Skip to content
Part 30 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kallo ɗaya za kai ma Altaaf ka ga ramewar da ya yi a dare ɗaya kawai. Ko wanka da zai yi da safe sai da Wadata yai ma Hajiyarsu magana aka dafo saboda zazzaɓin da yake ruf a jikinshi. Da ƙyar ya yi wanka, panadol Wadata ya sa aka samo da ƙyar ma, ya jima yana jujjuya shi a hannunshi saboda bai yarda da shi ba, amma Altaaf ɗin na buƙatar taimako ko yaya ne kafin su koma gida. Hajiya ma da ya faɗa mata Altaaf ne ba lafiya haka ta ce su wuce gida kawai. Sai da ya ɗauko ruwa tukunna ya ƙarasa inda Altaaf ya ke kwance ya miƙa mishi ruwan da maganin yana faɗin, 

“Tashi ka sha panadol Altaaf. In ɗauko maka kaya a mota ka sake mu tafi.” 

Da ƙyar Altaaf ya ɗago idanuwan shi, hasken da ke ɗakin na ƙara mishi ciwon kan da yake fama da shi. Ba maganin bane bayason sha, lafiyarshi na da bala’in muhimmanci a wajenshi. Yaune yake jin kamar ya cancanci rashin lafiyar da yake yi, kamar bai kamata ya sha magani ba. Don haka ya girgiza ma Wadata kai a hankali. 

“Bana son shegiyar gardama. Ka sha magani.”

“Don Allah ka barni. Mu tafi gida kawai.”

Hannun Altaaf ɗin Wadata ya kama yana ɗago shi zaune. Ya saka mishi robar ruwan a cikin hannunshi, tukunna ya ɓallo maganin guda biyu yana miƙa mishi, baki Altaaf ya buɗe da shirin yin magana, Wadata ya riga shi da faɗin, 

“Kana son in jiƙa a ruwa in ɗura maka ne ko?” 

Hannu Altaaf yasa yana karɓar maganin, muryar Wadata ta tabbatar mishi ba wasa yake ba, ko da lafiyarshi ƙalau ma ƙarfinshi da na Wadata ba ɗaya bane ba. Da ƙyar ya haɗiye maganin yana bi da ruwa tare da yamutsa fuska. Robar ruwan ya ajiye, tun ɗazun zuciyarshi ke bugawa, da ya ga giccin mutum sai bugun zuciyarshi ya ƙaru. Gani yake kamar su Nuwaira na iya shigowa kowanne lokaci. Wadata ne ƙarshen wanda zai so ya gane abinda ya yi. Gashi Ammi ta ce da safe zata zo itama don su yi ma Hajiyar su Wadata gaisuwa. 

“Ni dai mu tafi gida.”

Altaaf ya faɗi muryarshi cike da rauni. Kai Wadata ya daga mishi, baisan me yasa jikinshi yake sanyi da yanayin Altaaf ɗin ba. 

“Ba za ka faɗa min abinda ya faru ba?”

Ya sake tambaya yana tsare Altaaf ɗin da idanuwa. Miƙewa Altaaf ya yi yana ƙin yarda su haɗa idanuwa da Wadata. Ganin Altaaf ɗin ba shi da niyyar amsawa yasa Wadata jinjina kai kawai. 

“Ka bari in ɗauko maka kaya ka sake.”

Kai Altaaf ya girgiza, tsayawa sake kaya duk wani ɓata lokacin ne, da duk mintin da zai wuce da yadda fargabarshi take ƙaruwa. So yake yayi nisa da ƙauyen kinkiba, nisa na har abada. Don haka yai gaba yana zuwa bakin kofa ya fara saka takalmanshi, ko zaren jiki bai ɗaura ba ya wuce, sauran kayayyakinsu da wayoyi Wadata ya tattara, don Altaaf nan yabar wayarshi. Tukunna ya bi bayanshi, a kofar gida ya same shi a tsaye, don motar Wadata da suka zo da ita na can ƙofar gidan da ake zaman makokin. 

“Ka jira in dauko motar nan in ba zaka iya takawa ba.” 

Wadata ya faɗi 

“Zan iya.”

Altaaf ɗin ya amsa a taƙaice, don haka suka wuce tare, babu mai magana a cikinsu. Kowa da abinda yake saƙawa a zuciyarshi har suka ƙarasa kofar gidan inda motar Wadata take a ajiye. Buɗewa ya yi yana jefa kayayyakinsu a bayan motar, kamar an ce Altaaf da ke tsaye ya ɗaga idanuwanshi ya hango mutane na tunkaro su da ‘yan sanda guda biyu. Wani irin yamutsawa hanjin cikinshi suka yi, bai san ƙafafuwanshi sun motsa ba sai ganinshi ya yi a bayan Wadata, ko ina na jikinshi ɓari yake yi. 

“Altaaf? Meye haka? Lafiyarka?”

