanar ƙin ɗaukarta.

*****

“Tasneem!”

Muryar Samha ta katse mata tunanin da take yi, jan hanci tayi, muryarta a dakushe da kukan da take yi tace,

“Za mu yi magana da safe…ina son zama ni kaɗai…”

“Neem please…”

Samha ta faɗi ta ɗayan ɓangaren muryarta na karyewa. Cikin ƙarfin halin da Tasneem ba ta ji ta katse ta.

“Kar ki damu…kawai bana son magana ne yanzu.”

Ba ta jira amsar da Samha za ta ba ta ba ta janye wayar daga kunnenta ta yar da ita akan gadon. Dai-dai fitowar Rafiq da ƙugun shi yake ɗaure da towel. Da busassun idanuwanta da suka sha kuka har tana jin hawayenta sun ƙafe take binshi da kallo. Sif ɗin kayan da ke jikin bangon ya buɗe, wandon da hannunshi ya fara kai wa kai ya ɗauko ya sa wa jikinshi ya ɗauko riga ba tare da damuwa da kalar su ba. Asali ma ba su bane damuwarshi, wajen gadon ya ƙaraso ya sa hannu ya ɗauki mukullin motar shi da ke ajiye akan kafet da wayarshi ya zura a aljihu.

Ganin yana shirin fita ya sa Tasneem saurin saukowa daga kan gadon ta sha gaban shi. Kau da kai ya yi gefe, ba ya son ganinta sam-sam. Raɓa ta ya yi zai wuce ta sake shan gaban shi. Hawayen da take tunanin sun kafe suka sake zubo mata, ta sa hannunta ta goge.

“Ina za ka je cikin daren nan? Ba tuƙi kake iyawa ba…”

Bai amsata ba ya sa hannun shi ya ture ta gefe tare da takawa ya nufi ƙofa, cikin zafin nama ta kamo hannun shi.

“Ka bari sai da safe.”

Hannun shi ya ƙwace daga cikin nata yana kallonta cike da wani abu da ba zai iya fassarawa ba, zuciyarshi na ci gaba da tafasa, komai zai iya faruwa in yana ganinta a gabanshi.

“Bana son ganinki… Neem bana son ganinki wallahi.”

Runtse idanuwanta ta yi tana jan numfashi, maganganun shi na sukar zuciyarta da ciwon da ba ta taɓa sanin shi ba a rayuwarta.

“Control ɗina gab yake da samun matsala, komai zai iya faruwa in ina ganinki…”

Tasan shi, ta san halin shi, sai dai ba ta taɓa jin ɓacin ran da ta ke ji a muryar shi ba tunda take da shi. Komai ciwo yake mata, zuciyarta na rarraba raɗaɗin da take yi zuwa ko’ina na jikinta. Tana jin takunshi da murza ƙofar da ya yi kafin tace,

“Abin da yake faruwa yanzun…Shine dalilin yi maka ƙarya. Tsoron rasa ka ya hanani faɗa maka gaskiya…”

Bugo ƙofar ɗakin da ya yi ta faɗa mata cewa ya fice, nan inda take tsaye ta durƙushe tana sakin wani kuka da ya fito tun daga zuciyarta!

*****

Ringing ɗin da wayarta take yi ne ya katse mata tunanin da take yi, hannu ta sa tana goge fuskarta saboda hawayen da ba ta ma san suna zuba ba sun jiƙa mata kunci. Miƙewa ta yi da niyyar ƙarasawa kan gadon ta inda wayar take tana ƙara, babu shiri ta koma ta zauna ta runtse idanuwanta gam, ɗakin jujjuya mata kawai yake yi.

Ga ƙirjinta kamar an ɗora dutse saboda nauyin da ta ji ya yi mata.

“Ya Allah…”

Ta faɗi ta sake runtse idanuwanta gam ko za ta samu jirin da yake ɗibarta ya daina. Tana jin wayar har ta yanke, kiran ya sake shigowa amma ta kasa miƙewa, tana alaƙanta jirin da take ji da rashin cin abinci da rashin nutsuwa ya hana mata. Wajen mintina sha biyar ta ɗauka a haka kafin da ƙyar ta miƙe ta ƙarasa kan gadon ta kwanta.

Wayar ta ɗauka ta cire key ɗin da ke jiki tana dubawa, Azrah ce. Yanayin da take ji bai hana ɗan ƙaramin murmushi ya kuɓce mata ba. Kiran ta mayar tare da kara wayar a kunnenta, ringing ɗin farko Azrah ta ɗauka da faɗin,

“Ya Tasneem ina kika shige? Ina ta kira ba ki ɗauka ba, lafiya dai ko?”

Muryarta can ƙasa, wata irin kewar Azrah ɗin take ji.

“Ba na kusa ne Azrah, lafiya ƙalau. Ya kuke? Ina su Hamnah?”

“Lafiya ƙalau, na ci intro ɗina. Yanzun aka kira ni ake faɗa min.”

“Haba dai? Oh Allah. Ma Shaa Allah… Kin ga abin Allah ko?”

Tasneem ɗin ta ƙarasa muryarta da ƙwari fiye da sanda ta ɗaga wayar. Ta jima ba ta ji wani labari mai daɗi kamar na yanzu ba.

“Gabana yana ta faɗuwa. Kar ayi irin na wancen karon… Ki yi wa Ya Rafiq godiya please. Ko fara faɗa mishi na samu… Na kira shi bai ɗauka ba, na san dai zai kirani inya gani.”

Kiran sunan Rafiq ɗin da Azrah ta yi ya sake jefa Tasneem cikin yanayin da take ɗazu, don ji ta yi har cikinta sai da ya ƙulle, ƙirjinta da ya ɗan tsagaita da zafin da yake mata ya fara dawowa.

“Hello…”

Da ƙyar ta iya faɗin,

“Congrats Nurse Azrah… Zan faɗi mishi In shaa Allah.”

Tana jin dariyar Azrah ta cikin wayar.

“Tun yanzun har na zama Nurse ɗin ma?”

Sam Tasneem ta nemi dariya ko ya take ta rasa.

“Ki gaishe da su Hamnah. Bari in duba girki.”

“Tam za su ji… Ki kula da kanki.”

“Kema haka.”

Tasneem ta faɗi tana sauke wayar daga kunnenta. Cikin kanta tana lissafa kwanaki goma sha shida cif rabon da ta sa Rafiq a idanuwanta. Sai dai ta ji motsin shigowarshi da fitarshi a wasu lokutan. Duk da ba ta ga laifinshi ba, hakan bai hana abin yi mata ciwo na gaske ba. Hannu ta sa tana sake goge hawayen da ya samu wajen zama tare da ita yanzu. Yadda yake saurin zuba har mamaki abin yake bata. Mararta ta ji kamar za ta yi ciwo, ta lumshe idanuwanta, wannan karon ta yi ƙari har na kusan sati.

*****

Kano

Idanuwan shi kafe suke akan kwalaben kodin ɗin da ke gabanshi. Hannuwa shi da suke a dumtse har ƙaiƙayi suke mishi na son ɗaukar kwalbar. Zai iya rantsewa har kan harshen shi yana jin ɗanɗanon haɗin da yake cikin kwalbar da ya fi komai tafiyar mishi da damuwa. Agogon da ke bangon ɗakin ya ji ya soma kukan da yake a duk lokacin da awa ta cika, kafin ya soma bugawar da yake jin ƙirgar har cikin zuciyarshi. Sai da ya buga sha biyu cif tukunna ya yi shirun da ya gauraye ɗakin. Hannunshi ya miƙa ya ɗauki kwalba ɗaya, cike da sabo ya girgiza ta yana gauraye ƙwayoyin da ke ciki da ya san sun gama narkewa. Zuwa yanzu abu ɗaya yake ci mishi rai, damuwa ɗaya ce ta addabe shi, kuma hanya ɗaya ce ya sani da zai iya mantawa da koma menene.

