Skip to content
Part 40 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Abuja

Idanuwan shi ya buɗe a hankali yana jin kamar mota ta taka shi, don jikin shi kamar ba nashi ba haka yake ji. 

“Yaya?”

Ya ji muryar Zafira, miƙewa yake, Fawzan ya taimaka mishi ya tashi. Hannuwan shi yasa yana dafe kanshi da ke juya mishi, kafin komai ya soma dawo mishi a hankali. 

“Yayaa…”

Wannan karon Aroob ce ta kira shi. Kallon ta yayi, fuskarta har ta kumbura da alamun kukan da ta yi. Ɗan murmushi yai mata duk da yana jin ƙirjin shi kamar zai buɗe gida biyu saboda ciwon da yake ji yana mishi. 

“Ina Nuri?”

Ya tambaya. Ɗan ɗaga mishi kafaɗu ta yi da ke fassara ita ma bata sani ba. Kafin ya soma ƙoƙarin miƙewa tsaye. 

“Ina za ka je?”

Fawzan ya tambaye shi. 

“Ina son magana da Nuri ne.”

Ya amsa, kai Fawzan ya girgiza mishi.

“Yaya ka zauna. Mu zauna a nan kawai… Su Nuri bansan me ya same su ba yau… Ka barsu su nutsu tukunna…” 

Kallon Fawzan ɗin Rafiq yake yi sosai, kafin ya lumshe idanuwan shi ya fara jero Innalillahi wa inna ilaihir raji’un, saboda yafda yake jin zuciyar shi zata fito daga ƙirjin shi da tunanin ba jini ɗaya ba ne yake yawo a jikin su shi da Fawzan. A hankali ya buɗe idanuwan nashi, muryar shi can ƙasa ya ce, 

“Ban haɗa jini da ku ba Fawzan… Innalillahi wa inna ilaihir raji’un…” 

Ya ƙarasa, girman maganar da Nuri ta yi na danne shi, kokawa yake da numfashin shi, amma ya kasa samu ya dai-dai ta. Idan bai kasance ɗan Nuri da Daddy ba, ta ina zai fara? Su waye iyayen shi, me hakan yake nufi da duka rayuwar shi, ba asalin shi kaɗai hakan zai taɓa ba, duka rayuwar shi kacokan zata canza daga sanin da yai mata zuwa wani abu na daban. 

“Don Allah ka daina… Ka daina cewa haka Yaya…ni bana so wallahi.” 

Aroob ta ce, kuka na ƙwace mata, matsawa ta yi tana kwanciya jikin Zafira da ita ma kukan take. Numfashi Rafiq ya ja yana saukewa, kukan su na ƙara mishi nauyin da yake ji a ƙirjin shi. Juyawa yayi yana ficewa daga ɗakin, duk da kiran da ya ji suna mishi bai juya ba, kai tsaye ɓangaren Nuri ya wuce yana tsayawa a bakin ƙofar ɗakinta tare da ƙwanƙwasawa. Muryarta a dishe ya ji ta ce ya shiga. Murfin ƙofar ya murza yana wucewa ya shiga ɗakin ya ƙarasa gefen gadon da take zaune. A ƙasa ya zauna yana ɗora kanshi a jikin ƙafafuwanta. 

“Nuri ƙirjina ya min nauyi… Zuciyata kamar zata fito nake ji. Don Allah ki min bayani yadda zan fahimta.” 

Kuka take da yake jin sautin shi da wani irin yanayi, bai sake magana ba, bai kuma ɗago kanshi daga jikinta ba, ya ƙyaleta ta samu nutsuwar faɗa mishi ko me yake faruwa. Hannu Nuri tasa tana share hawayen da yake bin fuskarta, muryarta na rawa ta soma magana. 

“Ku duka kun san labarin matsalar da na samu da dangin Daddynku akan rashin haihuwar da ban samu da wuri ba. Kunsan yadda na bi shi ƙasar waje….baku dai san cikin ƙarya muka yi ba. Mun yi wa dangin shi ƙaryar ina da ciki kafin mu tafi…” 

Numfashi ta ja mai nauyi. Ranar da Rafiq ya shigo rayuwar su na dawo mata kamar lokacin komai ya faru.

***** 

Hannunta na dumtse cikin na Daddy, idan hankalin ta yayi dubu kowannen su a tashe yake. 

“Ya zan yi?”

