Skip to content
Part 14 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Zaman shi yai a masallaci har yai isha’i tukunna, har tsoron fitowa yake daga masallacin don yasan zai rasa nutsuwar da ya samu a cikin shi. Dole ta sa shi fitowa don cikin shi wayam yake jin shi. Bai samu kowa a babban falon ba, don haka ya wuce kitchen ɗin ƙasan, don yasan nan ne yake da tabbacin zai samu abinda zai ci. 

Shiga ya yi yana waige-waige, bai ga alamun komai ba, har leƙowa ya yi ko zai ga giccin ɗaya daga cikin masu aikin gidan, amma bai ga kowa ba. Don bai san da sun gama abinda za su yi suke komawa ɓangaren su ba, tunda abincin su a can kitchen ɗin su suke dafawa, Nuri ke shiga kitchen ɗinta da kanta in Daddy na nan, Su Zafira tunda ta tabbatar za su iya kula da kansu ta wannan ɓangaren ta ƙyale su, sai kuma idan Rafiq na nan, ya fi son cin abincin da ta dafa. 

Daƙuna fuskarshi ya yi, yanzun yasan yaudarar kanshi yake yi, babu yadda za’a yi ya ƙara kwana bai magana da Nuri ba, ba ma zai iya bacci ba, sabo ya sa shi laluben wayarshi a aljihu, ya tuna tana ɗaki, ji yake hanjin shi har ƙullewa suke, motsin da ya ji ya sa shi leƙowa da sauri. Wani sanyi-sanyi na lulluɓe shi ganin Nuri. Yadda ya yi kewarta na sa shi mantawa da fushin da yake mata, da murmushi a fuskarshi ya ƙarasa inda take yana rasa abinda zai ce, wani abu ne ya yi mishi tsaye a wuyanshi. 

Lokaci ɗaya komai ya dawo mishi, yana jin ƙirjinshi har zafi yake, ya manta yadda kuka yake, amma yanayin da yake ji a lokacin zai iya cewa ƙiris yake jira ya fashe da kuka, ya Nuri zata yi mishi haka, ya zata bari Daddy ya yi mishi haka. In bata yi tunanin Zafira ba ta yi mishi wannan, ya kamata ta yi tunanin yadda zai ji in ya dawo. 

“Ko auren ƙanwata da kin kira ni na samu, Nuri da kin kira ni an bada auren ta da ni bazan ji kamar banda wani muhimmanci ba…” 

Rafiq yake maganar can ƙasan maƙoshi, muryar shi ɗauke da abinda yake ji. 

“Rafiq…”

Nuri ta kira, idanuwanta na cikowa da hawaye, tana jin ciwon da yake ji har cikin zuciyarta, sanin tana da hannu cikin karya mishi zuciya haka na saka tata wani irin ciwo na ban mamaki, ta wani ɓangaren ta ji daɗi, tunda ya fara faɗa mata damuwarshi hakan na nufin fushin da yake ya ƙare. Don tana kewar ɗanta. Shi kaɗai ne yake sa tana jin kamar tana yin aikinta a matsayinta na mahaifiya. Ta yi kewar hakan, magana ya ci gaba da yi kamar bata ce komai ba. 

“Na san baki min alƙawarin komai ba, wani ɓangare na zuciyata kuma ya faɗa min kar in yarda da alƙawarin Daddy, yana zaɓan siyasar shi akan zama Daddyn mu kowanne lokaci…” 

Girgiza mishi kai Nuri take yi, amma ba zai yi shiru ba, in bai faɗa mata yadda yake ji ba, nauyin da ke ƙirjinshi zai ci gaba da ƙaruwa ne, ko numfashin kirki baya jin yana yi yanzun. 

“Amma na ɗauka za ki kira ni, ban isa in hana Daddy yin abinda yake so ba, amma zan fito a hotunan ɗaurin auren ƙanwata…Nuri me yasa ki ka yi min haka? Na yi son kai da na yi tsammanin wannan kawai daga wajen ki?” 

Ya ƙarasa maganar yana sauke wani irin numfashi, ƙirjinshi na mishi zafi, kafin ya ci gaba da cewa, 

“Na kasa kiranta, ban kira Zafira ba har yanzun saboda ina tsoron kar ta tabbatar min Daddy ya yi kuskuren zaɓa mata abokin rayuwa kamar yadda zuciyata take faɗa min….Nuri ban kira ƙanwata ba, ban kirata ba na kwanaki da yawa…” 

Ƙarasawa Nuri ta yi inda yake tsaye tana kamo hannuwan shi, kamar hakan yake jira ya dumtse su cikin nata gam, yana jin yadda jikin shi yake rawa saboda rashin tabbas ɗin da yake ji na rayuwa a yanzun ɗin nan. Kasancewar ya fi Nuri tsayi yasa shi ranƙwafowa kaɗan yana ɗora goshin shi saman nata. 

