Skip to content
Part 4 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Tuna Baya (Rayuwar Tasneem Muftahu Tafida)

Kasancewar Tasneem ta tsinci kanta da tasowa cikin gidan da Hausawa kan kira na yawa. Don a tasowarta kafun rayuwa ta tafi da su kan rubutun alƙalamin ƙaddarar da ya rarraba su wurare da dama, gidaje huɗu ne cikin gidansu har da nasu da ta tashi a cikin shi, ƙofa ɗaya za ka shigo kafin ka samu ƙofofin da za su shigar da kai sauran gidajen.

Hakan yasa ta fahimci akwai abinda yake ba dai-dai ba a nasu gidan. Da duk ranar da zata wuce da ƙarin hankalin da ke shigarta da kuma yadda take gane banbancin gidansu da na sauran mutane, musamman mahaifiyarta Bara’atu da suke kira da Ummi.

Ba zata manta ranar juma’ar farko da zuciyarta ta fara sanin asalin damuwa ba, lokacin tana aji huɗu Sakandire, duk da a shekarun zamanta da Ummi ta san menene ɓacin rai. Ta fito daga ɗaki Abban su na tsugunne yana Alwala zai fita masallacin juma’a.

“Abba lokaci har ya yi?”

Tasneem ta buƙata don ganin ranar bata kai ta ƙarfe ɗaya haske ba.

“A’a da saura, ina so dai inje ne in gabatar da addu’o’ina kafin lokacin ya cika…”

Murmushi ta yi.

“Allah ya karɓa m…”

Bata ƙarasa ba saboda muryar Ummi da ta katse ta.

“Ashe masallaci za ka tafi, kasan dai ba mu da abin da za mu ci a gidan nan ko?”

Numfashi Abba ya sauke yana kallon Tasneem da faɗin,

“Tasneem dame-dame ake yi da fulawa?”

“Abubuwa da yawa Abba, ka siyo mana ne?”

Kai ya girgiza mata.

“Bani aka yi tun jiya…”

“Kayya Abba, bamu sani ba ai, da na yi mana wainar fulawa na ga akwai manja, su Azrah na so.”

“Uban ki ne ya siya min manjan?”

Ummi da ke tsaye ta tambaya tana watsa ma Tasneem harara, da sauri ta matsa gefe don ta san halin Ummi, zata iya kai mata hannu daga hararar. Miƙewa Abba ya yi yana laluba aljihun ‘yar sharar shi, Naira talatin ya lalubo, ya duba na wandon shi ya ɗauko wata Naira hamsin da ta ji duniya ya haɗa su waje ɗaya ya miƙa ma Tasneem.

“Kuɗin da ke jikina kenan Tasneem.”

Hannu Tasneem ta sa ta ɗauki Naira hamsin.

“Wannan ma ya isa Abba.”

Tafa hannuwa Ummi ta shiga yi.

“Oh ni Bara’atu…”

Abba bai bi ta kanta ba ya mayar da talatin ɗin a aljihu ya sa kai zai fita. Da sauri Ummi ta riƙo mishi riga tana janyo shi, hakan yasa rigar yin wata ƙara ta yage daga wajen Aljihun zuwa bayan ƙugun shi.

“Ina kake nufin za ka je? Ga mahaukaciya ko?”

Runtsa idanuwanshi yayi yana jero,

“Inalillahi wa ina ilaihi raji’un…”

Don Allah ya bashi haƙurin jure abinda Ummi take ko don Tasneem da take tsaye.

“Inalillahi ta me kake yi? Sai an soma magana ka nuna ma kowa kai na Allah ne…me zan yi da wata fulawa? Yaushe rabon da mu ɗora wani abin kirki a gidan nan?”

Wani abu ne mai ɗaci Tasneem ta ji ya taso daga zuciyarta yana tsaya mata a maƙoshin ta. Idanuwanta cike taf da hawaye ta ce,

“Haba Ummi? Haba Ummi?”

A hasale Ummi ta juya tana ma Tasneem wani mugun kallo.

“Ki rufe min baki, baƙin hali irin na Ubanki ko? Banda ruwan koko meye a cikin ku tun safe? Ke bai dame ki ba ko? Kina tausayin uban da baya tausayin ki…”

Ɗaki Tasneem ta shige hawayen da take tarbewa suna samun zubowa. Hannu Abba yasa yana ɓanɓare na Ummi daga jikin rigarshi tare da wucewa ɗakin su. Wasu kayan ya ɗauka ya sake. Har ya fito tana tsaye tana tijara.

Bai ce uffan ba ya ɗauki buta ya sake zuba ruwa ya sake wata alwalar ya fita. Ɗakin su Tasneem ɗin Ummi ta bita, jin shigowar Ummin ne yasa ta saurin goge hawayen da ke fuskarta.

“Munafuka, kukan me kike?”

Shiru ta yi bata ce komai ba, don ta san maganar na iya ja mata duka indai Ummi ce. Sabeena da ke kwance tana bacci ta buɗe idanuwanta, kan Ummi ta fara sauke su tukunna ta juyar da kanta tana kallon Tasneem.

“Yaya yunwa nake ji.”

Sabeena ta faɗi.

“Kina cin wainar fulawa?”

Da sauri Sabeena ta miƙe tana murza idanuwanta.
“Za ki yi mana?”

Kai Tasneem ta ɗaga mata. Hakan yasa ta miƙewa tana ɗaukar Hijabinta kan ƙyauren ɗakin. Dai-dai shigowar Hamna da Azrah da sallamarsu.

“Ya kuka dawo da wuri haka?”

Ummi ta tambaya tana kallon su. Turo baki Azrah ta yi.

“Ba kowa gidan sai Anty.”

“To duk ina yaran suka je?”

Shiru su Hamnah suka yi.                                     

“Me ta baku to?”

Ummi ta sake tambaya.

“Babu abinda ta bamu.”

Azrah ta sake faɗi, magana ba damun Hamnah ta yi ba, don wucewa ta yi tana samun waje ta zauna.
“Matsiyaciya… Asabe ta ko yi shegiyar rowa.”
Girgiza kai Tasneem ta yi. Ta yaya ba zata koyi rowa ba, kowace dama Ummi zata samu sai ta aika su Azrah gidan ta sa su zauna ko za su samo wani abu. Halin son abin duniya irin na Ummi kan bata mamaki. Ta san tun tasowar su Abban su ba mai hali bane, sai dai mutum ne mai wadatar zuci.

Sana’ar gini ne aikin shi, ba zata manta lokutan da suke yara ba, abinci har da nama akan dafa musu akai-akai, har shayi suna sha da safe, don Abban su mutum ne da in yana da shi baya ma iyalin shi ƙwauro, sosai samun aiki yake mishi wuya yanzun. Ga jikin manyanta kuma.

Don ance sun jima shi da Ummi kafin Allah ya basu kyautar yara, kuma sai da suka jera su mata su duka. Ita Tasneem ɗin, Azrah, Hamna, sai autarsu Sabeena don shekararta bakwai yanzun. Rayuwa ta soma musu wahala ne sosai tun bayan haihuwar Sabeena.

Tun da can Tasneem ta san Ummin su mace ce mai faɗa da tsegumi, don ko me Abba zai kawo sai ta yi mita akai da nuna rainuwarta. Musamman lokacin da sauran matan ‘yan uwanshi na gidan. Don duk ranar da ta shiga ta ga sun sabunta daga rayuwar da ta san su ciki sai ta zo ta sauke wa Abba tashin hankali.

Danginta har sun gaji da halin rashin godiyarta, don ko yaushe tana cikin bin gidajen su da kai ƙorafin kasawar Abba akan su. Yanzun haka Asaben da take magana ƙanwar mamansu ce, ita ma ba wani halin suke da shi ba, sai dai wadatar zuci.

Hijabinta Tasneem ta mayar tana ce ma Azrah,

“Zo ki siyo mana manja da farin magi shagon Mudi.”

Murmushi Azrah tayi har haƙoranta suka fito, ko dariya take haka take yinta da duka fuskarta.

“Me zaki dafa mana? Daman yunwa muke ji fa, ko Hamnah?”

