Abuja
Idanuwan shi ya buɗe a hankali yana jin kamar mota ta taka shi, don jikin shi kamar ba nashi ba haka yake ji.
"Yaya?"
Ya ji muryar Zafira, miƙewa yake, Fawzan ya taimaka mishi ya tashi. Hannuwan shi yasa yana dafe kanshi da ke juya mishi, kafin komai ya soma dawo mishi a hankali.
"Yayaa..."
Wannan karon Aroob ce ta kira shi. Kallon ta yayi, fuskarta har ta kumbura da alamun kukan da ta yi. Ɗan murmushi yai mata duk da yana jin ƙirjin shi kamar zai buɗe gida biyu saboda ciwon. . .
Keep the good work