“Nuri ƙirjina na min zafi sosai…”

Ya faɗi a hankali yana sauke numfashi, sake dumtse hannuwan shi ta yi cikin nata, don bata da wani abu da zata ce mishi, ya yi haƙuri ba zai canja abinda ya riga ya faru ba, cikin son kare shi daga faɗan Daddy, saboda ta san dawowar shi ɗin zai sa shi yi wa Daddy musu akan auren, ta rage wani abu cikin yarda da ita da ya yi da take fatan zata iya dawowa da shi. 

Sun jima a haka a tsaye, har sai da ya ji ya samu nutsuwa tukunna ya raba goshin shi da nata, har lokacin hannuwanshi na cikin nata 

“Yunwa nake ji…”

“Nima banci abinci ba, bari in ɗauko mukulli mu fita sai mu ci wani abu, ka kira su Fawzan ko za su je…” 

Kai ya girgiza mata a hankali, yana shagwaɓe fuska, yaga Aroob taci dankali, koma bai ganta ba, yau shi kaɗai yake son su fita da Nuri, yadda ya yi kewarta baya son raba kulawarta da kowa. 

“Mu kaɗai…”

Murmushi ta yi, tana jin wani abu da ya yi mata tsaye a zuciya yana ficewa, ƙaunar da ke tsakanin su mai girma ce. Hannunshi ta saki tana wucewa ɓangaren ta, falo Rafiq ya fito, duk da ta kai mintina goma ya kasa zama. Tsaye ya yi a nan Fawzan ya shigo ya same shi. 

“Ina ka je cikin daren nan?”

Rafiq ya tambaya, agogo Fawzan ya kalla, ko takwas da rabi bata ƙarasa yi ba. 

“Yayaa…”

Daƙuna mishi fuska Rafiq ya yi, da zaɓen da ke kusantowa baya son yana fita da dare, kuma yasan taurin kan Fawzan, ba zai ma fara mishi magana kan a haɗa shi da masu tsaro ba, layi ne da baya son gwada ƙaurin shi a tsakanin su. 

“Ka daina yin dare haka a waje…”

Numfashi Fawzan yake saukewa cike da sanin yin gardama ba zai kaishi ko ina ba, kuma fitowar Nuri ta bashi damar ƙin cewa komai. Ganin shigar da ta yi ne yasa Fawzan faɗin, 

“Fita za ku yi.”

Da sauri Rafiq ya bashi amsa.

“Eh mu kaɗai kuma…”

Daƙuna mishi fuska Fawzan ya yi 

“Chaii Yayaa… Mamma’s boy….ba bin…”

Bai ga ƙarasowar Rafiq ɗin ba, sai hannunshi da ya ji ya tallabe mishi bayan kai. Tsugunnawa ya yi yana faɗin, 

“Ouchhh Yaya mana…”

Ganin ya ƙara ɗaga hannu yasa Fawzan rugawa. Nuri da ke murmushi Rafiq ya kalla, shi ma murmushi ya yi, Fawzan yasa shi jin kunya, yadda ya faɗi ‘Mamma’s boy’ na saka shi jin kamar ɗan shekara huɗu da ke buƙatar mamanshi a kusa da shi ko da yaushe, sai dai kunyar bata sa ya ji komai ba. Yana buƙatar Nuri a yanzun, ko da yaushe ma, in hakan na nufin bai girma ba har yanzun, yana da tabbacin ba zai taɓa girma ba. 

Tare suka jera da Nuri, har motar ta, tana kallon yadda sangartar Rafiq ɗin yau ta fi ta koda yaushe, hakan kuma na mata daɗi, don ta nata ne ita kaɗai, shi ne farin cikin zuciyarta, kafin sauran suka biyo baya, shi ya buɗe mata ɓangaren mazaunin driver, ta shiga ya zagaya ya shiga ɗayan ɓangaren yana kwanciya cikin kujerar sosai, gajiyar satika da nauyin komai na saka shi jin jikinshi babu ƙarfi, ko da Nuri ta ja motar suka fice ma ƙara gyara kwanciyarshi ya yi.  

