Skip to content
Part 16 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

A hankali ya buɗe idanuwanshi yana jin yadda jikinshi yai wani irin nauyi. Hasken da ke gauraye da ɗakin ya saka shi mayar da idanuwanshi ya rufe su gam. 

“Rafiq…”

Ya ji muryar Nuri, sake buɗe idanuwanshi ya yi ba gaba ɗaya ba wannan karon. 

“Nuri”

Ya faɗi yana kasa gane muryar da ya ji ta fito a matsayin tashi, saboda buɗewa da dakushewar da tayi. 

“Sannu.”

Wannan karon muryar Samira ya ji, kafin ta Fawzan da Aroob suna mishi sannun ne suma. Samu ya yi ya buɗe idanuwanshi gaba ɗaya. Kallon su yake yi yana son tuna abu na ƙarshe da zai gane. Muryar Nuri yake ji sa’adda take kiran waya tana faɗa bashi da lafiya. Hannunshi ya kalla ya ga ruwan da ke ɗaure a jiki. Ji yai tsikar jikin shi ta miƙe, ƙura wa hannun idanuwa ya yi ko ƙiftawa baya yi. 

Yana tunanin allura ce maƙale a jikinshi, ba zai tuna ranar ƙarshe da akai mishi allura ba, amma baya son abin ko kaɗan, ko ganinta baya son yi, duk sa’adda za su kai Fawzan in za ai mishi kauda kai yake yana runtsa idanuwanshi, ko ya fita ya bar ɗakin gaba ɗaya. Allah ya ɗora mishi son jikinshi ba kaɗan ba, tunanin wani ƙarfe ya huda ya shiga kawai na saka cikin shi yamutsawa. 

Kanshi ya ɗaga yana kallon ruwan da saura kaɗan ya gama ƙarewa, yana jin idanuwansu akan shi. Baya son yin magana, baya jin karfi ko kaɗan, don haka ya mayar da idanuwanshi ya lumshe, shirun su bai sa ya daina jin yadda gaba ɗaya hankalinsu yake a kanshi ba, yanayin na mishi wani iri ta fuskar da bazai fahimta ba. 

Samira kam sai yanzun ta ɗan samu nutsuwa, don su Fawzan sun ce mata bai tashi ba tun jiyan, ƙarfe bakwai a gidan ta yi mata, nan suka karya gaba ɗayan su a dakin Rafiq ɗin. Ruwan ne ya ƙarasa ƙarewa, don haka Fawzan ya taso yana kwancewa ya rufe cannula ɗin abarshi ya ɗan huta haka tukunna a sake mayarwa. Duk abinda yake Rafiq na jin shi. Agogo Fawzan ya duba ya ga ƙarfe tara, lokacin da za’a sake yin allura ya yi. 

“Har tara ta yi Nuri…bari in mishi allurar nan.” 

Kai Nuri ta jinjina tana miƙewa, Aroob da Samira na bin bayanta suka koma falon Rafiq ɗin, labulen daya raba tsakaninsu Fawzan ya ja yana rufewa, tukunna ya ɗauki syringe ɗin ya haɗa, sai kwalaben alluran guda biyu yana ɗaukar abin fasawa ya fasa bakin kwalbar, idanuwa Rafiq ya buɗe don kamar a cikin ranshi aka fasa kwalbar yana faɗin, 

“Karka sha wahala Fawzan ba za kai min allura ba…” 

Kallon shi Fawzan ya yi cike da mamaki, tukunna ya mayar da hankalin shi kan ruwan allurar da yake zuƙa tare da faɗin, 

“Ka tashi ashe, sannu, ya jikin naka?”

Idanuwan Rafiq na kan allurar da Fawzan ke haɗawa, in hankalin shi ya yi dubu a tashe kowanne yake. Bai san inda ya samu ƙarfin miƙewa zaune ba. 

“Ka ga ni sallah nake so in yi…”

Dan matsa ruwan allurar ya yi yana dai-daitata yadda ya kamata, tukunna ya mayar da hankalin shi kan Rafiq ɗin, yanayin shi na son saka dariya ta ƙwace wa Fawzan. 

“Yaya ka bari a yi allurar tukunna, kai da ka tashi yanzun, ko ƙarfin kirki baka da shi…” 

Kai kawai Rafiq yake girgiza mishi, babu yadda za’a yi yana ji yana gani a tsira mishi allurar nan a jiki. Murmushi Fawzan yake yi. 

“Meye abin nishaɗi anan?”

Rafiq ɗin ya buƙata a faɗace. Gintse dariyar shi Fawzan ya yi. 

“Yi haƙuri, juya kaga yanzun za’a gama…”

Yake faɗi yana kasa yarda Rafiq tsoron allura yake yi. Ikon Allah baya ƙarewa, Rafiq da abinda zai girgiza shi babba ne, amma ‘yar allura ta ɗaga mishi hankali haka. Ganin Fawzan ya riƙo allurar ya matso yasa Rafiq matsawa ya sauka daga kan gadon ta ɗayan ɓangaren, sai da ya dafa bangon ɗakin saboda jirin da ya ji yana neman kwasar shi. 