Ta tambaye shi tana jin hawaye sun ciko mata idanuwa. Hannun shi ya zame daga cikin nata, bai damu da mutanen da ke cikin Airport ɗin ba, don nutsuwarta ta fi mishi muhimmanci akan komai a lokacin, fuskarta ya tallaba cikin hannuwan nashi yana faɗin, 

“Ki yi numfashi Hafsatu…”

Kai take ɗaga mishi tana ƙoƙarin yin abinda ya ce ɗin. 

“Babu abinda zai faru. Zan faɗa musu cikin ya zube bayan mun isa.” 

“Daada ba zata yarda ba. Zata gane ƙarya ne.”

Nuri ta ƙarasa hawayen ta na zuba. 

“Zan faɗa mata har sai ta yarda. Kina jina babu wanda zai saka ni ƙara aure. Kuma bazan jima a nan ba, na ce miki ina neman transfer, Abuja za mu koma in sha Allah, mu yi nisa da su. Komai zai yi dai-dai ki yarda dani…” 

Ba sai ya buƙaci wannan ba, yarda da shi ba zaɓi ba ne a wajen ta, abu ne da ya riga ya gama faruwa. Sai dai har ranta tana tsoron dangin shi, bata son tashin hankali, damuwar da ke fuskar shi yasa ta ɗan ɗaga mishi kai, tana ɗora murmushin ƙarfin hali a fuskarta, shi ma murmushin yai mata yana goge mata hawayen da ke fuskarta, tare da riƙe hannunta suna takawa da nufin fita daga Airport ɗin gaba ɗaya. Hakan kuwa suka yi, bakin ƙofar suka zo inda masu Taxi ke ta hada-hadar su ta yau da kullum. Suna tsaye don ya fi so yai musu shatar duka Taxi ɗin da zata kaisu gida, suka ji an musu sallama. 

Nuri ce ta amsa tana juyawa ta kalli matar da take da tabbacin ta bata shekaru wajen huɗu ko fiye da hakan. Murmushi taima Nuri da wani yanayi cikin idanuwanta da Nuri ta kasa fassarawa. Hannunta da ke riƙe da abin saka yara ta bi da kallo, kafin ta sauke su kan yaron da ke ciki yana bacci, wani irin yanayi ta ji a zuciyarta da take alaƙanta shi da yadda take neman haihuwa ido rufe. Don ji ta yi kamar ta ƙwace yaron. 

“Don Allah ko za ki duba min shi in ɗauko jakata?” 

Daddy ya buɗe baki zai yi magana, Nuri ta riga shi da faɗin, 

“Babu matsala…”

Murmushin ta sake yi ma Nuri tare da cewa,

“Na gode.”

Tana juyawa ta wuce, yaron Nuri ta kalla da ba zai wuce wata biyu ba, ta juyo ta kalli Daddy. 

“Kalle shi don Allah, kamar ɗan larabawa wallahi.” 

Farin cikin dake fuskarta yasa Daddy faɗin, 

“Ma shaa Allah. Yana da kyau kam, amma nasan naki zai fishi kyau in sha Allah.” 

Murmushi Nuri ta yi a kunyace tana sake kallon yaron, sosai ya shiga ranta, bata jin nan kusa zata manta da hoton fuskar shi. Motsi ta ga yayi daya sata faɗin, 

“Bismillah…”

Tana tsugunnawa ta kai hannu tana taɓa shi, takarda ta gani a gefen shi a ajiye da ta ɗauka tana juyawa. 

‘KA KARANTA DON ALLAH’

Aka rubuta a baya da manyan baƙi da ya sa zuciyarta dokawa a tsorace tana miƙewa tare da ce ma Daddy, 

“Ka ga…”

Takardar ya karɓa shima yana duba rubutun, tare da miƙa mata ya ce, 

“Ki mayar inda kika ganshi. Matar nan ma ta daɗe…ko ki jira in shiga ciki in duba ta mu tafi.” 

Kai Nuri ta jinjina mishi jikinta a sanyaye. Cikin Airport ɗin Daddy ya koma, yai neman duniya bai ga matar ba. A hargitse ya dawo wajen Nuri ya faɗa mata, zuwa lokacin su dukkan su sun tsorata. Ita ce tai ƙarfin halin saka hannu ta ɗauki takardar tana buɗewa: 

‘Amincin Allah ya tabbata ga wanda yake karanta wasiƙar nan. Bansan me zance ba. Don Allah wanda duk ya tsince shi ya riƙe shi da amana. Dalilai da yawa ba za su bari in iya riƙe shi ba. A kira shi da Rafiq shine alfarmar da nake nema. Nagode.’