‘Ka min alƙawari zan iya yarda da kai wannan karon…’

Kamar maganar ta tunkuɗa hannunshi ne, zuciyar shi ta yi wani irin bushewa, yana jin ɗanɗanon kodin ɗin da ƙwayar akan harshen shi ya lumshe idanuwan shi cike da jin yadda take ratsa shi yana gamsar da ƙishin da ya yi watanni yana ji, da sauri ya kwankwaɗe kwalbar gaba ɗaya yana maida numfashi.

Ajiyewa ya yi ya sake ɗaukar wata tare da sake kwancewa, yana son ya daina ganin fuskar yayan shi a cikin zuciyarshi, yana son ya daina ganin fuskarta, yana son ya daina jin abin da yake ji. Ya ɗaga kwalbar kenan wayarshi ta yi ƙara da sai da ta tsorata shi har kwalbar na shirin suɓucewa daga hannunshi. Juyar da kanshi ya yi yana kallon wayar da ke gefen shi a ajiye. Ganin ko wace lamba ce aka kirashi da ita ya sa shi ajiye kwalbar ya ɗauko wayar da sauri.

“Yaa Faq…”

Ya faɗi zuciyar shi na dokawa.

“Muna Aminu Kano Tea….”

Bai bari ya ƙarasa ba ya yi wata irin miƙewa cike da tashin hankali.

“What? Ina Yayan? Me ya same shi? Me ya faru?”

Ya jero tambayoyin yana ƙarasawa ya zura takalman da bai tsaya ya duba kowanne kala bane ba.

“Inka ƙaraso zan faɗa maka… Ana buƙatar jini ne shi ya sa ma na kira ka.”

Ɗan dafe kai ya yi, yana jin an kashe wayar daga ɗayan ɓangaren.

“Damn… Dammit!”

Yake faɗi zuciyarshi na dokawa da sauri-sauri. Da sauri ya fita daga ɓangaren su, yana ganin mutanen dake kai kawo a harabar gidan nasu, bai tuna makullin motar shi ba ya jikin shi ba sai da ya ƙarasa inda motar take.

“Shit…”

Ya furta, ba zai iya ɓata lokacin komawa cikin gida ɗauko mukullin mota ba, da gudu-gudu ya fita daga gidan, haka ma ya ƙarasa bakin titin unguwar tasu, ya ko yi sa’a mai Napep yazo wucewa. Tare shi yayi ya shiga.

Hannunshi biyu dafe da kai yake zaune cikin Napep ɗin, in da zai iya da ya zane kanshi da kanshi, me yake tunani? Me yayi wa kanshi mintina kaɗan da suka wuce?

‘Jini ake bukata shi ya sa na kira ka.’

Dago fuska ya yi yana jan numfashi, group ɗin jinin su ɗaya da Ya Faq ɗin. Amma ba ya jin abinda ya sha zai bari a ɗiba, haɗin na da ƙarfi, duk da kanshi ya saba ɗaukar cajin yana jin yadda idanuwanshi ke buɗewa cike da izzar da haɗin ne kawai yake saka shi ji.

“Malam tsoron Napep ɗin kake yi ne?”

Tariq ya buƙata ranshi a ɓace, gaba ɗaya ya raina gudun da mai Napep ɗin yake yi. Da yake bai haɗu da ɗan rigima ba, murmushi kawai ya yi bai ce komai ba. Suna ƙarasawa AKTH ya zaro ɗari biyar ya bashi. Don bai ma tambaya ko nawa ba ya wuce. Lambar Yaa Faq ya ke laluba a wayarshi ya kira don ya ji ko suna ta ina. AKTH ba baƙon shi bane ba, asalima da asibiti na zama gida da an basu wani ɗan ɓangare a ciki saboda yawan zuwan da suke yi.

Kwatancen wajen ya yi mishi, sam baya son tunanin duk wani negative abu sai ya ƙarasa tukunna. Ganin Yasir tsaye ga kuma ‘yan sanda guda huɗu ya sa Tariq jin zuciyarshi ta dawo cikin ƙafafuwanshi kamar duk takun da yake yi zuwa inda suke yana take ta ne shi ya sa take bugawa da wani irin sauri. Zai iya jin yadda duk wani jini ya bar cikin fuskarshi saboda tashin hankali. Idanuwan shi yake yawatawa kan rigar jikin Yasir da take jiƙe da jini daga kafaɗar shi zuwa kan ƙirjin shi, ciwo yake nema don ganin ta inda jinin ya fito ya kasa gani. Don ko kaɗan ba ya son kawo wa kanshi jinin Ya Faq ne a jikin rigar Yasir. Muryarshi can ƙasa yana kallon Yasir yace,

“Yana ina?”

“Ka kwantar da…”

“Damn it! Yana ina?”

Tariq ya faɗi bai damu da mutanen da suke kallon su ba saboda ɗaga muryar da ya yi. Yadda abin da ya sha yake mishi yawo ba tare da ya ishe shi ba, inda zai ƙarasa juye ɓacin ran shi yake nema. Dalili kawai yake son samu, kuma Yasir yana son bashi ɗaya. Idanuwan shi cike da ban haƙuri yake kallon Tariq din da faɗin,

“Yana dakin Theatre…”

“Theatre?”

Kai ya dan ɗaga mishi. Sai da ya runtsa idanuwanshi da suke wani ƙasa-ƙasa da kansu tukunna ya buɗe su.

“Rashin haƙurina gab yake da rinjayar haƙurina…ka fara min magana yadda zan fahimta Ya Yasir.”

“Harbin shi akayi!”

Maganar Tariq yake ji na amsawa a ko’ina na jikinshi, kunnuwan shi sun yi wani dimm.

“Umm?”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi yana daƙuna wa Yasir fuska da ke nuna yana son ya sake maimaita mishi don ya fahimta.

“Harbin shi akai a hanyar mu ta dawowa…”

Dariya Tariq yayi saboda bai san abin da ya kamata ya yi da ya wuce wannan ba. Sosai yake dariyar da ya sa Yasir takowa ya ƙaraso inda yake yana dafa mishi kafaɗa da ya yi saurin kai hannu ya ture kamar an ɗora mishi wuta tare da juyawa ya hanka&a shi baya.

“Duk sanda kuka fita tare sai an samu matsala… Ya akai harbin akanshi kawai ya tsaya? Maganin bindiga ka sha da bai same ka ba?”

“Tariq…”

Yasir ya kira da damuwa tare da kashedi a muryarshi. Sosai Tariq ya matsa dab da shi, fuskarshi a cike da tashin hankali, muryarshi can ƙasa,

“Ina son sanin yadda akayi ne kake tsaye anan…. Yaa Faq yake duk inda yake yanzun…”

Tariq ya ƙarasa maganar yana barin Yasir ya ga abinda yake ji ta cikin idanuwanshi, tsoro ne bayyananne, daga cikin shi komai kyarma yake yi. Yana jin yadda duniyar ta ƙara mishi wani irin girma, fayau yake ganinta sai shi kaɗai a tsaye. Wannan karon kyarmar har wajen jikinshi ta nuna kamar mai jin sanyi.

“Wanda zai bada jinin bai zo bane?”