Kai kawai Hannah ta ɗaga mata, karɓar hamsin ɗin Hamnah ta yi tana ficewa. Ummi ta taɓe baki ta fice daga ɗakin da faɗin,

“Gara in tafi inda zan ci mai daɗi…Sai ku yi ta fama kukam.”

Babu wanda ya ce mata komai, su kansu su Hamnah sun fahimci shiru shi ne mafi alkhairi a lamurran Ummi. Hamnah bata wani jima ba ta dawo. Nan da nan Tasneem ta kwaɓa fulawar ta haɗa komai, albasa ta gani a kitchen har wajen biyar, ganin ta bi albasar da kallo yasa Hamna faɗin,

“Karki taɓa ma Ummi kayanta, ina da Naira Ashirin da Abba ya bamu kuɗin makaranta, a ƙafa muka je muka dawo.”

Ware idanuwa Tasneem ta yi.

“Hamnah da kun hawo mota wajen dawowa akwai rana yau fa.”

“Ni na ce mu dawo a ƙasa Ya Tasneem, mu da yawa fa muka taho, har da su Zahra.”

Jinjina kai kawai Tasneem ta yi zuciyarta na mata nauyi. Ɗaki Hamnah ta je ta ɗauko kuɗin ta wuce ta siyo musu albasa. Haka suka yi ta maneji da manjan Tasneem ta soya musu wainar fulawar. Addu’a take Abba ya dawo daga masallaci kafin ta ƙarasa.

Tun da babu yaji in ta yi sanyi ba zata mishi daɗin ci ba, kar ta saka mishi a kular Ummi ta ja mishi wata tijarar inta dawo ta gani. Aikam tana gab da gamawa ya yi sallama.

Da gudu Sabeena ta tashi tana tarbarshi.

“Beena karki shafa mai manja a kaya mana…. Abba sannu da zuwa.”

Cewar Hamnah.

“Sannun ku Hamnah…. Me aka samu haka?”

Abba ya faɗi yana riƙo hannun Sabeena suka ƙaraso tare, matsa mishi suka yi kan tabarma ya zauna a ƙofar kitchen ɗin da suka shimfiɗa tabarma.

“Sannu da zuwa”

Tasneem ta faɗi ta samun plate ta zuba mishi a ciki, ta fito ta ajiye mishi.

“Azrah ɗibo ma Abba ruwa, ki ɗauraye kofin.”

“Yaya ruwan ya yi ƙasa sosai fa… Tunda na gama bari in ɗibo ko bokiti biyu.”

Girgiza kai Tasneem ta yi.

“A’a Azrah bana so kina ɗaukar bokitin nan wallahi. Zo ki ƙarasa soya min in je da kaina.”

Mikewa Abba ya yi da faɗin,

“Na ga yara na ta ɗibar ruwa a fanfon ƙofar gidan Malam Musa kuwa. Ki zauna ki ƙarasa aikin ki bari in ɗibo.”

Sosai Tasneem ke girgiza kanta wannan karon.

“Abba don Allah ka zauna ka ci wani abu, ko karyawa baka yi ba fa….zan je in ɗibo.”

Jim ya yi, ya kalli wainar fulawar kafin ya kalli Tasneem don sosai yunwa ke cin shi, tun ranar jiya rabon shi da abinci, har jiri-jiri yake ji da yana hanyar dawowa daga masallaci.

“Ku harta ishe ku ne? Na ga an zuba min da yawa.”

Murmushi Tasneem tayi

“Wallahi kuwa Abba… Akwai saura ma in za ka ƙara, fulawar da yawa ashe… Bari in ɗibo ruwan in zo dai…. Ka zauna ka ci don Allah Abba kar ya huce.”

Tasneem ke faɗi tana nufar hanyar ƙofa da ɗaukar farin bokitin fentin, ɗauraye shi ta yi ta dawo ta ɗauki hijab tukunna ta fice. Sawu biyar ta yi ta cika ko ina tukunna ta dawo tana maida numfashi.

“Sannu.”

Sai da ta janyo kujerar da Azrah ta gama soya wainar fulawar akai ta zauna tukunna ta ce,

“Yawwa Azrah… Kai ana rana yau.”

Abba kam ya cinye wainar fulawar da Tasneem ta zuba mishi tas, ya zauna shiru, da alama ya yi nisa cikin tunanin da yake.

“Abba a ƙara maka ne?”

Ta tambayeshi, ɗago kanshi ya yi tare da girgizawa.

“Alhamdulillah, ban san na ƙoshi ba ma sai da na sha ruwa, cikina har wuya nake jinshi. Na gode Tasneem, Allah ya yi muku albarka.”

Su duka suka amsa da,

“Amin…”

“Ina Umminku?”

“Ta fita.”

“Ta fita?”

Ya maimaita da alamar bai san da fitar tata ba. Shiru Tasneem ta yi don bata san me zata ce mishi ba. Shi ma jinjina kai yayi da faɗin,

“Allah ya kyauta. Tasneem ba kya ganin giccin su Tariq ko?”

Sunan su Tariq ɗin da Abba ya kira ya saka zuciyarta jagulewa da wani irin yanayi mai haɗe da kewarsu da damuwar halin da suke ciki. Maƙoshinta ta ji ya bushe, ga hawaye na son cika mata ido, ji ta yi ba zata iya magana ba don haka ta girgiza wa Abba kai.

“Oh Allah… Allah ka kare yaran nan duk inda suka shiga.”

Abba ya faɗi a fili, a zuciyarshi yana ƙara tsorata da rayuwa, musamman yanzun da nashi yaran suke zagaye da shi, su kaɗai yake gani ya samu sauƙi, wata shida cikakku bai ji daɗin zama da Bara’atu ba, tun a farkon auren su har izuwa yanzun. Inda ya biye zuciya da rabon yaran ma ba zai gifta ba.

Ya kuma san duk da ba wani ƙarfi gare shi ba, kasancewar shi da su sauƙi ne a fanni da yawa na rayuwar su. Sai dai mutuwa bata sanarwa. Sai dai addu’ar shi Allah ya bashi tsawon rayuwa har sai sun yi girman da za su tsaya da ƙafafuwan su.

Ganin in ya zauna tunani zai haye mishi yasa shi miƙewa yana tattara takalmanshi da har tsakiyarsu ya kusan hujewa saboda jin jiki tare da faɗin,

“Ni na fita Tasneem…”

Addu’ar tsari da dawowa lafiya suka yi mishi. Tasneem na miƙewa ta zauna inda ya tashi.

“Azrah kin yi Sallah kuwa?”

“Yaya kefa kika sa mukayi kafin ki fara soya wainar fulawa. Kin manta?”

“Au…”

Dariya Azrah ta yi, Hamnah sarkin son jiki har ta matsa tana kwanciya a jikin Tasneem ɗin da ta ke kallon kan Sabeena 

“Beena kanki ya kwana biyu. Azrah ɗauki min abin taje kai da kibiya. Kuma anjima ku kwance naku kan in muku kitso, kunga gobe in Allah ya kaimu akwai Islamiyya…”

Miƙewa Azrah ta yi ta shiga ɗaki ta ɗauko mata. Ita ta kwance wa Sabeena, Azrah ta soma kwance nata. Ganin Hamnah na bacci yasa ta ƙyaleta ta yi wa Sabeena, itama ko rabi ba a yi ba tai bacci, don haka tana ƙarasawa ta kwantar da ita.

Kasancewar Azrah akwai son kitso ƙanana, sai da Tasneem ta sa ta matso don ta tayata kwancewa. Suna yi suna hira abinsu.

*

Har bayan Magriba Ummi bata dawo ba. Sauran wainar fulawar da suka rage da rana ta ba Hamnah da Sabeena suka ci. Ita da Azrah suka zauna suna Tilawar Qur’an.

Karatun su shi ya fara dukan kunnen Abba tun daga soron gidan. Musamman muryar Tasneem ɗin ma. Wani irin sanyi ya ji da nutsuwa ta saukar mishi. Ya fi mintina biyar a bakin ƙofar, baya son yin sallama ya katse musu karatun, kafin ya shigo, Hamnah ta amsa mishi sallamar, kafin su kai aya.