Cikin wani sabon tashin hankali Nuri ta miƙa wa Daddy wasiƙar. Shi ma karantawa yayi yana faɗin, 

“Wane irin rashin hankali ne wannan? Meye haka? Abinda yake faruwa a fim shi ne wata mahaukaciya take son yin shi a fili? Bata da hankali… Wallahi bata da hankali sam, ki tsaya in sake dubo ta…” 

Bai ma jira ya ji amsar Nuri ba ya wuce yana sake komawa. 

***** 

Numfashi Nuri ta sauke mai nauyin gaske, riƙon farko da tai ma Rafiq a ƙirjinta ta ji shi har cikin ranta, ba zata taɓa manta yanayin ba har mutuwar ta. Magana ta ci gaba da yi. 

“Babu neman da Daddy bai mata ba, amma bai ganta ba, na yi fama dashi sosai kafin ya yarda muka ɗaukoka zuwa gida. Daddy a tsorace yake, ni na tabbatar mishi da cewar ya yarda mu faɗa ma dangin shi cewar kai ne jaririn dana tafi da cikin shi, in yaso mu tattara mu koma Abuja da zama kar asirin mu ya tonu. Duk da haka sai da mukai sati da dawowa babu wanda yasan mun dawo. Kafin Daddy ya sanar da su Daada. Ko kaɗan basu kawo komai a ransu ba, asali ma ka siya mun mutuncin da ban taɓa samu a idanuwan su ba. 

Rafiq ka zamar min haske a rayuwa ta, ka sama min farin cikin da ban taɓa tunanin samun shi ba, asibiti muka je domin neman shawara don ina son shayar da kai ko yaya ne, ina son samun wannan kusancin da kai tunda jinina baya yawo a jikin ka. Shekarka uku Allah ya bani cikin Fawzan. 

Bansan ya zan faɗa maka ka gane ba, baka kwanta a cikina ba, baka fito daga jikina ba, wallahi ƙaunar da nake maka mai girma ce…Ka yi haƙuri ban faɗa maka ba, ka yi haƙuri na ɓoye maka… Ka yi haƙuri.” 

Ta ƙarasa da kuka mai tsuma zuciya. Sun kai mintina goma a haka. Kafin Rafiq ya ɗago yana miƙewa. Maganganunta yawo suke mishi, baisan ta inda zai fara tauna su ba ne ba. Yana buƙatar shaƙar iska daban da ta gidan. 

“Ina za ka je?”

“Gida…”

Ya amsa ta. 

“Rafiq…”

Lumshe idanuwan shi yayi yana buɗe su. 

“Kaina ya min nauyi, bansan me ya kamata in yi ba, ban san me nake ji ba Nuri. Gida nake son tafiya, shi ne abu na farko da ya zo kaina. Don Allah karki hana ni…” 

Hannu ta sa tana goge fuskarta, tana kuka ta ce mishi, 

“Ka je… Ka ɗauki dukkan lokacin da kake buƙata. Don Allah karka manta ɗana ne kai, ko me ya faru ɗana ne kai, babu abinda zai canza hakan…” 

Kai kawai ya ɗaga mata. Ya wuce, yana jin zuciyar shi na gaya mishi ya kamata ya faɗa ma su Fawzan ya tafi, amma ba zai iya ba, yana jin wani agogo da ke yawo a cikin jikin shi yana sanar da shi akwai ƙayyadajjen lokacin da yake jira, komai ya tarwatse mishi. Baya so yai breaking down a gaban su, gara ya bar gidan tukunna, in ya samu ƙarfin fuskantar su sai ya dawo. Zuwa yanzun ba zai iya ba, fita yayi yana barin gidan da sauri. Haka ma da sauri ya taka zuwa bakin hanya yana samun Taxi da zata kaishi gida don ba zai iya jiran isa ba. 

***** 

Bai ji gaba ɗaya ƙarfin shi ya ƙare ba sai da ya ji ƙafafuwanshi a cikin gida tukunna, tura ƙofar yayi ya rufe yana zame jikin shi ya zauna, bayanshi jingine da ƙofar, hannu yasa ya goge zufar da yake ji a fuskarshi. 