Wadata yake tambaya muryarshi na rawa, saboda ba ƙaramin tsoro Altaaf ɗin ya bashi ba, bayan Wadata Altaaf yake ƙara shigewa yana jin dama yana da siddabarun da zai yi ya ɓace daga garin, ko kuma ya shige jikin Wadata ya ɓoye, bai taɓa sanin tsoro irin wannan ba. Zuwa yanzun bama yajin maganar da Wadata yake yi, hankalinshi na kan mutanen da ke tunkarosu. Inda idanuwan Altaaf suke kafe Wadata ya juya don ya ga me yake ɓoye ma. 

‘Yan sanda ne guda biyu, sai wani mutum magidanci da babbar mace, matashin saurayi da zai kusa tsaranshi riƙe da hannun wata budurwa da take da matsalar ƙafa a yadda Wadata ya kula da shi saboda yanayin tafiyarta. Bai ga alaƙarsu da Altaaf ɗin ba, don haka ya juya yana faɗin, 

“Wai menene? Ni banga komai ba.”

Kai Altaaf yake girgizawa. Zazzaɓinshi na ƙaruwa, amai ma yake ji saboda tashin hankali. Saima da yaga da gaske su Nuwaira sun tunkaro su, idanuwanshi yai nasarar saukewa cikin na Nuwaira da suke a kumbure da alamar kuka, a cikin su yana ganin tsanarshi da yanayin daya girgiza shi. Ya ba mutane da yawa dalilin da za su tsaneshi bai taɓa damuwa ba, asalima basa gabanshi, amma ganin tsanarshi cikin idanuwan Nuwaira ya zo mishi da sabon yanayi. Sosai suke tunkarowa inda suke har sai da suka cimmusu. 

Kallonshi Nuwaira take, tunda ta buɗe idanuwanta a asibitin ƙauyen fuskarshi take gani akan duk fuskar da zata gani, jinshi take a kowanne ɓangare na jikinta, kwana sukai suna kuka ita da Inna, duk ƙarfin hali irin na namiji sai da Baba ya zubda ƙwalla, Yayanta Tawfiq kam har zuwa yanzun wayewar gari da suka je ofishin ‘yan sanda don shigar da ƙara bai iya ya ce komai ba. Yadda akai tasan gidan gaisuwar nan Altaaf suka zo taganshi da dare zaune yana danna waya da suka zo gaisuwa ita da Inna. Shi yasa ta ce ma ‘yan sanda ta san inda Altaaf ɗin yake, zata kuma gane shi in ta ganshi. 

Wadata kuma da mamaki yake kallon su, musamman yanzun da suka matso kusa, babbar macen nasa gefen hijabinta tana share ƙwalla, ƙare musu kallo ya yi, gaba ɗaya babu mai nutsuwa a cikinsu. Juyawa ya yi ya kalli Altaaf da idanuwanshi suke kafe akan Nuwaira, tukunna ya sake juyawa ya kalle su, lokaci ɗaya ƙwaƙwalwar shi ta haɗa abinda yake faruwa, amma zuciyarshi na kokawa da aminta da hakan. 

“A-Tafida…Altaaf…”

Wadata ya kira sunayen nashi duka biyu muryashi can ƙasan maƙoshi da ta fito da wani irin yanayi, runtsa idanuwa Altaaf ya yi, jikinshi na ci gaba da ɓari, bugun zuciyarshi ya ke ji har cikin kunnuwanshi. Musamman da ya ji yanayin da Wadata ya kira sunanshi yana roƙonshi da ya yi magana, ya ce wani abu, ya tabbatar mishi da abinda yake tunani bai faru ba. Altaaf ya ɗauka soyayya ce kawai take da ƙarfin karyar da zuciya, amma yanayin muryar Wadata ya karya mishi zuciya sosai. Hannu Nuwaira ta ɗaga tana nuna Altaaf ɗin. 

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un’.

Wadata yake faɗi cikin kanshi yana jin wani zazzaɓi na rufe shi, maimaitawa yake saboda yanayin da yake jinshi komai zai iya faruwa, ya kasa juyawa ma ya kalli Altaaf ɗin. Sake ɓoyewa Altaaf ya yi a bayan Wadata ganin Nuwaira ta nuna shi, saurayin da ke riƙe da hannunta ya ga ya saki hannun nata yana nufo shi. Kafin ya yi wani yunƙuri ya ƙaraso, Altaaf bai ga ɗago hannunshi ba sai haɗuwarshi da gefen fuskarshi da ya ji, wani irin raɗaɗi na kaiwa cikin kanshi, yana jin gishiri-gishiri cikin bakinshi. 

Yana ɗagowa ya sake kai mishi wani dukan cikin fuskarshi yana faɗin, 

“Ɗan iska…ƙanwata don ubanka… Ƙanwata. Duk matan birni sai ƙanwata don ƙanwar uwarka…” 

Wani dukan Tawfiq zai sake kai mishi don bai ga amfanin irin su Altaaf a duniya ba, kashe su ya kamata a yi, ya kasa magana ne tun cikin dare da hayaniyar su Inna ta sa shi fitowa daga ɗakinshi, ya so yana da wani makami ne yana zuwa ya kashe Altaaf ɗin, rayuwarshi zai yi ta cike da farin ciki a gidan yari sanin ya kauda babban yaron shaiɗan daga duniya, ya ji an riƙe mishi wuyan riga an janyo shi baya. Wadata bai ga dukan farko ba saboda yana can wata duniyar ta daban. Duka na biyu ya gani, ranshi ya ƙara ɓaci, banda tafasa babu abinda zuciyarshi take yi. 