“Ma shaa Allah, anata karatu ne Tasneem.”

“Wallahi kuwa Abba, ina taya Azrah ne…sannu da dawowa.”

“Yawwa… Ummin ku bata dawo ba har yanzun ko?”

“Eh wallahi.”

Duk da yasan fitar Ummin bai wuce bin gidajen ‘yan uwa zubda mutunci da ta saba ba bai hana hakan ɓata mishi rai ba. Ta wani fannin kuma ya ji daɗin dawowarshi bata nan. Don sai su yi shawarar su da Tasneem hankali kwance.

“Ɗari biyar na samo Tasneem, ban san ko za a iya yin wani abu da ita ba, ko za ku siyo abinci ne gidan Mariya?”

Girgiza kai Tasneem ta yi.

“Siyan abincin nan bai da albarka Abba, sai ka ga bai ishemu ba. Tunda muna da fulawa, bari in je da ita sai ta auni rabi, mu bata Naira hamsin zata bamu taliya yar kaɗi. A siyo manja da yaji sai mu ci dukkan mu.”

Ɗari biyar ɗin Abba ya bata, ta kuwa ɗauki Hijab da fulawar, nan da nan ta je ta amso ta dawo. Abban da kanshi ya fita ya siyo manja da barkono da farin magi. Cikin mintina talatin sun dafa taliyar su. Tasneem bata zuba musu ba sai da suka yi sallar Isha’i.

Sauran kuɗin ma ita ya ba ta ajiye a hannunta a yi wani abun da safe. Suna zaune suna hirar su Ummi ta yi Sallama. Hatta Azrah sai da gabanta ya faɗi. Cikin ɗar-ɗar suka amsa mata. Hannunta da baƙaƙen ledoji, waje ta samu ta ajiye su ta cire hijabinta ta rataye kan igiya.

“Da wuta kenan.”

Ta faɗi, babu wanda ya ce mata kanzil.

“Sai da ka fita na tuna yau Alhaji Sani yake dawowa daga Cotonou. In faɗa maka zan je in mishi sannu da zuwa.”

“Kin je ai ko?”

Abba ya faɗi yana binta da kallo. Murmushi ta yi da daga shi har su Tasneem kan jima ba su gani a fuskarta ba.

“Wallahi kuwa, na je a sa’a na samo abin arziƙi.”

Miƙewa Abba ya yi ba tare da ya ce komai ba ya fice daga gidan. Tasneem ma miƙewa ta yi ta ɗauki Sabeena da ke bacci ta kaita ɗaki ta kwantar kan katifarsu ta sakar mata gidan sauro. Ledojin Ummi ta janyo gabanta tana buɗewa ta ɗauko lemon zaƙi.

“Azrah ɗauko min wuƙa in yanka mana.”

Miƙewa Azrah ta yi ta ɗauko wuƙar ta ba wa Ummi tana nufar hanyar ɗaki.

“Ina zaki kuma? Zo ki karɓi naki mana.”

“Na ƙoshi.”

Azrah ta faɗi tana shigewa ɗaki abinta. Hamnah Ummi ta kalla, suna haɗa ido ta ɓata fuska tana girgiza wa Ummi kai tare da bin bayan Azrah. Cikin sanyin murya Ummi ta ce,

“Tasneem ga Lemon zaƙi.”

“Na ƙoshi Ummi, mun ci abinci.”

“Me kuka ci?”

Kallonta Tasneem ta yi fuskarta ɗauke da yanayi mai nauyi kafin ta ce,

“Taliya da manja.”

“Abban ku ya samo kuɗi ne?”

Kai kawai Tasneem ta ɗaga mata da faɗin,

“Sai da safe.”

Bata jira amsarta ba ta shige ɗaki ita ma. Lemon Ummi ta ci gaba da yankawa haka kawai ta ji ranta baya mata daɗi. Musamman da ta juyo dariyarsu, da alamun hira suke ba bacci ba. Shan lemon take ba don tana gane zaƙin shi kan harshenta ba. Guda uku ta sha ta miƙe ta ɗaura alwala don bata yi sallar Isha’i ba.

Sauran kayan ta kwasa zuwa kitchen, har da kayan miya ta ajiye, ta koma nasu ɗakin. Bata sa ran shigowar Abba ba, don ta riga da ta saba sai ta yi bacci yake shigowa gidan.

*****

Kasancewar safiyar ranar Asabar ce yasa suna tashi wanka suka fara yi. Tasneem ta yi wa Sabeena. Sosai take kewar Islamiyya, tunda suka yi sauka, Tahfiz ɗinsu sai dubu ɗaya kuɗin Term ga littatafan su da tsada, ta san Abba bai da halin yin hakan shi yasa bata ko yi mishi maganar ba.

Cikin kuɗin da ke hannunta ta fita da kanta ta siyo sabulun wanki, don da shi suke wanka su yi wanki ta ga ya kusan ƙarewa. Ta siyo sukari na Ashirin da ƙosai na Hamsin ta dawo. Koko ta haɗa musu. Ta sa su a gaba suka sha.

Sai da Azrah ta matsa mata tukunna ta ɗauki ƙosai ɗaya. Ta fi son ta ga sun ci, akwai sauran taliyar jiya ita take son dafawa ta ishe su ita da Abba. Tana tunanin abinda za su ci ne da rana kawai.

Har lokacin Ummi bacci take. Kasancewar har da Sabeena za’a je yasa Tasneem saka Hijabinta ta raka su tunda sai an tsallaka titi. Malan Musa ta gani, cikin ladabi ta gaishe da shi.

“Tasneem kin ƙi dawowa makaranta ko?”

Kanta a ƙasa ta ce,

“Kullum haka kike cewa za ki dawo, amma har yanzun shiru, kin sa shiririta ko?”

“Zan dawo Malam.”

Shiru ta yi din bata san yadda zata ce mishi ba.  Sosai tana son ta koma makaranta ita ma. Cikin sanyin murya ta ce,

“Sai anjima Malam. Azrah don Allah ku kula wajen tsallaka titi, ki riƙe Sabeena sosai.”

Ta faɗa musu tana juyawa. Sai lokacin da ta koma gida sannan Ummi ta tashi, alwala take, da kanta ta ƙwanƙwasa musu ƙofa da Asuba. Don gajiya na damun Abba, da yawan lokuta ita take tashin shi Asuba. Hatta Sabeena lokacin take tashin ta ta yi Sallah, tun tana mata kuka har ta saba yanzun.

Wani lokacin kafin ta tashe su sun farka, sai dai su koma bayan sun Idar.

“Ina kwana.”

Ta gaishe da Ummi ɗin

“Lafiya… Ina kika je ke kuma tunda sassafe?”

“Takwas fa ta wuce, su Azrah na raka Islamiyya.”

Taɓe baki Ummi ta yi.

“Don gulma? Su Azrah ɗin za ki raka Islamiyya, kin dai so gantali kawai.”

Maganganun Ummi sun sosa mata rai, ko ta yi mata bayani ba fahimta zata yi ba, don haka ma bata ɓata bakinta ba. Hijabi ta je ɗaki ta ajiye ta fito tana gyara kurfot ɗin gawayi tare da zuba ɗan sauran da ya rage.

“Me za ki yi?”

“Taliya zan dafa.”

Ta amsa tana ɗaukar mafici da fifita gawayin dan ya kama sosai.

“Kinga ga cefane nan, har da soyayyen nama, ki yi min miya ki juye min a kula, sai ki ta shirmen da za ki yi.”

Ummin bata jira amsarta ba ta shige ɗaki, taliyar Tasneem ta fara ɗorawa don garwashin ya kama. Ko da ta gyara cefanen ma, jajjagawa ta yi a turmi don batason ta je tambayar Ummi kuɗin markaɗe ta sauke mata buhun masifa.

A kitchen ɗin ta ci tata taliyar ta ajiye wa Abba tashi. Har Maggi akwai, bata fito daga kitchen ɗin ba sai da ta gama miyar, dai-dai fitowar Ummi daga wanka.

“Ummi na gama.”

