Skip to content
Part 35 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Kano

Kai tsaye daga gidan Wadata, Kaduna ya wuce, idan ya ce ga abinda yake tunani a hanyar shi ta zuwa har ya isa zai yi ƙarya, asalima hankalin shi gaba ɗaya ba akan tuƙin motar yake ba. Allah ne kaɗai ya mayar da shi Kaduna lafiya. Yana yin parking ya fito daga motar ya nufi ɓangaren da suka sauka. Majida ya samu a tsaye, bayanta jingine da bangon wajen, fuskarta kawai ya kalla ta tabbatar mishi da ranta a ɓace yake. 

“Lahiyar ka ƙalau ko?”                                                                

Ta tambaya muryarta can ƙasa, ɗan dafe goshi yayi yana kallon ta 

“Majee…”

“Ka hiɗiman, kana lahiya?”

Kai ya ɗaga mata a hankali, nata kan ta jinjina mishi tana juyawa 

“Majee…”

Ya kira, amma bata ko juyo ba, da sauri ya ƙarasa inda take yana riƙo hannun ta. Juyowa ta yi tana kiciniyar ƙwacewa tana dube-dube kar wani ya gansu 

“Ka sakan don Allah, ba ka ganin da kwai mutane.” 

Sake riƙe hannun nata yayi gam, ba za tai mishi fushi ba, yana buƙatarta fiye da yadda zata taɓa sani, yana jin kwanakin da suka rage mishi tare da ita basu da yawa. Janta ya soma yi. 

“Ina za mu? Ka sakan nikau hwa.”

Ko saurarenta bai yi ba sai da suka zo ƙofar gidan ya kama ƙofar yana murzawa, jan Majida ya yi har cikin ɗakin, tukunna ya saketa yana ƙura mata idanuwan shi cikin yanayin da yasa ta sauke nata idanuwan da suka soma cika da hawaye. Hannunta ya sake ja suka shiga cikin falon sosai tukunna ya zaunar da ita kan ɗaya daga cikin kujerun falon. 

“Majee…”

Ya sake kiran sunanta. Ɗagowa ta yi, hawayen da take ƙoƙarin tarbewa suna zubo mata, yau ta zo mata wani iri, tunda ya tafi bai kirata ya faɗa mata ya sauka ba, kuma ba haka ya saba mata ba, ya isan ta kira shi ta ji muryarshi wani iri, kuma ya ce zai kirata bai kira ba, bayan nan kira ya fi ashirin tai mishi saboda haka kawai ta ji zuciyarta na mata rawa, ta kasa tsaida tunaninta waje ɗaya. Cike da tsoro, muryarta na rawa ta ce, 

“Mi nai maka? Ka hiɗiman don Allah.”

Kai yake girgiza mata tunda ta fara magana, ba abinda tai mishi, ba ita bace ba, shi ne da laifin, shi ne da sirrikan shi da ya binne suka fito da kansu, yanzun kuma suna neman biyo shi su tarwatsa mishi komai. 

“Akan yara ne ko? Ya zan yi? Bansan mi ya kamata in yi ba, ina addu’a wallahi, don Allah ka yi haƙuri…” 

Majida ta ƙarasa, hawaye masu ɗumi na zubo mata, tana sa Altaaf ɗin jin kamar zuciyarshi zata faɗo, kamar ya gaya mata komai haka yake ji, amma yasan ba zai iya ba, bayani ba abu bane da yake yi ma mutane komin kusancin shi da su, yakan rasa ta inda zai fara, tsoron zasu barshi ma ba zai taɓa bari ya ce musu komai ba, sai dai in sun gano da kansu ne. Baisan me zai ce mata ba, don haka ya matsa yana riƙota jikin shi, kuka take sosai, ya tsani kanshi da yadda yasa ta damu sosai. 

“Baki min komai ba, ba akan yara bane ba Majee, kina jina ko?” 

