Skip to content
Part 13 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Har suka dawo gida babu wanda ya ce komai, Rafiq da Aroob ne suka raka Fawzan ɗakin shi, ita ta ɗauko glass cup ta zuba ruwa a ciki, Rafiq ya ɗauko maganin Fawzan ɗin ya ɓallo ya bashi, Aroob ta miƙa mishi ruwan ya karɓa ya sha. Kwanciya ya yi, in ya samu bacci ya tashi zai ji sauƙi, don har lokacin ba wai numfashin shi ya gama komawa dai-dai bane ba. Abin rufar Rafiq ya gyara mishi. Tare suka fita daga ɗakin, Aroob ta ja mishi ƙofar. 

Hanyar ɗakinta za ta yi ta kalli Rafiq da faɗin, 

“Yaya…”

Juyowa ya yi yana tsare ta da idanuwanshi. 

“Komai zai yi dai-dai…”

Ɗan murmushi ya samu ya ɗora kan fuskarshi ba tare da ya ce mata komai ba, ta juya ta tafi abinta, shi ya kamata ya gaya mata haka, ya sani, amma ya ji daɗin yadda take zaton ya fita buƙatar lallashi a wannan karon. Numfashi ya ja yana saukewa, takawa yake zuwa ɓangaren shi, kanshi a ƙasa. 

Kusancin Nuri ya fara ji a zuciyarshi kafin ya ɗaga kai ya ganta tana ƙarasowa, murmushi ne a fuskarta. Sai dai a karo na farko da ganinta bai bayyana nashi murmushin ba, karo na farko da ganinta yasa wani ɓangare daban a zuciyarshi ya fara raɗaɗi, bai ma san akwai ciwo a wajen ba sai da ya ganta. 

“Rafiq…”

Ta kira, kallonta yake yi, ya kasa amsawa, baya jin zai iya motsa bakinshi saboda yadda yake jin ƙirjinshi na ciwo kamar zuciyarshi zata fito waje, yasan son da Nuri take ma Daddy mai girma ne, yasan ta sha danne farin cikin su don na Daddy. Amma a wani waje a zuciyarshi yake jin a babban abu kamar wanda ya faru yau ko kaɗan Nuri zata goyi bayansu. 

A lokaci irin wannan ba zata biye Daddy a son kanshi ba. Sanin wannan ɓangaren na zuciyarshi ba gaskiya bane ba yazo mishi da wani yanayi. 

“Rafiq…”

Nuri ta sake kira, wannan karon murmushin da take yi ya bar fuskarta. Kallon Rafiq ɗin take tana roƙon shi da idanuwan ta da ya fahimta, Daddy ya mata bayani sosai kan yaron, ya fito daga babban gida, duk da ya taɓa aure, amma ba wai ya daɗe bane, don wajen haihuwa matar ta rasu. Kuma ta ji zuciyarta ta aminta da hakan. 

“Tana da wanda take so Nuri…”

Rafiq ya tsinci kanshi da faɗi, yana ganin yadda idanuwanta suka buɗe da mamaki. Ɗan murmushin takaici yayi mai sauti. 

“Ya kamata ki gane, yadda kike son Daddy har haka, ya kamata ki gane tana soyayya itama…” 

Rafiq ya ci gaba da faɗi, numfashin shi da yake ji yana wani tsai-tsaiyawa na sa shi zaton ko yana da ɓoyayyar asthma da ba’asan da ita ba. Buɗe baki ya yi zai ci gaba da magana, ya ga babu wani amfani, abinda duk zai faɗa ba zai canza abinda ya riga ya faru ba. Maganganun shi ba zai rage komai a yadda Nuri take son Daddy ba, haka ba zai hanata goyon bayanshi nan gaba ba. 

Ɗan tsayawa ya yi yana son ta ga yadda ta ruguza wani zato a tare da shi, da yadda hakan zai jima yana mishi ciwo na gaske. Tukunna ya ja ƙafafuwanshi yana zuwa zai raɓata ya wuce, damtsen hannunshi ta riƙo. 