Zagayawa Fawzan ya yi da sauri yana dafa kafaɗar Rafiq ɗin yana taimaka mishi ya tsaya sosai. 

“Yaya wai kan ‘yar allura ne kake abin nan?”

Fawzan ya tambaya cike da mamaki. Kallon shi Rafiq ya yi yana dafa shi tukunna ya zauna. 

“Bana so ne.”

“Tana da muhimmanci, in akai wannan shikenan sai abar sauran.” 

Kai Rafiq ya sake girgizawa, fuskar shi ɗauke da yanayin da Fawzan yasan babu wajen gardama, mamaki ya ƙi sakin shi har lokacin. 

“Nuri.”

Fawzan ya kira, da sauri ta tashi tana ƙarasawa don ta ga me yake faruwa. Kafin ta ce wani abu Rafiq ya rigata da faɗin, 

“Allura ce bana so Nuri.”

Ya ƙarasa yana sauke idanuwanshi da sukai zuru-zuru cikin nata. Da duk yadda take son ta ga ya samu sauƙi, ba zata takura mishi ba tunda tana ganin yadda baya son allurar. 

“Ka bashi magani mana a madadin allurar tunda baya so Fawzan. Ko abinci bai ci ba.” 

Nuri ta ce tana ƙarasawa ta zauna kusa da Fawzan ɗin. Kallon su ya yi su biyun, yasan ko ɗaya daga cikinsu zai yi gardama da shi babu wata nasarar da zai samu balle su biyun. Don haka ya je ya ajiye allurar yana sauka falon inda su Aroob suke. 

“Me ya faru?”

Aroob ta tambaya. 

“Yaya ne yake tsoron allura.”

Fawzan ɗin ya amsa yana jin dariyar da take neman suɓuce mishi, daga Samira har Aroob idanuwa suka warema Fawzan ɗin cike da rashin yarda. 

“Ina jinka Fawzan…”

Rafiq ya faɗi daga ɓangaren baccin shi da labule ne kawai a tsakanin su. Wata irin dariya suke su duka ukun, kafin Nuri ta ce musu, 

“Wallahi karku dame shi fa…in da daɗi ku karɓar mishi allurar mana…” 

Dariyar suke ƙasa-ƙasa, kafin Nuri ta fito falon tana wucewa ta fita daga ɗakin gaba ɗaya, ƙarar ruwa da suka ji ya tabbatar musu da cewar Rafiq ɗin wanka ya shiga. 

“Yaya ka bi a hankali fa da hannunka…”

Fawzan ya faɗi da ƙarfi yadda Rafiq ɗin zai ji shi, don kan jijiyar gaɓar hannu aka ɗaura ruwan, ya ga wajen har ya kumbura, yana tunanin sake waje in za’a ɗaura allurar. Pancake Nuri ta mishi da Tea, ƙananun kaya ya saka yana fitowa falon shi ma. Samira tana kallon yadda yai mata kyau. 

“Ya jikin?”

Ta tambaya, saida ya kurɓi shayin shi tukunna ya amsa da, 

“Na ji sauƙi fa.”

“Da ƙyar ka tako falon nan Yaya…”

Aroob ta faɗa. 

“Na ji sauƙi ni kam.”

Ya sake jaddada musu, da yai wanka ya ɗan ji ƙarfin jikinshi, kuma baya jin kamar zai yi amai da ya ɗan ci pancake ɗin, da ƙyar ya iya shan Tea ɗin rabi, yana duba agogo, tashi ya yi ya je inda dardumarshi take a shimfiɗe ya tayar da Sallah, Magrib da Isha’i na jiya, sai asuba duka ya gabatar, addu’a yayi sosai yana roƙar samun lafiya wa kanshi da musulmi gaba ɗaya. Rashin lafiyar na ƙara mishi imani da sanin akwai ni’ima mai tarin yawa a tattare da lafiya da baka fahimta sai lokacin da ka rasa ta. 

“Ka taso a ƙara saka ruwan nan Yaya, sauran guda biyu kawai sai ka huta gaba ɗaya.” 

Bai musa wa Fawzan ɗin ba ya tashi, sai da ya zuge labulen tukunna ya zauna kan gadon, yana ganin Fawzan ya ɗauki ruwan yana saƙalawa, har da wata allura ya zuba a ciki. Hannun Rafiq ɗin ya kama ya ga da gaske ya kumbura. 

“A sake waje, zai maka ciwo in aka ƙara sakawa a nan, hannun ya huta.” 

