Skip to content
Part 12 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

LITTAFI NA BIYU

Agogon shi yake dubawa, jira na ɗaya daga cikin abinda ya tsana a rayuwar shi. Ya fi awa ɗaya da kiran Fawzan, baisan me yake ba har yanzun, inda yasan ba zai zo da wuri ba ko ya yi nisa sai ya faɗa mishi ya sani. Wayar shi ya sake ɗauka yana kiran Fawzan ɗin, bugun farko ya dagae da faɗin,  

“Na kusa Yaya…”

Muryar Rafiq cike da gajiyar da yake ji har cikin ƙasusuwan shi ya ce, 

“Haba Fawzan…inda baka kusa ne sai ka faɗa min, kasan bana son jira.” 

“Ka yi haƙuri, na kusa wallahi.”

“Ka kyauta…”

Rafiq ya faɗa bai jira ko me Fawzan yake shirin cewa ba ya janye wayar daga kunnen shi yana katse kiran. Gajiyar da yake tare da ita ta ishe shi, ba saiya ƙara da ɓacin ran da Fawzan yake son saka mishi ba. Ko bayan wayarsu saiyda ya ƙara mintina talatin kafin ya hango shi. Bai miƙe daga inda yake zaune ba, har sai da Fawzan ɗin ya ƙaraso yasa hannu ya ɗauki jakar Rafiq ɗin da faɗin,  

“Cunkoso ya yi yawa a hanya ne, sannu da zuwa…” 

Idanuwa Rafiq ya kafe shi da su, yanajin ƙaryar Fawzan ɗin tun a muryarshi, ganin ya juya ba tare dayae yarda ya kalli Rafiq ɗin ba yasa ya miƙe yana bin bayanshi, har wajen motar suka ƙarasa, ya zagaya ya shiga ɓangaren driver, Rafiq ɗin ma ya buɗe ya shiga. Baya Fawzan ya jefa jakar Rafiq ɗin yana saka mukullin a jikin motar tare da murzawa. 

Hannun nashi da ke rawa Rafiq yake kallo, kafin ya mayar da dubanshi zuwa fuskar Fawzan ɗin yana son fahimtar meke faruwa. 

“Fawzan…”

Ya kira muryarshi cike da tambayoyin da baisan ta inda zai fara su ba. Motar zai ja Rafiq ya kai hannu kan mukullin yana kashe motar. 

“Me yake faruwa?”

Ya tambaya muryar shi babu alamun wasa a ciki. 

“Bakomai.”

Cewar Fawzan yana sake kai hannu kan mukullin ya kunna motar, wannan karon da sauri ya yi baya yana juyata, inda akwai wani tsaf zai doka musu, don ko dubawa bai yi ba. Saida zuciyar Rafiq ɗin ta doka. 

“Fawzan menene wai? Me yake damun ka haka?”

Ganin ya yi shiru yana maida dukkan hankalin shi kan tuƙin da yake yasa ran Rafiq ɓaci. 

“Tsayar da motar nan…”

Kamar bai ji me ya ce ba ya ci gaba da tuƙin shi yana fita daga airport ɗin. 

“Ka tsayar da motar nan kafin ranka ya yi mugun ɓaci Fawzan…” 

Wannan karon muryar Rafiq ɗauke take da kashedi da kuma yadda nashi ran yake a ɓace. Sauka Fawzan ya yi daga titi yana parking a gefen hanya, idanuwanshi na kan titi har yanzun. Yana jin idanuwan Rafiq na yawo a gefen fuskarshi, kamar suna ƙoƙarin shiga cikin jikinshi ta fuskar su ga me yake ɓoyewa. 

Tunda Rafiq ya ce yana airport komai ya sake kwance mishi. In hankalin shi ya yi dubu a tashe kowanne yake. Baisan me zai ce mishi ba, baisan ta inda zai fara faɗa mishi an ɗaura auren Zafira har yaune tarewarta ba, baisan ya zai mishi bayani ya fahimta ba. Duk da a kwanakin nan Zafira ta yi iya ƙoƙarinta na nuna mishi auren ba laifin kowa bane ba, ya riga ya faru, damuwar shi ba zata canza rubutun da alƙalamin ƙaddara ya yi mata ba.  