“Ɗana ne kai Rafiq…wallahi ban taɓa buƙatar haɗa jini da kai kafin in ji hakan ba…ɗana ne kai duk da baka fito daga cikina ba…” 

Maganganun Nuri suke mishi yawo, ji yake kamar ko ina na jikinshi a buɗe yake da sababbin ciwuka, maganganunta kamar gishiri a jikin ciwukan shi suke mishi. Hannu ya sa dai-dai ƙirjinshi inda zuciyar shi take yana murzawa ko zai samu sauƙin abinda yake ji, ƙafafunshi ya ja yana haɗe su da jikinshi kamar me jin sanyi, ya rasa inda zai tsoma ranshi ya ji sauƙi ko ya yake. Ya rasa ya zai yi, ina zai saka jikin shi, kayan shi ma nauyi yake jin sun mishi, da zai iya tashi ya je ya sakar ma kanshi ruwan sanyi, wataƙila da ya samu sauƙi. Amma baya jin yana da wannan ƙarfin. 

Numfashi yake fitarwa sama-sama mai sauti saboda ciwon da zuciyarshi take mishi. Yadda yake ji yasa shi tsammanin ko raɗaɗin fitar raine, ko mutuwar shi zata riske shi, hakan yasa wani irin tsoro marar misaltuwa dirar mishi, baya tunanin ya shirya, ba shi da tabbas akan cewar ayyukan shi za su ishe shi zaman lafiya a kabari. Sai dai yana da yaƙini kan rahmar Allah, yana da yaƙini kan sauƙin da mutuwar zata sama mishi a yanayin da yake ciki, don baisan ta inda zai fara gyara hargitsin rayuwar da yake fuskanta ba. 

“Sugar…”

Tasneem ta kira shi, muryarta a tausashe ganin yanayin da yake ciki, tunda ta fito ta hango shi a zaune ya dunƙule jikin shi waje ɗaya tasan ba lafiyar shi ba, sai yanzun da ta ƙaraso kusa da shi ta tabbatar da hakan. Idanuwan shi ya sauke cikin nata da wani irin yanayi da yasa zuciyarta karyewa, ciwo ne shimfiɗe cikin idanuwan shi. Hannun shi Rafiq ya ɗaga yana miƙa mata, kamawa ta yi tana jin yadda ya dumtse hannunta kamar zai karya mata yatsunsu. Tsugunnawa ta yi babu shiri, tana sa ɗayan hannun ta tallabi fuskarshi, yanayin yadda yake fitar da numfashin na sa hawaye tarar mata a idanuwa. Batasan meya same shi mai girma haka ba, bata sani ba ballantana tasan yadda zata sama mishi sauƙi ko ya yake. 

Gani tai tsugunnon ba zai mata ba, zama ta yi sosai tana sakin fuskarshi ta kamo ɗayan hannun shi, matsawa ta yi tana riƙo shi jikin ta, da sauri ya zame hannuwan shi daga cikin nata yana zagaya su a bayanta ya riƙe ta dam. Baisan me yake nema ba, ji yake kamar ta raba sauƙin da take ji tare da shi, kafin ya tuna yanayin da suke ciki ita da shi da ya ƙara mishi wani sabon ciwon zuciyar. 

“Ka daina… Ka daina ƙoƙarin danne abinda kake ji… Hakan kawai na da nashi ciwon na daban…” 

Tasneem take faɗa mishi don tasan raɗaɗin ciwo ko da bai kai nashi ba, tasan yadda rayuwa take tura ka sai ta kai ka bango, hakan baya mata wasu lokutan saita matseka jikin bangon, ta takura komai na duniyarka, ta sa ƙarfin da ya rage maka shi ne wanda kake amfani da shi wajen yin numfashi. 

“Kirjina yana mun ciwo…”

Rafiq ya fadi a wahalce, sake rike shi tayi gam tana fadin 

“Ka daina riƙe abinda kake ji…”

Numfashi yake ci gaba da yi cikin ƙoƙarin son ya dai-dai ta shi. Baisan me take nufi ba da ya daina riƙe abinda yake ji ba. 