“Bansan me zan ce ba Rafiq…”

Nuri ta ƙarasa tana ƙoƙarin haɗiye abinda yai mata tsaye a zuciyarta. Hannun shi ɗayan ya ɗago a hankali ya cire na Nuri daga jikinshi ya wuce wa ba tare da ya juyo ba. Ɗakin shi ya ƙarasa, daga cikin falon ya cire takalminshi yana ɓalle link ɗin jikin hannuwan rigar, nan ya rage kayan jikinshi yana ajiyewa kan kujera. Banɗaki ya wuce yana yin wanka. Ko daya fito, riga da wando ya samu na wani farin yadi marar nauyi ya sa a jikinshi. Wayarshi kawai ya ɗauka daga jikin kayan da ya cire yana barin su nan. 

Ɓangaren wajen baccin shi ya ƙarasa yana hawa kan gadon ya zauna. Lambar Muneeb ya lalubo yana kira, duk da zuciyarshi na matsewa, yana son jin ko yana lafiya shi ma. A kashe ya ji ta, ɗauka ya yi ko wulaƙancin ‘yan MTN ne da suka saba. Don haka ya sake kira har sau biyu yana ji a kashe tukunna ya haƙura. 

Faruk ya kira, har sai da ta kusan yankewa tukunna ya ɗaga da faɗin, 

“Maza. Ya ne?”

“Normal. Ya wajen ku?”

Rafiq ya amsa  

“Ba laifi. Ka dawo kenan.”

“Na dawo, Muneeb fa? Na kira wayarshi a kashe.” 

Rafiq ya ce, bai yi mamakin da Faruk ya san ya yi tafiya ba, duk yadda akai Fawzan ne zai faɗa mishi, za su haɗu wajen ɗaurin auren Zafira, Daddy zai sa a tura musu katin gayyata, tunda sun kai matsayin hakan, a cikin abokanshi Muneeb ne kawai ba zai samu hakan ba. Sai dai in akwai abinda Rafiq yake jin daɗi tare da su shi ne rashin tambayarsu da rashin bin diddigi. 

In wani ne zai fara mishi tambaya ya akai auren Zafira baya nan, ya akai bai gayyace su ba da sauran surutai da baya jin zai iya ɗauka a wannan karon. Amma da yake Faruk ne duk wannan bai shigo ba. 

“Man, auren nan ya taɓa shi sosai. Yana Kano wajen sati biyu kenan. Bashi da lafiya sosai, mun je mun duba shi a asibiti last week, gobe ma muke son komawa in sha Allah…” 

Ɗan dafe kai Rafiq yayi tare da faɗin 

“Da alama ni ne na ƙarshen sanin yana son ƙanwata…” 

Yana jin dariyar da Faruk ya yi ta ɗayan ɓangaren. 

“Dumbass…ya kamata ka gane ba tun yanzun ba…” 

Girgiza kai Rafiq ya yi, a gajiye ya ce, 

“Bana son iskanci Faruk. Goben sai mu je in shaa Allah. Ku zo ku ɗauke ni don Allah. Karfe nawa za mu tafin?” 

Ɗan shiru Faruk yayi kafin ya ce, 

“Shida da rabi…”

“Na safe?”

Rafiq ya tambaya muryar shi ɗauke da mamaki. 

“Da na yamma?”

“Faruk shida na safe fa…”

Numfashi Faruk ya sauke. 

“Fine, ƙarfe goma ne, na san halinka da jan jiki kamar mai…” 

Rafiq bai bari ya ƙarasa ba ya kashe wayar yana ajiyewa gefe. Yasan baya shiryawa kamar su, amma baya son sauri ne a lamuran shi, bai san me yasa hakan zai zama abin tsokana a wajen su ba. Kwanciya ya yi kan bayanshi yana lumshe idanuwan shi, yana jin yadda gajiyar ranar gaba ɗaya da komai suka haɗu suna danne shi.