Tambayar ta sa su Tariq juyawa su dukansu, da sauri Tariq ya ƙarasa inda likitan yake.

“Wallahi shi kaɗai ya ragemin…. Banda kowa…. Daga ni sai shi… Yana ina? Ya tashi? Ka barni in ganshi in ya ji maganata zai tashi.”

Ganin yadda Tariq ɗin yake maganganu kamar ba ya cikin hayyacin shi yasa likitan kama hannun shi yana jan shi suka nufi hanyar da ya fito. Yasir yana bin bayan su har office ɗin likitan. Zaunar da Tariq ya yi akan kujera ya miƙa hannu ya ɗauko robar Faro ɗin da ke ajiye akan table ya miƙa mishi. Ba musu Tariq ya karɓa ya buɗe ya sha ruwan sosai, duk da ƙishin da yake ji ba na ruwa bane ba bai hana shi jin ‘yar nutsuwa ba. A ƙasa ya ajiye robar yana kallon likitan.

“Yana ina?”

Ya buƙata yana ƙoƙarin saka nutsuwar da ba ya ji a cikin muryarshi.

“Ba abin da zan iya ce maka yanzun… Jinin shi O ne yana wahala…”

Bai bari ya ƙarasa ba ya katse shi da faɗin.

“Jinin mu iri ɗaya ne… Amma bansan ko za a iya ɗiba ba.”

Tariq ya karasa muryarshi na sauka ƙasa cike da wani yanayi mai wuyar fassarawa. In wani abu ya samu Yaa Faq….girgiza kanshi ya yi saboda tunanin wani abu zai iya samun shi ɗin ma na neman saka numfashin shi tsayawa. Idanuwan shi ya sauke cikin na likitan.

“Na sha kodin da mix… Ban san ko za a iya ɗibar jinina ba.”

Wani irin kallo likitan yake wa Tariq cike da fassarori kala-kala. Rai a ɓace Tariq yace,

“Kar ka ja layi a rayuwa ta ba tare da sanin farkon ta ba… Ka ji da matsalarka in ji da tawa…”

Da kallon dai a idanuwan likitan da Tariq ba ya so ko kaɗan, ba ya son mutane na yanke mishi hukunci tunda asalin ikon hakan ba a hannun su yake ba. Laifukan shi da rayuwar shi ba matsalar su bane.

“Za a iya samu…. Da tsada sosai in zaku iya siya.”

“Duk abinda ya kamata ayi mishi ayi…. Sau nawa zan faɗa maka haka?”

Yasir da ke tsaye ya faɗi. Kai likitan ya ɗaga musu yana fita, su ma bin bayan shi suka yiyhar sai da ya juyo yace musu,

“Iya nan za ku iya tsayawa…”

Kallon shi Tariq yake yi kamar yana son musa hakan, ko Yasir ya ɗauka zai yi gardama. Sai ya ga bai ce komai ba ya tsaya. Idanuwan shi dai na kafe kan likitan har ya shiga ɗakin Theatre ɗin. Sauke numfashi mai nauyi Yasir ya yi tare da zama akan doguwar kujerar da ke wajen.

“Tariq ka zauna.”

Shiru yayi kamar ba da shi yake ba.

“Tariq…”

Ya sake kira.

“In ba faɗa min za ka yi in ka bar asibitin nan ka bar rayuwar yayana ba kar ka sake min magana don Allah…Ka bar ni in ji da abinda yake damuna…”

Shiru ya yi ya ƙyale shi, bai san ta inda zai faɗa wa Tariq da duk wani abu da zai samu yayan shi yake ɗorawa a kanshi cewar ba haka bane ba. Zai iya komai saboda Ashfaq. In har bai fi ƙarfin ikon shi ba, ba zai taɓa bari wani abu ya same shi ba saboda dalilai da yawa. Bai san ko awa nawa suka ɗauka ba, banda bugun zuciyarshi babu abinda yake fahimta, sai zufar da yakan sa hannu lokaci zuwa lokaci ya goge daga goshin shi. Komai na asibitin na son dawo mishi da abinda ba ya son tunawa. Komai na yanayin na saka jikin shi yin sanyi.

Buɗe ɗakin Theatre ɗin ya ga an yi kafin a gunguro gado daga cikinshi ana nufar wani ɗakin da shi. Kamar wanda aka dasa haka yake jin ƙafafuwanshi sun mishi nauyi ya kasa ƙarasawa, jikinshi ya ɗauki wani irin sanyi. Har sai da ya ji Yasir ya ɗan taɓa shi tukunna ya ɗaga ƙafarshi da ta yi wani irin nauyi ya fara takawa zuwa ɗakin da aka shiga da Ashfaq ɗin. Hannuwanshi yake ji kamar babu jini a jiki, da ƙyar ya iya tura ƙofar a hankali ya tsayar da idanuwan shi kan Ashfaq da ke kwance akan gadon. Wani siririn tube ne dogo a hancin shi.

Ga ƙarin jini a hannun shi, fuskarshi ta yi wani irin haske da ya sa duka wani fargaba da tsoro da Tariq yake ji ya ƙara haɗe mishi waje ɗaya. Ƙafafuwan shi na rawa ya ƙarasa cikin ɗakin inda gadon yake. Ya ga bakin likitan na motsi, sai dai ko me yake faɗi ba ya ƙarasowa kunnen shi.

Tsugunnawa yayi yadafa gadon da hannayen shi.

“Ya Faq…”

Ya kira a hankali, ko shi da wuya in ya ji muryar balle Ashfaq da bai san duniyar da ake ba.

‘Ka cika damuwa… Ɗan yankan nan hankalin ka duk ya ta shi kamar ba namiji ba.’

Tariq ya ji muryar Ashfaq ɗin can wani lokaci.

‘Ka kalleni Tariq… Idan zan iya kauce wa mutuwa saboda kai zan yi okay? Kai kaɗai ne dalilin da ya rage min na rayuwa… Babu abin da zai same ni in shaa Allah… I promise.’

Idanuwan shi Tariq ya ji sun cika da wani abu mai zafin gaske. Zuciyarshi na raɗaɗi har wani zazzaɓi-zazzaɓi yake ji.

“Ka min alƙawari…Yaa Faq ka min alƙawari…In ramawa kake so ka yi dan na karya alƙawarinmu kar ka min ta wannan hanyar…ba na jin magana na sani…ina buƙatar wanda zai faɗa min hakan… Don Allah kar kai min haka… Kar kai min haka Yaa Faq…”

Tariq ya ƙarasa yana kifa kanshi da gadon da Ashfaq ɗin yake, hawaye masu ɗumi na zubo mishi. Hawayen da ya yi tunanin babu wani abu kuma da zai sake fito da su. Babu dalilin da ba su gani ba na fitowa a rayuwar shi. Bai zaci akwai sauran abin da zai fito da su ba sai yanzun, sai da ya ga Ashfaq kwance haka, ɗago kan shi ya yi ya sa hannu ya goge hawayen da suka zubar mishi.

“Yaa Faq ka tashi don Allah… Ka min magana kawai sai ka koma baccin da kake… Ina buƙatar sanin kana ji na…”

Ko numfashi bai ga Ashfaq na yi ba ballantana kuma ya nuna mishi alamar yana jin abinda yake cewa. Tashi daga tsugunnon Tariq ya yi tare da zagayawa ya zauna akan gadon ta gefen Ashfaq ɗin. Nutsar da hankalin shi ya yi akan fuskarshi yana son ganin ko motsi ya yi, kayan da ke jikin shi ne Tariq ba ya son kallo saboda suna son kai shi inda ba ya son zuwa. Shi ya sa ya ƙi yawo da idanuwanshi inda ya wuce fuskar shi.