Kai Rafiq ya ɗaga mishi, auduga ya dauka ya gutsura yana samu a hankali ya cire abinda aka naɗe da shi yana zare cannula ɗin, ya danne wajen yana faɗin, 

“Ɗan danne in buɗe wani sabon cannula ɗin…” 

Aroob ce ta taso daga inda take zaune tana saurin riƙo hannun Rafiq ɗin ta danne. 

“Ni zan rike…”

Basu hanata ba, abin ɗaurewa Fawzan ya ɗauka yana ɗaure hannun tare da ce wa Rafiq ya dunƙule don a samu jijiya, bai musa ba, abinda duk Fawzan ya ce ya yi shi yakeyi, hankalin shi bai tashi ba saida ya ga ƙyallin allura, ba don Samira da take wajen ba, babu abinda zai hanashi miƙewa, baya son ta ɗauke shi ragon namiji tun ba’a je ko’ina ba. Ai yana ganin Fawzan ya matso da bakin allurar saitin jijiyar hannunshi ya runtsa idanuwanshi gam yana faɗin, 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…”

Maimaitawa yake babu adadi, yana jin an tsira ya ƙara gudun maganar yana ɗorawa da, 

“Fawzan karka manta min allura a cikin jiki… Wallahi karka bar min allura a cikin jiki… Oh Allah, Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…” 

Yana ɗan buɗe ido ya ga jinin da ya ɗan fito jikin cannula ɗin da ake sakawa ya mayar da idanuwanshi gam ya rufe yana kiran Allah. 

“Bama ka yi jarabawar ƙarshe ba, karka naƙasani…Ya Rabb wai baka gama ba har yanzun…” 

Dariyar da Aroob keta dannewa ta suɓuce mata, hakan ya ba wa Samira damar sakin tata dariyar, Fawzan kam hararar Rafiq ɗin yake yi, ya sha ɗaura wa yara ƙanana cannula yanayi suna labari ko uhm basu ce ba. 

“Inda ka buɗe idonka tun ɗazun ai daka ga na gama…” 

Aikam idanuwan nashi ya buɗe, yana kallon hannun shi tare da sauke numfashi, tukunna ya kalli dariyar da su Samira suke yi, kunya na saka shi haɗe fuska, don yana tsoron allura ba shi zai sa su raina shi ba. 

“Yaya kamar ana zare maka rai.”

Aroob ta ƙarasa tana dariya. Harararta ya yi yana ƙin cewa komai. Sosai ya hau kan gadon ya zauna. Ruwan Fawzan ya ɗaura mishi, su duka suna samun wajen zama. Hira suke Samira da Fawzan na gardama tsakanin Merlin da Legend of the seeker wanda yafi wani yin kyau da ma’ana. Rafiq yasa kowa ya bashi labarin me ake a cikin kowanne don ba kallo yake ba. Haka suka ci gaba da hirarsu cikin nishaɗi. 

*****

Kwanan shi biyu, basa bari ya fita ko ina duk da ya samu sauƙi. A gidan Samira take wuni duk da shirye-shiryen biki da take yi tunda sauran kwanaki takwas a ranar. Babu yadda Rafiq bai yi da Nuri akan ta karɓi Master Card ɗin shi ba, amma ta ƙi, yana son ace yayi wani da kuɗin shi a bikin ko yaya ne. Gida Daddy ne ya bashi, wannan ma ace kowa na da shi, har Naadir. Amma lefe kam ya so ya haɗa ne da kuɗin shi, Nuri ta hana. 

Aroob ce take faɗa mishi ankai lefen tun sauran sati biyu bikin, kai kawai ya jinjina mata lokacin tunda ba sanin yadda abubuwan suke ya yi ba. Yau ma bai shigo gida ba sai bayan Magrib. Sun hanashi ya yi komai na bikin, wuraren da za’a yi occasion ma su Faruk ne suka ɗauke mishi wannan ɓangaren. Ɗakin shi zai wuce ya ga Aroob ta rugo da gudu, da Tape a wuyanta sai ɗan littafi da biro tana kiran, 

“Yayaaa… Yayaaa.”

Tsaye ya yi yana sauke numfashi, ya jira ta ƙaraso, ɗan littafin ta maƙale a kafafuwanta tana ce mishi, 

“Bansan me nake tunani ban aunaka ba…”

“Me za ki yi da awo na?”

Ya tambaya cikin rashin fahimta, yana ganin yadda ta soma ɗaukar awon nashi, tsayi, hannuwa, da kafaɗa, da duk abinda take buƙata. 

“Ɗinki…”

Ta amsa shi. 

“Ke za ki min ɗinkin?”

Kai ta girgiza mishi, bata ɗinkin maza, baya nufin bata san masu yi ba. 

“Karka ɗinka kaya ko ɗaya. Ni zan yi duka kayan da zaka saka…” 

“Ni ba zan yi komai bane ba?”