Kai take ɗaga mishi, cikin kuka ta ce, 

“Me yasa nai ta kiran ka baka ɗauka ba? Kuma baka kira ni ba?” 

Ɗayan hannun shi yasa yana laluba aljihun shi, bai ji wayar ba, ya mantata a mota. Idan akwai abinda bai taɓa shiga tsakanin shi da ita ba shi ne ƙarya, ba zai fara yanzun ba, zai iya ƙoƙarin shi na ganin ya kauce ma faɗa mata asalin abinda yake damun shi, ba tare daya mata ƙarya ba. 

“Wani abune ya taso, bazan iya faɗa miki ko menene ba yanzun, amma ba ke bace ba, karki ƙara ɗauka kin min wani abu in ba ni na faɗa miki da bakina ba…” 

Ɗagowa ta yi daga jikin shi, hannuwanshi yasa yana goge mata fuska. 

“You are going to be okay ko? Ka ce man babu abinda zai same ka.” 

Majida ta buƙata tana yawata idanuwanta kan fuskarshi, kafaɗa ya ɗan ɗaga mata fuskarshi ɗauke da yanayin rashin tabbas, ta ya ba zai so Majida ba, macece da yake da tabbas ba kowanne namiji yake dacewa da samu ba, da duk ranar da zai yi tare da ita yana jin yadda ba shi bane mijin da ya kamata ta aura, ko kaɗan bai cancanci ya auri Majida ba, saidai bai taɓa hango ayyukan shi bane za su raba su, bai ma taɓa hango rabuwar su ba, yanzun ma tunanin hakan kawai ji yake kamar zuciyar shi zata fito daga ƙirjin shi. Daren su na farko na faɗo mishi a rai. 

* * *** 

Ba wasu abokai yake da su na arziƙi ba, ya hango daren yau da yadda su Wadata ne za su rako shi, sai Ashfaq, su duka basa cikin rayuwar shi, har ya ƙarasa ɗakin yarinyar da baisan kalarta ba, don babu yadda Ammi bata yi da shi akan ya je ba ya ce duk abinda ta zaɓa ya mishi ba sai ya je ba. Tare da bugun zuciyarshi ya buɗe ɗakin, tana zaune kan gado, fuskarta a lulluɓe kamar sauran jikinta, zai iya rantsewa kamar a fim haka yake ganin abin. Ya kasa yarda cewar matar shi ce a zaune. Shi ne da aure a wannan lokacin, ba haka yai tsarin rayuwarshi zata kasance ba. 

Da sallama ya ƙarasa inda take yana ajiye ledar da ke hannunshi tukunna ya zauna bakin gadon, zufa yake duk da AC ɗin da ke kunne a ɗakin, baisan me ya kamata ya fara yi ba, baisan abinda zai ce mata ba. Murmushi yayi me sauti yana faɗin, 

“Bansan me ya kamata in fara yi ba.”

Sai da ya ji saukar maganar a kunnuwan shi tukunna yasan a fili yayi ta, 

“Addu’a…”

Ta ce mishi, muryarta a dakushe ta fito. Ga mamakin shi amsa ta ya yi da cewa, 

“Wacce iri?”

Ta cikin mayafinta ta fito da hannunta tana kama nashi hannun, ƙunshinta ya mishi kyau sosai, bai gama ƙare ma hannunta kallo ba ya ji ta ɗago nashi tana ɗorawa saman kanta . 

“Ka maimaita ko mi zan ce…”

Ta faɗi tana sakin hannunshi da ke saman kanta, kafin ya ce ga abinda yake faruwa ta fara magana. 

