Skip to content
Part 36 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Sallama suka yi da Majida da nufin zai koma Kano, ita sai an yi sadakar uku ne za su koma tare da su Ammi. Da damuwar da baya so a fuskarta shimfiɗe lokacin da zai tafi, wannan karon a vibration da ringing duka ya saka wayarshi ko da zata kira shi in bai ji ringing ɗin ba zai ji vibrating ɗin wayar. Da dukkan zuciyarshi yake son ya riƙe yaran shi a hannun shi, ya ji ɗumin su a ƙirjin shi, wata irin kewar su yake ta ban mamaki. 

Komai na jikin shi faɗa mishi yake ya yi ƙauyen Kinkiba, amma zuciyarshi na faɗa mishi yayi Zaria. Wannan faɗan ba zai iya shi kaɗai ba, baisan ta inda zai fara ba, zai ta zuwa har sai Wadata ya gaji ko ya haƙura ya yafe mishi su je Kinkiba tare, ko kuma ya gaji da nacin shi ya raka shi don ya ƙyale shi ya huta, yanzun kam babu yadda Wadata zai yi da shi, dukan shi ba zai kore shi ba wannan karon. Da wani irin ƙarfin zuciya ya tunkari Zaria. Yayi niyyar ya tsaya hotel ya kama ɗaki sai ya fasa, zai iya yin wannan kowanne lokaci tunda garin ba baƙonshi ba ne ba. Yana da kwanaki biyu ne rak yayi duk abinda zai yi kafin Majida ta koma Kano. 

Gidan Wadata ya ƙarasa har ciki da motarshi yana samun waje yayi packing ɗinta tukunna ya fito, numfashi ya ja mai ƙarfi yana fitar da shi da wani irin sauti, bugun zuciyarshi na ƙaruwa da duk takun da zaiyi zuwa cikin gidan. Kwanƙwasawa ya yi saboda baisan ko har yanzun zai iya shiga gidan kai tsaye kamar da ba, tunanin hakan na sa zuciyar shi matsewa da yadda yai kewar su Wadatan ba kaɗan ba. Ganin shiru ba ai magana ba yasa shi murɗa ƙofar yana turawa, komai na cikin falon ya canza daga yadda yasan shi, banda hotunan da ke jikin bangwayen ɗakin. 

Sai dai wannan karon ya ƙaru ne da na yaran Wadatan. Sosai yake kallon hotunan kafin ya shiga cikin falon tare da yin sallama, yayi mamakin yadda muryarshi ta fito lafiya ƙalau don jikinshi gaba ɗaya a sanyaye yake jinshi, sallama ya sake yi, yana jin aka amsa daga can cikin gidan, kafin Fatima matar Wadata ta fito, fuskarta ta fara nuna mamakin ganin Altaaf ɗin. 

“Matar Yaya…”

Ya kira yana jin kewarta har ƙasan zuciyarshi, girgiza mishi kai take yi fuskarta ɗauke da wani yanayi. 

“Idon ka kenan Altaaf?”

Ta tambaya muryarta na karyewa

“Matar Yaya…”

Altaaf ya sake kira wannan karon muryarshi ɗauke da ban haƙuri. 

“In ya maka laifi ni me na yi? Wannan tsakanin kune, duka saika haɗa mu ka hukunta.” 

Fatima ta ce don Wadata yasa har ranta tana ƙaunar Altaaf ɗin kamar ɗan uwanta, tun kafin aurenta da Wadata sukai wata irin shaƙuwa da ta ƙaru bayan auren, lokaci ɗaya zai ɓace daga rayuwarsu babu wani bayani. Kai yake girgiza mata 

“Ni na yi laifin, ba shi ba ne ba, ni ne Matar Yaya, ban iya ba da haƙuri ba ne ba, bansan ta inda zan fara ba, ina fatan ban yi latti ba yanzun… Din Allah ku yi haƙuri, ki yi haƙuri…bansan ya zan faɗa ba, ki yi haƙuri da dukkan zuciyata.” 