*****

Ba bacci yake iya komawa bayan sallar Subhi ba, don haka da ya gama Azkar ɗin shi wanka ya yi ya koma cikin kujera ya kwanta yana kallon wildlife a tashar NatGeo. Rayuwar tsuntsaye suke ta nunawa, ya nutsu yana kallon ikon Allah, bai san lokaci na tafiya ba sai da ya duba ya ga ƙarfe tara ta yi. Kamar an doka mishi wani abu akai ya tuna magana su Fawzan suka ce suna sonyiy da shi tun jiya. 

Da suka dawo da Nuri yana zuwa ɗaki, ko kaya bai iya sakewa ba, daga ya dan kwanta bacci ya kwashe shi, sai Asuba ya farka. Wayarshi ya ɗauka ya yi wa Fawzan ɗin text, 

‘Afuwan don Allah, kuna son magana da ni kai da Aroob, in ka tashi sai kai mata magana, ku taho min da duk abinda za ku ci.’ 

Don yana gudun kar ya kira ya tashe shi in bacci yake, wasa yake da wayar a hannunshi, zuciyarshi na faɗa mishi yadda ya kamata ya kira Zafira ya ji lafiyarta, amma zai yi ƙarya in baya jin tsoron kiran. Lumshe idanuwan shi ya yi yana tattaro duk wani ƙarfin gwiwa da yake da shi ya lalubo lambarta, sai dai a kashe ya ji. Sai da zuciyarshi ta doka, tana saka shi tashi zaune. Bai san ya kira Aroob ba sai da ya ji ta fara ringing. 

Ɗagawa ta yi. 

“Yayaaa. Ina kwana.”

Bai tsaya amsa gaisuwarta ba ya ce, 

“lambar Zafira a kashe, me ya faru? Me yasa wayarta a kashe? Bata kashe wayarta babu wani dalili, me yasa zata kashe wayarta?” 

Tunda ya fara magana Aroob ke kiran sunan shi amma bai ji ta ba sai da ya ƙarasa. 

“Ta sake lamba ne shi yasa… Bari in turo maka yanzun…” 

Wani numfashi da baisan yana rike da shi ba ya sauke, sai da ya ji ƙarar shigowar saƙo tukunna ya sauke wayar daga kunnenshi, lambar ya kwafa yana kira, bugun farko ta ɗaga kamar tana riƙe da wayar ne tana jira ya kirata. 

“Yaya…”

Ta faɗi muryarta cike da farin ciki, bai san sa’adda murmushi ya ƙwace mishi ba. 

“Zafira…”

“Ina kwana. Ka tashi lafiya?”

“Alhamdulillah, ke fa? Ya kika tashi? Ya kike?” 

Yake tambaya yana rasa me kuma ya kamata ya sake tambaya. 

“Alhamdulillah. Komai lafiya…”

Ta amsa da wani sanyin murya da ya yi mishi wani iri. 

“Ki yi haƙuri ban kira ba sai yau.”

“Ka kira yanzun ai, na ji daɗi da ka kira.”

Jinjina kai ya yi. 

“Kin tabbata komai lafiya? Babu wata damuwa ko?” 

Zai iya rantsewa kai take girgiza mishi duk da baya kusa da ita, nashi kan ya jinjina, don bata ce komai ba. 

“Bansan me ya kamata in ce miki ba, banda aure ballantana in baki shawarwarin yadda za ki zauna a gidan ki, sai dai ko a tunani aure ba abu bane mai sauki Zafira, ba auren ke da su Fawzan nake ba, amma damuwar ku kawai na saka min hawan jini lokaci zuwa lokaci…dole akwai haƙuri da juna, akwai juriya…” 

Ɗan jim ya yi, hakan yasa ta faɗin, 

“In sha Allah…”

Runtsa idanuwa ya yi ya buɗe su, ba son Omeed take yi ba, abin ya mishi tsaye a rai. Basu ma san ko kaɗan daga cikin halayen junan su ba, baya son ya fara ayyana yadda zaman su zai kasance. Wannan karon tashi muryar ce da sanyi. 

“Ban sani ba, amma ina fatan akwai sauran waje a zuciyarki da a hankali za ki samar mishi… Zaman zai muku sauƙi ku duka in hakan ya faru. Kin san za ki iya kirana ko yaushe ko?” 

Shirun da ya ji ta yi ne yasa shi kiran sunanta a hankali. Can ƙasan maƙoshi ta amsa shi, yasan kuka take yi, da yake ji yana saka ƙirjinshi ya fara zafi. Amma tana buƙatar jin maganganun da zai faɗa mata, maganganun da ya kamata ya faɗa mata tuntuni. Don haka ya ci gaba. 