A hankali ya juyo yana sauke idanuwan shi cikin na Rafiq ɗin. Sai dai ya rasa me zai ce mishi. 

“Menene? Wani abu ya faru da bana nan?”

Sai da Fawzan ya haɗiyi wani abu da yake ji tsaye a maƙoshin shi tukunna ya ɗaga wa Rafiq ɗin kai yana ɗorawa da faɗin, 

“Ka bari mu je gida don Allah…”

Saida ya ɗan kalle shi na mintina tukunna ya jinjina kai, bugun zuciyarshi da yake ƙaruwa a hankali yana sashi ƙin jin lokacin da Fawzan ya tashi motar yana janta. Yawo tunanin shi yake yi wajaje daban-daban yana son guessing ɗin abinda ya faru ya kasa. A haka suka ƙarasa gida, da ƙyar ya raba kanshi da tunanin da ya maƙale mishi yana buɗe murfin motar ya fito, wayar da ke riƙe a hannunshi ya saka cikin aljihu. 

“Alhamdulillah…”

Ya faɗi a fili tare da yin miƙa saboda gajiyar da yake tare da ita, wuyanshi ya juya, sai dai me, motoci ne birjik a cikin gidan, har wajen parking ɗinsu ya cika taf an ajiye wasu a harabar gidan. Cike da rashin fahimta ya kalli Fawzan dake kallon shi da wani yanayi a fuskarshi da baya so. 

“Me ake yi? Motocin meye?”

Daga inda Fawzan yake tsaye, muryarshi na karyewa ya ce, 

“Ka yi haƙuri Yaya…don Allah ka yi haƙuri wal…”  

Hannu Rafiq yasa duka biyun yana toshe kunnuwanshi kafin ya ɗaga wa Fawzan su yana girgiza mishi kai, alamar baya ji. Saboda dalili ɗaya ya sani da za’a yi wannan taron, kuma Daddy ba zai taɓa yi mishi haka ba. Ba don bai saba canza maganganun shi akan abubuwa da yawa ba, sai don wannan ya fi kowanne a cikin waɗancan girma da muhimmanci. 

Daddy ba zai mishi haka ba, ba zai taɓa aurar da Zafira bai sanar da shi ba, ko ba komai ƙanwarshi ce, yana da haƙƙin a sanar mishi shi ma. Kuma ai sun yi waya da Nuri da zata faɗa mishi, ita kanta Zafira ɗin ya kirata bata ce mishi komai ba, ta tabbatar mishi da cewar komai lafiya, hakama Aroob da shi kanshi Fawzan ɗin. Saboda me zai tsaya a gabanshi yanzun da yanayin nan a fuskarshi, da yanayin da ke fassara yana shirin faɗa mishi abinda ba zai taɓa son ji ba. 

Ganin yadda fuskar Rafiq ɗin ta canza lokaci ɗaya, da asalin ruɗani da tashin hankalin da ke cikin idanuwanshi yasa Fawzan jan numfashi, yanajin wani irin abu a zuciyarshi, sai yanzun ya ga dalilin da yasa Zafira ta roƙi kowa kar ya faɗa wa Rafiq ɗin, a bari sai ya dawo, bai ma tabbatar ba yanzun amma fuskar shi na yin kamar babu jini a jikinta, kamar zai iya faɗuwa a kowanne lokaci. 

Zagayowa Fawzan ya yi yana tsayuwa gaban Rafiq ɗin da kai hannu zai riƙo kafaɗarshi, matsawa ya yi da sauri yana girgiza mishi kai, kafin ya yi wata irin dariya da babu nishaɗi a cikinta. Juyawa yayi yana nufar cikin gidan da sauri. In har abinda yake tunani ne ya faru Daddy ya mishi rashin adalci marar misaltuwa da bayajin zai iya yafuwa. 