Altaaf ya ƙarasa maganar muryarshi can ƙasa saboda karyewar da ta yi, ya bar mutanen da basu nuna mishi komai ba sai ƙauna, saboda yana tsoron laifin shi zai sa su guje shi, sai ya fara gudunsu da kanshi, yana ganin hakan zai mishi sauƙin ɗauka, duk idan yai kewarsu zai faɗa ma kanshi shi ya barsu basu suka barshi ba, sai yanzun ne yake fara ganin kuskuren shi. Ľifta idanuwa Fatima take tana ƙoƙarin mayar da hawayen da suka tarar mata a idanuwa, sannan ta ce, 

“Ka zauna…”

Zaman yayi kuwa yana jin yadda ƙafafunshi sukai sanyi, da bai zaunan ba, gab suke da kasa ɗaukar nauyin shi, ciki Fatima ta koma ta ɗan jima kafin ta sake fitowa da plates har guda biyu tana janyo teburin tsakiyar falon ta ajiye a gabanshi, soyayyen dankali ne da wainar ƙwai a guda daya, ɗayan kuma farfesun kayan ciki sai ƙamshi suke yi. Tunda ta shirya yara da safe ta kaisu makaranta ta dawo tana kitchen, tana gama haɗa musu kayan kari ta soma gyara kifin da Wadata ya kawo tunda dare ya ce ta yi komai amma da kifi, bata son ƙarnin shi, shi yasa take aikin shi da wuri don ta gama ta wanke duk abinda ta ɓata. 

Wadata na hutun ƙarshen shekara, sai ya kai goma na safe ma bai tashi ba wani lokacin, in ba yana jin rikicin shi ba ne, ta ma fi son yai baccin don inya tashi fitinarta yake ya hanata ayyukanta, sai ta yi ranar girki don ba zai zauna shi kaɗai a falon ba, in kitchen ɗin ya biyota ma damunta zai yi. Tana ajiye ma Altaaf ta sake komawa kitchen ta fito da jug na glass da kofi, zoɓo ne ta zubo don bata manta Altaaf bai damu da shayi ba. Shi kanshi sai da yai murmushi ganin bata manta ba duk shekarun nan. 

“Ki yi haƙuri…”

Ya sake faɗi yana jin rashin kyautawarshi, ɗan jim Fatima ta yi tana ɗan ɗaga mishi kai, zata yi karya in ta ce bata yi fushi da shi ba, amma riƙe shi bai da wani amfani, abu mai muhimmanci shi ne ya dawo ya kuma gane kuskuren da yayi da dukkan alamu. 

“Ka ci abinci, na san yanzun zai tashi. Bari in ƙarasa aiki a kitchen.” 

Ta faɗi tana wucewa. Numfashi Altaaf ya sauke, dama ruwan shayi ne kawai a cikin shi, shi ma don Majida ta damu da kar ya fita bai ci komai ba, abincin ya fara ci da yai mishi daɗi, duk da akwai ɗanɗanon da girkin Majida yake da shi da yakan ji banbancin shi a abincin duk da zai ci da ba nata ba ne ba. Sai da ya ji ya ƙoshi har cikin wuyanshi tukunna yai hamdala yana gyara zaman shi cikin kujerar sosai. Idanuwan shi ya lumshe, bacci mai ƙarfi na ɗaukar shi, don ya kwana biyu bai samu wadataccen bacci ba. 

***** 

Daga kitchen ɗakin su ta wuce, Wadata ya fito wanka yana shiryawa. 

“Zo ki balle mon maɓalli…”

Ya ce don wandon jeans ne a jikinshi sai riga mai dogon hannu. 

“Da ban shigo ba fa?”

Fatima ta tambaya. 

“Kin shigo ai…”

Ya faɗi yana kallon ta a kasalance, takawa ta yi tana kai hannunta ta soma ɓalle mishi maɓallan rigar, da yake ita ma doguwa ce sosai, da kaɗan ya fita tsayi. Ta kai na wuyan shi ne ta ce, 

“Dee…”

Kamar yadda take kiran shi. 