Sam bai ji turo ƙofar ba sai maganar Yasir da ya ji,

“Doctor ya ce He will be fine…

Sai dai ba yanzu zai tashi ba.”

Bai nuna wa Yasir yadda maganar ta sa kamar an ɗauke mishi wani ƙaton nauyi a zuciyar shi ta yi ba, balle yadda kunnuwanshi suke buƙatar jin wani ya ce mishi babu abinda zai samu Ashfaq da ya wuce zuciyarshi ba. Asalima ko inda yake Tariq bai kalla ba, har ya ji ya tako ya ja kujera ya zauna.

*****

Abuja

Sosai ya jingina bayanshi da kujerar motar, in da wani ya ce ya hango mishi kasancewar rayuwar auren shi a wannan yanayin murmushi kawai zai yi don ya san ba abu bane mai yiwuwa, yarda da Tasneem ba za ta taɓa barin shi amincewa ba. Zafin da zuciyarshi take yi da azababben kishi har kanshi yake jin ya soma ciwon da ya samu wajen zama tare da shi a wata ɗayan nan. Bai ma yi yunƙurin shan ko magani ba, don ya san babu abin da zai mishi. Lumshe idanuwanshi ya yi yana maida numfashi.

‘Ina son ka. Ba zan iya rasaka ba.’

Maganganun Tasneem suka dawo mishi. Kamar yadda amsar da ya bata take yawo cikin kanshi.

‘Kar ki min ƙarya, ita ce abu na farko da zai iya shiga tsakaninmu. Na fi buƙatar gaskiyar ki akan soyayyarki Neem. Na samu soyayya mai yawa a rayuwata, gaskiya ce take da ƙaranci.’

Buɗe idanuwanshi ya yi babu shiri, ba ya son tuno yanayin fuskarta, ba ya son tuna yadda ta kalli ƙwayar idanuwanshi, yadda ta kalli zuciyarshi da ya buɗe mata ta cikinsu ta yi mishi ƙarya. Ciwon da yake ji a yanzu ya ishe shi ba sai ya ƙara da wani sabo ba.

“Isah, mu biya ta K.F.C zan siya abu.”

Rafiq ya faɗa wa direban shi da ke jan motar.

“To Yallaɓai.”

Isah ya amsa tare da shan U-turn ɗin da zai kai su K.F.C ɗin. Suna Karasawa Rafiq ya buɗe bayan motar ya fito ya shiga wajen. Burger ya siya da waffles, ledoji uku ya yi, ya biya kuɗin kenan yana ɗaukar ledojin ya ji zuciyarshi ta yi wata irin dokawa cikin yanayin da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba.

Har tsigar jikinshi ya ji tana tashi, kusanci yake ji da bai san daga inda yake ba, da sauri ya juya jin takun tafiyar da ke ƙara jefa shi cikin yanayin da ya tsinci kanshi. Matashiyar budurwace da ba za ta shige shekaru sha takwas ba, jikinta sanye da Abaya.

Akwai wani abu tattare da ita da ya kasa fahimta, musamman yadda suna haɗa ido duk wata fara’a da ke fuskarta ta ɗauke, mamaki, shakku, da wani abu da Rafiq ya kasa fahimta yana maye gurbin fara’ar, sosai take kallon shi. Zuciyarshi ta ci gaba da dokawa, ji yake tamkar ya santa a wani waje, kusancin da yake ji a tsakanin su ya mishi wani iri.

Cikin hanzari ya damƙe bakin ledojin ya fita daga wajen, iska yake shaƙa, yana jin kamar ta mishi kaɗan, murfin motarshi ya buɗe yana shirin shiga ya ji zuciyar shi ta sake bugawa da ƙarfin da ya fi na ɗazun , juyawa ya yi, daga babban mayafin da ya lulluɓe jikinta ya gane mace ce, sai dai ba zai ce ga yadda kalarta take ba, saboda bayanta kawai yake iya gani, kafin ta shiga cikin K.F.C ɗin.

Da dukkan wani abu da zuciyar shi take da shi take faɗa mishi ya bi bayan matar, runtse idanuwanshi Rafiq ya yi yana girgiza kanshi, cikin son rabuwa da koma menene yake ji. Da sauri ya shiga motar ya ja ya rufe. AC ɗin da ke aiki bai hana shi kai hannu ya goge gumin da yake ji a goshin shi ba. Sosai kanshi ya ɗaure, abin da ya faru baƙo ne a wajenshi. Yakice koma menene ya yi gefe ɗaya, bai da lokacin shi a yanzun. Musamman da ya hango gate ɗin gidan shi, ya ga isa ya tunkari gidan, koma me ya ke ji sai ya yi gefe, sauke numfashi ya yi lokacin da suka ƙarasa cikin gidan. Leda ɗaya daga cikin ukkun ya ba wa Isa da bai tsaya jin godiya da addu’o’in da yake mishi ba. Ya shiga cikin gidan, da sallama ya taka babban falon duk da bai tsammaci amsa ba, don ya san da wahala ya ga Tasneem ɗin a falo. Rabon da ya sata a idanuwanshi tun daren auren su, sai dai yakan ji motsinta wasu lokutan, yana son ya ji ko tana lafiya, ko ba komai zaman shi take yi a cikin gidan. Amma zuciyar shi ba ta son ganinta, ko kaɗan ba ya jin zai iya jure zama waje ɗaya da ita a yanayin da yake ji. Area ɗin dining ɗin ya ƙarasa ya ajiye leda ɗaya, ya juya da niyyar nufar sashen shi. “Sugar…”

Muryarta ta tsayar da shi cak, kafin ya juyo kamar wanda aka yi  dole. Idanuwanta ta ware akan shi, kallon ta yake, zuciyarshi na matsewa a ƙirjin shi da wani irin ciwo. Kumburin da idanuwanta suka yi bai hanashi ganin damuwa da ramar da ke ƙasan su ba. Hakan bai yi komai ba sai ƙara mishi ƙuncin da yake ciki. Yana kallon ta har ta ƙaraso dab da shi, tsayin da ya yi mata ne ya sa ta ɗan ɗaga kanta don ta ga fuskarshi. Idanuwanta cike taf da hawaye.

“Na cancanci hukunci fiye da wanda kake min a yanzun…”

Tasneem ta faɗi tana sa hannu ta goge hawayen da ya zubo mata. Kafin ta kai hannunta tana tallabar kuncin shi.

“Sanin muna zaune gida ɗaya…amman ganinka na mun wahala… Zuciyata na ƙuna sosai…”

‘Fuskar maza nawa hannunta ya taba?’

Zuciyarshi ta tambaye shi. Zame fuskar shi Rafiq ya yi daga hannunta yana matsawa baya kaɗan, don ji ya yi kamar wuta ta ɗora mishi. Fuskarta yake kallo yana jiran zuciyar shi ta buga mata yadda ta saba amma sam. Ba ya jin komai game da ita a yanzun sai ƙyama, da tarin da na sani.

Bai da abin da zai ce mata, bai da kalaman da zai ɗora akan harshen, don haka ya juya kawai ya nufi ɓangaren shi.

*****

Bin bayanshi da kallo Tasneem ta yi, ba ta san meya sa ta fito da tajie motsin shi ba, ba ta san me zuciyarta ta zata ba. Hannu ta kai ta dafa kujerar dake wajen kafin ta samu ta zauna tana runtse idanuwanta saboda jirin da take ji.