Wani irin sama-sama yake jin shi, da duk takun da yake yi zuwa cikin gidan da tashin hankalin da yake ji yana rufe shi. Daddy bai yi amfani da farin cikin Zafira kacokan don siyasarshi ba, son kan Daddy bai kai haka ba, Nuri ba zata barshi ba, son da take mai ba zai rufe mata ido kamar koyaushe ba. Shi ne abinda Rafiq yake maimaitawa cikin kanshi ko zuciyarshi zata yarda. 

“Yaya…Yaa Rafiq…”

Yake jin muryar Fawzan can ƙasa, don ba ta shi yake yi ba yanzun, cikin gidan su kawai yake son ya ganshi, dai-dai bakin ƙofa ya ci karo da su Anty Shafa, da sauran mutanen da gane su bai da muhimmanci a yanayin da yake ciki. 

“Rafiq…”

Anty Shafa ta faɗi muryarta cike da fara’ar da baisan menene alaƙarshi da ita ba, hannu da take riƙe da shi mai ɗauke da ƙunshi ne matsalarshi, dan ko sare hannun aka yi aka saka cikin wasu zai gane shi, ko da babu zoben da ke jiki da su dukkansu akwai shi a nasu hannayen. Kafin ya ɗauke idanuwan yana yawatawa da su kan Zafira da ke sanye da doguwar riga ruwan toka kanta a ƙasa, fuskarta lulluɓe da mayafi, ba za ka gane kuka take ba saika kula da yadda kafaɗunta ke ɗagawa da saukar numfashin ta. 

Wani irin dokawa zuciyar Rafiq take yi kamar zata fito a ƙirjinshi, duka duniyar na mishi tsaye cik, hannun shi kamar an ɗaura dutse saboda nauyin da duka jikinshi yayi, da zai iya da ya adana yanayin nan ko don gaba, in wani ya tambayeshi ya tashi hankalin yake sai ya nuna mishi, don kuwa ba zai taɓa misaltuwa da kalamai ba.  

Hannun Zafira da ke cikin na Anty Shafa ya riƙo tare da fisgewa. 

“Zaf..”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi yana sakin hannunta tare da kama mayafin da ke lulluɓe da fuskarta ya ɗaga shi baya. 

“Zaf…Zafira…”

Ya ƙarasa yana jan numfashi, runtsa idanuwan shi ya yi yana buɗe su, ƙirjinshi da kanshi sun ɗauki zafin gaske, akwai abinda ya kamata yayi don ya ji sauƙi amma ya kasa, zuciyarshi bata da lafiya. 

“Ka yi numfashi Yaya…”

Yaji Zafira ta faɗi muryarta na karyewa tana ƙara mishi abinda yake ji. Numfashin ya ja kuwa yana jin yadda iskar ta yi mishi kaɗan, sosai ya ci gaba da maida numfashi kamar wanda asthma ke shirin kamawa. 

“Rafiq lafiyarka kuwa?”

Ya ji wata da bai san wacece ba na tambaya, yana jin yadda sunan shi da lafiya a layi ɗaya suka zama baƙin juna, dafa shi ya ji anyi. 

“Yaya…”

Wannan karon ya gane muryar Fawzan, ya kasa juyawa ne. Zafira yake kallo da take wani irin kuka. Kai yake girgiza mata yana son wani ya taimaka ya tashe su daga wannan mugun mafarkin da suke, yana son farkawa daga tunanin cewa Daddy zai yanke rayuwar Zafira haka, zai mata wannan rashin adalcin, zuciyarshi kokawa take da yarda da cewa Nuri zata bari Daddy yayi haka. 

“Yaya…kai min addu’a…”

Zafira ta ƙarasa muryarta a dakushe saboda kukan da take, ganin Rafiq ɗin ya dawo mata da komai sabo, ta ɗauka tun satin auren ta gama jin ciwo irin haka, don ta riga ta karɓi ƙaddarar ta da hannuwa biyu, ta ma Muneeb bankwana tuntuni, bata san ya zata cire son shi ba, amma ba zai kaita da halaka ba, ta san yadda daraja ta aure take, lahirarta kuma na da muhimmanci sama da duniyarta. 