“In kuka za ka yi ka yi, in wani abu kake son fasawa ka tashi in rakaka akwai abin fasawa da yawa a gidan… Ko me kake jin yi, idan akaina za ka huce ka yi, ka yi ko me kake tunanin zai sama maka sauƙi Sugar, don Allah, ganin ka haka na karya mon zuciya…” 

Kai yake ɗaga mata tunda ta fara magana, yana zame jikin shi daga nata ya sauke idanuwan shi cikin nata. Yanayin muryarta, yanayin da ke fuskarta, yadda take kallon shi da wata irin ƙauna da bai taɓa tunanin tana mishi ita ba yasa shi jin wani abu na buɗewa a ƙirjin shi, numfashi yake ja yana fitarwa da nauyi, kafin ya ji wani irin abu mai ɗumi na bin fuskar shi, hannuwa Tasneem ta kai ta tallabi fuskar shi, yatsunta da yake ji suna share mishi abinda yake ji na bi mishi kunci ya tabbatar mishi da kuka yake. 

Hannuwan nata ya kama yana sauke su daga fuskar shi, ta bar mishi hawayen su zuba, don ya tara su na tsawon lokaci, bayan kanshi ta zagaya da hannunta tana riƙo shi, bai yi musu ba ya kwantar da kanshi jikin kafaɗarta yana wani irin kuka da take ji har ƙasan zuciyarta. Kuka yake kamar ƙaramin yaro, ba zai kuma ce ga ranar ƙarshe da hawayen shi suka zuba ba ko a yarinta, balle kuma da girman shi. Amma yanzun kuka yake na rashin tabbas da bashi da shi akan asalin shi, kuka yake na girman ƙaunar da ke tsakanin shi da Nuri. 

“Ɗana ne kai Rafiq…wallahi ban taɓa buƙatar haɗa jini da kai kafin in ji hakan ba…ɗana ne kai duk da baka fito daga cikina ba…” 

Maganganun ta yake ji a zuciyar shi, kuka yake sosai na yadda bata taɓa nuna mishi bai fito daga cikin ta ba, kuka yake na ƙaunar su Fawzan da ya samu, kuka yake na ciwon jinin su baya yawo a jikin shi, wannan kukan shi yake yi da wani irin ciwo, kafin ya fara kukan inda rayuwa ta kawoshi, kukan yadda bata bashi halin tuna matarshi da yarinyar shi ba. Hannun Tasneem da ya ji ɗumin shi akan bayan shi tana shafa shi cikin sigar lallashi yasa shi jin rashin adalcin da ke cikin zaman su da ya ƙara fito da hawayen shi, baisan me ya same shi da kuka ba yau. Amma duk wani ƙaramin abu da ya tuna kamar ƙarin dalili ne na yin kuka a wajen shi. 

A yadda yake ba tare da ya ɗago ba ya miƙa hannunshi kan ƙirjinta, yana jin yadda bugun zuciyarta yake harbawa a tafin hannun shi, in har abinda yake ji a yanzun ciwon zuciya ne yana jinjina ma ƙoƙarinta, yana jinjina ma yadda ta iya zama da ciwon na lokaci mai tsayi haka. Tana buƙatar sauƙi itama, su dukkan su suna buƙatar sauƙi, ɗago kai yayi daga kafaɗarta yana sa hannu ya share hawayen shi kafin ya zame nata hannuwan daga jikin shi yana miƙewa, da idanuwa Tasneem take binshi ba tare da ta ce mishi komai ba, idanuwan dai ta raka su da shi har ya bar wajen, yana tafiya kamar wanda ya sha wani abu. 

Ɗaki ta so wucewa itama. Amma bata jin ƙarfi ko kaɗan a jikin ta, don haka ta matsa jikinta da bangon tana jingina da shi, wasu siraran hawaye na zubar mata. Da dukkan abinda take da shi ta yi amfani tana danne son tambayar Rafiq abinda yake damun shi, saboda har ƙasan ranta take jin yadda bata da wannan hurumin yanzun a rayuwar shi, bata tunanin ko ta tambaye shi zai faɗa mata, tunda ta rasa yardar shi, shi yasa ma bata tambaya ba. Bata san iya lokacin da ta ɗauka a hakan ba, sai da ta ji motsin Rafiq ɗin tukunna ta ɗaga kai tana kallon shi. 

Yanayin da ke cikin idanuwan shi na saka ta runtsa nata da faɗin, 

‘Innalillahi wa inna ilaihir raji’un.’