Kitchen ɗin ta ƙarasa ta shiga, ta ɗauki wani kwano da kular miyar ta zuba ta ƙirga nama yanka takwas ta saka a ciki ta ba Tasneem ɗin.

“Gashi nan kowa bibbiyu. Ga biredi nan ku ɗauki ɗaya ki miƙo min ɗayan.”

Miƙa matan ta yi, tana ƙirga naman da idanuwanta. Buɗe baki ta yi zata yi magana Ummi ta katse ta da faɗin,

“Ban yi niyya ba mai Uba, ya nemo ya kawo min ne?”

Maida bakinta Tasneem ta yi ta rufe tana ɗaukar kwanon miyar da biredin ta wuce ɗaki, lokacin da take yi har miyanta ke tsinkewa da ganin naman, amma sam yanzun ya fice mata a rai. Har miyar ji take ba zata iya ci ba. Da biredin ta rufe don bata jin zata iya sake fita kitchen ɗauko murfi.

*****

Daga Sallar Asuba, a masallaci ya zauna yana gyangyaɗi har gari ya soma sha, tun jiya ya wuce ta wajen layin birji ya ga an kawo motar bulo, saukewar da suka yi ne ma yasa ya samu ɗari biyar ɗin da ya kawo gida. Ya roƙe su ko da ɗibar ruwa ne su bashi ya samu ɗan wani abu shi ma.

Shugaban maginan wajen ya ce ya zo, don da alama ya tausayawa ma yanayin Abban, don haka gari na wayewa ya nufi wajen, aikam har sun fito, da alama shaguna ne za’a zuba a wajen. Don fili ne babba, sai kuma wasu gidajen ƙasa da aka soma rugujewa duk za’a shigar ciki.

Abban aka ce ya fara aikin ruguje gidajen kafin wasu su zo su kama mishi.

“Indai ba akai ga ɗauko su ba, zan yi ni kaɗai ma.”

Kallon shi shugaban maginan ya yi,

“Anya kuwa Malam, aikin da yawa fa…”

Ɗan murmushi Abba ya yi.

“In sha Allah zan iya, in na gaza sai a ɗauko wani.”

Jinjina kai ya yi kawai. Kayan aiki Abba ya ɗauka ya fara. Yadda yake ganin katangun a idanuwanshi ya raina su da, sai da ya fara aikin ya ga suna da ƙwari, ko ya hannuwanshi suka gaji, in su Tasneem suka gifta mishi ta cikin idanuwanshi sai ya ji ya sake samun ƙarfin ci gaba da aikin.

Har sha biyu yana abu ɗaya, ga rana ta soma takewa, ya haɗa zufa yai sharkaf, jikinshi ya yi futu-futu da jar ƙasa. Ga ƙishi da ya addabe shi. Wani waje ya zabtro, ƙura ta cika mishi hanci da ido, bai lura da katangar dake rawa gabanshi ba sai da lokaci ya ƙure.

Ya matsa amma wani ƙaton bulo ya faɗo mishi a ƙafa, runtsa idanuwanshi ya yi don azaba, yana tsugunnuwa ya ɗaga da sauri, a wajen ya zauna yana kallon wata farar tsoka da ta fito kafin jini ya soma ambaliya, abinka da wanda ya sha rana.

Ƙafar ya ja yana fitowa daga wajen, ruwa ya hango cikin tanki wanda ake aiki da shi, da hanzari ya nufi wajen, bai ma damu da yadda ƙasa take kwance a ciki ba, ɗiba ya yi ya fara sha tukunna ya zuba yana ƙoƙarin tsaida jinin da ke zuba a ƙafar tashi, amma sam abin ya faskara.

“SubhanAllah. Malam ciwo ka ji haka?”

Shugaban maginan ya faɗi yana miƙa wa Abba baƙar ledar da ke hannunshi da ruwa. Karɓa ya yi cike da dauriya ya ce,

“Abu ne ya faɗo, ban kula da wuri ba. Amma zan ci gaba da aikin a haka.”

Girgiza kai ya yi.

“Don Allah ka je gida ka huta… Ka je kemis a duba ƙafar kuma. Gobe in Allah ya kaimu sai ka shigo. Akwai yaro ɗaya da zai kama mana ginin, an mishi rasuwa bazai samu zuwa ba. Sai ka maye gurbin shi, ai ka ce kana sana’ar dama ko?”

Jinjina kai Abba ya yi cike da farin ciki.

“Sosai kuwa. Na gode ƙwarai. Allah ya dafa maka yadda ka duba min.”

“Amin…”

Ya faɗi yana saka hannu a Aljihunshi, dubu biyu ya ƙirga ‘yan ɗari bibbiyu ya miƙa wa Abba, duk da aikin da ya yi bai kai hakan ba. Sosai Abba ya yi mishi godiya. Sai da ya ɗan wawwanke jikinshi tukunna ya ɗingisa zuwa gida. Da ledar abincin a hannu.

Da sallamar shi mai ƙwari ya shiga, Tasneem ta amsa mishi tana fitowa daga ɗaki, kallo ɗaya ta yi wa ƙurar da ke jikinshi zuwa ƙafarshi ta ware idanuwanta cikin tashin hankali, idanuwanta na cika da hawaye. Da sauri ta ƙarasa inda yake.

“Na shiga uku… Abba jini… Jini a ƙafarka… Innalillahi… Garin ya ka ji ciwo?”

Tasneem take tambaya a rikice, kujera ta ja wa Abba ya zauna, ta kama ƙafar tana hurawa da bakinta, ta ma rasa me ya kamata ta yi. Murmushi Abba ya yi.

“Tasneem ba wani ciwo ba ne babba, jinin ne kawai.”

“Haba Abba… Garin ya ka ji ciwon nan?”

Janye Kjafarshi ya yi.

“Ke kam ki bar ciwon nan, ɗauko mana kwano mu ci abinci…”

Ranta a jagule ta ce,

“Ni bana jin yunwa… Abba mu je chemist a duba ƙafar nan… Akwai sauran kuɗi ɗari da goma a hannuna.”

“Raba ni da kemis ɗin nan kin ji.”

“Abba…”

Tasneem ta kira muryarta na rawa. Ya san hankalinta ba zai kwanta ba. Hijab ta ɗauko, jan ƙofar gidan kawai ta yi, hakan na nuna mishi alamun Ummin su ta sake fita, ya manta rabon da ta tambaye shi zata je unguwa.

‘Allah ka shirya Bara’atu ko don yaranta. Na yafe mata Allah ka yafe mata.’

Yake faɗi a cikin zuciyarshi, kemis ɗin Emma suka je, don duk in ba su da lafiya nan suke zuwa, kasancewar shi Inyamuri kuma kirista bai hanashi zama mai kirki da tausayi ba. Ko da Abba bai da kuɗi yakan basu bashin magunguna in Abba ya samu a hankali ya biya shi.

Duba ƙafar Abban ya yi, yai mishi dressing ɗinta, bai karɓi ko sisi ba ma, sai maganin da suka siya ɗari da hamsin. Suka dawo gida, faranti ta ɗauko ta zuba mishi abincin, shinkafa da miya ce, ɗaki ta shiga ta ɗauko naman da Ummi ta basu ta zuba wa Abba nata yankan naman guda biyu ta mayar da sauran.

“Ina kuka samo nama?”

“Ummi ce ta kawo.”

Bai sake cewa komai ba ya ɗauki abincin ya ci. Ruwan ɗumi Tasneem ta ɗora ta sirka ta kai mishi ya yi wanka. Har ya shirya zai sake fita, kuɗin aikin da ya samo duka ya ɗauko su, dubu ɗaya ya ware gefe, ya ɗauki sauran da ya taɓa aka siya magani a ciki ya miƙa wa Tasneem.

“Ki riƙe a hannunki kar ki bari Ummin ku ta gani…”

Tana shiga ɗakinsu ta ɓoye kuɗin ta fito Ummi na shigowa da Sallama. Abba ne ya amsa mata, binshi ta yi da kallo tana tsayar da idanuwanta kan ƙafarshi.

“Kai kuma ina ka je ka ji ciwo?”