“Aure ba abin wasa bane ba, lahirarki ta fi komai muhimmanci Zafira, mijinki ne kawai ya halarta a zuciyarki, ki yi addu’a sosai Allah ya shiga tsakanin ki da shaiɗan, za ki iya jure komai saboda na wani lokaci ne, wallahi ba za ki iya jure ƙuncin kabari da wutar Allah ba, bana son fama miki ciwon da na san bai warke ba, amma kina buƙatar ji, Muneeb ya miki nisa, matar wani ce ke yanzun, kina da aure, lahirarki farko kafin komai…” 

Zuwa yanzun yana jin sautin kukan ta, hakan bai hana shi ci gaba ba, duk da yanayin muryarshi ya fara canzawa. 

“Kuma don za ki iya faɗa min komai baya nufin dukkan matsalarki ta zama abin kawo ƙara ko da yaushe, girma ya kamaki yanzun, akwai abubuwan da za ki yarda da cewar da kanki za ki iya shawo kansu ba sai kin nemi wani ba… Don Allah ki kula da kanki, Allah ya kula mana da ke… Kina addu’a sosai kin ji ko?” 

Da ƙyar ta iya cewa, 

“In sha Allah. Na yi kewar ku sosai…”

Murmushi yake son mata duk da bata gani ya kasa. 

“Muma mun yi kewarki da yawa…”

“Yaushe za ku zo?”

Sai yanzun ya ɗan yi murmushi yana tuna bai ma san inda aka kaita ba. 

“Wanne gari ne?”

“Lagos.”

Ta amsa shi. Jinjina kai ya yi. 

“Zamu zo, ba yanzun ba amma. Ki kula da kanki, zan sake kira.” 

Da sauri ta ce, 

“Kar ya daɗe kamar wannan…”

“In sha Allah…”

Ya faɗi tukunna ya sauke wayar daga kunnen shi yanajin yadda duk wani karfin shi ya tafi tare da wayar da ya gama. Amma yana jin kamar ya sauke wani nauyi daya danne shi. Yasan tana lafiya yanzun, ko ba komai ya samu nutsuwa. Komawa zai yi ya kwanta ya ji ana ƙwanƙwasa ƙofar. 

“Ku shigo ba sai kun karya min ƙofa ba…”

Rafiq ya faɗi yana sanin babu mai aikin ƙwanƙwasa ƙofar sai Aroob, turowa suka yi suna shigowa da sallama, babban faranti ne a hannun Fawzan da kuloli da plate duk a ciki, sai da ya sauke kan table ɗin da ke tsakiyar ɗakin yana janshi gaban Rafiq tukunna ya kula har da cokula. Kayan shayi ne a wajen Aroob cikin ɗan kwando har da flask da kofuna. Yadda ta ajiye na saka daga Fawzan har Rafiq runtsa idanuwan su. 

Zuciyar Rafiq na dokawa ya buɗe su a kan Aroob, don ya ɗauka ta fasa flask ɗin. 

“Yaushe za ki yi hankali ne wai? Ba za ki ajiye a hankali ba…” 

Turo laɓɓa ta yi. Fawzan ya ɗora da faɗin, 

“Wallahi bansan ranar da za ki daina rawar kai ba…” 

Table ɗin da ke gaban Rafiq ɗin ta soma ja zata kaishi gabanta da nufin ta zuzzuba musu, yadda take kacau-kacau da komai yasa Rafiq riƙe ɗayan ɓangaren Table ɗin dam yana faɗin, 

“Me za ki yi?”

“Zuzzuba mana zan yi fa…”

Ta amsa tana turo laɓɓa har lokacin, ita har a ranta komai a nutse take yin shi, ba hankali ne bata da shi ba, rawar kai ce tai mata yawa. Kai Rafiq yake girgiza mata. 

“Allah ya saka da alkhairi… Bari in zuba.”

Bai manta wani lokaci da suka ci abinci a ɗakin shi ba, tsalam ta tashi daga inda take zata sake waje, ita kaɗai ta yi tuntuɓe, sai ga farantin taliya saman kanshi, har da koren wake cikin aljihun gaban rigarshi. Kuma suka tusa shi gaba suna dariya, har da kiran Nuri. Ko kusa da shi da cokali baya so ya ga Aroob. 

Table ɗin ya ja gabanshi, da kanshi ya zuba ma kowa farfesun kayan cikin, haka Tea ɗin ma shi ya haɗa musu, su da dankali da kwai suka haɗa. Yana kallon su, sam cikin shi ba irin nasu bane ba, baya son haɗe-haɗe. Suna karyawa suna hira abinsu, ko da suka gama Fawzan yasa ya fita da komai, kafin Aroob tai mishi ɓarin farfesu akan kujera. 