“Umm…”

Ya amsa

“Altaaf yazo…”

Lumshe idanuwa Wadata yayi yana buɗe su da sauke wani siririn numfashi, ya ɗauka ba zai zo ba, bai ma fara saka ma zuciyarshi cewar Altaaf ɗin zai dawo ba shi yasa bai faɗa mata ya zo bama. 

“Ya zo jiya…”

Ware idanuwanta Fatima ta yi. 

“Baka faɗa min ba.”

Ɗan ɗaga kafaɗunshi ya yi. 

“Na kore shi ne, ban ɗauka zai dawo ba.”

“Dee mana…”

Fatima ta faɗi cike da roƙon shi, hannuwan ta ya kama yana saukewa daga wuyanshi. 

“Yunwa nake ji ni…”

“Yanzun na ɗora, bacci na koma nima.”

Cewar Fatima, tana saka Wadata ware mata idanuwanshi gaba ɗaya. 

“A’a kam, wallahi mu fita, yunwar da nake ji ba zata iya jira ba. 

“Na zuba dankali cikin mai ne za mu fita? Ya zanyi da shi? Ka bari kaskon farko in juye maka.” 

Kai yake girgiza mata, hanjin shi na ƙullewa waje ɗaya, kasa jure dariyarta ta yi, daga shi har yaran basu da haƙurin yunwa. Ganin tana dariya yasa shi damko hannunta yana faɗin, 

“Na zama abokin wasanki ko?”

Kai take girgiza mishi tana dariya har lokacin tare da ƙoƙarin ƙwace hannunta, hakan na saka shi ƙara riƙeta dam, cikin shi ne ya sake murɗawa da yunwa, don ita ta tashe shi daga bacci. 

“Ki ban abinci kafin yunwa ta kashe ni Tee.”

Yai maganar yana takawa ya haɗe space ɗin da ke tsakanin su tare da matseta a jikin shi. 

“In baka sake ni ba ya zan yi in baka abincin?”

Ta ce tana ƙoƙarin zame jikinta daga nashi, sakinta yayi suna takawa tare zuwa falon, Altaaf ya gani yana bacci a zaune hankalin shi a kwance, ƙarasawa Wadata yayi yana ɗirka ma Altaaf ɗin dukan da yasa Fatima faɗin, 

“Baka san ƙashinka ɗaya ba ko? Za ka karya shi.” 

Altaaf kuwa buɗe idanuwan shi yayi yana shagwaɓe fuska ganin Wadata tsaye a kanshi 

“Bacci nake ji fa… Don Allah ka ƙyale ni.”

Ya ƙarasa yana gyara zamanshi tare da mayar da idanuwanshi ya lumshe. Harbin ƙafarshi Wadata yayi da tashi ƙafar. 

“A nan za kai baccin? Tashi…”

Kamar Altaaf zai yi kuka ya buɗe idanuwa. 

“Cin zali ba kyau. Matar Yaya ki ce ya barni tunda ba ɗakin shi ba ne…” 

Murmushi Fatima ta yi, sosai tayi kewar su biyun a tare, tana kuma kallon yadda ko menene ya faru tsakaninsu Wadatan ya yafe mishi, shi kanshi Altaaf ɗin yana jin kamar an ɗauke mishi wani ƙaton dutse daga zuciyar shi, in har Wadata na takura mishi haka da alamun ya soma yafe mishi ne, in yana fushi da shi zai yi kamar baya wajen ma ne gaba ɗaya. 

“Ka tashi ka koma dakin Babba…”

Girgiza kai Altaaf yayi

“Bacci na yana gudu. Ka barni ni kam.”

“Allah ba za kai bacci a zaune ba, gara ka tashi.” 

Miƙewa Altaaf yayi. 

“Kaine mutum na farko a baƙin littafina.”

Ɗaga kafaɗu Wadata yayi tare da nuna ma Altaaf hanya da hannun shi. 