Bai amsata ba don ya san ba damuwa ta yi ba. Dubu ɗayan dake hannunshi ya miƙa mata, ta karɓa fuskarta ba yabo ba fallasa ta ƙirga. Kallon shi ta yi a sheƙe.

“Me zan siya da dubu ɗaya? Duk ciwon da ka ji dubu ɗaya ka samo?”

Numfashi ya sauke.

“Ki siyi duk abinda dubu ɗaya zata siya.”

“Kamar me?”

“Nima ban sani ba.”

Ya amsa yana wucewa zai fita.

“Kar fa ka sa ran dawowa ka ga abinci don bansan abinda zan yi da dubu ɗaya ba wallahi, kuma sabuluna ya ƙare ga man shafawa zan siya.”

“Yadda duk kika ga ya kamata ki yi.”

Abba ya faɗi yana sa kai ya fita. Innalillahi yake ta jerawa don ita kaɗai ce tsakanin shi da hawan jini ko ciwon zuciyar da ya san Bara’atu zata iya saka mishi. Ya bata kuɗin ne don akwai haƙƙinta da Allah ya ɗora a kan shi. Ba don haka ba zai ba Tasneem duka kuɗin ne, don ya san ba tausayi Bara’atu ta cika ba, don ta bar su da yunwa ba matsalarta bane ba.

Bayan Sati Huɗu

Haɗuwar Abba da Alhaji Zanna sai ta zame mishi alkhairi, don sosai ya kula Abba ya iya aiki, sannan shi ba mutum bane mai ha’inci. Don yau kwana huɗu kenan da ya ɗauki Abban zuwa Gusau. Za su yi aikin ginin wani kamfani.

‘Yan kuɗin da ya samu ne ya bar wa Ummi dubu biyar. Ya ba Tasneem dubu biyu ta riƙe a hannunta suna hidimar makaranta. Sai dai Tasneem bata zaton kuɗin da Abba ya bar wa Ummi sun kwana. Don kaji ta siyo har biyu. Da kanta ta yi miya ta dafa musu shinkafa. Aka yi cin dare ɗaya.

Ba don kuɗin da Abba ya bar wa Tasneem ba, da yunwa ta galaɓaitar da su ba kaɗan ba. Dabara ta yi ta siyo fulawa ta ɗari biyar ta kai aka kaɗa musu taliya ta zo ta ajiye don suna da yaji da manja. Yanzun haka da ta tashi safiyar naira hamsin ta rage a hannunta.

Su Azrah ta ba su yi kuɗin makaranta, ta shirya ita ma ta fito Ummi ta ce ba zata je ba.

“Ni fita zan yi gaskiya, ki zauna da Sabeena.”

Idanuwan Tasneem taf da hawaye ta ce,

“Ummi mun fara jarabawa fa jiya, kuma ta canjen aji ce.”

“Sai meyene matsalata da jarabawarki?”

Ɗaki Tasneem ta koma ta cire uniform ɗinta ta ninke su. Ɗacin da take ji a maƙoshinta ya ma hana hawaye su zubo mata. Kwanciya ta yi a gefen Sabeena. Tana jin Ummi ta fice daga gidan, karatun su ko rashin shi bai taɓa damunta ba. Abba ne dai yana matuƙar ɗaukar karatun su da muhimmanci.

So take Allah ya dawo da shi lafiya. Indai yana da wadata a ɗinka wa Sabeena Uniform, tunda hutun ƙarshen zango ne, in an koma ita ma a sakata. Don da yawan lokuta sai dai ta haƙura da zuwa makaranta ta zauna da Sabeena a gida.

Bacci ne ya ɗauke ta ita ma , su dukkan su ba su tashi ba sai wajen goma. Babu abinda zata yi, ta riga da ta gama gyaran ko’ina na gidan tunda sassafe. ‘Yar Radio ɗin da take ji don rage kewa ta lalace tun tuni. Ta kai a duba aka ce ɗari uku ta dawo ta ajiyeta.

Ɗari uku kuɗi ne masu daraja a wajenta, za su ci abinci da su. Ba zata yi amfani da shi ta gyara Radio ba. Tana ɗaki ta ji kamar sallama ake, saurarawa ta yi sosai ta ji sallama ce da gaske. Amsawa ta yi tana fitowa. Gaba ɗaya fuskarta ta canza da murmushin da ta yi.
Don tun daga zuciyarta ya fito.

“Ya Tariq.”

Ta faɗi. Shi ma murmushin ya yi mata, yanayin rayuwa yasa ya yi wani irin duhu, hasken nan babu shi, ga wata irin ramewa da ya yi, sai dai ya ƙara tsayi na ban mamaki.

“Tasneem.”

Dariya ta yi cike da farin ciki.

“Ya Tariq.”

Ta sake maimaita sunanshi har lokacin ta kasa yarda shi ɗin ne a gabanta.

“Na ɗauka ma kina makaranta.”

Girgiza kai ta yi.

“Ban je ba fa… Ummi ta fita sai na zauna da Beena.”

Jinjina mata kai ya yi.

“Oh… Ko kujera ban baka ba.”

Ta ƙarasa maganar tana janyo kujera ta miƙa mishi. Kitchen ta shiga ta ɗauko kofi ta ɗauraye ta kawo mishi ruwa. Kaɗan ya sha ya ajiye.

“Oh Allah Ya Tariq…”

Murmushi ya yi.

“Kinata magana kamar kina mamakin zuwana.”

“Sosai wallahi… Ai ban kawo a raina bane fa….Ya Faq ma baya zuwa kwata-kwata, kai ma ɗin yaushe rabo. Abba yana ta tambayarku.”

“Allah sarki Abba… Mun gaisa ai, kafin in tafi.”

“Ya je Gusau aiki… Yaushe za ka tafi?”

Ɗan jim ya yi kamar yana tunani, kafin ya ce,

“Ƙilan zuwa jibi in sha Allah. Yaushe zai dawo?”

Ɗan ɗaga kafaɗa Tasneem ta yi.

“Nima ban sani ba, ya ce dai ba za su shige sati biyu ba. Ko kwana bakwai ba su yi ba kuma…”

Gyara zamanshi Tariq ya yi.

“Allah ya dawo da shi lafiya”

“Amin dai… Don Allah me yasa ba za ku dawo gida ba? Me yasa kuka tafi?”

Yanayin da ya mamaye cikin idanuwa da fuskar Tariq ɗin da tambayarta yasa ta dana sanin yinta. Ta sani, saboda Arfa ne, me yakaita sake tambayarshi ma. Muryarshi can ƙasan maƙoshi ya ce,

“Me yasa ba za mu tafi ba Tasneem? Me ya rage?”

Jinjina kai ta yi, zuciyarta na mata nauyi.

“Rayuwa akwai wahala ko?”

“Sosai…. Fiye da zaton ki.”

Fuskar shi take nazari na ɗan lokaci kafin ta ce,

“Kun bar mu da kewa.”

Ɗan murmushi ya yi mai sauti da ke cike da fassara kala-kala, tana son ta fahimci kaɗan daga cikin nufin haka, na cewar bai da kalaman da zai ganar da ita abinda yake ji.

“Ina Ya Faq?”

“Wajen aiki.”

Ya amsata a taƙaice.

“Allah ya taimaka… Gidan ya yi ƙura ko?”

Girgiza kai ya yi.

“Ba sosai ba. Tsintsiya ma na zo ara wajen Ummi.”

Miƙewa Tasneem ta yi tana shiga ɗaki ta ga Sabeena bacci ta koma. Taɓa jikinta ta yi ko bata da lafiya ne, ta ji ƙalau take. Gyara mata kwanciya ta yi tana ɗaukar tsintsiya da ruwa a bokiti.

“Mu je in tayaka a share gidan.”

“Beena fa?”

“Bacci take… Sai in dinga dawowa ina dubata ko da zata tashi.”

Bokitin ya karɓa, aikam tare suka share ko’ina na gidan tas, lokuta irin yau in Ummi bata nan, takan shiga ta share gidan. Don kasancewa ciki kawai yana saka tata damuwar ta ragu. Don duk halin da take jin tana ciki, ganin gidan kawai kan sa ta jin ba komai bane ba.