Sai da Fawzan ya dawo tukunna Rafiq ya kalli su biyun yana faɗin, 

“Menene? Me ya faru?”

Kallon juna Fawzan da Aroob suka yi, da ido take ce mishi, 

‘Ka faɗa mai kawai.’

Ware mata nashi idanuwan ya yi yana son ce mata, 

‘Kema kin sani ai, ki faɗa mishi mana.’

Girgiza kai Rafiq ya yi. 

“Wani zai fara magana, ko za ku tsaya kuna ware waren idanuwa?” 

Idanuwan kuwa Aroob ta ware akanshi wannan karon. 

“Yaya dama Samee ce fa…”

Numfashi Rafiq ya sauke, yana jin daɗin canjin abin tattaunawa da aka samu, tunda ba Daddy bane komai da sauƙi. 

“Me ta yi? Ta zo nemana ko?”

“Ta kirani ta ce bata samunka…su Faruk sun ƙi faɗa mata inda kake.” 

Cewar Fawzan. Numfashi Rafiq ya sake saukewa a karo na biyu. Samira na son ganin ta saka mishi ciwon kai. Yana haɗuwa da mata yau da kullum, ba ita bace mace ta farko da ta ce tana son shi, amma ita ɗin tana cikin rayuwar shi ta yau da kullum, tana da kyau, duk da akwai ɗabi’unta da baya so, hakan baya nufin ba zai iya auren mace mai irin su ba. Amma yana son samun soyayya ko ya take tare da yarinyar da zai yi fatan yin rayuwar har abada tare da ita. 

Bai taɓa son Samira yadda take son shi ba, ya faɗa mata a mutunce, ta ƙi fahimta, gani take nacin da take mishi zai sa ta so shi, sai dai bai yi komai a tare da shi ba sai nisanta shi da ita, ko kaɗan ba ya jure takura in bata Daddy bace ba. In ma aurenta ya yi ba zata ji daɗin zama da shi ba, ya fi son ta auri wanda yake son ta. Shi ma ta bar shi ya auri wadda yake so, duk da bai sameta ba har yanzun. 

“Ta faɗa a gidan su tana soyayya da kai, Babanta zai samu Daddy…” 

Fawzan ya faɗi da sauri yana katse wa Rafiq tunanin da yake yi, maganar ce take yawo tana neman wajen zama a cikin kanshi yadda zai fahimce ta sosai, kafin ya kalli Fawzan ɗin sosai. 

“Me?”

Ya tambaya yana son ya tabbatar da abinda ɓangaren ƙwaƙwalwar shi ke son fahimtar da shi. Aroob ce ta sake maimaita mishi tana kallon shi a tsorace, dariya Rafiq ya kwashe da ita, sai da ya kula dukkan su kallon shi suke babu alamun nishaɗi a fuskokin su tukunna ya ce, 

“Wasa kuke ko?”

Don ba ma ya son ya fara tunanin ba wasa suke ba, a tare suka girgiza mishi kai alamar a’a, shi ma nashi kan yake girgiza musu da idanuwan shi yake roƙon su da su faɗa mishi ba gaskiya bane, su faɗa mishi wasa suke, Samira bata yi wannan rashin hankalin ba. Amma kallon shi kawai suke. Bai ce komai ba ya miƙe, ƙaramar wayarshi da ke ajiye gefe ya ɗauka ya saka a aljihun shi. Tukunna ya ƙarasa inda Aroob ta ajiye mishi mukullin motar shi tun jiya ya ɗauka. 

Ya wuce su yana zuwa ya zira wa ƙafarshi takalma farare. Hanyar fita daga ɗakin ya nufa yana rasa asalin yanayin da yake ji tsakanin ɓacin rai da asalin mamakin ƙarfin hali irin na Samira. Muryar Aroob ya ji cike da damuwa ta kira shi. 
“Yaya…”

Ba tare daya juya ya kalleta ba ya ce, 

“Yanzun zan dawo. Fawzan karka kwanta min a gado…” 

Ya ƙarashe da kashedin da ya san da wahala Fawzan ya ɗauka, ficewa ya yi ya sauka ƙasa, Nuri ma text yai mata cewar ya fita ya dawo, tunda sun gaisa da Asuba. 