Ba ta yi ƙoƙarin goge hawayen da suka zubo mata ba, tari ta fara yi da ciwon shi yake tasowa daga ƙirjinta, zuciyarta na mata ciwo kamar ana hura wuta, hannu ta sa ta rufe bakinta, tarin na sake taso mata babu ƙaƙƙautawa, ta kai mintina biyar tanayi, numfashin ta har Sama-sama yake yi, ga kanta kamar zai rabe biyu.

A hankali tarin ya soma tsagaitawa, wajen mintina sha biyar tana hutawa kafin ta samu ta miƙe da ƙyar ta nufi ɗakinta, banɗaki ta nufa ta kunna fanfo ta wanke hannuwanta. Ciwon kirjin da take ji ya kusan wata uku, amma tarin satin bikinta ta fara yin shi kaɗan-kaɗan, ya soma haɗowa da jini randa aka ɗaura aurenta, har zuwa yanzun. Kurkure bakinta ta yi ta samu da ƙyar ta fito daga banɗakin. Ta san ko da bakinta ba ya so, jikinta na buƙatar abinci, don haka ta sake fita daga ɗakin ta nufi hanyar dining ɗin, kamar koda yaushe leda na ajiye, hakan yakan yi mata, in za ta ci ta ci, in ma ba za ta ci ba ta wani fannin ya sauke wannan nauyin.

Ɗauka ta yi ta sake nufar ɗakinta, hawaye na sake zubo mata da ta tuna da yanayin ƙyamar ta da take gani a fuskar Rafiq ɗin. Yadda ya zame fuskarshi daga riƙon da ta yi mishi kamar wuta ta zuba mishi. Har ta samu waje ta zauna a ɗakin, zuciyarta ba ta ga laifin shi ba. Ta ba shi dukkan wani dalili da zai ƙyamace ta. Buɗe ledar da ke gabanta tayi, waffle ɗin ta fiddo da shi, ta soma gutsura tana sakawa a bakinta, ko taunawa ba ta yi ba balle ta gane daɗin shi, haɗiyewa  kawai ta yi. Haka ta ci gaba da yi sai da ta ji in ta ƙara amai zata yi tukunna ta ja ledar gefe ta haɗe kanta da gwiwarta. Komai ba ya mata daɗi.

Wata irin tsana ce take mata yawo a zuciya, tsanar kanta da ta Umma da ta zama silar jefata cikin wannan bala’in. In da za ta samu dama da ta koma baya ta sake yin wasu zaɓin. Sai dai a wasu abubuwan rayuwa dama ɗaya take baka. Wani lokaci can baya na dawo mata.

*****

“Tasneem! Tasneem!!”

Umma take kira a fusace, da sauri Tasneem ta sauko daga kan katifar da take kwance akai tare da fitowa tsakar gida inda Umma take tsaye. Fuskarta kawai ta kalla ta san ranta a ɓace yake. Duka Umma ta kawo mata, cikin hanzari Tasneem ta kauce tana yin nesa da Ummar.

“Ke wacce irin yarinya ce marar rabo? Arziqi na binki kina runtse ido? In ke halin ƙuncin da muke ciki ba ya damunki sai aka ce miki ni ba ya damuna? Dan ubanki yaushe za ki yi hankali?”

Umma take faɗa cikin ɓacin rai. Kallon ta Tasneem take yi cikin ƙunan rai. Umma ta ci gaba da faɗa kamar za ta ari baki.

“Ki wuce ciki ki ɗauko hijabinki, Alhaji Mando na ƙofar gida yana jiran ki. Ashe tun Shekaranjiya yake binki kuje siyayya kin ƙi. Saboda baƙin ciki ko? Kwana nawa rabon da mu ɗora tukunyar abinci a gidan nan? Tun randa saurayin Azrah ya ba ta dubu biyu…”

Kallon mamaki Tasneem take wa Umma kafin rai a ɓace ita ma ta ce,

“Au umma! Kuɗin nan sai da kika bari ta karɓa? Duka Azrah nawa take da zatae dinga fita zance…

Kuma kin ma ga ɗan iskan yaron?”

Juyawa Umma tayi tana rarumar wani tsohon takalmi da ke ajiye ta wurga wa Tasneem ɗin.

“Dan ubanki sai ki faɗa min abin da ya kamata…Za ki ɓace min da gani ko sai na karya ki? Kuma wallahi ki ɗauko Hijab ki bi shi.”

Da gudu Tasneem ta wuce ɗaki, ta ɗauko wani tsohon hijabinta, hawayen baƙin ciki taf da idanuwanta. Abu ɗaya zai sa ta bin Alhaji Mando, don hakan zai iya sa Umma ta ɗaga ma Azrah da fita zancen da Tasneem ba ta ga alkhairi a cikin shi ba.

*****

Ƙwanƙwasa ɗakin da ta ji ne ya katse mata tunanin da take yi. Ba tare da ta ɗago kanta daga jikin gwiwarta ba ta amsa da a shigo. A hankali Rafiq ya turo ƙofar yana shigowa kamar wanda aka yi wa dole. Har ɗakin shi yana juyo tarin da take yi dazun. Duk yadda ya so ya jure ya kasa. Akwai muryar dake faɗa mishi ya zo ya duba lafiyar Tasneem ɗin, duk girman laifinta a wajenshi in wani abu ya sameta ba zai yafe wa kanshi ba. Sai dai ya kasa ƙarasawa. Daga nan bakin ƙofar yace,

“Lafiyarki? Na ji kina tari ɗazun.”

Da sauri Tasneem ta ɗago kanta, to wama take zaton zai ƙwanƙwasa mata ɗaki in ba shi ba, ba ta jin banda maigadi, akwai wani a gidan bayan shi da ita. Zuciyarta ta matse waje ɗaya cike da buruka da dama. In har ya damu da halin da take ciki, ya ɗauko ƙafar shi ya zo yaga ya take, tana da sauran hope. Muryarta na rawa, cike da yanayoyi da dama ta amsa shi da,

“Lafiya ƙalau. Na gode.”

Dariya Rafiq yayi mai sauti da ba ta da alaƙa da nishaɗi. Tasneem ce take mishi godiya don ya tambayi lafiyarta, yanayin rayuwa ba zai daina bashi mamaki ba. Yadda komai yake canzawa cikin ƙanƙanin lokaci. Girgiza kanshi kawai yayi ya juya haɗi da ja mata ƙofar.

Kano

“Arfa! Arfa!! Arfa!!”

Yake kira cikin tashin hankali yana jijjiga ta, ɗago ta ya yi ya rungumeta a jikinshi, ya san yadda tashin hankali yake, abin da yake ji ba shi da suna, ji ya yi kamar kayanta a jiƙe suke, hakan ya sa ya kai hannunshi yana taɓa dai-dai inda yaji lemar yana dawo dashi ga dubanshi. Idanuwanshi a ware cikin sabon firgici da tashin hankali yake kallon jinin da ke hannunshi, sake kallon Arfa yayi dake jikinshi, maimakon ya ganta sai Ashfaq ya gani da jini na malala daga inda baya iya gani a jikin Ashfaq ɗin. Waigawa ya yi gefe ko zai ga wani don ya kawo mishi ɗauki. Bai ga kowa ba sai Arfa da ke kwance a kasa ba ta motsi, ya rasa wane irin rikitaccen al’amari ne yake faruwa da shi.

“Arfa!!!”

Ya kira da dukkan ƙarfin shi.

*****

“Tariq ka buɗe idanuwanka…Tariq!”

Buɗe idanuwanshi yayi yana maida numfashi da sauri-sauri, kafin ya soma yawatawa da idanuwan nashi ko’ina na dakin.