Bata fito daga gida ba yanzun sai da niyyar zama saboda Allah a rayuwar aurenta. Aroob ce ta fara sata kuka sosai, don ko nasihar da Nuri tai mata zuciyarta a bushe take jinta. Yanzun kuma ganin Rafiq yasa komai ya kwance mata, yadda yake kallonta kamar duniyarta ta zo ƙarshe bai kuma san yadda akai hakan ya faru ba, ƙaunar shi na da muhimmanci a wajenta. 

Jan Zafira ya fara yi yana kutsawa cikin matan da ke zagaye da ita da dole suka fara bashi hanya ya wuce. Anty Shafa ce zata bi bayansu Fawzan ya tsayar da ita. 

“Ki ƙyale su…”

“Wane irin a ƙyale su? Baka ga mutane na jiranta ba, angon sun yi waya tun ɗazun suna Airport za su wuce…” 

Anty Rabi ce da wannan maganar. 

“In ba za su iya jira ba su tafi…”

Fawzan ya faɗi yana bin bayan su Rafiq ɗin. A falon gidan ya same su zaune kan kujera. Tsaye ya yi yana kallon su, Rafiq kam ya rasa ta inda zai fara, saboda bai shirya ba, kallon Zafira yake yana so ta tabbatar mishi cewar mafarki yake yi. Cikin idanuwanshi ta karanci tambayar shi. 

“Ya faru Yaya, tun sati biyu da suka wuce ina da aure…” 

Numfashi ya ja wani abu na tokare mishi ƙirji da tabbacin ta. 

“Yaya…”

Ta kira wasu sabbin hawayen na zubo mata. Kai yake girgiza mata tare da faɗin, 

“Minti ɗaya Zaf, ina shiryawa ne… Ki ban minti ɗaya don Allah…” 

Shirun ta yi kamar yadda ya buƙata. Shi ma idanuwanshi ya runtse yana ƙoƙarin tattaro duk wata nutsuwa da zai iya ko da ta lokacin ce kawai, buɗe idanuwan ya yi akan Zafira, sai dai ya rasa abinda zai fara ce mata, yana jin da bai yi tafiyar da ya yi ba ƙila da ya iya yin wani abu akan auren. Muryar shi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Kiyi haƙuri… Don Allah kiyi haƙuri…”

Wannan karon ita ta girgiza mishi kan. Tana ƙoƙarin shanye kukan da take yi ko don Rafiq ɗin, bata son ganin yanayin da yake ciki saboda ita.  

“Ba laifinka bane… Don Allah karka ɗora laifin nan akan ka…kamin addu’a kafin su zo…” 

Addu’ar yake son yi mata, amma ya rasa ta inda zai fara, yin Addu’ar zai zama kamar ya amince da auren ne, kuma abu ne da baya hango faruwarshi. Fawzan ya kalla. 

“Kira Aroob, ku zo mu tafi airport ɗin…”

Fawzan bai jira ya faɗa mishi sau biyu ba ya nufi ɓangaren su Aroob ɗin da gudu. Baifi mintina uku ba suka fito shida Aroob, ɗankwalinta a hannu, fuskarta a kumbure tana jan hanci da alamun har lokacin kuka take yi. Miƙewa Rafiq ya yi tare da Zafira, da kanshi ya kama mayafin ta yana sauko da shi ya rufe mata fuska tukunna ya jata suna yin hanyar ƙofa. 

Aroob da Fawzan na bin bayansu, ko takan mutanen da ke jira a waje bai yi ba, Fawzan ne ya tsaya faɗa musu Airport ɗin za su yi. Shi ma bai jira yaji surutun da su Anty Rabi Suke yi ba, in sun ga dama su biyo su, inma ba za su biyo su ba wannan duka matsalarsu ce. Shi ya buɗe wa Zafira mota ta shiga, ya zagaya yana shiga, Aroob da Fawzan suka shiga baya. Wayarshi ya haɗa jikin motar tukunna ya kunna yanayin baya don su fita daga gidan. 