‘Yan uwanshi na da muhimmanci a wajenshi, Altaaf kuma na cikinsu, babu wanda ya isa ya hukunta su, in duka Altaaf ya cancanta shi kadai ne yake da ikon dukanshi ba Tawfiq ba, idanuwan Wadata sun gama rufewa da ɓacin ran abinda Altaaf ɗin ya aikata da zuciyarshi ta ƙi amincewa da shi har yanzun, ga dukan da wannan bagidajen ɗan kauyen yai ma Altaaf ɗin ya ƙara harzuƙashi. Wani irin Mari ya watsa ma Tawfiq cikin fuska yana sa duka hannayenshi biyu ya cakumi wuyan rigarshi tare da girgiza shi.

“Wa ya ce kakai matsayin ka taɓa min kani? Me yasa ƙazamin hannunka zai taɓa shi?” 

Wadata yake faɗi cikin ƙaraji yana sake watsa ma Tawfiq ɗin wani marin cikin fuska, inda zai huce haushin shi yake nema dama, ƙarfin da yake da shi ne yasa ko rikici ya haɗa shi da wani sai dai ya biya kuɗi ai ma mutum duka a madadin shi, da wahala ya ɗaga ma mutum hannu saboda ciwo yake jima mutane sosai. Hajiyarsu kance ƙashi ɗaya gare shi, yana ganin yadda ya gigita Tawfiq. Duka abin ya faru ne cikin ƙasa da mintina uku, su kansu ‘yan sandan da ke tsaye sun yi kan Tawfiq don su raba tsakanin shi da Altaaf ne Wadata ya shaƙo shi. 

Inna da Nuwaira kuwa sun riƙe hannuwan juna ne suna kuka, tunda suke ko a mafarki basu taɓa hango tashin hankali irin wannan ba. Da ƙyar ‘yan sandan suka samu suka ɓanɓare Tawfiq daga hannun Wadata da ya zame musu kamar wani ƙaramin me taɓin hankali, don sai da ya naushi ɗan sanda ɗaya har ya fasa mishi baki, haƙorinshi ma ɗan sandan ke ji yana girgiɗi daga ciki. Zuwa lokacin mutane sun fara taruwa ana tambayar lafiya. Musamman wanda suka san Malam Bashari. 

Tawfiq mutanen da ya fara gani suna taruwa ne yasa jikinshi mutuwa, shi yasa bai yi yunƙurin ƙwacewa daga hannun Wadata ba, yanzun yake ganin kuskuren da sukai na shigar da ƙara, yadda abinda ya samu Nuwaira zai gauraye duka ƙauyen, yadda gaba ɗaya rayuwarta ta gama canzawa kenan har abada, ko da ‘yan sandan suka raba tsakanin shi da Wadata wajen Nuwaira ya je da ke jikin Inna tana wani irin kuka kamar za ta shiɗe, kallonta yake yana rasa abinda ya kamata ya yi, tukunna ya mayar da hankalinshi kan Altaaf, har ƙasan zuciyarshi yake jin son kashe Altaaf ɗin, da duk wani abu da yake da shi yake jin tsanar Altaaf da bai taɓa yi ma komai irinta ba. 

Altaaf kam yana tsaye, ko hannu bai kai ba, ballantana ya taɓa fuskarshi, yana jin kumburin da take yi a wajajen da dukan Tawfiq ya same shi, bai taɓa zaton akwai ranar da za ta zo mishi irin haka ba, bai taɓa tunanin ƙaddara za ta buɗe mishi shafi mai hargitsin na yanzun ba, inda jiya ne da yanzun hankalinshi ya tashi kar ya yi tabo a fuska, kar wani abu ya taɓa kyawun fuskarshi, amma yau kam kyawun nashi ne ƙarshen damuwarshi. Wadata yake kallo da kanshi yake a ƙasa, ya rasa abinda ya kamata ya yi. Inda yasan haka dana sani yake da bai fara kusantar abinda zai sa shi jinshi ba. 

Baisan ɗan sanda ɗaya ya zo kusa dashi ba sai da ya ji ya riƙe mishi gefen wando, su duka aka tarkata zuwa ofishin ‘yan sandan da ke nan ƙauyen. Mutane ‘yan son ganin ƙwaf kuwa suka rufa musu baya, sai da aka tsaya kan hanya saboda Altaaf da ya fara kwara amai, jikinshi ko ina ɓari yake, ji yake kamar zai sume kowanne lokaci, amma ba rashin lafiyarshi bace matsalarshi, yadda Wadata ko juyowa bai yi ba ballantana ya ga halin da yake ciki, ya yi tsaye ne kawai shi ma kamar yadda kowa ya tsaya ana jiranshi ya gama aman su tafi. 