Bokitin ta ɗauka da tsintsiya Tariq ya ce mata,

“Ina zuwa?”

‘Yar jakarshi da ke ajiye ya buɗe, Radio ƙarama ya ciro a kwali ya miƙa mata, kafin ta gama mamaki ya miƙo mata kwalin batiri ƙanana sai tocila.

“Ya Tariq…”

Ta soma ya katse ta da faɗin,

“Don Allah karki ce za ki min godiya Tasneem.”

“Ka san godiya dole ne.”

Ta faɗi muryarta ɗauke da yanayin da take ji. Bai manta ba, zuwan da ya yi na ƙarshe ta je gyaran Radio ɗinta ne. Fitilar ma haka, don ya shigo mata sallama da daddare cewar da sassafe zai wuce ya same su cikin duhu, Ummi ma bata nan.

“Nidai bana so… Babu godiya a tsakanin mu ai.”

Duk da haka sai da ta ce,

“Nagode sosai. Allah ya saka da alkhairi ya bar zumunci.”

“Ki je kar Beena ta tashi.”

Murmushi ta yi tana wucewa. Ranta wasai, zuwan Tariq a ko da yaushe na kawo mata sauƙi. Ko yaya ne sai ya bar mata abinda zata ƙara jin kewarshi duk idan ya tafi kafin ya dawo. Tana shiga gida ɗaki ta nufa ta fara adana batirin ɗin.

Ta buɗe rediyon, da battery a ciki. rungumeta ta yi a ƙirjinta tare da yin dariya. Ta san sosai an wuceta a shirye shiryen duk da take bi, amma samun rediyon zai rage mata kaɗaici, su Azrah ma za su ji daɗi, don tare suke ji da daddare, tunda ba kayan kallo suke da shi ba.

Kunnawa ta yi kuwa, ta koma gefen Sabeena ta kwanta.

“Allah ya kawo muku sauƙi kamar yadda kake kawo min da duk zuwanka Ya Tariq.”

Ta tsinci kanta da faɗi. Ko da Sabeena ta tashi zamansu suka yi a ɗaki. Bata fito ba sai da ta ji kiran Sallah. Sannan ta san su Azrah na gab da dawowa. Don haka ta dafa musu taliyarsu ‘yar kullum. Zubawa ta yi a kwanon silver ta rufe ta ba Sabeena ta kai ma Tariq.

Dawowa ta yi da ledoji har biyu a hannunta, ɗayan kuma a dumtse ta miƙa ma Tasneem duka biyun.

“Wai a kawo miki.”
Karbar ledojin tayi ta ajiye sai kuɗi a duƙunqune, buɗewa ta yi, dubu biyu ne. Ɗan dafe kai ta yi tana rasa abinda take ji.  Jakar makarantarta ta janyo ta saka kuɗin a ciki. Sannan ta buɗe ledojin, awara ce sai dankalin Hausa soyayye.

Dariya Tasneem ta yi, kafin kewar lokutan da ita da Tariq ɗin kan je siyan dankalin da awara su danne ta. Ɗiba ta yi suka ci ita da Sabeena ta ajiye ma su Azrah nasu suma.

****

Da La’asar sakaliya Ummi ta shigo gidan, da buhunnan bakko har uku ta ajiye, Tasneem kawai ta samu a gidan da rediyonta tana ji. Ta amsa sannun da Tasneem ta yi mata. Kallo ɗaya tai mata ita da rediyon da take ji ta ɗauke kanta ta shiga ɗaki ta fito da tabarma.

Shimfiɗawa ta yi ta shiga zazzage kayyakin da ke cikin buhunnan da faɗin,

“Su Azrah su zo, kwana biyun nan kafin Abban ku ya dawo su zagaya min da gwanjon nan.”

Ba shiri Tasneem ta miƙe tana kashe rediyon.

“Gwanjo kuma Ummi?”

“Eh gwanjo na saro, na gaji da zama haka nan. Gara kafin ɗan baƙin cikin Abban ku ya dawo su zagaya min da shi. Kema da za ki ɗauka ai ba daga nan ba”

Cike da tashin hankali Tasneem ta ce,

“Wai talla Ummi?”

Kafeta Ummi ta yi da idanuwa.

“Eh talla. Akwai wani abu ne a ciki?”

“Abba fa ya hana maganar tallar nan tun tuni.”

Tasneem ta faɗi muryarta can ƙasa, don ranar da Ummi ta ɗora wa Azrah tallar gyaɗa ne ranar farko da zata ce ta ga ɓacin ran Abba. Marin Ummi ne kawai bai yi ba, duk faɗanta shiru ta yi don ita kanta ta tsorata. Bata kuma sake gwadawa ba sai yanzun da baya nan.

“Uban me Abban naku yake tsinana min? Eye? Na ce uban me yake tsinana min da zan haife ku ya ce ba zan mora ba? Ku duka kun fi son shi a kaina. Ba za mu taru mu rufa wa juna asiri ba? Har da ke Tasneem? Kina zaton in auren ki ya tashi Abban naku zai iya tsinana wani abin kirki ne?”

In akwa abinda ya fi ɓata wa Tasneem rai bai wuce ta ji Ummi na wa Abba irin wannan tozarcin ba. Zuciyarta har zafi-zafi take mata saboda ƙunar da take.

“Ni dai Ummi don Allah kiyi haƙuri ki bar maganar tallar nan…”

A hasale Ummi ta ce,

“Sai in yi me da kayan? In zauna ina kallon su? To wallahi bada ni za ai wannan asarar ba. Ko ke ki ɗauka ki zagaya min da su ko su Azrah su ɗauka.”

Tashi Tasneem ta yi ta shiga ɗaki. Idanuwanta cike taf da hawaye har dishi-dishi take gani, ta buɗe jakarta ta lalubo dubu biyun da Tariq ya bata ta fito. Miƙa wa Ummi ta yi.

“Meye wannan din?”

Ummi ta tambaya a fusace, ware kuɗin Tasneem ta yi, ganin dubu har biyu yasa Ummi saurin kawo hannu ta karɓa, faɗan da take na juyewa da fara’a.

“‘Yar albarka…”

“Don Allah ki bar maganar tallar nan.”

Murmushin Ummi ya faɗaɗa.

“Da muna haka ai da ba aji kanmu ba. Ɗan zancen nan Tasneem kin biye ma Abbanku ba kya fita. Ke ba kya ganin su Dije yadda samari ke musu hidima.”
Juyawa Tasneem ta yi, bata son Ummi ta ga hawayen da suka samu damar zubo mata. Ta ɗauka Ummi zata tsareta da tambaya akan inda ta samu kuɗin ne, sai ta ga bata damu ba sam. Asalima ta fi damuwa da yadda zata samo wasu. Rediyonta ta ɗauka ta shige ɗaki.

Kuka marar sauti har ta ƙware akanshi. Tana jin Ummi na hidimarta a tsakar gida. Kafin ta jiwo muryarta da faɗin,

“Kin fanshi su Azrah. Ni bari in fita in zagaya da kaina kafin Magriba ta yi.”

Dafe kanta Tasneem ta yi da hannuwanta duka biyun tana girgiza shi. Neman dalilin da yasa Ummi take daban da sauran iyaye mata take yi ta kasa samu. Kuka take sosai har idanuwanta sun kumbura, ta ji Sallamar Tariq. Da sauri ta goge fuska tana ƙaƙaro murmushi ta ɗora a fuskarta ta fito.

Kallo ɗaya ya yi wa fuskarta ya ce,

“Waya saki kuka?”

Girgiza mishi kai ta yi tana kasa magana.

“Tasneem…”

Yadda ya kira sunanta na sa zuciyarta sake yin rauni. Kuka ta fashe da shi wannan karon mai sauti. Tsaye Tariq ya yi yana kallonta, har sai da ta yi mai isarta, da kanta ta wuce ta ɗauki buta ta wanke fuskarta ta dawo ta zauna ƙofar ɗaki.

Kujera ya ja ya zauna yana kallonta da ke fassara ta ɗauki duk lokacin da take buƙata zai jira ta nutsu ta faɗa mishi me ke damunta.