*****

Parking ya yi yana fitowa daga motar, gidan su Samira ba baƙon shi bane, babu wanda bai san shi ba har ‘yan aikin gidan, kanshi tsaye ya wuce ciki yana shiga da sallama, bai samu kowa a falon ba, nan ya tsaya yana kiran wayar Samira. Bata ɗauka ba, tunawa ya yi bata san lambar ba, ba ɗagawa zata yi ba, don haka ya yi mata text, 

‘Rafiq ne, ina falon gidan ku.’

Yana tura text ɗin, ko fita bai yi daga kai ba kiranta ya shigo. Ɗagawa ya yi yana faɗin, 

“Samee…”

Yana jin yadda take maida numfashi kamar wadda tai gudu. 

“Ki fito magana za mu yi…”

“No…”

Ta faɗi muryarta a dakushe. Lumshe idanuwan shi ya yi, baya son ranshi ya ɓaci, yanayin da yake ji kawai ya ishe shi. Wayar ya sauke yana kashewa. Ɗayan ɓangaren gidan ya wuce, a falon da zai haɗa shi da ɗakin Samee ya tsaya. Baya son shiga ɗakin baccin ta, saboda yana jin rashin kyautuwa a cikin yin hakan. Ƙofar ɗakin nata ya lura a buɗe take kaɗan. Yasan zata jishi don haka ya ce 

“Samee!…”

Shiru ko motsi baiji ba. 

“Samee!!! Ki fito mu yi magana, in na ƙara minti biyu baki fito ba tafiya zan yi…” 

Ya ƙarasa yana saka wayarshi cikin aljihun rigar da ke jikinshi, a hankali ta ƙarasa buɗe ƙofar ta leƙo da kanta da babu ɗankwali. Idanuwanta take buɗewa akanshi cike da tsoro a cikinsu.

“Ki koma ki sa ɗankwali.”

Ya umarta, bata yi musu ba ta koma cikin ɗakin, fitowa ta yi da wata irin hula da ta yi mishi kyau, yasan doguwar rigace a jikinta, amma ba zai ce ta mecece ba. Tsaye ta yi tana jin bugun zuciyarta har cikin kunnuwanta. Tasan tsoro kala-kala, amma wanda take ji a yanzun ya banbanta da sauran. 

“Don Allah ka yi haƙuri, ka ji, ka yi haƙuri don Allah…” 

Ta ƙarasa muryarta na karyewa, idanuwanta na cikowa da hawayen da ta sa hannu tana goge su da sauri. Zuciyarta ta matse a cikin ƙirjinta, tana jin yadda ganin shi kawai yake sata jin yanayi a wajajen da batasan suna da rai ba a jikinta. Zata rantse don ta so Rafiq kaɗai Allah ya halitta mata bangaren nan a zuciyarta. Soyayyar da take mishi na bata tsoro, yadda yake kallonta na saka ƙafafuwanta yin sanyi suna fara mata barazanar kasa ɗaukar nauyin ta. 

Kallon ta Rafiq yake yi, yana rasa kalar son da take mishi haka, girman soyayyar ta da ta ajiye kunyarta ta mace a gefe, ta ajiye ajinta da yake ganin tana nuna wa sauran mazan da suka fishi kyau da komai ta zaɓe shi. A ɓangare na zuciyar shi yana girmamata, saboda yasan ba kowa ne yake da ƙarfin zuciyar daure halin da take ciki ba. Yakan ga soyayyar da ke idanuwanta a na Nuri duk sa’adda Daddy ya gifta. 

Ƙarasawa ya yi ya samu kujera yana zama, gefenshi ya bubbuga yana ma Samira alamu da ta zo ta zauna, babu musu ta zagayo tana zama gefen shi tare da ɗora ƙafarta ɗaya akan kujerar yadda zata fuskance shi sosai. 

“Raafik…”

Kai ya girgiza mata. 

“Son da kike min baisa kin iya faɗar sunana dai-dai ba har yanzun…” 

Ya faɗi yana jin yadda ya gaji da gyara mata, murmushi ta yi, hawaye na sake zubar mata, zuciyarta na buɗewa da yadda yake son maganar da za su yi ta yi sauƙi. Tasan halin shi, ta ɗauka zai shigo gidan da ɓacin rai, zai mata faɗan shin nan da yake hautsina mata lissafi, amma yau tana ganin Rafiq ɗin da ta jima bata gani a tare da shi ba, tana ganin abokinta da ta rasa, hakan ya sanyaya wajaje da yawa masu mata zafi. 