Wadata na jinshi, yana son juyawa amma baison ganin fuskar Altaaf ɗin, in ya kalle shi yanayin shi zai tabbatar mishi da gaske yayi ma yarinyar nan fyaɗe. Da gaske ya kusanci abinda ya fi komai ƙazanta a littafin laifuka a wajen shi, da gaske Altaaf ya ƙasƙantar da kanshi har haka, baisan me zai ba in zuciyarshi ta gama yarda da abinda Altaaf ɗin ya aikata. Yana jin yanda zuciyarshi take mishi da son zuwa ya kama Altaaf ɗin ya tabbatar da lafiyarshi, baisan lokacin da kusancin shi yai nisa da Altaaf har haka ba, kula da shi ya zame mishi wani ɓangare a rayuwarshi. 

Bai motsa ba saida ya ga wasu cikin mutanen da ke tare da shi sun ci gaba da tafiya tukunna, sauri yake ƙarawa don baisan Altaaf ɗin ma ya matso kusa da shi ballantana ya kalle shi, haka suka ci gaba da tafiya har suka ƙarasa ofishin ‘yan sandan. Kai tsaye aka wuce da Altaaf ƙaramin cell ɗin da ke cikin ofishin suka rufe shi, ƙarar rufe ƙyauren har cikin ran Wadata ya ji ta, sai lokacin ya zaro ƙaramar wayarshi da ke cikin aljihu yaima Hajiya text cewar suna ofishin ‘yan sanda da Altaaf amma baisan me yayi ba. Don yana da tabbacin labari ma ya je mata, don ƙauye sun fi radio saurin isar da rahoto. 

Gyara tsayuwarshi Wadata ya yi tukunna ya kalli ɗan sanda ɗaya yana faɗin, 

“Kun kwaso mu ba tare da mun ji laifinmu ba.”

Cikin fuska ɗan sandan da Wadata ya nausa ya kalle shi yace 

“Au bakasan me ka yi ba? Ko don ban haɗaka da ɗayan ɗan iskan can na garƙame ku ba?” 

“Ka ƙyale shi kofur Ado. Laifukanshi na ƙaruwa ne ai, ga na dukan ɗan sanda ga kuma na dukan wanda ya shigar da ƙara.” 

Cewar ɗayan ɗan sandan, hannu Wadata ya kai yana murza goshin shi saboda alamun ciwon kai da yake ji. Yana gab da sake kwaɗa ma ɗan sandan mari a yanayin da yake jinshi, don haka ya ce, 

“Na ji nawa laifukan. Shi meye nashi laifin?”

Gyara tsayuwa kofur Ado yayi don ya nunama Wadata girmanshi baya tsorata shi. 

“Wannan bayin Allah sun shigar da ƙarar cewa ya yi wa ‘yarsu fyaɗe…” 

Sai da Wadata ya runtsa idanuwanshi yana haɗiye wani abu da yai mishi tsaye a wuyanshi da kalmar ƙarshe da kofur Ado ya faɗa. Ya kai mintina biyu kafin ya iya cewa, 

“Mene ne shaidar su?”

Ya ƙarashe maganar yana maida idanuwanshi kan Nuwaira da take tsaye tana wani irin kuka da yake ji har bayan zuciyarshi. Ba zai yi ƙarya ba in yace yanayinta baisa shi jin son kashe mata Altaaf ba in har hakan zai samar mata wani dai-daito a duniyarta da yasan Altaaf ya gama wargazawa. 

“Shaidar su kake tambaya?”

Cewar ɗayan ɗan sandan a hasale, amma Wadata bama jinshi yake ba, hankalin shi ya tashi daga kan Nuwaira ya koma kan Altaaf, a hankali ya raba idanuwanshi daga kanta yana ƙare wa ofishin ‘yan sandan kallo, duka girmanta ba zai wuce ɗakin baccin shi ba, ƙazantar da ke ciki ne ma yasa shi tunanin inda suka jefa Altaaf ɗin da ba cikakkiyar lafiya yake da ita ba, numfashi Wadata ya ja yana saukewa haɗe da danne ko me yake ji yana mayar da shi can gefe ya ajiye, zai fuskance shi amma ba yanzun ba. Abu mai muhimmanci fitar da Altaaf daga wannan tarkon da ya jefa kanshi ciki. 

* * *** 

A ƙofar gida Ammi ta samu Hajiyar su Wadata, don da Asuba suka taho ita da Barrah, su yi gaisuwar su ɗan zauna wajen Azahar su juya, shi yasa suka iso da wuri ma. Su kuma su Hajiya zata kira Daddyn su Wadata ne, lambar wayarshi ta ƙi shiga don aje ofishin ‘yan sandan a ji me yake faruwa. Da fara’a Ammi take ƙarasawa wajen Hajiya, don sanadin zumuncin su Altaaf da Wadata ba ƙaramin shaƙuwa sukai ba, sun zama ƙawaye duk da Hajiya ta girmi Ammi ɗin, siyayyar kayansu duk wajen Ammi suke yinta ita da iyalanta yanzun. 