“Ummi… Na gaji da matsalar Ummi Ya Tariq.”

Sauke numfashi ya yi.

“Me ta yi?”

“Hmm…”

Kawai Tasneem ta furta, don bata san ta inda zata fara ba. Meye ma Ummi bata yi ba. Juya kujerar Tariq ya yi ya fuskance ta.

“Ɗazun ki ke tambayata tabbaci kan wahalar rayuwa Tasneem. Komai ba zai dawwama a haka ba… Komai zai yi sauƙi in kika jure… Akwai wahala….amma ki yi haƙuri zai wuce kinji?”

Kai ta ɗaga mishi.

“Don Allah ki yi haƙuri. Ki rage yawan damuwa. Gobe da safe zan wuce.”

Muryarta a dakushe ta ce,

“Da sauri haka? Baka ce kwana biyu za ka yi ba?”

Girgiza mata kai ya yi.

“Wani abu ne ya taso… Shi yasa.”

Rausayar da kai gefe Tasneem ta yi, ɗan sauƙin da zuwanshi  ya kawo mata na dishewa.

“Yanzun sai yaushe?”

Ta buƙata idanuwanta na kawo hawaye.

“In sha Allah ba zan daɗe ba. Zan dawo… Ki kula da kanki.”

Kai ta ɗaga mishi tana share hawayen da ya zubo mata.

“Zan sake ganin ka kafin ka tafi?”

Wannan karon shi ya ɗaga mata kai yana miƙewa. Sai da safe ya yi mata yana ficewa daga gidan. Bai jima da fita ba su Azrah suka dawo.

“Ummi ta dake ki ko?”

Hamnah ta tambayeta muryarta na rawa da alamar gab take da yin kuka. Murmushi Tasneem ta yi tana girgiza mata kai.

“In ji wa ya ce Ummi ta dake ni?”

“Kuka kika yi. Idonki ya yi ja.”

Hamnah ta faɗi. Tasneem kan danganta kular Hamnah kan abubuwa da yawa da rashin yawan maganarta. Ta fi bin komai da idanuwanta fiye da bakinta. Hakan yasa tana lura da duk abinda yake faruwa a kusa da ita.

“Idona ne zai min ciwo…. Yana zafi tun ɗazun.”

Tasneem ta amsa, tana ƙin kallon Azrah da ke mata kallon tuhuma. Ta san su duka ba yarda suka yi ba. Sun kai matakin da wayonta baya tasiri akan su.

“Ku tsaya ku gani.”

Ta faɗi da sauri ta shiga ɗaki ta ɗauko Rediyo da fitilar da Tariq ya siyo tana nuna musu.

“Fitila… Mun samu fitilar karatu in ba wuta… Wa ya siyo mana?”

Azrah ta faɗi muryarta cike da farin ciki.

“Ya Tariq.”

Tasneem ta amsa ta. Karɓar fitilar Azrah ta yi tana duddubawa. Rigar ta Sabeena ta kama tana son cirewa. Don haka Tasneem ta ajiye fitilar tana kama mata rigar don ta cire. Tsayin da take yi na ba Tasneem ɗin mamaki.

Ita da Azrah su suka biyo tsayin ‘yan gidan su Abba. Su ukkun babu tazara a tsakanin su don kuwa Ummi kwanika ta yi, tsakanin Azrah da Hamna shekara ɗaya da wata biyar. Ita da Azrah ne shekara biyu. Sai Hamna da Sabeena akwai tazara sosai. Yanzun ita Tasneem shekaru cikin na sha bakwai take.

Azrah Sha biyar, sai Hamnah sha huɗu. Duk da makarantar su Azrah da Hamna ɗaya, Ita Gwammaja take. Kasancewar lokaci ɗaya aka saka su makaranta da Azrah don har ma ta fi ta tsayi yasa matakin karatun su ɗaya.

Sai bayan ta cire ma Sabeena rigar ne ta kula Hamnah bata nan.

“Ina Hamnah?”

Ta tambaya. Ɗan ɗaga mata kafaɗa Azrah ta yi alamar ita ma bata sani ba. Ta san su dukansu babu inda suke zuwa. Ta san Hamnah ba zata wuce shiga ta yi su gaisa da Tariq ba. Aikam gidan su Tariq ɗin ta shiga. Ta sa hannunta ta shafi katangar gidan.

Tanajin kamar ace tana da ikon dawo musu da komai yadda yake. Sallama ta yi a hankali tana ƙwanƙwasa ƙofar ɗakin duk da a buɗe take.

“Waye?”

Tariq ya tambaya da razana a muryarshi.

“Nice…”

Ta amsa a taƙaice.

“Shigo.”

Ya amsa. Labulen ta ɗaga ta ɗora shi kan ƙyauren ƙofar duk da akwai fitila da ta cika ɗakin da haske, tunda Magriba ta doso kai. Kwalaben da ke gabanshi ta soma kallo tukunna ta kalli fuskarshi da idanuwanshi da sun fara sake launi.

“Hamnah…”

Ya kira da wani yanayi a muryarshi. Jin muryarta yasa bai ko yi ƙoƙarin ɓoye kwalaben ba. Ya ɗauka Tasneem ce da ya ji ƙwanƙwasawar.

“Ba ka daina ba. Ba ka daina sha ba.”

Zame jikinshi ya yi kan katifar ɗakin yana kishingiɗa tare da lumshe idanuwanshi.

“Muryoyin da ke cikin kaina…ina son jin shiru. Surutu ya yi yawa a duniyata.”

“Me yasa shi kaɗai ne hanya? Me yasa babu wata hanyar?”

Buɗe idanuwanshi ya yi da suke wani lumshewa da kansu.

“Na gaji da jin tambayoyin da ba su da amsa…”

Juyawa Hamnah ta yi tana kama labulen zata sakar mishi.

“Baki ce komai ba… Ba za ki faɗa min yadda da duk kwalba nake nisa da hankalina ba?”

Ba tare da ta juya ba ta ce,

“Me zan faɗa maka da ba ka sani ba Ya Tariq?”

Maida idanuwanshi ya yi ya rufe gam. Don bakin shi ya yi nauyi baya jin zai iya magana. Yana jin yadda yake ɓacewa zuwa wata duniyar ta daban. Labulen ɗakin Hamnah ta sakar mishi tana ficewa ta koma ɓangaren su.

“Ina kika je?”

Tasneem ta tambaya ba don bata sani ba, sai don tana son tabbaci.

“Gaisawa da Ya Tariq.”

Hamnah ta amsata tana wucewa ɗaki don ta cire uniform ɗinta. Ta san rashin maganarta na ƙara zama dalilin da suke ganin kamar bata san abinda take ba, kamar shekarunta sun yi ƙaranci ta fahimci abubuwa da dama.

Sai dai har a zuciyarta bata son magana kan abinda ba zata iya canzawa ba. Shi yasa ta fi binsu da kallo akan ta yi magana. Banda Tariq ko su Tasneem ba su cika jin maganarta ba. Shi ma ɗin tun tashinta in ta ganshi ne kawai tana son mishi magana. Ko da ba zata yi magana ba zata tsinci kanta da zuwa inda yake ta tsaya.

Ta san yadda fuskar Tasneem take in ta yi kuka, ba tun yanzun ba, tun tana ‘yar ƙaramarta wayon Tasneem bai taɓa tasiri akanta ba. Shiru kawai take yi mata.

*****

Ranar Ummi ma bata dawo ba sai bayan Isha’i. Suna zaune sun fara jin shirin Inda Ranka a gidan radiyon Freedom wani yaro ya shigo da sallamar shi, hannun shi riƙe da baƙar leda.

“Wai gashi a ba Tasneem.”

Ai kafin Tasneem ɗin ta ce wani abu tuni Ummi ta taso ta karɓi ledar hannun yaron tana faɗin,

“In ji wa?”

“Alhaji Madu kuma wai ta zo.”