Yadda take sa hannu tana goge hawayen ta yake kallo, sun kuma ƙi daina zubowa, duk da ba shi bane na farko da ya ga kukanta, yau tana jin nauyin hakan, ta kuma rasa dalili. 

“Na rasa me yasa sun ƙi daina zuba…”

Ta faɗi muryarta na rawa, wasu sabbin hawayen na zubo mata. Zuciyar shi ya ji ta cika da tausayi. Muryarshi da sanyi sosai ya ce, 

“Ki barsu, akwai abubuwa da yawa da bamu da iko akan su…” 

Jinjina kai ta yi tana yarda da maganarshi, don abubuwan sun haɗa har da zuciyarta, yanayin shi yasa ta jin rashin adalcin da ta yi mishi, yadda ta zaɓi kanta da farin cikin ta, a lokacin ne ta ji wani irin ƙarfin gwiwa da bata san daga inda ya fito ba, bata samu zaɓi daga zuciyarta ba akan soyayyarshi, amma wannan karon tana da zaɓi da yadda zata yi da ita. 

“Ka yi haƙuri don Allah, zan kira Baba, zan faɗa mishi ƙarya nake….tunanin me nake yi? Wa nake yaudara?” 

Ta ƙarasa tana wata ‘yar dariyar takaici, hawaye na sake zubar mata kafin ta ci gaba da faɗin, 

“Ina son ka, na jima da daina kunyar faɗar haka, abinda na kasa yarda shi ne yadda kai baka jin abinda nake ji, sai yanzun, idan har tunanin auren wani da ba kai ba yana sani jin kamar ƙarshen rayuwata ya zo bana son ka ji haka, Raafik bana son ka takura ko kaɗan a rayuwar ka, sanin ni ce sanadin hakan zai fara kashe ni kafin tunanin auren wani…” 

Maganganunta yake ji kamar tana watsa mishi ruwan zafi. Katse ta yayi da faɗin, 

“Wanne irin so kike min haka?”

Dan ɗaga kafaɗunta ta yi, muryarta can ƙasa ta ce, 

“Nima ban sani ba…”

Numfashi ya sauke, son da take mishi ya yi yawa, yana sa shi jin da wahala ya samu macen da ke mishi rabin son da Samira take mishi, ko matar da yake hangowa zai so ta, zai so yin rayuwa ta har abada tare da ita, da wahala tai mishi irin wannan son. Kukan ta na ƙara karya mishi zuciya. 

“Idan na ga wata ina son ta fa?”

Ya tambaya yana kallon fuskarta, ɗan murmushi ta yi. 

“Duk yadda zuciyata ke karyewa da hangoka da wata, don mutum huɗu aka halicci zuciyar ka Raafik, tunda ka kasa sona na yarda da wata zata iya shigowa rayuwarka ko da yaushe…” 

Girgiza kanshi da ya yi bala’in nauyi yake yi , bai san Samira bata da hankali ba sai yau. Yana son ƙara tabbatar da ta haukace. 

“Idan na aureki ba zan so ki yadda ya kamata ba, ba kya tunanin in na sake auro wata zan so ta yadda kike mafarkin in soki?” 

Dariya ta yi wannan karon, tana saka hannuwanta duka biyun ta goge fuskarta, ciwon da zuciyarta take yi da tambayoyin shi ba baƙon abu ba ne, tambayoyi ne da ta sha yi wa kanta su ita kaɗai, bata jin akwai wani abu da bata yi tunani kanshi ba. 

“Na sani…In ka sota zuciyata zata yi ciwo sosai, amma zata yi ciwo ko bana tare da kai, gara ina tare da kai.” 

Dafe kanshi ya yi, yana saki kuma ya ce, 

“YaaRabb Samee, baki da hankali, kin san hakan ko?” 

Kai ta ɗaga mishi, ta sani, akan son shi bata da hankali, hauka take musamman yanzun da maganganun shi ke sa zuciyarta yin wani tsalle-tsalle don kamar yana tunanin amincewa da aurenta ne. 

“Rashin tabbas ɗin ko zan soki na tsorata ni, ina tsoron lahirata, kar rashin miki adalci ya kamani…” 

Yake faɗi, duk wani gashi da ke jikinshi na miƙewa kamar an watsa mishi ruwan ƙanƙara, yana tsoron ƙuncin kwanciyar kabari, yana tsoron ya aureta ya kasa mata adalci, Allah ya kamashi. 