Cikin zuciyarta tana ci gaba da maimaitawa sai da ta ɗan samu nutsuwa tukunna ta buɗe su, kallon dai yake mata har lokacin. 

“Tasneem…”

Ya kira muryarshi a dakushe, zuciyarta na wani irin dokawa take girgiza mishi kai, ya jure ‘yan watannin nan tare da ita, wani lokacin takan ga gilmin yafiya cikin idanuwan shi in ya kalleta, hakan ba zai faru ba, tana jin tarin da yai mata sauƙi yana fara tasowa saboda numfashin da baya kaimata inda ya kamata, da sauri ta miƙa mishi hannu, yasa nashi ciki don shima bai jima da buƙatar ta taimaka mishi ba, janshi ta yi ya zauna, sosai ta dumtsa hannuwan ta cikin nashi, yanayinta baya ƙara mishi komai sai ƙarfin gwiwar yin abinda yake shirin yi, su dukkan su suna buƙatar sauƙi, shi ba sauƙi kawai yake buƙata ba, yana buƙatar yadda zai fara tattaro rayuwar shi. 

“Tasneem…”

Ya sake kiran ta wannan karon muryarshi a karye, kai take ci gaba da girgiza mishi hawaye na zubar mata, ta manta yadda zuciyarta ke son jin ya kira sunanta ko yaya ne, yadda ta yi kewar maganar shi, yanzun kam shirun shi ta fi buƙata, bata son jin duk wani abu da zai faɗa mata. 

“Ki yi haƙuri…”

Kukan ta ta ji ya fara fita da sauƙi, bakinta ya mata nauyin gaske balle ta iya yin wata magana. Ɗayan hannun shi ya ɗago, sannan ya zame hannun shi daga nata, yana buɗe tafin hannun ta ya ɗora mata takardar da ke linke yana dumtsawa. 

“Ina buƙatar dai-dai to a rayuwata, kina buƙatar sauƙi Tasneem…” 

Kai take girgiza mishi tana wani irin kuka har jikinta na ɓari. 

“Don Allah… Kar ka yi haka, kar ka min wannan hukuncin, ka barni a gidan ka… Ka daina min magana…Ka ji… Don Allah karka min haka…” 

Take faɗi tana jin takardar da ke hannunta kamar garwashin wuta. Hakan yasa ta sakin takardar tana riƙe kafaɗar Rafiq ɗin da ya ƙi haɗa idanuwa da ita, girgiza shi take yi. 

“Don Allah…Don Allah ka yi haƙuri, ya zan yi da sonka? Ya zan yi da kewarka?” 

Ya ƙi ɗagowa ya kalleta, so take ya kalleta, duk da tasan yana jin sautin kukan ta, amma in ya kalleta zai fi tausaya mata, in ya ga yadda zuciyarta take tarwatsewa da abinda yake yi zai ji tausayinta ya mayar da ita, don tana da tabbacin mutuwa zata yi in ya rabata da kan shi, ba zata iya jure sonshi ba, jikinta ko ina barii yake, hannun shi ta kamo da sauri tana ɗorawa kan jikinta. 

“Yaron mu, ka duba darajar abinda yake cikina in baka duba tawa ba…don Allah… Ka duba wani abin ka yafe min.” 

Yanayin yadda take magana da sauri-sauri kamar zata shiɗe yake ji har ƙasan ranshi, sai dai zuciyarshi na cikin wani yanayi, ba zai zauna da ita ba, ƙarin hargitsi ce ita a rayuwar shi a yanzun, zai rantse akwai sauran ɓangaren da ke doka mata a zuciyar shi, wasu abubuwan da suka fi shi girma ne suka danne shi, yana buƙatar space don ya ji ko zai iya ɗaga su, ko ba zai iya ɗaga su ba. Cikin nata ya shafa da bai fara alamar tasowa ba har yanzun. Cikin zuciyarshi yake maganar sirri da komenene a cikin nata, kafin ya zame hannunshi yana ɗagowa ya saka idanuwan shi cikin nata. 