“Hajiya…”

Ɗan murmushin ƙarfin hali Hajiya tai wa Ammi, kafin Barrah da ke tauna cingam ɗinta hankali a kwance ta kalli Hajiya da faɗin, 

“Ina kwana.”

A iya girmamawar da zata iya, a shekarun nan ta yi wani irin girma, tana aji huɗu ne a sakandire,yanayin fuskarta zai nuna maka yarinya ce, ta zama ‘yan mata, rashin kunya babu kama hannun yaro, bata ganin kan kowa da gashi, musamman yanzun da take jin tashen ‘yan matanci, Ammi tasa ta ɗora after dress kan wando da rigar da ke jikinta saboda gidan gaisuwa za su zo, ranta bai so ba, duk da haka bata saka mayafi ba, hula baƙa ta saka a kanta. Ta kuwa yi matuƙar kyau, don takan ce ta fi Altaaf kyau. 

Amsawa Hajiya ta yi, suka gaisa da Ammi da ta ɗora da, 

“Ina su Altaaf ne? Inata kiran wayarshi ba’a ɗauka. Lafiyar su dai ko? Jiya ya ce mun nan za su kwana shi da Imrana.” 

Numfashi Hajiya ta sauke, ta so su wuce cikin gida ne ta sauke su Ammi, tukunna ta sa a nemo mata Daddy a shawo kan matsalar ba sai Ammi ta ji ba, amma ta ga alama hakan ba zai yiwu ba. 

“Wallahi an ɗan samu ‘yar matsala ne, Wadata ya ce min suna police station, to bansan me ya faru ba, nama kira Wadata ɗin bai ɗauka ba, shi ne na fito inga Daddynsu ya je a ji me ya faru.” 

Tunda ta fara magana, hankalin Ammi in yai dubu ya tashi, bata ma kawoma ranta cewar Wadata ba ne yai wani abin, saboda ta san halin rikicin Altaaf, duk da tafiyarshi jami’a ya zo mishi da shiriyar da ta bata mamaki, ko kaɗan a shekarun bata taɓa jin wani abu da ya yi ba. 

“Ina police station ɗin yake?”

Ammi ta tambaya. 

“Bari in kira Daddy to.”

Kai Ammi ta girgiza. Babu yadda Hajiya batai ba, dole suka samu wani saurayi nan suka shiga motar Ammin zuwa ofishin ‘yan sandan. 

***** 

Suna isa, ko mukullin motar ma Barrah ce ta cire ma Ammi daga jiki tana riƙewa a hannunta, don Ammi har ta shiga ofishin. Duddubawa take bata ga Altaaf ba. 

“Yana ina?”

Ta buƙata tana kallon Wadata da ke tsaye yana ƙoƙarin shawo kan matsalar. 

“Ammi?”

Ya faɗi cike da mamakin ganinta, ɗan ƙaramin cell ɗin ta hango Altaaf a ciki, yana kwance ne ma, tunda suka jefa shi bai damu da dattin da ke wajen ba ya kwanta, don jiri yake ji yana ɗibarshi har a kwancen. Sama-sama yake jinshi. Dafe ƙirji Ammi ta yi. 

“Na shiga uku ni Amina, Uban waya saka min yaro a ƙazamin wajen nan?” 

Ta ƙarasa maganar cikin ƙaraji, ɗaya daga cikin ‘yan sandan ta kalla. 

“Na ce wanne daƙiƙin ne a cikinku ya saka min yaro a wajen can?” 

Su duka mamakin ƙarfin halin Ammi suke, kafin ta hango mukullai a hannun wani ɗan sanda, ƙarasawa ta yi tana fisgewa, ya kuwa bi hannunta ya riƙo, wani irin mari ta wanka mishi da hannunta na haggu da ya sa shi sakinta babu shiri, Wadata baisan sa’adda murmushi ya ƙwace mishi ba sai da ya ji bakinshi ya motsa, a tare da Ammi yake ganin rikicin Altaaf, don da alama tama fishi ƙarfin hali. Da kanta ta ƙarasa har cell ɗin tana gwada mukullan, jikinta ɓari yake yi ganin Altaaf kamar baya motsi. Juyowa ta yi. 

“Wallahi duk in kuna son aikin ku ne za ku zo ku buɗe min yaro!” 

Ganin basu da niyyar zuwa yasa Ammi faɗin, 

“Me kukai mishi? Wallahi wani abu ya sami yarona sai na sa an kulle ku! Ba Za ku zo ku buɗe shi ba!” 

Ɗaya daga cikin ‘yan sandan Wadata ya kalla. 

“Ku buɗe mata yaro…”

Gardama ɗan sandan zai yi, Wadata ya katse shi. 

“Ka yarda dani, ku duka ba za ku so ganin abinda zai faru ba… Ku buɗe shi.” 

Ƙarasawa yayi ya karɓi mukullin daga hannun Ammi da ke sauke numfashi cike da ɓacin rai ya buɗe cell ɗin, da hanzari Ammi ta ƙarasa tana tsugunnawa ta tallabo Altaaf ɗin. Jikinshi ta ji kamar wuta. 