“Kana sa ina jin kamar kana shirin amincewa da aurena ne, don Allah in ba haka bane ka bari , karka ɗora zuciyata kan benen buri ka faɗo da ita….ba zan iya jurewa ba…” 

Yana jin rashin hankalin maganganun shi da son kan da ke tattare da su tun kafin ya furta su, don zai yi ƙarya in ya ce baya tsoron rasata ko ba zai samu mai sonshi kamarta ba, koma ba zai samu wadda yake so ba gaba ɗaya. Zuwa yanzun yasan yadda komai yake da rashin tabbas. 

“Allah ya yafe min son kan nan…Allah ya yafe miki kema…” 

Dariya ta yi, shima dariyar yake yi. Tana jin ta kamar ta sha wani abu, ta san giyar son shi ce kawai ta bugar da ita haka. 

“Ba za ki ce amin ba ko? Son kanmu na da yawa…” 

Dariyar ta ci gaba da yi, hawayen farin ciki na zubo mata, tana jin yanayin na mata kamar a mafarki, kallon ta yake yi, dole a tare da matarshi yana son samun ƙawa, da za su yi irin dariyar nan tare, ko ba komai yasan zai samu ɓangarori da yawa a tare da ita. 

“Bazan iya miki kalaman nan ba, bazan iya ba…” 

Yake faɗi yana jin wani iri da tunanin zama yana mata kalaman soyayya. 

“Ina so ni kuma.”

Girgiza kai yake yi kafin ya kula da murmushin da take yasan tsokanar shi take, filon kujera ya ɗauka yana jifanta da shi, ta riƙe tana dariya. Harararta yake, yana jin cewa zama da ita ba zai mishi wahala ba, zai yi duk ƙoƙarin shi wajen yi mata adalci ko don halarcin soyayyarta, zai yi ƙoƙarin ya nuna mata yadda yake ganin darajarta da kimarta. Ba zai iya bata abinda take so ba, zai bata abinda ba zata taɓa dana sanin auren shi ba. 

Zai kuma fara da yima Daddy magana don ya riga Babanta yin maganar auren, su ya kamata su zo neman aure, shi ne dai-dai, shine dai-dai. Da hawaye a idanuwanta ta ce, 

“Na gode…Na gode fiye da yadda zaka fahimta.”

Yanayin yadda tai maganar kamar ya bata wani ɓangare mai muhimmanci a duniyarta na sa wani abu matsewa a zuciyar shi. In bai ma Samira adalci ba sai Allah ya kamashi ya sani, tunda son kai ba zai bari ya ƙi aurenta ba ya bar wanda yake sonta ya aura, dole ne ya darajtata. Miƙewa ya yi yana tsintar kanshi da zare zoben da ke ƙaramin ɗan yatsan shi, da ba zai tuna tun yaushe Nuri ta bashi shi ba, azurfa ce, guda biyu ne kuma a hannun shi, amma wannan ɗin ya fi so. 

Kan kujerar inda ya tashi ya ɗora zoben yana faɗin, 

“In ya ɓace karki nuna min fuskarki…”

Ware idanuwa ta yi tana ɗaukar zoben da sauri kafin ya canja zuciyar shi, ba zata manta lokuta da dama da ta sha roƙon shi ya ciro ta gani kawai yana ƙi ba, amma yau shi ne ya cire ya bata da kanshi. Ta kasa magana, sai zoben da take juyawa, wani irin yanayi na ratsata. Zoben nashi yake bi da kallo shi ma, yana jin kamar ya karɓi abinshi, amma yasan in zai yi zaman aure da ita dole ya fara da yarda da ita. 

Ba zai faru lokaci ɗaya ba, zai fara da yarda da ba zata bar wani abu ya samar mishi zoben nan ba, don wani ɓangare ne na rayuwar shi. A yatsanta na biyu ta sa zoben, gaba ɗaya hankalinta na kan hannunta kamar ta kasa yarda zoben shi ne a jikin yatsan nata. 

 “Daddy za su zo nema min aurenki, mu ya kamata mu zo…” 

Kai kawai ta iya ɗaga mishi tana shigewa cikin kujerar sosai. 

“Za mu yi waya…”

Ya faɗi yana juyawa, ta kasa cewa komai, bin bayanshi take yi da kallo, gaba ɗaya soyayyarshi ta kashe mata jiki. Abinda ya faru take yawo da shi a kanta, bata son manta komai, ko da zai kasance mafarki ne, sa’adda wani zai zo ya tashe ta farin cikin da take ji yanzun zai biyota har duniyarta, a hankali ta lumshe idanuwanta tana murza zoben, tana jin bacci na fara kawo mata ziyara don ta jima bata samu wadatacce ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 13Alkalamin Kaddara 15 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×