“Allahumma inna’as’aluka khairaha wa khairama jabaltha alaihi wa a’udhu bika min sharri ha wa sharri ma jabaltha alaihi…” 

Sai dai me, kasa maimaitawa ya yi gaba ɗaya, a hankali ta bi ɗaya bayan ɗaya, in ta faɗa sai ya maimaita har ƙarshe, kafin ta sauke hannunshi daga kan nata, tana mayar da nata a nashi, addu’ar da suka karanta tare ta karanta yana jin canjinta a harshenta, ba zai ce ga kalaman da ta canza ba, yana tunanin jinsin mace ne zuwa na namiji, bai da tabbas tunda ba larabci yake ji ba, da Aslam ne dai. Sauke hannunta ta yi tana ƙoƙarin mayar da shi cikin mayafin. Baisan lokacin da yai sauri ya riƙo hannun ba, dumtsewa yai cikin nashi yana jin ƙarantar hannun. 

Kafin yasa duka hannayen shi biyu yana buɗe nata a ciki, zai rantse an halicci hannuwan Majida ne kawai saboda su zauna cikin nashi, wata irin nutsuwa yake ji ta fannonin da bazai zata ba ballantana ya iya misaltawa. 

“Muyi sallah ko?”

Ya buƙata cike da rashin tabbas, kai ta ɗaga mishi, fuskarta yake son gani da duk wani abu da yake da shi. Shi ya fara miƙewa, har lokacin hannunta na cikin nashi, tukunna ya taimaka mata ta miƙe, sakin hannunta yayi yana kama mayafinta ya daga ya mayar dashi bayan kanta, idanuwanta na kafe a ƙasa, don haka yasa hannunshi a haɓarta yana ɗago da kanta, idanuwanta da duka fuskarta a kumbure suke da alamun kuka ta yi ba kaɗan ba. Ba fara bace, tana da duhu sosai, ya sha ganin mata kala-kala, ciki har da wanda ba ‘yan Ƙasa bama, amma suke zaune a Nigeria. 

Ba zai ce Majida na da muni ba, sai dai kyawunta ba wanda za ka gani bane a kallo ɗaya, baya tunanin in shi zai zaɓo mata zai nemo kalarta, duk da farar mace ko baƙa basu dame shi ba, ba fuska yake dubawa a jikin mace ba, sai dai akwai wani yanayi a fuskarta da yake ji kusa-kusa da zuciyarshi yana mishi zagaye kamar yana neman hanyar shiga ciki, yana kuma ganin kunya shimfiɗe a tata fuskar, hanyar banɗaki ya nuna mata da hannu, tana wucewa, sai da ta ɗauro alwala ta fito tukunna ya je yayi. 

Bai taɓa jin taimakon da Aslam yai mishi ta fannin sallah ba sai yanzun, da kanshi Aslam yake rubuta hukunceghukunce sallah da duk wani abu a kanta yana ajiye ma Altaaf ɗin akan gado a ɗaki inda zai gani, don ya ga rubutun Aslam ne kawai yasa yake karantawa, bai taɓa tambayarshi ko ya gani ba ballanta ya ji ko ya karanta, abinda duk yasan shiriritar shi ta hanashi zuwa Islamiyya ballanta ya koya yakan rubuta mishi da Hausa ya ajiye mishi, murmushi yayi da tunanin Aslam ɗin, a duniya shine mutum na farko da Altaaf yake matuƙar jin kunya, akwai abubuwa da zai iya yi a gaban Ammi amma ba zai iya a gaban Aslam ba. 

Shi ya ja su sallah raka’a biyu, tukunna ya juya yana kallon Majida da take wasa da yatsun ta, hannuwanta sun mishi kyau sosai, matsawa ya yi kusa da ita, yana kama su ya riƙe, yana mamakin nutsuwar da hakan ta saukar mishi da bai taɓa samu a tare da wata mace ba, ya kuma rasa bambancin Majida da sauran matan. 

“Me yasa kika amince da aure na?”

Ya tambaya, saboda yana son sanin dalilinta, yasan ba zata rasa wanda take so ba, shiru ta yi kamar ba zata amsa mishi ba, kafin ta ce, 

“Sabida Babana…”

Daƙuna mata fuska yayi cike da rashin fahimta. 

“Baki da wanda kike so?”

Itama cike da rashin fahimtar take kallon shi. 

“Mi yasa kake tambaya?”