“Is okay…”

Da sauri ya dawo da dubanshi kan Ashfaq.

“Yaya…”

Ya kira kamar yana kokwanton in ya ɗaga muryarshi zai ga Ashfaq ɗin ma mafarki ne. Murmushi Ashfaq ɗin ya yi mishi.

“Karka sake bani tsoro irin wannan… Duniyar za ta yi min girma in ba ka nan.”

Tariq ya faɗi muryarshi na rawa. Kai kawai Ashfaq ya iya ɗaga mishi, don ko kaɗan ba ya jin ƙarfi a jikinshi. Turo ƙofar da aka yi ya sa su duka maida hankalinsu wajen. Yasir ne ya shigo da Sallama, hannunshi riƙe da ledojin Oasis. Ƙarasowa ya yi ya ɗora ledojin akan table ɗin da ke wajen.

“Bacci ya kamata ace kana yi har yanzun.”

Faɗar Yasir.

“Ba na jin wani bacci… Yaushe suka ce zan bar wajen nan.”

Ashfaq ya buƙata yana ƙoƙarin miƙewa, da sauri Tariq ya mayar dashi.

“Za ka bar wane wajen? Yaya za ka fara ko? Wallahi babu inda za ka je in ba sallamarka aka yi ba.”

Yasir ya kalla.

“Ka daina kallona, da gaskiyar Tariq. Wannan ba ciwukan da za ka iya yawo da su bane.”

Hararar shi Ashfaq yayi. Yasir bai bi ta kan shi ba ya ɗauko leda ɗaya daga cikin wanda ya ajiye yana buɗewa. Sabbin brush ne a ciki, ya ɗauki ɗaya ya miƙa wa Tariq ɗaya.

“Yadda ƙwaƙwalwarka take tunanin abubuwan da ya kamata a cikin yanayi irin wannan yana bani mamaki.”

Tariq ya faɗi yana miƙewa ya nufi banƙakin da ke cikin ɗakin. Yana turo ƙofar Ashfaq ya kalli Yasir.

“Aikin Seyi ne ko?”

“Faq ba yanzun ba…”

“Ka faɗa min kawai. Shine ko ba shi bane?”

Ledar da ke gabanshi Yasir ɗin ya ture gefe ya ja kujerar da yake zaune zuwa gab da gadon Ashfaq, lokaci ɗaya fuskarshi ta canza zuwa wani irin yanayi da zai tsorata ka, tabon ɗinkin dake gefen fuskarshi tundaga wajen goshi yabi ta gefen kuncin shi har kusan wuya yana haɗuwa da yanayin da ke fuskar tashi. Sai dai yanayin fuskar Yasir ko ɗar ba ta sa Ashfaq yaji ba.

“Yanzun kake son yin maganar nan? Da ciwon dake jikinka? Da Tariq a cikin ɗakin?”

Kau da kai gefe Ashfaq ya yi, ciwon jikin shi ba zai hanashi son yin maganar ba, Tariq ne matsalar shi.

“Ina son sani ne kawai.”

“Tunanin me kake yi? Me ka sha da za kai Deal da Seyi? In da wani abu ya sameka fa? Faq kasan a halin da ka sakani? Me kake so in faɗa wa Tariq?”

Kallon shi Ashfaq ya yi da ke fassara ka cika zuzuta abu.

“Da wacce tambayar kake son in fara?”

“Kar ka gwada haƙurina Ashfaq Hisham Tafeeda.”

Dariya Ashfaq ya yi, dai-dai fitowar Tariq daga banɗakin.

“Me ake yiwa dariya?”

Ya buƙata, shiru suka yi su duka, Yasir najan kujerar shi baya.

“Ga darduma nan a ninke.”

Ya faɗi maimakon amsa tambayar da Tariq ɗin ya yi mishi. Jinjina kai Tariq yayi yana kallon Yasir ɗin.

“Babu sirri a tsakanin mu har sai da kazo.”

Cikin idanuwa Yasir ya kalle shi.

“Tsanarka ba sabon abu bane a wajena Tariq, kayi Sallah lokaci na wucewa.”

“Meye matsalar ka da Sallah ta? Gefena za’a binne ka?”

Tariq ya faɗi rai a ɓace, buɗe baki Yasir ya yi zai ba shi amsa Ashfaq ya katse shi.

“Ba za ku sa min ciwon kai ba…Tariq kayi abinda yake gabanka…”

“Amman Yaya…”

Idanuwa Ashfaq ya kafa mishi da ya sashi kasa ƙarasa maganar da ya soma. Ƙarasawa ya yi ya ɗauki dardumar yana shimfiɗawa. Kunya ta rufe shi da yadda hasken rana ya cika ɗakin. Baccin da bai yi ba daren jiya da kuma kodin ɗin da ya sha suka haɗe mishi waje ɗaya. Muryar Yasir ƙasa-ƙasa yace ma Ashfaq,

“Kaga abin da ka ja ko? Bai tsane ni haka da farko ba.”

“Wa ya ce ya tsaneka yanzun ma?”

“Hmm…”

Kawai Yasir ya faɗi ya janyo leda ɗaya ya ɗauko burger da lemon exotic don yunwa yake ji. Rabon cikin shi da wani abu tun safiyar jiya, da sauri yake ci, don haka bai ɓata lokaci wajen gamawa ba.

Miƙewa ya yi.

“Ina za ka je?”

Ashfaq ya buƙata, muryar Yasir can ƙasan maƙoshi ya amsa shi.

“Dattin da ka zubar zan goge.”

Ashfaq ɗin bai ce komai ba, kamar yadda Yasir bai jira amsar shi ba ya fice daga ɗakin.

“Allah ya sa ya tafi kenan.”

Cewar Tariq da ya idar da Sallah. Lumshe idanuwanshi Ashfaq ya yi yana buɗe su akan Tariq.

“Meye matsalar ka da Yasir?”

“Kafi kowa sanin matsalata da shi… Ba haka kake ba kafin ya zo… Yaya mu biyu ne kawai, a komai mu biyu ne. Tun zuwanshi kuka zama ku biyu… Kana kwanaki baka nan, ban san inda kake ba, amma shi ya sani… Abu irin wannan zai sameka shi ne farko a wajen bani ba…”

“Tariq…”

Girgiza mishi kai Tariq ya yi.

“Kar ka soma gaya min abinda ba zai faru ba. Ba ina faɗa maka don na san komai zai canza bane, ina faɗa maka ne don ka tambaya.”

Kai Ashfaq ya ɗaga mishi. Wani abu ya tokare mishi wuya. Girman sirrin da ke tsakanin shi da Tariq ɗin na mishi nauyi sosai.

“Ka zo ka ci wani abu.”

“Ba na jin yunwa.”

Tariq ya amsa mishi.

“Ba tambayarka na yi ko kana jin yunwa ba. Cewa ba yi ka zo ka ci wani abu.”

Yanayin muryar Ashfaq ɗin ya faɗa mishi babu wajen gardama. Don haka ya miƙe yana nannaɗe dardumar tare da komawa kujerar da Yasir ya tashi ya zauna.

*****

Abuja

Sallama ya sake yi a karo na uku, bai ji motsin kowa ba, har ya ƙarasa tsakiyar falon.

“Nuri!”

Ya kira yayin da ya samun waje ya zauna akan kujerar tare da sauke numfashi mai nauyi. Yana ficewa daga ɗakin Tasneem kasa zaman gidan ya yi kuma. Shi yasa yayo gidansu. Ƙila ko Nuri ya gani zuciyarshi za ta yi sanyi.