Rafiq ya tambaya, Fawzan yana ce mishi zai siya takalman da zai saka da agoguna harda huluna ma. Yana jin yadda babu abinda suka barshi ya yi. Dariya Aroob ta yi. 

“Zakayi aure mana…”

Ta ƙarasa tana juyawa ta tafi abinta. Ɗakin shi ya wuce, tun kafin ya ƙarasa kan kujera ya zauna ya fara danna wayarshi yana kiran Naadir. Bugun farko ya ɗauka. 

“Yanzun nake son kiran ka…”

“Baka kira ba ai, yaushe zaka taho?”

“Sai Friday tukunna.”

Naadir ya amsa. Numfashi Rafiq ya sauke, Zafira ma da ya sa ta tura mishi lambar Omeed ya tura mishi gayyata, daya kira cewa ya yi sai Juma’a tukunna, tunda ɗaurin auren asabar ne ƙarfe taran safe. Yana kewar ƙannen shi. 

“Har sai Juma’a Naadir?”

‘Yar dariya Naadir ya yi. 

“Kana kewata ne?”

“In ji wa? Ina son shirya ma takurarka ne shi yasa nake tambaya…ka kula da kanka.” 

“In sha Allah, kaima haka, love you.”

Rafiq bai ce komai ba ya sauke wayar daga kunnen shi, ba ko yaushe yake faɗa wa Naadir ɗin yana son shi ba, abu ne da ya riga da ya sani ba sai ya tuna mishi ba. Wayoyinshi ya kashe ya tafi sallar Isha’i, yana dawowa ya kwanta. Don ya gaji, in bai kashe ba su Faruk ba zasu barshi ya huta ba, za su kira ya zo ya ga in wani abin ya yi ko bai yi ba, bayan yabar komai a hannun su. 

***** 

Tun daga ranar Laraba komai ya fara, tun ranar aka fara shiga hidimar biki, Rafiq zai ce daga ranar babu abinda yake yi banda amsa addu’ae mutane da Amin, karbare kyautuka, sallah, shiga wanka ya fito ya sake kaya, su Faruk su daukee shi su tafi wajen wannan partyn, a koma can, sama-sama yake jinshi, abinci ma Aroob ce takan ja hannunshi ta samu waje ta sa ya zauna ta miƙa mishi plate da cokali, haka za ta yi tsaye sai ta ga ya ci ta bashi ruwa ya sha tukunna. 

Da ya ɗora kanshi saman pillow bacci yake daukee shi, haka aka yi ranar Alhamis ma, don bai dawo gida ba sai karfe sha biyu na dare, suna wajen wani party da bai masan na menene ba daga ɓangaren Samira, roƙon Allah yake yasa hotunan da aka ɗauka na karshen idanuwanshi ba a rufe suke ba saboda gajiya da rashin wadataccen bacci, don kam yana cikin abubuwan da Rafiq baya wasa da su a rayuwarshi. Bacci na da muhimmanci a wajen shi, abubuwa ƙalilan ne suke iya shiga tsakanin shi da bacci. 

Da ƙyar yai Sallar Subhi, shi ma a ɗaki don gani yake kafin ya sauka ya je masallaci bacci ya ɗauke shi a hanya. Nan kan dardumar ya kwanta saboda ba zai iya ƙarasawa kan gado ba. Bacci yake hankalin shi kwance, ya ji ana jijjigashi, ture hannun ko waye ya yi yana sake juyawa. Jijjigashin akaci gaba da yi ana faɗin, 

“Yayaaaa…Yayaaaaaa ka tashi…Yayaaa Allah saika tashi…” 

Daƙuna fuska ya yi idanuwanshi a rufe, don yadda yake ji gab yake da rushewa da kuka in basu ƙyale shi ba. Yana jin dariyarsu sama-sama, kafin ya ji an kama hannuwanshi ana ɗago da shi zaune, buɗe jajayen idanuwanshi ya yi, yana ganin Naadir na dariya, sai Aroob, su biyu ne ke riƙe da hannuwanshi, Fawzan da Zafira na tsaye suna dariya. Magana yake son yi, wani irin sauti da shi kanshi bai fahimta ba kaɗai ya iya fiddowa, hannuwanshi ya ƙwace yana dafe fuskarshi da su. 

Saida ya ji wuyanshi zai iya ɗaukar nauyin da kanshi ya yi tukunna ya ɗago yana kallon su da faɗin, 

“Kuna da burin mutuwa ne yasa kuka zo kuna tashi na?” 

Naadir ne ya yi dariya yana maƙalo Rafiq ɗin tare da rungume shi gam kamar wani zai ƙwace musu shi. 

“Na yi kewarku sosai Yaya…”

Naadir ya faɗi, ture shi Rafiq ya yi yana sake daƙuna musu fuska, zuciyarshi cike da ƙaunarsu, hankalin shi ya mayar kan Zafira, bai san ko don ya daɗe bai ganta ba, sai ya ga kamar ta ƙara ramewa, duk da ba ƙiba gareta ba. 