“Bai dame ni ba, ka wuce, ɗakin farko in ka shiga lungun can…” 

Wucewar Altaaf yayi yana jin kamar ya raba damuwarshi da Wadata, bacci yake ji sosai da sanin Wadata na cikin rayuwar shi yanzun, zai yi baccin da ya rasa kwana biyun nan. Ɗakin Babba ya shiga, yana mamakin yadda ɗakin yake kamar ba na yara ba, babu kayan wasa, babu duk wani abu da zai nuna maka ɗakin yara ne banda keken yaron, sai jakunkunan makaranta da takalman shi, sai kujeru na yara guda wajen shida, shi ne kawai, kan gadon ya kwanta yana lumshe idanuwan shi, wani baccin na sake ɗauke shi. 

Abuja

Kamar tashin bomb haka ya ji saukar maganganun Omeed, idanuwan shi ya lumshe yana buɗe su da jin yadda wani abu ya tarwatse a tare da shi, Daddy ne kusa da shi, don haka fuskar shi ya fara kallo yana neman ƙaryatar kalaman da Omeed ɗin yayi amma ya rasa. Don haka ya juya yana kallon Nuri, banda tashin hankali babu abinda yake gani a fuskarta. 

“Yayaa…”

Fawzan ya kira shi yana jin muryarshi ɗauke da yanayin da ya ƙarasa karya mishi zuciya gaba ɗaya. Wannan ne abinda kowa yake ɓoye mishi, abinda Muneeb ya ce gara ya haƙura da bincike akai don shi ne zaman lafiyar shi. 

‘Oh babu wanda ya faɗa maka? Ka kashe matarka da ‘yarka?’ 

Maganar Omeed ta dawo mishi tana kashe mishi gwiwoyi, faɗuwa ya zo yi da sauri Daddy ya riƙe shi yana zaunar da shi kan kujera tare da faɗin,

“Rafiq…Fawzan miƙo ruwa.”

Ƙasa Rafiq yake kallo kamar yana son fahimtar wani abu a tattare da kafet ɗin da ke ɗakin da bai taɓa gani ba, zufa yake ji a fuskarshi don haka yasa hannuwanshi yana goge fuskar. Ruwan Fawzan ya ɗauko yana miƙa ma Daddy, su dukan su Rafiq suke kallo, Aroob kuwa kuka take tunda Omeed ya fara magana, shi yasa ta so sa’adda Rafiq ya tashi su faɗa mishi da kansu, a wajen su ya kamata ya ji mutuwar Samee ba wajen wasu ba, ba a bakin Omeed ba da kalamai masu matuƙar muni. 

Yawo tunanin shi yake iya inda zai iya ya kasa tuna lokacin da yai aure ma ballantana mata har da yarinya. Baisan dariya ta kubce mishi ba sai da ya ji sautin ta cikin kunnuwanshi da wani irin yanayi marar daɗi. 

“Yayaa…”

Fawzan ya sake kira muryarshi cike da damuwa, ɗagowa Rafiq yayi yana kallon Fawzan ɗin. Ruwa Daddy ya miƙa mishi yana kasa cewa komai, kai Rafiq ya girgiza ba tare da ya kalli Daddy ba, baya so, ba ruwa yake so ba, wani a cikinsu yake so ya fara magana, ya gaya mishi ƙarya Omeed yake yi, abinda ya faɗa bai faru ba, don in ba taɓin hankalin yake kamar yadda Omeed ya dangantashi da shi ba baisan ya zai yi aure har da yarinya ya kashe su kuma ya kasa tuna yayi hakan ba. 

Fuskokin su yake kallo ɗaya bayan ɗaya, Nuri ma ta ƙi yarda su haɗa ido balle yayi tunanin zata ce wani abu, Aroob na jikinta tana wani irin kuka, Daddy ma tashin hankali ne a fuskarshi, balle Fawzan da yake fitar da numfashi kamar Asthma ɗinshi na shirin tashi. Dariya Rafiq ya sake yi. 

“Da gaske haukan nake…”

Ya faɗi cikin wata irin murya da ya kasa yarda tashi ce. 

