Tura ƙofar ɗakin ya yi yana shiga, numfashi ya sauke a gajiye ya cilla wayarshi kan gado, bangon da ke gefenshi ya dafa yana zare takalman ƙafarshi. Ya sha yawo, da gidansu Ashfaq ya je ƙarshe zai yi kwanciyarshi ne don ya gaji sosai. Washe garin ranar zai tafi makaranta, duk da an kawo mishi motarshi tun jiya, amma bada ita ya fita ba yau, yadda yake ɗokin mota kafin ya yi tashi, har mamaki yake yi yanzun da ya ji ta fitar mishi akai kuma. Sai yanzun ya gane duk ɗokin motar da yake yi don ba shi da. . .