“Zaf…”

Ya kira yana bari ta ji yadda ganinta yai mishi daɗi, da yadda ya yi kewarta. Da murmushi a fuskarta ta ce, 

“Yayaa…”

Kai ya ɗan ɗaga mata, yana shirin komawa ya kwanta, Fawzan yai saurin riƙo mishi kafaɗa. 

“Karfe sha ɗaya har da kusan rabi Yaya…”

Cike da alamun bacci Rafiq ya ce, 

“Ku barni sai sha biyu da rabi don Allah, ina yin wanka masallacin juma’a za mu tafi…” 

Kai suke girgiza mishi su dukansu. 

“Ka tashi ka shirya, mutane na son gaisawa da kai, ga hotuna za’a yi, yau ranar Nuri ce ko ka manta?” 

Fawzan ya faɗi yana dariyar yanayin da ke fuskar Rafiq ɗin. Shagwaɓeta ya sake yi yana faɗin, 

“Kai din Allah, bani da lafiya fa…”

Dariya suke, Aroob ta ce, 

“Mun sani, cutar bacci ce take damun ka.”

“Ba zai kashe ka ba inka haƙura na yau kawai…” 

Cewar Naadir. 

“Auren ku ne wai ko nawa? Ku barni in yi bacci na nikam…” 

Rafiq ya ƙarasa yana ƙoƙarin kwanciya, jikinshi ciwo yake yi mai, amma suka hana, kamashi sukai suna miƙarwa, dole ya tashi babu shiri, har bakin ƙofar toilet suka raka shi. Fawzan na faɗin 

“Minti goma Yaya…”

“Karkai bacci a banɗaki”

Aroob ta ce, Naadir na ɗorawa da, 

“Zamu ci gaba da dukan ƙofar ne saika fito.”

Rafiq ji yake kamar ya rufe su da duka, amma bacci ya cinye mishi duk ƙarfin da yake tare da shi. Zafira ya ɗan kalla, da take ta binsu da idanuwa tana murmushi, aure yasa ta ƙara yin sanyi, dama kwaramniya bata dame ta ba, sune dai fitinannu. Wankan ya shiga, baya jin ma ya fita sosai, don yadda Naadir yake dukan ƙofar duk ‘yan seconds yana faɗa mishi Kar fa ya yi bacci a kwamin wankan. 

A falo sukai mishi tsaye, sai da ya gama shiryawa cikin shaddar da Aroob ta kawo mishi, ya saka hularshi da takalmi, har agogo ya ɗaura, tukunna ya feshe jikinshi da turaruka, kallo ɗaya za kai mishi ka ga hasken aure da ke kan fuskar kowanne ango da ba sai an faɗa maka ba zaka gane daga kallo ɗaya. 

“Yaya kayi kyau kamar in ɓoye ka…”

Naadir ya faɗa yana saka hannunshi ya goge hawayen da ke shirin zubo mishi, yatsina fuska Rafiq yayi yana kallon shi. 

“Zama da turawa ya lalata mana kai, abin kuka baya maka wahala…” 

Murmushi Naadir ɗin ya yi, ya kasa magana saboda da gaske kukan zai yi, Rafiq ɗin ya yi kyau, gashi cikin ‘yan uwanshi, yanayin ya fi ƙarfin zuciyarshi, dole ya rage shi ta hanyar zubar da hawayen farin ciki, ba lallai su gane ba. Sai lokacin ya kula har Naadir ma shadda ce a jikinshi iri ɗaya da ta Fawzan, har da hula. Zafira kam doguwar riga ce ta saka ta wani material ruwan madara, sai Aroob tasa doguwar riga itama mai kalar ruwan ƙwai, yanayin kwalliyar hulunan da takansa baya gajiya da ba Rafiq mamaki. 

Sai da suka tsaya Rafiq ya karya tukunna suka fita, kamar yadda suka faɗa ne, gidan a cike yake da mutane, ‘yan uwan Nuri da na Abba, da nasu iyalan sai abokan arziƙi, kafin ya gaisa da kowa wajen Hajja ya fara wucewa kamar yadda suke kiran Kakar tasu wato mahaifiyar Daddy. Yana zuwa ya rungumota ta gefe yana sumbatar kuncinta da faɗin, 

“Hajja masoyiya…”

Dariya ta yi tana cire mishi hular da ke kanshi da faɗin, 

“Ka ji mayaudari ko? Za kai min kishiyar ne kake kirana masoyiya…” 

Dariya aavka kama yi, shi da Hajja aka fara yi ma hoto a tare su kaɗai, sannan ya yi da Nuri, tukunna suka fara yi 

da sauran mutane, yana yi yana duba agogon shi saboda lokacin sallah, suna gamawa kuwa masallaci suka wuce, daga masallaci kuma suka ɗauki hanya zuwa gidan su Samira don a taho da mutane da za’a yi Mother’s Day a nan gidansu Rafiq ɗin. 