“Rafiq…”

Daddy ya kira, ya manta ranar ƙarshe da ya kasance cikin yanayi irin haka, zai iya cewa tun ranar hatsarin motar Rafiq ɗin, tsoro bai cika samun wajen zama a tare da shi ba, amma Omeed na buɗe bakin shi da kalaman da ya furta ya ji cikin shi ya ƙulle waje ɗaya, zuciyarshi ta fara dokawa, Rafiq yake kallo yana jin wani irin tsoro na shigarshi da halin da ɗan nashi zai shiga. 

“Da gaske ne Daddy? Na kashe matata da ‘yata? Na taɓa aure dama?” 

Rafiq ya tambaya, bugun zuciyar shi na ragewa da duk mintin da zai wuce, yawo tunanin shi yake, baya jiran tabbacin Daddy, da gaske ne ya taɓa aure shi yasa yasan abinda ya sani akan Tasneem. Baisan lokacin da dariya ta sake suɓuce mishi ba, sautinta na saka su Nuri gaba ɗaya kallon shi. Ya za’a yi ya kasa tuna yana da mata, yana da yarinya, ya za’a yi su ɓace daga tunanin shi gaba ɗaya? In ko shi ya kashe su, to girman laifin da yai yasa ya zaɓi ɓatar da su daga tunanin shi, domin babu yadda za’a yi ya manta su. Ya akai ko hoton su bai taɓa gani ba, bai taɓa tunawa da su ba. Yaushe ne ma yai auren? 

“Yaushe nai aure? Ya akai na kasa tuna komai?” 

Yake tambaya yana kallon su Fawzan. 

“Yayaa…”

Fawzan ya kira don kalmar da take iya fitowa daga bakin shi kenan 

“Shi yasa bana iya tuƙi? Na san akwai dalilin da yasa bana iya tuƙi, saboda ina tuna lokuta da dama da nake fita da mota….” 

Rafiq ya ce yana sa hannuwa biyu ya dafe kanshi da yake juya mishi, filin da yake ji cikin kanshi na fara cikewa, ruwan da ke hannun Daddy ya miƙa hannu ya karɓa, yana buɗewa, sosai ya sha ruwan, don maƙoshin shi gaba ɗaya ya bushe, ajiyewa ya yi yana kallon su, an rasa wanda zai mishi magana. 

“Nuri…”

Kauda kai ta yi gefe ɗaya,

“Aroob…”

Rafiq ya kira, kafin ya rufe bakin shi ma ta miƙe tana barin wajen da gudu, binta yai da kallo har ta hau benen. Numfashi Rafiq ya sauke yana jin komai ya hargitse mishi. Kusa da shi Daddy ya zauna 

“Rafiq…”

Ya kira a hankali, kai kawai Rafiq ya girgiza mishi, in dai ba zai mishi bayanin wani abu da ya danganci gaskiyar maganganun Omeed ba gara yayi shiru. 

“Ba kai ka kashe su ba…”

Hannu Rafiq yakai yana dafe ƙirjin shi, kokawa yake da numfashin shi da maganar da Daddy ya faɗa, ba shi ya kashe su ba, yana nufin akwai su ɗin kenan, yana nufin sun rasu, yana ƙara tabbatar mishi yana da mata da yarinya duk sun rasu, lumshe idanuwanshi ya yi yana kiran sunan Allah duk wanda ya zo mishi, amma ya kasa tuna komai, wani irin tashin hankali yake ji marar misaltuwa. Ya za’a yi ya manta su? 

“Kayi aure shekara biyu da suka wuce, kana da yarinya guda ɗaya….” 

Daddy ya soma faɗa, maganganun na maƙale mishi da yadda ƙirjin shi yai nauyi. 

“Sunana ka saka mata, kuna kiranta da Imaan…” 

Nuri tai maganar muryarta na rawa saboda kukan da take ƙoƙarin tarbewa. Fawzan ne ya kalli Rafiq ɗin da yanayin da ke fuskarshi, ga dukkan alamu so yake ya tuna Imaan, amma ya kasa. Yana tuno Imaan lokuta da dama, duk in zai ga yara a asibiti sai fuskarta ta faɗo mishi, sosai yarinyar ta shiga ranshi, yasan hakan na da alaƙa da cewar ta fito daga jikin Rafiq ne, ko yanzun tunaninta ya bayyana murmushi a fuskarshi. 

