A hankali ya buɗe idanuwanshi yana jin yadda jikinshi yai wani irin nauyi. Hasken da ke gauraye da ɗakin ya saka shi mayar da idanuwanshi ya rufe su gam.
"Rafiq..."
Ya ji muryar Nuri, sake buɗe idanuwanshi ya yi ba gaba ɗaya ba wannan karon.
"Nuri"
Ya faɗi yana kasa gane muryar da ya ji ta fito a matsayin tashi, saboda buɗewa da dakushewar da tayi.
"Sannu."
Wannan karon muryar Samira ya ji, kafin ta Fawzan da Aroob suna mishi sannun ne suma. Samu ya yi ya buɗe idanuwanshi gaba ɗaya. Kallon. . .