Shi Rafiq gida suka koma da shi da Muneeb, da ya samu da ƙyar ya rakashi don ya ƙara watsa ruwa ya sake kaya. Duk da haka cewa ya yi a mota zai zauna, Rafiq ɗin dai karya daɗe. Yasan baya son ya haɗu da Zafira ne shi yasa, kuma in dai zai zo wajen sauran hidimar bikin ba zai iya kauce wa ganinta ba. Har sai da su Abdallah suka fara kiranshi daga can gidansu Samira ana jiransu don su shiga mota ɗaya shi da ita su taho tukunna ya ƙarasa shiryawa a gaggauce. 

Sam bayason shiri babu nutsuwa, links da maɓallan rigar ma a mota ya ɓalle su, yana jin Muneeb nata faɗan yadda ya daɗe, bai ce komai ba ya ɗaura agogon shi yana saka hula, har suka ƙarasa gidansu Samira yana jin mitar Muneeb ɗin, ba zai kula shi ba, idan yi mishi surutu ne zai sa Muneeb ɗin ya samu sauƙin sanin cewa Zafira na wajen, zai yi shiru ya barshi ya yi. 

Nan ma sai da suka ƙara ɓata lokaci a gidansu Samira don sai da aka yi wasu hotunan, ta yi mishi kyau sosai, cikin doguwar rigarta fara mai baƙin stones, shi gezna ce fara a jikinshi, kowa a wajen na fadar yadda daga shi har Samira suka yi matuƙar kyau. Bayan motar shi suka shiga, sai Muneeb da ke tuƙin, Faruk na zaune a ɗayan ɓangaren, masallacin farko da suka fara hangowa yasa Rafiq faɗin. 

“Ku tsaya muyi Asr…”

“Haba Rafiq, kana ganin yadda muka ɓata lokaci?” 

Faruk ya ce, Muneeb ne ya taya Rafiq da faɗin. 

“Gaskiyar Rafiq gara mu yi Sallah don ita ce gaba da komai, babu mai tambayar mu me yasa muka yi latti, amma za’a tambaye mu jinkirta Sallah…” 

Shiru Faruk ya yi, tunda gaskiya suke faɗa, parking Muneeb ya yi suka bari Samira ita kaɗai a motar suka fita don gabatar da Sallah. Jingina bayanta ta yi sosai da motar, tana jinta kamar a mafarki, da yardar Rafiq da auren su, da kawo lefenta, da duk wani abu da ya faru zuwa yanzun yana mata kamar ba gaskiya ba, har lokacin tana jin kamar kowanne lokaci zata iya farkawa ta ga abubuwan sun tabbata mafarki take yi. Shigowar su Rafiq ne ta katse mata tunaninta. Muneeb ya ja motar suna wucewa. 

Taron ya ƙayatar sosai, duk da ba wani tsayi ya yi ba. Kamar yadda suka ɗauko Samira daga gidansu, haka suka mayar da ita gida, don suma za su yi nasu taron ƙarfe takwas na ranar. Hidima suka yi sosai, ko kaɗan Rafiq bai samu kanshi ba sai sha biyu saura, ko wanka don rage gajiya bai iya yi ba, asalima kayan da ke jikinshi da su ya kwanta. 

*****

“Don Allah Rafiq ka yi sauri.”

Zaid ya faɗi yana duba agogon shi, takwas har da kwata, hankalin Rafiq a kwance yake shiryawa, kamar babu wani abu mai muhimmanci da zai yi banda shirin. 

“Mtswww…Allah karka haɗa ni da mata mai nauyin jiki irin na Rafiq.” 

Cewar Abdallah rai a ɓace. Ko inda suke Rafiq bai kalla ba, ballantana ya tanka tsegumin da suke yi, zasu iya tafiya in sun gaji da jiranshi, auren ne ko yana wajen ko baya wajen dole a ɗaura. Babbar rigar shi yake sakawa, su dujkansu manyan kayan ne a jikinsu har da manyan rigunan, tunda sune abokan ango. Dama Fawzan ba zai iya jiransu ba, shi da Daddy da Naadir sukai tafiyarsu tun da wuri. 

Shi da Muneeb suka shiga mota ɗaya. Yana kula da yanayin Muneeb ɗin , inda ya zauna nan Omeed mijin Zafira ya zauna, sai ita kuma tana gefenshi, hankalin kowa na kan hidima, nashi yana kansu ne. Zuciyarshi na mishi wani iri da takurar da suka yi. Wajen ɗaurin auren a cike yake danƙam, don ko cikin babban masallacin na nan garin Abuja basu samu sun shiga ba. 