“Tana kama da kai sosai, tana kuma kama da Anty Samira…banma san yadda akai take kama da ku biyun a lokaci ɗaya ba…” 

“Samee…”

Rafiq ya faɗi mafarkin da yai na dawo mishi, amma babu fuskar, fuskarta ta ɓace daga cikin kanshi gaba ɗaya. Kallon shi suke jin ya kira Samee, suna tsammanin ya tuna wani abu, hakan ya kula da shi ya girgiza musu kai yana roƙon su da idanuwan shi da su taimaka mishi. 

“Na kasa tuna su, me yasa na kasa tuna su?”

Rafiq ya tambaya muryar shi can kasa kamar me yin rada. 

“Hatsari kuka yi Rafiq shi yasa, ba kai ka kashe su ba, ba ma kai kake tuƙin ba…” 

Daddy ya faɗa yana tabbatar da sun haɗa idanuwa da Rafiq. Numfashin da Rafiq baisan yana riƙe da shi ba ya saki, bashi ya kashe su ba, duk da bai tuna su ba, hakan ba ƙaramin rage mishi nauyin da yake ji yayi ba. 

“Tashi mu je…”

Fawzan ya ce yana sa su Daddy na kallon shi cike da alamun tambaya. Don haka ya ce. 

“Gidan shi zan kai shi…”

Kai Nuri take girgiza ma Fawzan. 

“Nuri me ya rage? In ba so kike wani ya nuna mishi hotunan su a titi ba…” 

“Fawzan…”

Rafiq ya kira cike da kashedi, yanayin da yake ciki bai hana shi duba na Nuri ba, yasan tana son kare shi ne kamar ko da yaushe. Kamar Fawzan bai ji kashedin da Rafiq ɗin yai mishi ba ya ci gaba da magana. 

“In ba za ki bari in kai shi ba, ke ki kaishi to…” 

Numfashi Nuri take ja tana fitarwa a hankali, inda tana da iko da ta karɓar ma Rafiq duka damuwar da yake ciki yanzun da wadda tasan zai shiga, tana jin yana kallon ta, yana son zuwa ta sani, amma in bata ce ta yarda ba Rafiq ba zai je ba, shi yasa babu kamarshi a duka yaranta, yana saka farin cikinta akan nashi ko wanne lokaci. 

“Ku je.”

Bata ma rufe bakinta ba Rafiq ɗin ya miƙe, gaba Fawzan ya yi yana binshi a baya suka fice daga gidan. Daddy Nuri ta kalla, hannu ya miƙa mata, yaran ne suka hana ya riƙeta dama, da sauri ta taso daga inda take tana kama hannun shi, kusa dashi ya zaunar da ita yana riƙeta a jikin shi, sai lokacin kukan ta ya ƙwace. Kuka take sosai. 

“Ya za mu yi?”

Ta tambaya, da wani nisantaccen yanayi a muryar Daddy ya ce, 

“Ki kula dasu kamar yadda kika saba…”

“Kaifa?”

Ta buƙata. 

“Zan tashi hankalin gaba ɗaya jinin Modibbo…” 

Hannun shi da ke cikin nata ta dumtse, tana yarda da abinda ya faɗa, tana kuma bashi goyon baya. Babu wanda zai taɓa mata yara ya tafi haka kawai. Gyara zamanta ta yi tana kwantar da kanta a kafaɗar Daddy. Su dukan su da tunanin da suke yi. 

***** 

Tunda suka fita kan Rafiq yake jingine a gaban motar, bai ɗago ba sai da yaji Fawzan ya tsayar da motar. Shi ya fara fita ya zagaya ya buɗe ma Rafiq ɓangaren da yake zaune ya fito shi ma. Ba don ya tuna rayuwa a cikin gidan ba, amma bugun zuciyarshi ƙara gudu yake yana sauko da ƙafafuwan shi cikin gidan. Tsayawa yai sai da Fawzan ya fara yin gaba tukunna yake binshi a baya. Har suka ƙarasa ƙofar gidan. Yana kallo Fawzan yana duba mukullan da ke hannun shi kafin ya samu na gidan ya saka a jikin ƙofar. 