“Nuri!”

Ya sake kira a karo na biyu. Asabe ‘yar aikin su ce ta fito da sauri tana gaishe da Rafiq ɗin da ya amsa tare da ɗorawa da.

“Ina Nuri?”

“Sun fita ita da Aroob…amma kamar Fawzan yana nan.”

Kai kawai Rafiq ya ɗan ɗaga mata, ta juya. Numfashi ya sake saukewa, yammacin dai yau ya zo mishi wani iri. Wayarshi ya ciro daga Aljihu ya kira lambar Fawzan, har ta yi ringing ta yanke bai ɗauka ba. Ɗan daƙuna fuska Rafiq ya yi, yasan Fawzan sarai, in ya kwanta ko da baccin rana ne to ba shi da lafiya, balle kuma bayan Asr.

Ba wayarshi yake sakawa a silent ba. Sake kira ya yi, wannan karon ma har ta yanke bai ɗaga ba, miƙewa ya yi ya nufi ɓangaren Fawzan ɗin, har ya kai ƙofar ɗakin shi, kwankwasawa yayi yaji shiru, don haka ya tura yajie ƙofar a kulle. Bai san me ya sa zuciyar shi ke mishi wani iri ba. Wayarshi da ke ɗayan hannun ya yi swiping, har ya soma saka lambar Nuri, sai kuma ya fasa, Aroob ya kira, dokawa ɗaya ta ɗauka.

“Hello Yaya…”

“Aroob, kina kusa da Nuri?”

Ya fara tambaya.

“A’a gidan Hajiya Turai muka zo, suna ɗakinta. Ka kira wayarta ne? Ko in kai mata?”

Girgiza kai Rafiq ya yi kamar tana ganin shi, kafin ya ɗora da faɗin,

“Na zo gida ne, babu kowa sai Asabe. Tace Fawzan yana nan, kuma ɗakin shi a kulle. Ban san ko meye ba… Kawai bana jin yanayin na min daɗi.”

“Ka kira wayarshi to… Amma ya ce babu inda zai je da zamu fita.”

Ɗan dafe kai Rafiq ya yi, yana maida numfashi.

“Shi ne damuwar, na kira sau biyu bai ɗaga ba.”

Da sauri Aroob tace,

“Bari in gwada kira in gani.”

Rafiq bai amsa ta ba ya sauke wayar daga kunnen shi ya saka ta a cikin Aljihu. Hanyar da za ta fitar da shi daga gidan ya nufa, motocin da suka rage ya ƙirga, ya ga biyu ne kawai babu. Ya san Abba ya ɗauki ɗaya, su Nuri sun fita da ɗayar. Lokaci ɗaya zuciyarshi ta soma dokawa. Wajen Maigadi ya je ya tambaye shi ko ya ga fitar Fawzan ɗin.

“Tun bayan La’asar da ya shigo gaskiya bai fita ba, su Hajiya ne kawai…”

Rafiq bai jira ya gama ba da gudu ya juya cikin gidan, zuciyarshi na ci gaba da dokawa kamar za ta fito daga ƙirjinshi. Ya na shiga falo, wayarshi na soma ƙara, ɗaukowa ya yi ya ɗaga kiran. Muryar Aroob cike da damuwa tace,

“Wallahi bai ɗaga ba, wajen kira biyar. Me yake faruwa ne yaya?”

Shi kanshi cikin damuwar yake, ga zuciyarshi da ta ƙi daina bugawa, da ƙyar ya iya dai-dai ta muryarshi.

“Ban sani ba tukunna Aroob. Ki nutsu, ina kuke ajiye keys ɗin gidan nan? Kar ki faɗa wa Nuri komai tukunna… Kina ji na?”

“Suna… Su… Su”

Dafe kai Rafiq yayi, jin yadda Aroob ɗin take jan Numfashi, ya san tashin hankali ko ɓacin rai na saurin tasar mata da Asthma ɗin ta.

“Aroob…Aroob! Ki nutsu don Allah. Kinga ga ma Fawzan ɗin na kira na…Kashe in amsa…”

Kashewar ta yi kuwa, sai yanzun yake ganin shirmen kiran da ya yi wa Aroob din, ba ya son hankalin Nuri ya tashi ne shi ya sa, to gara nata da Aroob ɗin. Wayar Nuri ɗin ya kira, tana shiga kuwa ta ɗauka.

“Assalamu alaikum. Rafiq kazo bama nan ko?”

Nuri ta fadi da murmushi a muryarta. Lumshe idanuwanshi ya yi, muryarta na sama mishi yar ƙaramar nutsuwa. Duk da bai iya ya amsa mata Sallamar da tayi ba.

“Nuri ina kuke ajiye spare keys ɗin ku? Inajin Fawzan na ɗakin shi, kuma ya kulle, ina ta kira bai ɗaga ba, na ƙwanƙwasa ma shiru…. Jikina na min wani iri…”

Ya ƙarasa yana kai hannu da goge zufar da yake ji a goshin shi, har hannuwanshi ma sun yi zufa saboda tashin hankalin da yake ji.

“Ka duba a ɗakina, wajen drawer ɗin gado, duka suna ciki.”

Kai yake ɗagawa tunda ta fara magana.

“Rafiq… Ka nutsu… Ga munan zuwa muma.”

Kan ya sake ɗagawa, bai san ƙafafuwan shi ma na ɗaukar shi zuwa ɓangaren Nuri ba, bai cire wayar daga kunnen shi ba sai da ya ji ta kashe kiran daga can ɓangaren ta tukunna, aljihu ya mayar sanda ya tura ɗakin Nuri ya shiga, inda tace mishi ɗin ya nufa kuwa, yana janyo drawer ɗin farko ya gansu a ciki, ɗaukowa ya yi tare da komawa ɓangaren ɗakin Fawzan.

Soma gwada mukullan ya yi a jikin ƙofar, ya sa sun kai guda goma, amma babu wanda ya buɗe mishi ƙofar, ga hannunshi da dukkan jikinshi da ke ɓari, bai taimaka wajen nutsuwar da yake buƙata ba.

“Damn it…”

Ya faɗi yana dukan ƙofar da ƙafar shi.

“Fawzan… Don Allah kar abinda ya same ka…”

Ya faɗi muryarshi can ƙasa, zuciyar shi kamar za ta faɗo, babu mukullin da bai gwada ba a jiki amma sun ƙi buɗewa.

“Asabe! Asabe!! Asabe!!!”

Yake kira cikin ƙaraji da ƙosawa, ci gaba da kiranta ya yi babu ƙaƙƙautawa, kafin ta ƙaraso da gudu. Mukullan hannunshi Rafiq ya miƙa mata.

“Buɗe min ƙofar nan.”

Ya buƙata muryarshi a dakushe da yanayin da yake ji. Tsayawa ya yi yana kallonta tana saka kowanne mukullin kamar yadda ya gama yi babu jimawa, sai da ta gwada kowanne tukunna ta kalle shi, muryarta a ɗan tsorace da yanayin da take gani a ciki.

“Hajiya tace wani lokaci in anga haka, akwai mukulli a jikin ƙofar daga ciki.”