Ware idanuwa Ummi ta yi, Alhaji Mado tsohon sanata ne, bayan unguwarsu yake da tanƙamemen gida, amma an ce iyalanshi na zaune a unguwar Rijiya Zaki. Yaron ya juya yana ficewa. Ƙanƙance idanuwa Tasneem ta yi da suke a kumbure har lokacin saboda kukan da ta ci.

Tun kwanaki da take dawowa makaranta ya dinga binta a mota. Ta ƙi sauraren shi, don tasan tsoho dai mai shekarun shi inda mutunci ba zai bita ba. Don a haife ya kusa jika da ita.

“Tasneem kinga arziƙin Allah ko?”

“Tun rannan ya dinga bina na dawo makaranta. Ashe sai da ya gano gidan nan… Bari Abba ya dawo wallahi in faɗa mishi ya yi mai magana.”

Da hanzari Ummi ta ƙarasa inda Tasneem ɗin take tana riƙo mata riga.

“Ki yi me? Ke baki da hankali ne wai? Yaushe za ki nutsu? Kina dai fita kin kuma ga girman gidan shi da ke bayan mu. Wallahi tun kafin in yi ƙasa-ƙasa da ke ki tashi ki je ku gaisa.”

“Cikin daren nan?”

Azrah ta faɗi tana bin Ummi da wani kallo da Tasneem ɗin bata so. Don haka ta miƙe, ta san ƙaunar ƙannen nata, bata son ransu na ɓaci da Ummi akanta, dama ɗazun suna ɗauka Ummi ta daketa. hijabinta da ta yi Sallah da shi na jikinta don haka ta saka a jikinta, ta kama hanya.

Ummi na can na buɗe ledar da aka kawo cike da kaji da fresh milk Hamnah ta faki idonta ko takalmi bata tsaya sawa ba balle hijab ta bi bayan Tasneem ɗin da tana fita Alhaji Madu ke washe mata haƙoran shi.

“Tasneem?”

Kallon shi ta yi , yanayin yadda yake kallonta yana wani ƙyafta idanuwa yasa ɗan sauran mutuncin shi da take gani ya ƙarasa zubewa. Buɗe baki ta yi zata amsa shi ta ji an fisgo hannunta. Juyawa ta yi cike da mamaki take kallon Hamnah da ke maida numfashi.

Tunda take da Hamnah ko faɗa da yara kan yi bata taɓa ganin ta yi ba, a Islamiyya da boko lokacin da take Primary, amma yanayin da ke shimfiɗe akan fuskarta a yanzun ya tsorata Tasneem ɗin. Gaban Tasneem ta shiga tana son zama katanga tsakanin ta da Alhaji Madun.

Tana jin ɗaya daga cikin ‘yan ajinsu na cewa mamanta ta ce ko ya kirata karta sake ta je. Ta ruga gida, ɗan iska ne, bata gama sanin cikakken abinda kalmar take nufi ba, amma yanayinta sam ko daɗin ji bai mata ba, ba kuma ta son ko kusa da Yayarta ta gifta balle ta raɓe ta.

“Banda girma sosai, amma ina da ƙawaye da yawa kuma dukkan mu munsan inda kake ajiye motarka, in ka sake zuwa wajen yayata sai mun kunna ma motarka wuta. Kuma Wallahi sai na yi Addu’a Allah ya kashe ka.”

Ware idanuwa Tasneem ta yi tana kallon Hamnah kafin wata irin dariya ta kubce mata. Shi kanshi Alhaji Madu mamaki ne bayyane kan fuskar shi. Kama hannun Tasneem da ke dariyar da ta jima bata yi irinta ba Hamnah ta yi tana watsa ma Alhaji Madu harara.

“Yaya zo mu tafi.”

Binta Tasneem ta yi, ta kasa daina dariyar da take har lokacin. A soron farko Hamnah ta tsaya, ko ina jikinta ɓari yake yi, rungume Tasneem ɗin ta yi a jikinta.

“Yaya gabana faɗuwa yake Wallahi…”

Riƙeta Tasneem ta yi a jikinta tana dariya har lokacin.

“Haba jarumata… Ku da za ku kunna wa motar Alhaji Madu wuta ke da ƙawayen ki?”

Dariya Hamnah ta yi, su dukkansu dariya suke. Hamnah na riƙe jikinta suna dariya suka shiga gida. Ummi ta kalle su.

“Har kin dawo?”

Kai ta ɗaga wa Ummi tana ƙoƙarin gintse dariyarta.

“Haka ya ce dare ya yi.”

Hamnah ta faɗi. Sosai Ummi ta kalleta, kafin ta ce,

“Ku zo ga kaza.”

“Ni dai bana ci.”

Hamnah ta faɗi tana zamewa daga jikin Tasneem zuwa ɗaki, Azrah na bin bayanta don ita ma bata jin zata iya cin naman in dai ba Tasneem da kanta zata bata ba.

“Ki zo ki karɓa ki basu…na san za su karɓa in ke kika basu da kanki.”

Ƙarasawa Tasneem ta yi ta karɓi ƙunshin kazar guda ɗaya da fresh milk ɗin. Murya Ummi ta sauke da faɗin,

“Tasneem ki rufa mana asiri kafin Abban ku ya dawo ki lallaɓa mu kwashi arziƙin mu wajen Alhaji Madu.”

Kai kawai ta ɗaga ma Ummi da murmushi a fuskarta, hakan yasa Ummi washe baki.

“Yawwa ‘yar albarka.”

Ɗaki Tasneem ta wuce tana samun waje ta zauna. Labarin abinda ya faru ta ba Azrah, har tsakar gidan Ummi na jin dariyarsu kamar taɓaɓɓu. Ta wani fannin zuciyarta na mata wani iri da rabon da su yi dariya haka a gabanta.

Wani lokaci ko hira suke a tsakar gida in ta sa baki sai su duka su yi shiru. A hankali za su dinga tashi suna bar mata wajen suna komawa ɗaki komin zafin da ake yi kuwa. Sabeena ma yanzun bata nemanta. Ko da Tasneem na makaranta a yarinyar zata yi ta zama a ɗaki tana jira sai ta dawo ta faɗa mata tana buƙatar wani abu. Tashi ta yi ta shige ɗaki ita ma da sauran kazar dake cikin ledar.

*****

Bacci ne ya ɗauketa bayan ta yi Sallar Asuba, don ta daɗe bata same shi ba daren jiya sabo da tunani da ya yi mata yawa. Don haka a gurguje take haɗa komai ta taya su Azrah suka ƙarasa shiryawa, don ta ma haƙure ma ranta zuwa makaranta ranar.

Sai da ta ga fitarsu tukunna, da hanzari ta ɗauki hijabinta tana nufar sashin su Tariq. Ƙofar ɗakin da ta gani a rufe an maida labulen ciki ya fara sanar da ita ya tafi. Duk da haka ta ƙi barin zancen ya ƙarasa zuciyarta sai da ta ƙarasa ta buɗe ƙofar ta ga baya ciki.

Zuciyarta ta ji ta yi tsaye waje ɗaya. Haka ya ce za su yi sallama kafin ya tafi, ko godiya bata samu ta ƙara mishi ba. Ta san zai iya watanni kuma bai dawo ba. Tana kewar lokutan da katanga ce kawai tsakanin su, har makaranta tare suke fita.

Idanuwanta ta ji sun cika da hawaye. Ga tsoro da ya cika mata zuciya, yadda komai yake canzawa lokaci ɗaya na firgitata. Sai ta ji kewar Abba ta danne ta, inda yana nan ko ganin shi ta yi suka yi labari ranta zai yi sanyi.

“Allah ya tsareka a duk inda rayuwa ta kai ka Ya Tariq. Na gode da sauƙin da zuwanka yake kawo min… Allah ya dawo da kai lafiya…”

Take faɗi a tsakar gidan ta saka gefen Hijab ɗinta ta share hawayen da ke cike da idanuwanta.

“Don Allah karka daɗe da yawa… Kai ka san inda nake, ni ban san inda zan ganka ba…karka daɗe…”

Ta ƙarasa muryarta can ƙasa, wani abu na tsaya mata a zuciya.

<< Alkalamin Kaddara 3Alkalamin Kaddara 5 >>

2 thoughts on “Alkalamin Kaddara 4”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×