Sai da suka fita tukunna ya yi dialing lambar Naadir, ƙarar kiran ya gauraye motar gaba ɗaya, sai da ta kusan yankewa tukunna ya ɗaga. 

“Yaya you home safe I guess? (Yaya ka isa gida lafiya nake zato?)” 

Aroob da muryarta take a dakushe ce tace

“Kaje wajen Naadir ne Yaya?”

“Aroob!”

Naadir ya kira kamar zai fasa musu kunne, sai da Fawzan ya ɗan runtsa idanuwanshi. 

“Kai zaka fasa mana kunne ne, a speaker kake fa cikin mota kuma…” 

Dariya Naadir ya yi. 

“Yayaaaaaaa Fawzan!”

Ya sake faɗi da ƙarfi fiye da yadda ya kira Aroob ɗazun, muryarshi cike da farin ciki. 

“Naadir ranka zai ɓaci.”

Wannan karon Rafiq ne yai maganar, saboda kanshi da yake sarawa, ihun Naadir ɗin na ƙara mishi ciwon kai. Dariya Naadir ya yi da faɗin, 

“Sorry babban Yaya… Tsaya ku duka kuna tare, Zaf fa?” 

“Naadir…”

Ta kira muryarta na karyewa, kewarshi take ji sosai, kamar ta bi ta cikin wayar ta ganshi. 

“Zaf, are you okay?”

Ya buƙata muryarshi ɗauke da damuwa. 

“Lafiyata ƙalau, kaifa?”

“Are you missing me this much? (Kina kewata har haka ne?)” 

Duk da yanayin da take ji sai da murmushi ya ɗan ƙwace mata. 

“Zafira ta yi aure Naadir…”

Rafiq yace yana jin kalaman baƙi a muryarshi. 

“What? Wait, how? When? Why? (Me? Tsaya, tayaya? Yaushe? Saboda me?) 

Naadir ya jero tambayoyin mamaki fal a muryarshi. Ɗan ɗaga kafaɗa Rafiq ya yi. 

“Saboda Daddy yana so shi yasa, sati biyu kenan, zamu rakata Airport ne yanzun ita da mijin za su tafi.” 

Shiru Naadir yayi na ‘yan daƙiƙu kafin cikin sanyin murya ya ce, 

“Zaf…”

Sanyin da ya kirata da shi ne yake son saka sabon kuka ƙwace mata. 

“Naadir…”

“Kina son shi?”

Kuka ne mai sauti ya kwace mata. 

“Yaya me yasa ka bari? Bata son shi kana ji, don Allah kar ku kaita, me yasa Daddy zai yi haka. Ku dawo nan mu yi zaman mu, ba’a haka a nan…” 

“Kiranka na yi mu rakata tare…”

Rafiq ya faɗi yana jin kamar ya juya da motar su koma gida. 

“Me yasa ka bari?”

Naadir ya sake maimaitawa. Jin Rafiq ɗin ya yi shiru yasa shi kashe wayar daga ɗayan ɓangaren. 

“Ya kashe ko?”

Fawzan ya faɗi yana jin wannan laifin nashi ne, tambayar shi ya kamata Naadir yayi ma ba Rafiq ba, tunda a hannunshi Rafiq ya bar komai kafin ya tafi. Rafiq bai amsa shi ba ya sake kiran Naadir ɗin, har sai da ta yanke bai ɗauka ba, sake kira ya yi bugun farko Naadir ya ɗaga. 

“Ka kashe min waya Naadir…”

“Na sani…”

Naadir ya amsa muryarshi babu walwala. 

“Yaushe kai girman da za ka kashe min waya don kana tunanin na maka wani abu?” 

Rafiq ya tambaya muryar shi a dakushe da ɓacin rai. Raini na cikin abubuwa manya da baya ɗauka, kasancewar Naadir nesa da su baya nufin dokar bata bi ta kanshi. Shiru ya ziyarci motar na wani lokaci kafin a hankali Naadir ya ce 

“Ka yi haƙuri…”

Jinjina kai Rafiq ya yi. 

“Ban ji ka ba…”

“Yaya mana… Ka yi haƙuri na ce.”

