LITTAFI NA BIYU
Agogon shi yake dubawa, jira na ɗaya daga cikin abinda ya tsana a rayuwar shi. Ya fi awa ɗaya da kiran Fawzan, baisan me yake ba har yanzun, inda yasan ba zai zo da wuri ba ko ya yi nisa sai ya faɗa mishi ya sani. Wayar shi ya sake ɗauka yana kiran Fawzan ɗin, bugun farko ya dagae da faɗin,
"Na kusa Yaya..."
Muryar Rafiq cike da gajiyar da yake ji har cikin ƙasusuwan shi ya ce,
"Haba Fawzan...inda baka kusa ne sai ka faɗa min, kasan bana son. . .
Bed books
Best books