Ɗan ɗaga kafaɗa yayi, baisan dalili ba, kawai yana son sani ne, saboda haka ya tsareta da idanuwan shi, yana jiran ta amsa. Yana kallo tana kokawa da amsar da zata bashi kafin a hankali ta girgiza mishi kai, numfashi ya sauke da baisan yana riƙe da shi ba, ballantana dalilin fitowarshi da nauyi haka. Ledar da ya ajiye ya miƙa hannu yana janyowa tare da buɗewa. 

“Mu ci abinci.”

“Banjin yunwa.”

Majida ta amsa, dai-dai lokacin da cikinta yai wata irin ƙara, yana sake wata, kamar yana son ƙaryata maganar da tayi, da sauri ta sauke idanuwanta cikin na Altaaf da kamar hakan yake jira dariya ta suɓuce mishi, ita ma dariyar take yi a kunyace, sosai suke dariya daga ita harshi. 

* * *** 

Yanzun ma saida murmushi ya ƙwace mishi, komai ma Majida dabanne, kamar yadda take ta daban ita ma. 

“Ka yi shiru baka ce man komi ba.”

Majida ta ce cike da damuwa, murmushi yayi, a duk yanayin da yake baya zaton zai rasa nishaɗi ko ya yake in tana tare da shi.

“Zan yi ƙoƙari.”

Ya ce, hannuwanta ta zagaya tana rungume shi sosai a jikinta. Tana roƙon shi da kar ya bari wani abu ya sameta, bata san shi ya kamata ya roƙeta kar ta bari wani abu ya shiga tsakanin su ya samu auren su ba. Amma bazai iya ba. 

“Mi ka ci?”

Ta buƙata tana riƙe da shi har lokacin. Kai ya girgiza mata, don yama manta da wani abinci, a hankali ya zame jikinta daga nashi. 

“Bari in kawo ma abinci.”

“Ki kawo mana dai, sai mu ci tare.”

Kai ta ɗaga mishi tana murmushi kamar ba yanzun ta gama mishi kuka ba, ba don yana jin yunwa ba ne ya ce ta kawo, don yasan bata ci komai ɗin ba itama, shi yasa, tana fita cikin kujerar ya kwanta, yana jin yadda duniyar take juya mishi a hankali, so take ta birkice da shi tukunna ta sake shi ya faɗo ta kai, bai kuma san ta inda zai fara tsayar da ita ba. 

* * ***

ABUJA

Tana tashi ta watsa ruwa ƙasa ta sauko, don a ɗakin Nuri ta kwana, Aroob ta samu a kitchen ɗin, jikinta sanye da doguwar riga pink, sai wani takalmi ƙato kamar na ulu da hoton mage a jiki shima pink ɗin ne, hular kanta Zafira take kallo tana dariya. 

“Aroob wacce irin hula ce wannan?”

Ta tambaya, sai da ta juye pancake ɗin da take yi, tukunna ta juya ma Zafira idanuwanta. 

“Na tashi lafiya Zaf, ke fa?”

Dariya Zafira ta sake yi. 

“Ki ƙyale ni, yunwa nake ji nikam, me kika dafa?” 

Kafin Aroob ta bata amsa Fawzan ya shigo kitchen ɗin, riga da wando ne a jikinshi, farar suit ɗinshi na rataye akan kafaɗarshi, plate ɗin da ke kusa da Aroob ya kai hannu don ya ɗauki pancake ɗin, ta doke hannun shi. 

“Aroob mana, don Allah sauri nake wallahi, yunwa nake ji kuma.” 

“Ina za ka je?”

Ta tambaya tana nuna shi da abin juya pancake ɗin da ke hannunta 

“Aiki za ni Nuri.”

Ya amsa yana hararar ta. 

“Da gaske nake, Yaya ya ce in kula da kai, kuma bai ce min yau za ka je wajen aiki ba, babu inda zaka.” 

Ware idanuwa Fawzan yayi cike da mamaki.