Ya maimaita kamar zai yi kuka. 

“Good, ka sake tambayata yadda ya kamata”

“Me yasa ka bari aka yi auren tunda bata son shi?” 

Numfashi Rafiq ya sauke

“Saboda babu yadda zan yi da Daddy…”

Ya faɗi, gaskiyar kalaman na zama tare da shi. Ko da yana nan baya tunanin akwai abinda ya isa ya yi, Daddy na nuna ƙarfin ikonshi akansu koda yaushe. 

“Karka damu Naadir, zan soshi a hankali…”

Zafira ta ce muryarta na karyewa. Muryar Naadir ɗin ma rawa take wannan karon. 

“Yaya don Allah ka kashe wayar da kanka, ba zan iya ji ba wallahi, don Allah ka kashe…” 

Hannu Rafiq ya kai yana katse kiran ya zare wayar ya saka a gaban aljihun shi. Wannan karon gaba ɗaya hankalin shi yana kan tuƙin da yake yi, kamar babu wani abu mai muhimmanci da ya kamata yayi banda tuƙin. 

Sun fi mintina biyar da ƙarasawa Airport ɗin, amma babu wanda ya ko motsa daga zaman da yake yi ballantana ya yi niyyar fita daga cikin motar. Rafiq ne ya ja wani irin numfashi mai sauti yana fitar da shi, tukunna ya zare mukullin motar daga jiki ya kai hannu ya buɗe ɓangaren shi yana fita. Zagayawa ya yi ya buɗe wa Zafira yana miƙa mata hannunshi. 

Da idanuwanta da suke cike da hawaye ta kalli hannun nashi, kafin ta sa nata a ciki, ya taimaka mata ta fito daga motar. Zuciyar shi ta kasa yarda da auren nan, bai ma san ta inda zai fara ba. Nasiha ko addu’a ya kamata ya yi mata, amma in ya yi ɗaya daga cikin biyun, zai zamana kamar ya yarda da auren ne, abu ne da ba zai faru nan kusa ba. 

“Allah ya tsare ki a duk inda kike, ki kula da kanki sosai, ki kirani ko me ya faru, kina kirana zanzo in ɗauke ki mu dawo gida…” 

Rafiq yake faɗi yana jin kamar lokacin da take Secondary School ne, don boarding ta yi, zuciyarshi kuma bata so a lokacin, kullum jiran kiranta yake yi, har sai lokacin da take aji uku tukunna ta kirashi bata da lafiya, tunda ya ɗaukota bata sake komawa ba. Wannan karon ma zai jira har sai lokacin da ta gane wannan auren sam ba irin shi bane ya dace da ita. 

“Kina jina ko? Ki kirani, zan jira harki kira ni…” 

Ya sake maimaitawa da wani nisantancen yanayi a muryarshi. Hawayenta ne suka zubo, tana jin ɗumin su na bin kuncin ta, bata da ƙarfin zuciyar da zata tuna mishi aure ne wannan, fatan kowa ya zamana har abada, don haka ta jinjina mishi kai kawai. Tana kallonshi ta cikin mayafinta ya sauke numfashi, kamar ya samu tabbacin da yake buƙata na cewar zata kirashi lokacin da ya kamata. 

Suna nan tsaye har su Anty Rabi suka ƙaraso, lokacin ne ma Rafiq ya kula Aroob da Fawzan sun fito daga motar suma. Ganin su yasa Fawzan matsowa kusa da su, hannun Zafira ɗayan ya kama yana dumtsawa da nashi, kamar yana son bata karfin gwiwa, a lokaci ɗaya yana son tabbatar wa kanshi fiye da ita, yadda komai zaiyi dai-dai. 

“Be well Sister…”

Ya faɗi can ƙasan maƙoshi. Kai Zafira ta jinjina mishi shima, tana jin yadda kewarsu ta fara cika mata zuciya tun bata yi nisa da su ba. Baisan me zai sake cewa ba, saboda ya fara jin numfashin shi baya kaiwa ƙirjinshi yadda ya kamata, hakan na sa shi runtsa idanuwan shi yana wani irin maida numfashi. Dai-dai ƙarasowar su Anty Rabi inda su Rafiq ɗin suke. 