“Altaaf…Altaaf…”

Take kira tana kamar zata fashe da kuka saboda tashin hankali, bata taɓa ganin Altaaf cikin yanayi haka ba, ga fuskarshi gefe ya kumbura har cikin idonshi ɗaya, leɓenshi na ƙasa ma a fashe yake. Wasu hawayen baƙin ciki suka cika mata idanuwa. Altaaf kamar a mafarki ya ji muryar Ammi, bai tabbatar da ita bace ba sai da ta ƙaraso ya ji hannuwanta kan fuskarshi. Miƙewa ta yi tana kama hannuwanshi ta taimaka mishi ya miƙe da ƙyar, da taimakonta ya fito daga cikin cell ɗin, ‘yan sandan Ammi ke watsa ma wani kallo. 

Babu abinda zai hanata jin dalilin da yasa suka rufe mata yaro cikin wannan ƙazamin wajen. 

“Cikin ku wanne mai ƙarfin halin ne ya mishi wannan dukan!?” 

“Ammi…”

Wadata ya fara, kallon da Ammi tai mishi yasa shi yin shiru, yakan ga kallon a tare da Altaaf, ya kuma san ma’anarshi, babu abinda zai hanata magana, gara ma ya barta ta faɗi abinda take son faɗi. 

“Hajiya kinsan me yayi?”

Kofur Ado ya faɗa. Harara Ammi ta watsa mishi. 

“Ko ma uban me ya yi.”

“Fyaɗe fa ake tuhumar shi da shi.”

Duk da maganar ta zo ma Ammi kamar saukar hadari bai hanata faɗin, 

“Wa yai ma fyaɗen?”

Da hannu kofur Ado ya nuna mata Nuwaira da ke rakuɓe jikin Inna. Wani irin kallo Ammi take binta da shi, kafin ta mayar da kallonta kan kofur Ado. 

“Dusar dawa ce a ƙwaƙwalwar ka ko? Ka kalli yarona, ko cewa akai maka yayi fyaɗe za ka soma duba yarinyar ko? Ta yi kama da ajinshi?” 

Wannan karon Inna ce take kallon Ammi da wani irin yanayi mai wuyar fassara. Wannan karon Altaaf kanshi ya kwantar jikin kafaɗar Ammi, yana jin kamar zai faɗi, nauyin laifukanshi yake ji suna danne shi. Ammi bata san komai ba, idonshi yake yawatawa saida ya sauke su kan Wadata tukunna ya tsayar da su, so yake Wadata ya kalle shi ko da idanuwanshi ne ya roƙe shi ya ce wani abu, yai mishi ihu, yai mishi faɗa kamar yadda ya saba. Amman ya ƙi ɗagowa. Faɗa Ammi take yi kamar zata tashi ofishin, dole Hajiya ta kamata suka fita har lokacin Altaaf ɗin na riƙe a jikinta, mota ta saka shi tana ci gaba da bambami. 

Anan Wadata ya so a kashe case ɗin, ‘yan sandan suka ce dole sai an je babban ofishin su da ke cikin garin Zaria. Ammi ta so su wuce asibiti ne da Altaaf ɗin, amma batai magana ba ta yarda aje Zaria ɗin ko don ta nuna wa ‘yan sandan nan iyakarsu da kuma wannan kucakan ‘yan ƙauyen da suke tunanin Altaaf ɗinta zai taɓa ƙazamar ‘yarsu. A nan sukai sallama da Hajiya, Wadata ma sai da ya koma ya ɗauki motarshi ya bi bayansu, shi ya ba ‘yan sandan kuɗin mai da za su zuba a motarsu don su kwashi su Inna. Suka nufi garin Zaria gaba ɗaya. 

Zaria

Ran Ammi in yai dubu ya ɓaci da yadda Nuwaira ke kuka tana faɗin kawai cikin gidan ta ga Altaaf, bata san ya akai ma ya shigo ba, da yadda babanta yake nuna wani result ɗin asibitin ƙauye. Bata ma san yadda akai suka san Altaaf ɗin ba har suke neman manna mishi wannan sharrin, Altaaf ɗinta ya yi rashin ji ta sani, amma ba’a taɓa kawo mata ƙararshi ta ɓangaren mata ba. Ganin ana neman bata mata lokaci yasa ta fita ta kira wani abokin wasanta da kwamishina ne a garin Kano ta faɗa mishi abinda yake faruwa. 

Nan take yai kiran waya daga can sama ya fara magana a kashe wutar. Abinka da ƙasar Najeriya da masu farcen susa sune masu gaskiya a koda yaushe. Lokaci ɗaya zancen ya fara sauyawa. 

“A ina ta haɗu da kai?”

Ɗan sandan ya tambayi Altaaf, Ammi ya kalla yana rasa abinda zai ce. 

