India
Kwanansu na huɗu kenan a ƙasar, kallo ɗaya zakai ma kowa a cikinsu ka ga ramar da ke tattare da fuskarshi da rashin kwanciyar hankali. Aiki uku aka yi ma Rafiq saboda kumburin da ƙwaƙwalwar shi take yi ta ciki. Likitocin na faɗa musu cewar akwai alamun samun nasara, maganar farkawarshi kuwa zai iya faruwa kowanne lokaci, Nuri ce ma da tambayarsu ko zai iya kai yaushe, Fawzan ya ce su ci gaba da mishi addu'a don shi kaɗai ne ya fahimci girman raunukan da Rafiq ɗin ya samu.
Robar ruwa. . .