“Fawzan…”

Rafiq ya kira.

“Yaa Fawzan…”

Zafira ta faɗi tana sake dumtsa hannun shi da ke cikin nata. 

“Me ya same shi?”

Anty Shafa ce da wannan tambayar. Su Anty Rabi da sauran wanda suke tare na zuba musu idanuwa suna son jin amsa. Daga Rafiq har Aroob babu wanda yabi takansu, a yadda suke ji yanzun babu wani abu mai muhimmanci da ya wuce su. 

“Yayaaa…”

Aroob ta faɗi tana kamo ɗayan hannunshi ta saka mishi inhaler ɗinta ciki. Bata ma san ya akai ta ɗauko ba, Rafiq yasa su sabawa da ɗauka ko ɗaki za su fito, yanzun ta saba ma, bata sanin lokacin da take ɗauka, wasu lokutan har banɗaki in zata shiga sai dai ta ganta a hannunta. Wannan karon ɗaukar ta zo da muhimmanci da Rafiq kan kwatanta musu. 

“Calm down… Fawzan ka kalle ni…”

Rafiq yake faɗi, don ganin yadda Fawzan ke ƙara runtsa idanuwan shi gam yana kokawa da numfashin shi. 

“Wai me ya same shi…”

Wata ta sake tambaya da Rafiq ɗin bai damu da ita ba, ballantana ya juya ya kalleta har ya bata amsa. 

“Yaa Fawzan zuciyata ba zata taɓa nutsuwa ba in na tafi sanin baka da lafiya… Ba za ka yi min haka ba yau….ba za ka yi min haka ba… Don Allah kar kai min haka…” 

Zafira ta ƙarasa cikin kuka. Lumshe idanuwan shi Rafiq ya yi yana buɗe su. Sakin hannun Zafira ya yi yana ƙarasawa inda Fawzan yake tsaye, yasa hannuwanshi duka biyun tare da tallabar fuskar Fawzan ɗin. 

“Ka buɗe idanuwanka Fawzan…”

Rafiq ya ce, yana jin yadda muryarshi ta fito a raunane, duk yadda ya yi ta da ƙarfi a zuciyarshi. Can sama Fawzan yake jinsu, kamar suna wata duniyar ta daban, ƙirjinshi zuwa maƙogwaron shi kamar an kunna mishi wuta, iska bata kai mishi inda yake so, zuwa yanzun ya fara kokawa da numfashin shi sosai. Cikin nutsuwa Rafiq ya ce, 

“Fawzan don Allah ka buɗe idanuwan ka…”

Don ba yau ne farko da irin hakan yake faruwa da su ba. 

“Wai bakwa ji ana muku magana?”

Anty Shafa ta tambaya ranta a ɓace. 

“Don Allah ku ƙyale mu!”

Aroob ta faɗi a ƙagauce, hawaye masu zafin gaske na zubo mata. Kowa bakinshi ya ja ya yi shiru, suna kallon ikon Allah. A hankali Fawzan ya buɗe idanuwanshi da suka sake launi yana sauke su cikin na Rafiq ɗin. 

“Ka ja iska… A hankali, ta bakinka ko hanci, duk inda kake jin ya fi maka sauƙi, a hankali, karka yi tunanin komai….ka bada muhimmanci akan iskar kawai…” 

Rafiq yake umarta, duk abinda yace Fawzan ɗin yake yi, ko da ya so ma yadda kanshi ya ɗauki ɗumi ba zai iya tunanin komai da ya wuce samun sauƙi a ƙirjinshi ba. 

“Ka ja iska, a hankali… Mu yi tare…”

Taren suka ci gaba da yi, har na tsawon mintina biyar, har sai da Fawzan ɗin ya fara samun nutsuwa, tukunna Rafiq ya saki fuskarshi yana sauke ajiyar zuciya. Aroob ya kalla 

“Ku zauna a mota yanzun zan dawo…”

Saida Aroob ta zo ta rungume Zafira gam.