“Yana wajena tun bayan hatsarin… Na ajiye ne kawai.” 

Fawzan ya faɗi saboda shirun ya mishi yawa, zuciyarshi bugawa kawai take, musamman yadda yake ganin fuskar Rafiq kamar takarda saboda farin da ta yi, babu alamar jini a jikinta. Baisan me kuma zai yi ba in ya shiga cikin gidan. Yana buɗewa ya ɗauka zai samu ƙura, sai ya ga ko ina tsaf-tsaf, yasan aikin Nuri ne, ba zai taɓa wuce ita ta sa ake gyara gidan haka ba. Wani irin dokawa zuciyar Fawzan ta sake yi, zai rantse yana jin dariyar Samira a cikin gidan, yana ganin giccinta tana hidimarta kamar komai bai faru ba, babu abinda ya canza a ɗakin. 

Juyawa Fawzan yayi ya hango Rafiq tsaye a bakin ƙofar, ƙafafuwanshi yake jin sun mishi nauyi na gaske. Ya kasa motsa su, ji yake kamar ya juya ya ruga, amma yana son ganin su ko zai tuna su, tsoron tuna sun yake yi, in yanzun yana jin abinda yake ji, baisan halin da zai shiga idan ya tuna su ba. Kallon shi kawai Fawzan yake yana bashi dukkan lokacin da yake buƙata. 

“Ko mu juya ba yau ba Yaya?”

Fawzan ya ce cike da kulawa, kai Rafiq ya girgiza mishi yana ɗaga ƙafarshi da ƙyar ya taka cikin ɗakin, idanuwan shi ya fara saukewa akan hoton Samira jikinta sanye da farin lafaya, kyawunta na samun waje yai mishi tsaye a zuciya, kafin ya yawata da idanuwan shi yana sauke su kan wani hoton, lafaya ne a jikinta a hoton ma, ammanm ita dashi ne a tsaye, ya miƙa mata hannu yana murmushi, ita kuma ta ɗan sunkuyar da kanta tana dariya. Hannun shi ya murza da ɗayan kamar zai ji nata a ciki, ko zai tuna sa’adda hakan ya faru. 

Hotunan su ne wajen kala bakwai, juyawa Rafiq yayi, zuciyarshi gaba ɗaya ya ji kamar tana sauka ƙasa da ya sauke idanuwanshi kan hotunan Imaan, Fawzan baiyi ƙarya ba, yarinyar na da kyau sosai, kawai ta yi kama da mamanta ne fiye da shi, ba kamar yadda Fawzan ɗin ya faɗa ba, a hankali yake takawa yana ƙarasawa, hannu yasa ya ciro hoton yana sauke shi ƙasa, haka yaita ƙarasawa duk inda hoton Imaan yake a ɗakin sai da ya ciro ya ajiye a kasa, tukunna ya tsugunna kan gwiwoyin shi, hannu yasa yana shafa fuskar Imaan.

“Yayaa…”

Fawzan ya kira. 

“Ya zan manta su? Ya zan mantata? Fawzan ya zan manta yarinyar nan? Saboda me?” 

Rafiq ɗin yake tambaya yana sake shafa fuskar Imaan, yana jin wani irin kusanci da yarinyar na ban mamaki. 

“A ina na haɗu da mamanta?”

Yai tambayar ba tare da ya ɗago ba, wani irin numfashi Fawzan yake ja a wahalce, sam bazai iya saka kanshi a yanayin da Rafiq yake ciki ba, dole zai ji kamar taɓin hankali ya same shi, ya zaka manta wanda kai kusan gaba ɗaya rayuwarka a tare da shi? Baya so ya misalta ya hakan yake ma, don yanzun abin yake ƙara tsorata shi, ba ƙaramar Rahma bace Allah yake maka in ya barka da memories ɗin mukusantanka da ka rasa, tare da zafin rashin su akwai murmushi na tuni da rayuwar da ka samu tare da su. Amma babu wannan a tare da Rafiq. 