Hayaniyar da yawan mutanen na saka kanshi juyawa, balle yadda kowa yake miƙo mishi hannu yana son su gaisa ya mishi Allah ya sanya alkhairi, Muneeb ke ta kakkare shi, don Nuri sai da ta roƙe shi da ya tayata kula da Rafiq ɗin, akwai mutane da yawa da za su yi komai akan Daddy, ciki kuwa har da taɓa lafiyar Rafiq ɗin tunda yana da kusanci da Daddy. Musamman yadda alamun nasara a zaɓen da zai zo yake tare da gwamnatin su Daddy. 

Hankalin Muneeb bai kwanta ba sai da ya ga Rafiq ɗin ya koma mota, suna cikin motane ya ɗan tashi ya zaro wayarshi daga aljihun shi. Lambar Samira ya lalubo yana kai inda zai bashi damar canza suna ko ƙara wani abu. Shiru ya yi yana tunanin sunan da ya kamata ya saka mata, ta zama matarshi, da duk wani abu da ke zuciyarshi yake jin girman alaƙar da ke tsakanin su yanzun. 

Bari ya yi in tazo gidanshi ta zaɓa da kanta, sai ya tura mata saƙo kawai, 

‘Allah ya sa mana albarka a auren mu. Allah ya bani ikon kula da ke cikin aminci. Ina taya mu murna.’ 

Yana sauke wayar ya ji ƙarar shigowar saƙo, alamar ta dawo mishi da amsa, 

‘Amin. Na kasa yarda ka zama mijina. Ina jina kamar a mafarki. Ina sonka Raafik Mustafa Shettima.’ 

Murmushi yayi kawai yana riƙe da wayar a hannunshi. Gidan Faruk suke sauran hidimarsu, wasu cikin sauran abokansu ma nan suka sauka. Yanzun ma can suka nufa, Rafiq ya cire babbar rigar suna shiga, don ta gama isarshi, kujera ya samu ya ɗora ta, yana wucewa ɗaya daga cikin ɗakunan da ke gidan, ko yunwa baya ji duk da bai karya ba, daga ciki ya kulle yana kwanciya abin shi. Tun yana jiyo hayaniyar surutun su Muneeb ɗin da dariyarsu har bacci ya ɗauke shi, a karo na farko baccin cike da mafarkin Samira. 

*****

Ya kasa sauka daga dardumar da suka yi Sallah akai shi da Samira, yau wani matsayi ne da Allah ya kawo shi, matsayin da ya zo mishi babu shiri, kasancewar ya bar ikon komai a hannun Allah sai ya zo mishi cikin sauƙi. Maganganun Nuri ne suke mishi yawo. 

‘Ka kula da amanar yarinyar mutane Rafiq, don tana ƙarƙashin ikon ka ba shi bane zai baka damar wulaƙantata, basu baka aurenta don basa sonta ba, basu baka aurenta don sun gaji da ita ba, basu baka aurenta don basu da halin kulawa da ita ba. Ka ga ta bar gidansu, ta bar rayuwar da ta saba da ita duk saboda kai, ta aureka don ta zama sarauniya a fadarka ne ba don ta zama baiwa ba. Don Allah ka riƙe ta da amana, Allah zai tambayeka haƙƙinta in ka yi wasa dashi.’ 

Kallon Samira da take zaune kusa da shi ya yi, gyara nashi zaman ya yi suka dai-daita da juna kafin ya ce mata, 

“Ki taimaka min in kula da ke yadda ya kamata, bazan iya ba in babu taimakon ki…” 

Sosai ta matso tana ɗora kanta saman kafaɗarshi, gyara zama ya ƙara yi yadda zai iya ɗora nashi kan saman nata. 

“Kowa sai ca yake min ga amanarki nan, ko sau ɗaya babu wanda ya ce miki ga tawa amanar… Sun fi sonki.” 

Ya ƙarashe yana sauke muryarshi. Murmushi Samira ta yi. 

“Suna da tabbacin na ɗauki amanarka ne, ba sai sun jaddadamin ba…” 

Shiru yayi yana juya maganganunta a zuciyarshi. 

“Allah ya bani ikon sauke dukkan nauyin ki.”

Ɗan ture shi ta yi a wasance. 

“Kana son kanka da yawa, nima ina buƙatar Allah yaban ikon sauke nauyinka ai.” 

Maganarta ta sa shi faɗin, 

“Allah ya bamu iko.”

“Yawwa yanzun ka yi magana.”

Tana rufe bakinta cikin Rafiq na yin wani irin ƙugin yunwa da ya saka su dukansu dariya. 

“Allah yunwa nake ji tun ɗazun.”

Ya ƙarasa yana tashi ya janyo ledojin da su Muneeb suka ajiye musu, kaji ne a ciki sai lemuka, yamutsa fuska ya yi yana ƙarasa bubbuɗewa. 

“Nifa yunwar abinci nake ji ba ta nama ba.”

Kallon shi Samira take yi, tana faɗin mijina a zuciyarta, tana jin yadda hakan kawai yake saka mata nishaɗi. 