“Altaaf ɗina ya yi rashin ji a baya. Da rigima ka ce min ya yi bazan taɓa musa muku ba. Amma neman mata ba halin shi bane ba. Imrana ka faɗa musu raina yana ɓaci wallahi…” 

Shiru Wadata ya yi, Ammi ba zata taɓa fahimta ba, saboda Altaaf yana abinshi ne da lissafi, shi yasa yake mamakin yadda akai lissafin ya ƙwace mishi wannan karon, ko matan ajinsu baya taɓawa, yana kuma da tabbacin haka a unguwarsu ma, ko cikin dangi, duk yadda zai yi kar lalacewarshi ta kai kunnen Ammi ya sani. Maganganun Ammi suka sa jerin matan da suka zubar ma Altaaf ciki gifta mishi, ƙazanta da girman laifin da yayi na danne shi ta fannin da bai taɓa zato ba. Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce, 

“Awara na siya wajenta da yammaci. Shi ne kawai haɗuwar da muka yi.” 

Ƙaryar ta fito daga bakin Altaaf, a karo na farko da ya ji ɗacinta kan harshen shi. Yana ganin yadda Nuwaira ta ɗago ta kalle shi, hawaye na zubar mata. ‘Yan rubuce-rubuce ɗan sandan ya yi. 

“Duk daren jiya kana ina?”

“Ina gida gaba daya, gaisuwa ya kai ni ƙauyen Kinkiba, ba kowa na sani ba balle in fita.” 

Kai ɗan sandan ya jinjina, da duk ƙaryar da za ta fito daga bakin Altaaf da yadda yake jin girmanta na danne shi. 

“Waye shaidarka”

“Yaya Imran.”

Altaaf ya faɗa yana sauke idanuwanshi kan Wadata da ke zaune. Sai lokacin Wadata ya ɗago ya kalli Altaaf ɗin, yana tabbatar da sun haɗa idanuwa don ya ga asalin ƙarfin halin Altaaf ɗin, abinda ya yi bai ishe shiba, sai yasa shi yin ƙarya, sai ya ja shi sun lulluɓe abinda ya fi komai muni a wajenshi, ba wai zai taɓa iya tona ma Altaaf asiri bane ba, amma Altaaf ɗin zai iya kashe wutar ba tare da ya sakoshi a ciki ba. Idanuwanshi na cikin na Altaaf ɗin ya ce, 

“Ina tare dashi duk daren jiya. Saboda ba shi da lafiya ma, ba mu yi bacci ba, ‘yan sandan da muka taho da su za su iya shaidawa saboda a gabansu ma yana ta amai. Sa’adda suka ganmu asibiti za mu tafi.” 

Jinjina kai Ammi take tana kallon su Inna da ke girgiza kai. Cikin kuka Inna ta ce, 

“Da idona na ganshi, wallahi ƙarya suke yi da idona na ganshi… Inda zan iya canza komai da ya faru zan goge ganinshi da na yi saboda yanayi ne da zai kasance da ni har abada…” 

Hannu Tawfiq yasa yana dafa kafaɗar Inna. Jikinshi a sanyaye yake, zalunci da rashin adalci na ƙasarshi ya gama sanyaya mishi jiki, tabbas wata shari’ar sai a lahira, wannan kam sun rasa ta, tun suna Kinkiba ya ga alamar ƙarar da suka shigar bata ƙare su da komai ba sai tabon Nuwaira da suka nuna wa ɗaukacin Kinkiba. 

“Inna… Akwai Allah.”

Tawfiq ya faɗi yana jin zuciyarshi kamar zata buɗe, musamman da ya ga mahaifinshi na share ƙwalla. A wulaƙance Ammi ta kalle su tana faɗin, 

“Kunsan akwai Allah ashe. Wallahi bazan yarda ba, ina shigar da ƙarar sharrin da suka liƙa wa ɗana, ‘yan sandan nan ma ina shigar ƙarar cin zarafi da dukan da sukai mishi.” 

Da sauri Kofur Ado ya ce, 

“Wallahi Hajiya ba mu taɓa shi ba. Kinga wanda ya dake shi nan.” 

Ya ƙarashe yana nuna Tawfiq ɗin, shi banda hakorinshi ma da Wadata ya girgiɗe babu abinda ya same shi, yaso tashin maganar, amma ta ko ina ya ga ko su Ammi basu san kowa ba suna da kuɗin kashe case ɗin cikin mintina, kuma ko bai rasa aikinshi ba, za su iya ja mishi abinda za’a tsayar mai da albashi, dama ya maƙale ma case ɗin ne don ya ɗan samu na cefane. Tawfiq Ammi ta kalla. 

“Daman kai ne ka taɓa min yaro? Bayan uwarka da ƙanwarka sun liƙa mishi sharri bai isheka ba.” 

Miƙewa Ammi ta yi tana ma DPO ɗin da suke ofishin shi alama daya bita. Jakarta ta buɗe tana nuna mishi bandir ɗin ‘yan ɗari bibbiyu. Murmushi ya yi. 

“Ina son su gane kuskuren da suka yi.”

Kai ya jinjina mata. Yana komawa kujerarshi ya zauna. Tukunna Ammi ta bi bayanshi itama tana zama. 