“Ka santa tun yarintar ka, tare duka muka taso…’Yar abokin Daddy ce.” 

Sai lokacin Rafiq ya ɗago yana ware ma Fawzan idanuwan shi. 

“Family ɗinta fa? Samee… Suna ina yanzun?” 

“Suna nan Abuja su ma.”

Kai Rafiq yake girgizawa yana jin da gaske taɓin hankalin yake tare da shi. 

“Na taɓa zuwa?”

Wannan karon Fawzan ne ya girgiza mishi kai. 

“Duk wani abu daya dangance ta ka manta, memories ɗin sun maka girma ne shi yasa ƙwaƙwalwar ka ta zaɓi ta shafe su…” 

Numfashi Rafiq yaja me sauti

“Me yasa? Nace ina so in manta ne? Me yasa ba za tai shawara da ni kafin ta min wannan abin ba? Sun bani ‘yarsu na aura, ta rasu ban ma tuna ba ballantana in taya su raba rashin ta…” 

Idanuwan shi Fawzan ya ji sun cika da hawaye. 

“Yaya…”

Miƙewa Rafiq yayi, yana tattara hotunan Imaan yana son ɗaukarsu duka, sai dai sun mishi nauyi, ajiyewa yayi yana taka ƙafafuwanshi cikin gidan, ɗakin farko da ya samu ya buɗe, ɗakin bacci ne da yai mishi kyau, shiga yayi ciki sosai yana fara dube-dube, wata ƙofar ya gani ya buɗe yana shiga, wajen sake kaya ne, shiga yayi, ba don ya tuna sa’adda ya siyi kayan da ke wajen ba, sai dai yasan zaɓin shi ne, daga ɗayan ɓangaren kayan Samira ya gani ya sa hannu yana taɓa su. Kafin ya ga wata riga da yasan ta Imaan ce, ɗaukota yayi yana kaiwa jikin fuskarshi tare da lumshe idanuwan shi. 

“Na san kuna wani waje ɓoye a zuciyata, don Allah ku fito…. ku taimaka min in tuna ku ko zan ji sauƙi…” 

Yau ya ƙara sanin akwai rahma a tare da zubar hawaye. Da zai iya zama yayi kuka kamar ƙaramin yaro da zuciyar shi ta rage nauyin da yake jin ta mishi, rigar ya riƙo a hannun shi ya fito, hoton Samira ita kaɗai ya ciro daga bango yana ƙarasawa ya ɗauki na Imaan guda ɗaya tukunna ya fice daga gidan, bai ko juya ba da ya ji Fawzan na kiran shi. Gurin mota ya ƙarasa, ya buɗe bayan motar ya saka hotunan tukunna ya shiga yana zama tare da ɗaukarsu ya ɗora kan cinya ya jingina frame ɗin da kujerar motar. Kallon su yake ko zai tuna su, amma ya kasa, yana jin wani irin kusanci tare da su amma hakan bai sa ya tuna su ba. 

Yana jin Fawzan ya buɗe gaban motar ya shigo. 

“Ka maida ni gidaba…”

Rafiq ya ce mishi, baya son ganin su dukan su na wani lokaci, suna son kare shi ne ya fahimta, amma shekara biyu yai yawa, ƙila da sun faɗa mishi da wuri da su Imaan basu yi nisa a zuciyarshi ba, da ya iya tuna su ko yaya ne. Yana jin sautin muryar Fawzan da alama magana yake mishi, amma ba fahimta yake ba, ya kaishi gida kawai, ya jima yana jin sautin muryar Fawzan ɗin, kafin daga baya ya haƙura yai shiru, gidan kuwa ya kaishi. Suna ƙarasawa ko gama parking bai bari yayi ba ya buɗe murfin motar, fitowa yayi yana ɗaukar hotunan ya tallabe su a ƙirjin shi tukunna ya wuce ba tare da ya juya ya kalli Fawzan ɗin ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 35 Alkalamin Kaddara 37  >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×