“Karki karya min haƙarƙari…”

Zafira ta faɗi muryarta a shaƙe. 

“Kiyi shiru, za ki yi kewata na sani…”

Cewar Aroob, hannuwanta Zafira ta zagaya tana riƙe Aroob ɗin ita ma, kafin ta ce, 

“Ko kaɗan…”

“Ƙarya ne…”

Aroob ta faɗi, sunayin dariya duk da kukan da suke. 

“Allah ya kareki a duk inda kike, ki kira Yaya ko me ya faru, zai zo ya dawo mana da ke gida…” 

Kai kawai Zafira ta ɗaga mata, sai da Aroob ɗin ta sake matse ta tukunna ta saketa. Idanuwan Rafiq bai bar kansu ba, sai da ya ga Fawzan da Aroob sun shiga mota sun zauna tukunna. Hannun Zafira ya kamo ya riƙe, sai lokacin ya kalli su Anty Shafa. 

“Ku yi haƙuri, mu je…”

Ya faɗi, jikin su a sanyaye suka fara tafiya, Rafiq na bin su a baya. Gaba ɗayan su ƙaunar da ke tsakanin su Zafira ta taɓa su, a wani ɓangaren ta basu mamaki, din basu taɓa ganin kalarta ba. Anty Rabi ce ke jagorantar su har inda aka ce mijin Zafirar yake yana jiransu. 

Shi ya fara hango su, don haka ya ƙaraso, jikinshi sanye da shaddar Getzner baƙa da take ta ɗaukar idanuwa, haka hular kanshi, da yake yana da haske, shaddar ta matuƙar karɓar jikinshi. Kallon shi Rafiq yake yi, ko a cikin abokanshi yafi kowa tsayi, duk da rashin ƙibar shi, ya kuma sha ganin dogaye, amma bai taɓa zaton akwai ɓirɓishin samudawa a duniya ba sai yau. 

Duk yadda aka yi saurayin da ke gabanshi ya haɗa jini da su, wani irin dogo ne ga ƙirar ƙarfi a tare dashi. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Kawai Rafiq yake iya furtawa cikin ranshi. Baisan ya mayar da Zafira bayanshi cikin sigar son ɓoyeta ba. Har lokacin da Anty Shafa suka gaisa, baya gane me suke faɗa, kawai so yake ya ɓoye Zafira daga wannan basamuden da ke gabanshi. Hannu ya ga ya miƙo mishi, da sauri ya kauce, kafin ya gane gaisawa yake so suyi, miƙa mishi hannu ya yi suka gaisa. 

“Omeed…”

Ya faɗi, ɗan daƙuna fuska Rafiq ya yi cikin rashin fahimta. 

“Omeed Modibbo…”

Ya maimaita. 

“Oh… Rafiq Mustafa Shettima…”

Rafiq ya faɗi, gani ya yi Anty Shafa ta miƙa mishi wani ƙaramin akwati, sannan ta kamo hannun Zafira da ke bayan Rafiq tana janta kusa da Omeed ɗin. Kallon su Rafiq yake, duk da ita ma Zafira ba gajera bace, sai ya ga kanta da ko damtsen Omeed baikai ba, bai san ko idanuwanshi bane suke ganin kamar wani zai ɗauka Zafira ‘yar Omeed ɗin ce, duk da babu wannan shekarun a fuskarshi. 

Matsawa Rafiq ya yi kusa da Omeed sosai, muryarshi can ƙasa ya ce, 

“Ka kula da ita, girmanka ba zai tsorata ni ba, garin da zaka kaita zai mana kaɗan in wani abu ya same ta…” 

Dariya Omeed yake sosai. Yana ɗaga ma Rafiq ɗin kai. Zafira ya kalla yana ɗan ɗaga mata kai, kamar yana son gaya mata komai zai yi dai-dai, itama kai ta ɗaga mishi, tukunna ya juya, baya son ya ga tafiyarta, don wani iri zuciyarshi take yi, kamar tana tara ruwan da take jira ta kawo cikin idanuwanshi. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 11Alkalamin Kaddara 13 >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×