“Ko in dafa maka wani abu? Akwai komai da muke buƙata…” 

Ware idanuwanshi ya yi akanta. 

“Ki rufa min asiri kafin a sakani a jaridar safe, na saka amarya girki a daren farkonta.” 

Dariya Samira take yi a kunyace, ita kanta yunwar take ji don tun safe rabonta da cin abinci. 

“Nima ban iya cin nama a matsayin abinci ba.”

Kai Rafiq ya ɗaga mata, don yawancin duk abubuwan da suke ci kala ɗaya ne ya sani, suna da zaɓi da yawa iri ɗaya shi da ita. Wayarshi ya tashi ya ɗauko ya dawo ya zauna yana kiran Nuri, bugu ɗaya ta ɗaga da sauri take tambayar, 

“Rafiq lafiya dai ko?”

Murmushi ya yi. 

“Lafiya ƙalau Nuri, don Allah ki aiko mana da abinci, yunwa muke ji ni da Samee, ba komai sai Nama.” 

Yana jin Nuri na musu dariya. 

“Ku dai anyi ‘yan ƙauye, naman ne ba za ku iyaci ba?” 

Sauke muryarshi ya yi. 

“Nuri mana, don Allah fa… Yunwa har hanjina ya ɗaure.” 

Sosai Nuri take dariya, sannan ta ce, 

“Shikenan, zan aiko Fawzan babu daɗewa.”

Tukunna ya sauke wayar, tashi yayi ya shiga banɗaki yana watso ruwa, sai dai me ba’a kai da kawo mishi kayan shi gidan ba, ya ma manta da wannan, dole na jikinshi ya mayar. Samira ma wankan ta je ta yi don rigar jikinta ta isheta, ta shiga ɗakin sake kayan da ke haɗe da na baccin nasu ta saka doguwar riga ta atamfa tana fitowa. 

Gaba ɗaya ta gaji, sai yanzun take jin gajiyar da ta yi har a ƙasusuwan jikinta. Kallonta Rafiq yake yi , gashinta yake ƙare wa kallo tunda yana da damar yin hakan yanzun, kafin ya kwashe da dariya ganin ‘yar jelar da ta kama daga ƙarshe. 

“Samee ko ni na tara gashi sai ya fi naki yawa…” 

Numfashi ta ja tana dafe ƙirjinta inda zuciyarta take. Tana ƙoƙarin danne dariyar da ke son ƙwace mata tana faɗin, 

“Ka kyauta…”

Hannu ya miƙa mata ta ƙaraso tana kamawa, ɗan janyota ya yi alamar ta zauna, zaman ta yi yasa hannu yana cire ribbon ɗin tare da hargitsa mata gashin, ture hannuwanshi take yi. 

“Saboda me zaka warware min.”

Dariya yake yana ƙara jan gashin waje-waje yana kallon yadda take hararar shi. 

“Baima ƙarasa nawa yawa ba.”

Hannu ta sa cikin nashi gashin itama tana janyowa, da sauri ya saki nata yana ture hannuwanta tare da shafa kanshi. 

“Ouchhh ke, baki san da zafi ba?”

“Oh da gaske? Naka da zafi, nawa ne babu zafi ko?” 

Ta ƙarasa maganar tana ɗaukar ribbon ɗinta ta tattara gashinta tana ƙullewa waje ɗaya, wayarshi ce ta yi ƙara yana dubawa ya ga driver ɗin Nuri ne, bai amsa wayar ba ya miƙe ya fita gidan. Ashe mai gadi ne ya hanashi shigowa tunda bai san kowa ba tukunna. 

Kwandon ya karɓa yana mishi godiya ya dawo ciki. Da kanshi yaje kitchen ya ɗauko musu plate, Samira ta zuba musu, suna cin abincin suna hira, yana sa tanajin kamar tana tare da abokinta ne ba mijinta ba, duk wannan kunyar cin abinci ranar farko a gaban miji da ake labari bata ji ta ba ita kam. Rafiq ma hakane a nashi ɓangaren, yana jin yau na da banbanci da sauran ranakun, a lokaci ɗaya kuma kamar ko yaushe ne a wajenta. Ko da suka gama tare suka tattara komai suka kai kitchen. 

Riƙo hannunta Rafiq yayi yana damtsewa cikin nashi, har ranshi yake jinjina amanar ta da ya ɗauka , yanajin nauyin ta sosai a tare da shi, yana kuma jin ƙofofin sabuwar rayuwa tare da ita da suka buɗe mishi, da yadda daren yake nufin abubuwa da yawa a tare da su, a cikin hakan akwai ƙaruwa da ya samu, akwai samun abokiyar ɗaukar komai na rayuwa tare, da wannan ne yake hamdala marar misaltuwa.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.6 / 5. Rating: 9

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 15Alkalamin Kaddara 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×