“Zaki matsa ko sai na kwɗeki?”

Ya faɗi yana harararta, ture ta yayi yana ɗaukar pancake ɗin tare da faɗin, 

“Ki haɗa min Tea ni, saura ki min hauka kuma.”

Turo laɓɓa ta yi. 

“Allah sai na faɗa ma Yaya baka jin magana ta.”

Ƙaramin tsaki kawai Fawzan ya ja yana gutsurar pancake ɗin, sai da ya tauna tukunna ya ce, 

“Zaf kin tashi lafiya?”

Kai ta ɗan ɗaga kafin ta amsa Aroob da ke haɗa mishi Tea ta ce, 

“Nima na tashi lafiya duk da baka tambaya ba.” 

Numfashi ya sauke.

“Ya akai yarinyar nan ta zo cikin mu?”

“Nima ban sani ba fa.”

Zafira ta amsa tana yin murmushi.

“Ina jinku…”

Aroob ta ce tana saka cokali a cikin kofin shayin, hira suka ci gaba dayi kamar basu jita ba, har ta gama ta miƙa mishi kofin ya karɓa, kurɓa yayi yana ɓata fuska 

“Baki saka min sugar ba Aroob.”

Juyowa ta yi tana kallon shi. 

“Oh na ɗauka Yaya ne.”

Da kanshi Fawzan ya ƙarasa yana ɗaukar sugar ya saka dai-dai yadda zai mishi, a tsaye yake kurɓa da sauri da sauri don ya makara, da bai yi niyyar zuwa aikin ba, amma bai ga zaman da yake a gida ba tunda babu abinda zai yi kuma ya ji sauƙi. 

“Ka ɗauki inhaler ɗinka?”

Kai ya girgiza ma Aroob ɗin. 

“Yaya Fawzan!”

Hannu ya ɗaga mata yana ƙoƙarin haɗiye shayin da ke bakinshi kafin ya ce, 

“Yi haƙuri zan ɗauka.”

“Me yasa kake yin haka?”

Aroob tai maganar kamar zata yi kuka, tana ɗorawa da, 

“Ka kyauta…”

Tukunna ta juya tana ci gaba da abinda take yi , kofin shayin ya ajiye yana ƙarasawa ya ɗora hannuwanshi kan kafaɗun Aroob ɗin. 

“Haba ‘yar ƙanwata Aroob.”

Tureshi ta yi. 

“Ka barni, bana magana da kai…”

Kallon su Zafira take yi tana murmushi, tunda ba yawan magana gareta ba tunda can, sosai ta yi kewar su da nutsuwar da take samu tare da kasancewa da ‘yan uwanta, lumshe idanuwa ta yi tana jin nutsuwar na ratsa ta, kafin ta buɗe su da wani irin tashin hankali marar misaltuwa jin muryar Omeed na kiran, 

“Zafira! Zafiraa!!”

Hannu ta kai babu shiri tana dafe cikinta da take jin gaba ɗaya hanjin ciki na hautsina mata saboda tashin hankali. Bata san lokacin da ta koma bayan Fawzan tana laɓewa ba. 

“Innalillahi wa inna ilaihir raji’un… Yaaya don Allah karka bari ya tafi da ni… Na shiga uku…” 

Zafira take faɗi ko ina na jikinta yana ɓari, ji take kamar a ce tana da wani sihiri da zai bata damar shigewa cikin ƙasa ta ɓoye ma Omeed. 

“Zafiraa!”

Ya sake kira tana jin sautin muryarshi har cikin zuciyarta. 

“Wane irin rashin hankali ne wannan?”

Fawzan ya faɗi rai a ɓace, saboda bai taɓa ganin kalar shi ba, ya Omeed zai shigo musu gida yana ƙwala mata kira haka kamar bashi da hankali. Aroob kanta tambayar da ke fuskarta kenan. Kallon su Fawzan ya yi yana faɗin, 

“Aroob karki bari ta fito. Ku tsaya nan ina zuwa.” 