*****

Prologue 

Ƙofar ta turo tare da yin sallama, yana kwance kan bayanshi, Imaan na kan ƙirjinshi tana bacci, da alama shi ma baccin yake yi, shigowarta ce ta sa shi buɗe idanuwanshi yana sauke su akanta. Buɗe baki ta yi zata yi magana, Rafiq ya yi saurin katse ta da ɗora ɗan yatsan shi akan laɓɓanshi. 

“Shhh….karki tasar min yarinya…”

Girgiza kai Samira ta yi, yadda yake iya bacci kan bayanshi haka na bata mamaki, shi yasa in baya gari sai dai Imaan ta sha kukanta, in ta gaji ta haƙura ta yi bacci don ba zata iya wannan wahalar ba. 

“Shikenan ba zan yi magana ba? Wa ya ce maka tashi za ta yi?” 

Daƙuna mata fuska ya yi tare da hararta. 

“Yau ta gaji sosai, tunda muka je gida Aroob bata barta ta huta ba, sai jagulata take…” 

Ɗan ware idanuwa Samira ta yi akanshi da fadin. 

“Don Allah ka ce min ba ka karɓeta a hannun Aroob ba?” 

“Nuri na wajen shisa…”

Ya ƙarasa maganar yana turo laɓɓanshi duka biyu. Dariya Samira take yi kafin ta zagaya tana kwanciya kan gadonta ɗayan gefen. Sosai ta matsa jikinshi tana pillow da damtsen hannun shi. 

“Hannuna ya gaji…”

Ya faɗa cikin raɗa, yana tureta a wasance. Sake gyara kwanciya ta yi, zuciyarta ɗauke da wani yanayi na son shi da baya gajiya da bata mamaki. Lokuta irin haka nasa ta daɗewa bata bacci ba, don takan ji tsoro ko mafarki take yi, ba za taso ta farka da wuri ba. Muryarta can ƙasan maƙoshi ta ce, 

“Bansan ya zan yarda duk wannan gaskiya bane ba, lokuta irin yau na sani ji kamar mafarkin rayuwa da kaine da na saba yi…” 

Saida ya gyarama Imaan kwanciya a ƙirjinshi yana tallabe bayanta da hannu ɗaya da yaji ta motsa. Maganganun Samira na zauna mishi, Imaan dake bacci ya kalla, zuciyarshi ta matse waje daya. Ba zata gane yanda shi ne yake jin Imaan kamar mafarki ba, duk idan ya kalleta yakan ji kamar bai kai ace ta fito daga jikinshi ba. 

Sai ta motsa, ko ta riƙo mishi riga, ko tana ƙoƙarin riƙo mishi fuska da ƙananun hannuwanta, son ta da bai taɓa sanin akwai irin shi a duniya ya cika zuciyarshi taf, imanin shi yake ƙaruwa, don iko na Allah ne yake gani akan Imaan kawai. 

“Nasan me kike ji, lokutta da dama nakan ji Imaan kamar ba daga jikina ta fito ba…” 

Ɗaga ido ta yi tana kallon shi, dariya ya yi. 

“Yi haƙuri, daga jikin mu, ni da ke…”

Ya ƙarasa yana dariya don har lokacin hararar shi Samira take yi, saida ya hura mata iska cikin idanuwanta tukunna ta yi murmushi tana lumshe idanuwan.

* * *** 

Kallon ta yake cikin tashin hankali yana girgiza mata kai. Ba baƙon abu bane a wajenshi don kalmomi ‘yan kaɗan sun birkita mishi komai cikin ƙanƙanin lokaci, amma wannan karon kalmomi ne da ya kamata su saka nutsuwa. Kallon shi take yi itama, idanuwanta ɗauke da wani irin yanayi da baya son gani, kafin a hankali hawaye su cika su taf suna maye gurbin yanayin. 