“Wannan case ɗin ba shi da wani tushe. Ko da anma ‘yarku fyaɗe. Ba ku da wata shaida ƙwaƙƙwara, saboda haka ana tuhumarku da laifin ɓata suna da cin zarafi na mutum mai mutunci kamar Altaaf da kuka yi, da kuma mahaifiyarshi da kuka wahalar…Sergeant!” 

Da sauri wani ɗan sanda ya taho yana faɗin, 

“Sir…”

“Ka kulle min su.”

Kafin ka ce meye ya kira wasu ‘yan sandan sun cakumi Malam Bashari da Tawfiq kamar ɓarayi suna soma jansu. Wani irin kuka Inna da Nuwaira suke yi. Ƙasa Inna ta tsugunna tana soma ba wa Ammi haƙuri . Wadata kuwa Altaaf yake kallo, da idanuwanshi yake daring ɗinshi daya bari a wulaƙanta su fiye da yadda aka yi. 

“Ammi.. Ki bar su don Allah.”

Altaaf ya faɗi muryarshi na rawa. Musamman da ya ga yanda Malam Bashari ke zubda hawayen takaici. Kai Ammi ta girgiza. 

“Baka da hankali ne halan?

Baka ga abinda sukai maka ba.” 

Kan shi Altaaf ya dafe da yake ji kamar zai faɗo saboda ciwon da yake yi, sabon zazzaɓi ne ya rufe shi. 

“Gida kawai nake son tafiya in manta abin nan ya faru. Ammi don Allah.” 

Ya ƙarasa maganar kamar zai yi kuka. 

“Sai sun faɗa da bakinsu ƙarya suke maka.”

Da sauri Inna ta ce, 

“Ƙarya nake, ƙarya muke mu dukkanmu. Don Allah mun janye ƙarar nan. Ku yi haƙuri.” 

Take ƙarasawa cikin wani irin kuka, faɗan da ya fi ƙarfinka sai ka mayar da shi wasa, sai lokacin Tawfiq ya ji wasu irin hawaye masu ɗumi tarar mishi, ganin yadda ake wulaƙanta su akan gaskiyarsu saboda abin duniya. Sai lokacin Ammi ta kalli D. P. O ɗin tai mai alamu da abar maganar. Duk da ta so a kulle mata su ko kwana biyune. Amma lafiyar Altaaf ce farko akan komai. Nan sukai ‘yan rubuce-rubuce aka rufe case ɗin. Inna Nuwaira ta kama tana ɗago da ita, kuka take kamar ranta zai fita, Altaaf take kallo, bata jin akwai wani ɗan Adam da zata tsana a tsawon rayuwarta kamar shi. 

“Allah ya ɗauke maka farin ciki kamar yadda kai min, Allah ya tsayar maka da dukkan al’amuranka kamar yadda ka tsayar mana da namu, Allah ya tarwatsa maka rayuwarka ta fannin da baka taɓa zato ba, A-Tafida ko? In shaa Allah sunan ka kanshi sai ya zamar maka tashin hankali kamar yadda ya zamar mumin, ka ji ni? Wallahi ba zaka taɓa samun wadataccen farin ciki ba.” 

Nuwaira ta ƙarasa tana jan Inna suka juya ba tare da ta tsaya ta ji abinda suka ce ba, Ammi kanta addu’ar ta girgiza ta, ballantana Altaaf da yake jin kamar Nuwaira ta watsa mishi ruwan ƙanƙara, sosai maganganunta suke mishi yawo, tunda yake a duniya ba’a taɓa mishi addu’a mai munin wannan ba, ko ma an taɓa mishi bata taɓa zuwa kunnenshi ba, wani irin tsoro ne yake shigarshi marar misaltuwa, baisan ya riƙo hannun Ammi ya riƙe gam cikin nashi ba sai da ya ji ta ce, 

“Bakai mata komai ba, babu abinda kai mata, saboda haka babu abinda zai same ka.” 

Amman akwai wani yanayi a muryarta da yasa shi jin kamar tana son tabbatar wa kanta ne bai ma Nuwaira komai ba fiye da yadda take son tabbatar mishi, idanuwan Tawfiq da ke yawo akanshi ne yasa shi maida hankalinshi kanshi. Da wani irin yanayi shima yake kallon Altaaf ɗin kafin ya ce, 

“Kuɗin ka da matsayin ka ba za su shiga tsakanina da illata ka fiye da yadda kai mana ba in har idona ya sake sauka akan ka, ba ɗauri ba, kasa a ɓatar da ni, saina illata ka in ka tako ƙafa hamsin tsakanin ka da gidan mu.” 

Da sauri Ammi ta kalli D.P.O

“Kana jinshi ko? Kana jin abinda ya ce…”

“Ammi don Allah. Mu tafi kawai…”

Shiru Ammi ta yi tana bin bayansu Tawfiq da suka fita daga ofishin ‘yan sandan da kallo, duk da haka sai da ta jaddada wa DPO ɗin da ya rubuta ya ajiye maganganun Tawfiq ɗin, ta kawo kudaɗe ta bashi tukunna suka tafi suma.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.3 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 29 Alkalamin Kaddara 31  >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 30”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×