Kai Aroob ta ɗaga mishi tana dudduba wayarta, don ta kira Rafiq tunda Daddy baya nan, shi kaɗai yasan yadda zai yi musu da Omeed. Fawzan kuwa falon ya ƙarasa yana kallon Omeed da ke tsaye, shigarshi yake kallo, riga da wando ne a jikin shi, amma maɓallan rigar ba a mazauninsu ya saka su ba, da alama babu nutsuwa a tare da shi sa’adda ya saka rigar, duk da yanzun ɗin ma babu alamarta a tare da yanayin shi gaba ɗaya. 

“Baka taɓa jin wasu kalamai da ake kira sallama ba?” 

Fawzan ya buƙata, hannu Omeed ya saka cikin gashin kanshi yana ƙara hargitsa shi tukunna ya saki yana maida numfashi a hankali kamar yana son controlling ɗin kanshi. 

“Bana son tashin hankali, bana son hayaniya, basu na zo yi ba. Matata kawai za ku bani in tafi.” 

Dariya ce ta suɓuce ma Fawzan, sosai yake kallon Omeed ɗin yanzun. 

“Ka sha omo ne halan?”

Ya buƙata, don yana da tabbacin Omeed ɗin baya cikin hankalin shi. Ba ma zuwa yayi a zauna a tattauna yadda zai ba Zafira takardar ta cikin sauƙi ba, ya ba su haƙuri i kar su maka shi kotu kan dukan da yai mata, zuwa ya yi a bashi ita da gadara kamar wadda suka siyar mishi da ita. Takun tafiyar da Fawzan ya ji ne yasa shi juyawa, Nuri ce ta fito, idanuwanta na kan Omeed da yake faɗin, 

“Yauwa Nuri, gara da kika fito, ni ba ma zama na zo yi ba. Zafira na zo tafiya da ita.” 

Wannan karon Fawzan ta kalla, da idanuwanta take tambayar shi ko me yake faruwa. 

“Yadda kika ganshi haka na ganshi nima.”

Fawzan ɗin ya amsa muryarshi cike da mamakin ƙarfin halin Omeed ko ya ce rashin hankali, suna nan tsaye sun rasa me ya kamata su ce mishi sai ga Daddy ya shigo da sallama, yana fara ƙare wa Omeed kallo kafin ya kalli Nuri. 

“Me yake faruwa?”

Ya tambayeta da harshen Kanuri

“Yazo ne yana faɗin a bashi Zafira su koma.”

Nuri ta amsa Daddy da yaren itama. Cikin falon Daddy ya ƙarasa, yana amsa Fawzan da yai mishi sannu da zuwa da kai, zama yayi yana musu Nuni su ma da su zauna don baya son harkar da babu kintsi a cikinta. Tukunna ya kalli Omeed da yake zaune ƙarshen kujerar kamar yana jiran abu kaɗan ne ya tashi. 

“Me ya faru?”

Daddy ya tambayeshi ganin bashi da niyyar gaishe da shi ballantana a tambayi juna ya aiki da sauran abinda ya kamata, shi yasa ya tsallaka tambayar kai tsaye. 

“Nima ban sani ba, bana gida su Fawzan suka je suka taho min da mata, shi yasa na biyo in ɗauke ta mu koma” 

“Daddy ita ta ce mu je mu ɗauke ta, saboda yana dukan ta.” 

Fawzan ya faɗi da sauri yana watsama Omeed ɗin harara, ba don ƙirarshi ba, babu abinda zai hana ya kwaɗa mishi mari da ya fito ya ganshi, sai dai yasan in dambe ya kaure zai matuƙar wahala kafin a raba su, shi yasa ya kama mutuncin shi. 

“Duka?”

Daddy ya buƙata, maganar na zuwa mishi kamar daga sama, yana juyawa ya kalli Nuri da ta tabbatar mishi da haka zancen yake, wani abu Daddy ya ji yana taso mishi tun daga ɗan yatsan ƙafarshi zuwa tsakiyar kanshi. 