“Ba sai ka ce komai ba Yaya Tariq, nima bana gaya maka bane don ina tsammanin za ka so ni ko wani abin, na faɗa maka ne ko zuciyata zata barni in huta haka, ko zata haƙura ta fara kallon wani…” 

Ta ƙarasa tana sa hannuwa ta goge hawayen da ta ji sun zubo mata. Ƙirjinta ya mata nauyi kamar an dora dutse. Ji take kamar ƙasar wajen ta tsage ta nutse da ita. Ya buɗe bakin shi ya kai sau huɗu amma komai ya ƙi fitowa, muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Hamna…”

Ganin ya kasa cewa komai ya sa ta raba bayanta daga jikin bangon tana juyawa ta bar mishi wajen. Har cikin ranshi ya so kiranta, ya ma kirata ɗin, muryarshi ce ta ƙi fitowa fili, akwai shaƙuwa ta daban a tsakanin shi da Hamna, ta fara sanin sirrikanshi da ko Ashfaq bai sani ba, amma bai taɓa kallon ta sa wani abu da ya wuce ‘yar uwar da ta maye mishi gurbin Yasir ba. 

Duk lokacin da zai yi magana da ita, zai yi ba tare da tsoro ko fargabar dangantakar su zata canje bayan ta ji mugayen halayenshi ba, baisan ya akai ya sani ba, ya akai yake da tabbacin komin lalacewar da zai yi Hamna na cikin mutanen da ba za su guje shi ba, sai dai bai taɓa wuce hakan a wajenshi ba. 

Ta ya zai fara kallonta da wasu idanuwan bayan zuciyarshi na doka wa Tasneem? Ko da ta yi aure bawai ya rage sonta bane ba, yana nan daram a zuciyarshi, burin mallakarta ne kawai ya ƙarasa dishewa. Amma yanzun, daga ranar da yasan ta dawo gida zuciyarshi ta saka shi a gaba. Wannan karon ba zai taɓa wasa da damar da ya samu ba. 

Shi ya kamata ya faɗa wa wani baƙo ba ko yaushe rayuwa take sake baka dama ba, yanzun haka in akwai abinda kalaman Hamna sukai mishi bai wuce bashi ƙarfin gwiwa ta ɓangare da dama ba, a cikin yanayin da take ya samu ƙarfin zuciya, zai faɗa wa Tasneem yana sonta ko da zuciyarta ba zata iya doka mishi yadda yake so ba, kamar yadda Hamna a matsayinta na mace ta faɗa mishi tana son shi duk da sanin ba lallai yana jin yadda take ji ba. 

Numfashi ya ja yana fitarwa a hankali, zai fara faɗa wa Tasneem, sannan zai fara ƙoƙarin ganin son da Hamna take mishi bai canja dangantakarsu ba. 

‘Son kai Tariq, kana son kan ka da yawa.’

Wata murya ta faɗa mishi can cikin kanshi. Bai bi takanta ba, ba laifin shi bane ba, rayuwa ce bata barshi da wani zaɓi ba. Ba zai taɓa bari ya rasa Hamna ba, ya iya rayuwa da son Tasneem da rasa ta, zuciyarshi data tarwatse baisa ƙarshen duniyarshi zuwa ba, ya kuma san Hamna ta fishi ƙarfin zuciya. In hakan son kai ne, bai dame shi ba. 

* * *** 

Ya kai mintina goma yana tsaye, ya jingina bayanshi da motarshi. Tunanin shiga gidan yake yi, har ƙasan zuciyarshi bai huce ba, bai san ranar da zai gama fushin daya ɗauka da su Daddy ba, amman tun yana mota da ya hango gate ɗin gidan kawai yasa shi jin kewar Nuri har cikin ƙasusuwan jikin shi. So yake su zauna su yi hira ya faɗa mata duka abinda yake damun shi. 

Yana son ya faɗa mata yadda yake jin tsoron kiran Zafira karta faɗa mishi auren nan kuskuren da yake gudu ne Daddy ya yi, yana buƙatar ta bashi ƙarfin gwiwar kiran Zafira, saboda zuciyarshi na jin ciwon son sanin yadda take. Bata kira shi ba itama, ta barshi ya ɗauki duk lokacin da yake buƙata wajen shiryawa magana da ita, hakan kawai na karyar mishi da zuciya da wani sanyi na ban mamaki. 