“Damn it, Fawzan…”

Rafiq ya faɗi yana ja da baya tare da dukan ƙofar da kafaɗar shi. Amsawar da ta yi kamar ƙashin wajen ya karye na aika wa ƙwaƙwalwar shi da wani irin raɗaɗi mai zafin gaske. Sake gwadawa yayi amma ko motsin kirki bai ji ƙofar ta yi ba. Matsawa ya sake yi da baya ya sa ƙafar shi wannan karon dai-dai inda wajen mukullin ƙofar yake. Sau huɗu ya yi hakan, wajen ya karye, ƙofar na buɗewa, Asabe na tsaye tana kallon shi don ba ta san me ya kamata ta yi ba. Da gudu Rafiq ya shiga ɗakin, ƙafafuwan shi suka tsaya cak, ganin Fawzan kife a ƙasa, hannun shi ɗaya miƙe da alama yana son ɗaukar wani abu ne, inhaler ɗin shi dake can gefe Rafiq ya hango.

Girgiza kanshi yake yana faɗin,

“Fawzan… No… No… No… Please No…”

Zuciyar shi na gaya mishi ya ƙarasa ya taɓa Fawzan ɗin, yadda yake ganin shi kwance ko alamun numfashi babu a jikinshi balle motsi na ƙara wa bugun zuciyar shi gudu cike da bayyanannen tsoron da ya nuna har akan fuskar shi. Cikin ƙarfin halin da ba ya ji sam ya ƙarasa tare da tsugunnawa. Hannunshi na ɓari ya dafa kafaɗar Fawzan, kafin ya sa ɗayan hannun ya juyo da shi, idanuwan Fawzan ɗin rabi a buɗe, rabin su a lumshe, sosai ya ja shi ya ɗora shi a jikin shi tare da girgiza shi.

“Fawzan… Fawzan… Don Allah ka tashi. Kar kai mana haka… Ba za kai mana haka ba… Ka tashi.”

Fawzan bai ma san duniyar da yake ba, balle ya ji me Rafiq yake faɗi, dube-dube yake a ɗakin cikin tashin hankali ko zai ga wani abu da zai taimaka musu, mukullin motar Fawzan ɗin ya hango.

‘Asibiti’ wata murya ta faɗa mishi. A hankali ya sauke Fawzan daga jikinshi ya ɗauko mukullin motar ya saka a aljihun shi. Dawowa ya yi ya tallabi Fawzan da yake jin ya mishi nauyin gaske, da ƙyar ya kaishi waje yana maida numfashi. Wajen motar Fawzan ɗin ya ƙarasa dasu, ya jingina rabin jikin Fawzan da motar, rabi da jikinshi ya ɗauko mukullin ya buɗe bayan motar. Da ƙyar ya samu ya saka Fawzan a ciki tukunna ya rufe ya zagaya ya zauna a mazaunin driver. Ya saka mukullin motar a jiki, ya murza, kan shi na bugawa kamar wanda aka dokawa wani abu, numfashi ya ja da sauri yana fito dashi. Steering wheel ɗin yake kallo, zuciyarshi na bugawa fiye da ɗazun. Hannu ya sa a jiki, kanshi ya sake bugawa a karo na biyu. Runtse idanuwanshi ya yi, jan abu yake gani ko’ina cikin kanshi kafin ya fahimci jini ne, da sauri ya bude idanuwanshi yana kallon motar a tsorace.

Juyawa yayi ya sake kallon Fawzan dake kwance a bayan motar, yasan ya kamata ya ja su tafi Asibiti, hannun shi ya kai jikin steering wheel din, kanshi ya sake dokawa, kamar zai rabu da gangar jikinshi. Dukan steering wheel din ya yi da karfin gaske ya saki karamar ƙara saboda ciwon da kanshi yake yi har a ko’ina na jikinshi.

Ya manta rabon da ya gwada tuƙi, ya manta azabar da yake shiga duk lokacin da ya gwada yin hakan, kamar yadda ya kasa tuna dalilin faruwar hakan. Don sosai yake tuna lokuta da dama da yake kai kanshi ko’ina a mota, har ma da ƙannen shi.

“Fawzan na kasa…. Na kasa wallahi.”

Ya faɗi muryarshi na rawa kamar zai fashe da kuka. Jikin shi ko’ina ɓari yake yi. Dafe fuskar shi ya yi cikin hannuwan shi biyu yana jin komai ya haɗe mishi waje ɗaya. Ya rasa da abinda ya kamata ya ji, sam bai ji buɗe murfin motar ba, sai dafa shi da ya ji anyi.

Hakan ya sa shi buɗe fuskar yana kallon kafaɗar shi kafin ya maida dubanshi inda Nuri take tsaye.

“Nuri…”

Rafiq ya faɗi yana fitowa daga motar da sauri, ganinta na sa duk wata damuwa da yake ciki sake danne shi, rungumeta ya yi a jikinshi, zuciyarshi na ciwo, yana jin kamar ya cire ta ya ajiye a gefe.

“Na kasa Nuri…”

Yana jin tana ɗaga mishi kai da yake fassara ta fahimta. Kafin ta zame jikinta daga riƙon da Rafiq ɗin ya yi mata.

“Shiga bayan muje…. Aroob koma ta can ɓangaren.”

Cewar Nuri, su dukansu abin da ta ce ɗin suka yi, Rafiq na ɗago Fawzan zuwa jikinshi sannan ya zauna yarufe murfin motar.

*****

Da gudu aka shiga ɗaya daga cikin ɗakunan dake ward B na King’s hospital da Fawzan da aka sa wa oxygen mask kafin a shiga da shi. Binsu Rafiq yake shirin yi. Nuri ta riƙo hannunshi tana girgiza mishi kai. Kallon ta yake cike da tashin hankali.

“Da baku zo ba… Da sai dai ya mutu? Nuri me yasa ba zaku faɗa min abin da yake damuna ba? Me yasa bana iya tuƙi?”

Kallon juna Nuri da Aroob suka yi. Kafin Nuri ta maida hankalinta kan Rafiq da ya daƙuna fuskarshi kamar zai yi kuka.

“Munzo yanzun ai, babu abinda zai same shi…”

Girgiza mata kai Rafiq yake yi, wannan karon yana son sani. Wuri ya samu ya zauna cikin ɗaya daga cikin kujerun silver ɗin da ke wajen jiran. Muryarshi can ƙasa yake kallonta.

“Ina son sani, ina son sanin koma menene Nuri.”

Juyawa Nuri ta yi ba ta son Rafiq ɗin ya ga hawayen dake cike da idanuwanta. Ta fanni da yawa mantawarshi alkhairi ce, halin da yake ciki yanzun ya fi sauƙi akan wanda zai shiga in ya sani.

“Nuri…”

Rafiq ya kira sunanta, da ƙyar ta samu nutsuwar da ta juya ta kalle shi sosai cikin fuska. Damuwa ce shimfiɗe a cikin idanuwan shi, ta rasa yadda akai ba ta kula da ramewar da ya yi ba, don ta fi ƙarfin ta tashin hankalin da yake faruwa dasu yau din nan.

“Ba yanzun ba… Sai wani lokacin Rafiq.”

Yanayin yadda ta yi maganar a gajiye ne ya sa Rafiq ɗin jingina sosai da kujerar tare da yin shiru. Ko ba da Nuri ba, ba ya son jan magana. Aroob ce ta ƙarasa gefen Rafiq ta zauna, a hankali ta matsa ta kwantar da kanta a kafaɗar shi, ɗan kallon ta ya yi, hakan ya sa ta riƙo hannunshi ta dumtse cikin nata tana faɗin,

“Komai zai yi dai-dai.”

Sauke numfashi ya yi, in da ta san yadda yake tsananin buƙatar jin kalaman nan da ta sake maimaita mishi. Lumshe idanuwanshi ya yi kawai yana ci gaba da maida numfashi.

Alkalamin Kaddara 2 >>

4 thoughts on “Alkalamin Kaddara 1”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×