“Ina Zafira?”

Ya tambaya. 

“Tana cikin gida”

Fawzan ya amsa

“Kira min ita.”

Miƙewa yayi yana nufar hanyar kitchen, can ya same su kuwa, Aroob na riƙe da hannun Zafira da ke kuka. 

“Daddy ya dawo, ki zo Zafira.”

Kai ta girgiza mishi. 

“Na kira Yaya Rafiq na ce ya zo.”

Aroob ta ce ma Fawzan, kai ya ɗaga mata. 

“Zafira mana… Daddy ne ya ce ki zo.”

“Zai ce in bishi ne ko? Yaya Fawzan kashe ni zai yi wallahi.” 

Zafira take faɗi a firgice tana wani irin kuka. 

“Babu abinda zai miki, ba zamu bari ki koma ba.” 

Kallon shi take ba don ta yarda da shi ba, da ƙyar shi da Aroob suka jata zuwa falon, suna fita idanuwanta na kafe kan Omeed da yake zaune, ɗago kai yayi yana kallon ta, da idanuwan shi da ta ko yi karanta a zaman su yake faɗa mata ta yi kuskuren tahowa, kai take girgiza mishi tana kuka. 

“Dan Allah ka yi haƙuri.”

Take faɗi tana ƙwace hannunta daga na Aroob, bata ganin kowa a falon banda Omeed da alƙawurran da ke cikin idanuwanshi na dukanta har sai tunanin yin abu irin wannan ya ɓace mata, jikinta gaba ɗaya ya ɗauki ɗumi, akwai wajejen da basu warke ba na dukan da yai mata, hawaye ke zubar mata wani na bin wani, kai kawai take girgiza ma Omeed, ta san da wahala in Daddy bai sa ta bishi ba, gara ta fara bashi haƙuri tun daga nan kafin su tafi. Daddy kuma ita yake kallo da firgicin da ke fuskarta da ya sha gani a kan fuskar matan da ke fama da mazaje irin Omeed wani ɗaci na samun wajen zama a zuciyarshi. 

An rasa wanda zaice wani abu, har saida Rafiq ya shigo ɗakin da sallama, kai tsaye wajen Zafira ya wuce yana riketa, tana ganin shi ta ruƙunƙume shi kamar zata koma cikin shi don ta ɓoye ma Omeed ɗin. Bai ce komai ba ya kamata yana wucewa da ita sama, ɗakin shi na gidan ya shiga da ita yana zaunar da ita kan kujera, sai da ya koma ya ɗauko mata ruwa ya bata ta sha tukunna ya goge mata fuskarta. 

“Ki zauna nan… Kina jina, babu abinda zai miki, ba za ki koma gidan shi ba. Na miki alƙawari…” 

Kai take ɗaga ma Rafiq ɗin tana karantar gaskiyar alƙawarin da yai mata cikin idanuwanshi tukunna ta ji jikinta ya daina barin da yake, amma zazzaɓin tashin hankali ya rufe ta ruf, tana kallo Rafiq ya fita daga ɗakin yana ja mata ƙofar, zuciyarshi tafasa take yi tun suna kan hanya, ƙarfin halin Omeed na bashi mamaki, da yadda ya iya shigowa har cikin gidansu ba tare da kunya ba bayan abinda yayi, yana fitowa falon bai kalli kowa ba ya ƙarasa inda Omeed yake yana kai mishi duka a fuska da dukkan ƙarfin shi. 

Da sauri Fawzan da Daddy suka yi kan Rafiq ɗin suna riƙe shi, yana ƙwacewa, har da ƙafa yake ƙoƙarin kaima Omeed ɗin duka. 

“Rafiq ya isa haka…”

Cewar Daddy, girgiza mishi kai Rafiq yake yi. 

“Ta ya zai shigo gidan nan? Daddy ta ya zai shigo saboda bashi da kunya… Bayan abinda ya yi?” 