Yana buƙatar Nuri, ko ba su yi magana ba, in yana tare da ita yakan ji saiti a duniyar shi. Kamar daga sama ya ji muryar Fawzan 

“In nan zaka kwana in fito maka da tent mana…” 

Guntun murmushi Rafiq ɗin ya yi mai sauti 

“Creep…”

Dariya Fawzan ɗin ya yi, yana girgiza kai kawai, bai sake ce wa Rafiq ɗin komai ba ya wuce cikin gida abinshi. Yasan sa’adda ya shirya shigowa gidan zai shigo, damuwar daya gani a fuskarshi na mishi wani iri, don yasan gab suke da ƙara mishi wata sabuwar damuwar. Rafiq kam ganin Fawzan ɗin ya shige gida yasa shi raba bayanshi da motar cikin nauyin jiki shima yana wucewa cikin gida. 

Da sallama ya shiga, Aroob da ke zaune kan kafet da farantin soyayyen dankalin a gabanta ta amsa mishi sallamar tare da ɗorawa da, 

“Yayaaaa…”

Runtsa idanuwa ya yi yana buɗe su tare da sauke numfashi, harararta ya yi, hakan yasa ta dariya 

“Sannu da zuwa…”

“Yawwa…”

Ya amsa, dube-duben da ya ga Aroob na yi gefe da gefen shi yasa shi saurin maida nashi idanuwan inda duk nata ya bari, amma bai ga komai ba, har baya ya juya baiga komai ba. 

“Lafiyar ki?”

Ya buƙata yana kallon ta. 

“Hannun ka nagani wayam…”

Ta bashi amsa, hakan na saka shi ɗago hannuwanshi ya kalla shi ma. 

“Ya kike son ganin su?”

“Da ledoji mana Yaya…”

Kallon ta yake yana son fahimtar abinda take nufi. Girgiza kai take kamar ya mata laifi, hakan nasa shi ƙara ware mata idanuwa cike da alamar ita yake jira ta ci gaba da bayani. 

“Tsaraba…Tsaraba mana Yaya… Abin nan da mutane suke yi in sun yi tafiya za su dawo gida…” 

Ƙaramin tsaki ya ja, inda yasan shirmen da zata faɗa kenan da ya jima da wucewa abin shi, zuwa yanzun sun san banda Nuri baya ma kowa wata tsaraba, baya son ɗaukar kaya, ya fi gane in ɗaukar su ya yi suka fita suna son wani abin sai ya siya, amma haka kawai ya fara kwaso kaya daga Kano zuwa Abuja, ko daga duk inda yaje. Bayan haka ma baisan me zai siyo musu ba. Mukullin motar shi da ke sagale jikin ɗan yatsan shi ya zare yana faɗin, 

“In kin gama surutun ki ɗauko min wayoyina a cikin mota…” 

Ya ƙarasa yana jefa mukullin kan kujera don baya son ƙarasawa ya bata a hannunta, sai ya cire takalman shi don bazai iya taka kafet da su ba, gefe ya bi yana hawa bene ya nufi ɓangaren shi. Agogo ya kalla, yana da mintina talatin kafin a kira sallar Magrib, don haka ya shiga ya watsa ruwa ya yi alwala ya fito, yadi ya saka wa jikin shi fari marar nauyi, ɗinkin plain ne sai maɓallai da links jikin hannuwan. Ya samu hula blue mai haske ya saka hakama takalmanshi da agogon daya ɗaura. 

Ya fi son saka manyan kaya akan ƙanana, yakan jima bai saka ƙananan kaya ba, in ba bacci zai yi ba, ko inda zai je na da buƙatar hakan. Fitowa ya yi daga ɗakin yana cin karo da Aroob, wayoyin shi da mukullin motar ta kawo mishi. 

“Masallaci zanje Aroob, ki ajiye min a ɗaki…” 

Ya faɗi a gajiye. 

“Wanne waje?”

Ta buƙata. 

“Banɗaki, cikin sink…”

Ya amsa ta yana wucewa, yana jin dariyar ta har ta buɗe ɗakin ta ajiye mishi kan ɗaya daga cikin kujerun falon shi tukunna ta fito ta ja mishi ƙofar. 

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 12Alkalamin Kaddara 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×