Sosai Daddy ya riƙe Rafiq ɗin, don haka Fawzan ya sake shi, da ƙyar ya janye shi gefe yana juyawa ya kalli Omeed da ke goge bakin shi da Rafiq ya fasa, kamar yadda ya faɗa ma su Nuri ba tashin hankali yazo yi ba, matarshi kawai yake so a bashi yana nufin maganganun har ranshi, ba don haka ba saiya nuna ma Rafiq yayi babban kuskuren ɗaga mishi hannu. 

“Ni matata kawai na zo tafiya da ita.”

Omeed ya faɗi muryarshi can ƙasa. 

“Ka tafi Omeed zan yi magana da babanka.”

Daddy ya faɗi, miƙewa Omeed yayi yana girgiza ma Daddy kai, su bashi matarshi kawai, saboda ji yake komai zai iya faruwa, a airport ya kwana saboda bai samu jirgin da zai kawo shi Abuja ba daga Lagos a jiyan, ba zai koma babu Zafira ba, ita ce nutsuwar shi, ba za su gane ba.

“Ku ban mata ta.”

Omeed ya faɗi. 

“Bashi da hankali Daddy, wallahi bashi da hankali.” 

Rafiq yake faɗi yana ɗaga hannuwanshi cikin ɓacin rai da rasa dalilin da zai sa Daddy ya hanashi dukan Omeed ɗin sai hankalin shi ya dawo jikin shi, Nuri kuwa kallon su take ta rasa abinda ya kamata ta yi. 

“Ni kake kira marar hankali?”

Omeed ya tambaya yana ma Rafiq ɗin wani irin kallo. 

“Kana da hankalin ne? Ka rasa shi ranar farko da ka ɗaga wa mace hannunka, yanzun ma asibitin mahauka ya kamata a wuce da kai.” 

Dariya Omeed yayi yana girgiza ma Rafiq kai.

“Ni kake kira marar hankali bayan kai kake tare da ciwon hauka.” 

Daddy Rafiq yake kallo.

“Ka barni in daki mutumin nan Daddy. Don Allah ka matsa…” 

Rafiq yake faɗi yana ƙoƙarin wucewa, amma Daddy na riƙe da shi, a kotu ya kamata su daki Omeed inda yake da tabbacin za su yi nasara, ba nan ba da yake da yaƙinin su ukun babu abinda za su ɗiba a jikin Omeed, baya faɗan da yasan babu nasara. 

“Ka barshi ya ƙaraso, in na dake shi ƙilan ya tuna ya ɗauki mota ya je ya kashe matarshi da ‘yarshi, rashin gaskiya yasa ya manta hakan.” 

Nuri bata san ta miƙe ba sai da ta ƙarasa wajen Omeed tana ɗauke shi da mari, kallonta yayi kawai yana yin murmushi, in sun hanashi Zafira ba zasu taɓa samun kwanciyar hankali ba kamar yadda yasan in ya tafi ba zai samu ba harsai babanshi ya zo yasan yadda ya yi ya dawo mishi da matarshi. Gara su duka kar hankalin su ya kwanta. 

“Fita… Ka fita kafij in sa security su fitar da kai.” 

Nuri tai maganar muryarta can ƙasa, kallon Rafiq da yake tsaye kamar gunki Omeed ya yi. 

“Oh babu wanda ya faɗa maka? Ka kashe matarka da ‘yarka?” 

“Omeed Modibbo duka danginka ne za su biya abinda ka yi yau.” 

Daddy ya faɗi cikin alƙawari, babu wanda zai taɓa mishi iyali haka bai biya ba. Dariya Omeed yayi yana juyawa ya fice daga falon, Fawzan kuwa hankalin shi na kan Rafiq tun maganar farko da Omeed yayi. 

“Yayaa…”

Fawzan ya kira muryarshi can ƙasa, ganin yanayin fuskar Rafiq ɗin da tai fari kamar babu jini a jikinta.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 34 Alkalamin Kaddara 36  >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 35 ”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×