“Ban ce akwai sauƙi a ƙaddarar rabuwa da ke ba…ina buƙatar dai-daito a rayuwata, yaron mu zai iya jira, za ki kula mana da shi…” 

Kai take ɗaga mishi, tana wani irin kuka kafin ta katse shi da faɗin, 

“Zan kula da shi sosai, don Allah ka barni in yi hakan a gidan ka, karka raba ni da kai…” 

Kai Rafiq yake girgiza mata, yana kai hannu ya ɗauki takardar yana saka mata a hannunta, kafin ya ɗan miƙe don ya zaro wallet ɗinshi da ke aljihun shi, ya koma ya zauna, buɗewa yayi ya ɗauki credit card ɗinshi guda ɗaya yana juyashi don ya ga ko na wanne bankin ne, mayarwa yayi ya ɗauko wani yana saka mata a hannunta shi ma da faɗin, 

“3696 shi ne password ɗin, akwai kuɗi da yawa a ciki, zan dinga tura miki wasu…” 

“Ba kuɗi nake buƙata ba…”

Ta faɗi muryarta a karye. 

“Banda wani zaɓi, Tasneem hakan ne kawai sauƙin mu.” 

Idanuwan shi take nazari tana neman wani rauni a cikin su da zata fake a bayanshi, amma bata ga hakan ba, wani irin kuka ya sake ƙwace mata, zuciyarta kanta ta sarara mata wannan karon, don tasan ba zata iya ɗaukar rashin shi da ciwonta a lokaci ɗaya ba. Ba wai bata hango zai rabu da ita ba ne, bata dai hango cewar zata ji abinda take ji yanzun ba ne. Da ƙyar ta iya jan wani numfashi tana sauke shi a wahalce, matsawa ta yi ta riƙo shi jikinta tana zagaya hannunta kamar zata mayar da shi cikinta. Riƙeta yayi shi ma wasu siraran hawaye na zubo mishi da yadda babu adalci a cikin rayuwa gaba dayan ta. 

Sun jima a hakan, kafin ya zame hannun jikin shi yana miƙewa. 

“Isah zai kaiki gida. Zai jira ki har ki gama shiryawa…” 

Wani sabon kukan ta ji ya sake ƙwace mata.

“Rafiq…”

Ta kira sunanshi a karo na farko, sautin na dirar mishi da wani yanayi mai wahalar fassarawa. 

“Na gode… Na gode da ƙaunarka… Na gode da komai.” 

Kai kawai ya iya ɗaga mata yana buɗe ƙofar tare da ficewa, sannan ya rufo ƙofar tare da wani shafi na rayuwarta da kuma wani ɓangare na zuciyarta da wani irin ciwo na gaske.

***** 

Ya daɗe a ƙofar gida a tsaye baisan inda ya kamata ya nufa ba, kafin ya ja ƙafafuwan shi zuwa bakin hanya yana tare me taxi, office ɗin su Muneeb ya nufa saboda ba zai iya zuwa gida ba. Kanshi tsaye ya wuce har office ɗin, ko sallama bai yi ba ya tura ƙofar ya shiga, ya wuce kan kujerar da ke gaban tebur ɗin Muneeb ɗin ya zauna yana haɗa kanshi da tebur ɗin. 

“Rafiq?”

Muneeb ya kira da wani irin yanayi a muryarshi. Rafiq ɗin bai ɗago ba, ko motsawa bai yi ba, hakan ya tabbatar ma da Muneeb cewar ba lafiya ba. Miƙewa yayi yana faɗin, 

“Bari in ɗauki excuse in zo mu wuce gida.”

Bai jira amsar Rafiq ɗin ba ya wuce yana ficewa daga office ɗin, ko mintina goma bai cika ba ya dawo. 

“Tashi mu je.”

Babu musu Rafiq ya miƙe yana bin bayan Muneeb ɗin har suka fita daga wajen aikin nashi zuwa inda yai packing ɗin motarshi, shi ya buɗe ma Rafiq ɗin ya shiga, tukunna ya zagaya ya shiga shi ma suna nufar gidan shi, kamar mutummatumi haka Rafiq yake bin Muneeb ɗin duk inda yayi, har cikin gidanshi, zuwa bedroom. 

“Bani wayoyinka.”

Muneeb ya buƙata, hannu Rafiq ya saka a aljihun shi yana fito da wayoyin da wallet ɗin shi duka ya miƙa ma Muneeb da ya karɓa yana saka su a nashi aljihun, wajen ajiye kayanshi ya ƙarasa ya buɗe, baƙar riga ya ɗauko marar nauyi da wani wando mai laushi iya gwiwa yana zuwa ya miƙa ma Rafiq ɗin. 

“Ka yi wanka ka sake kaya.”

Kai Rafiq ya ɗaga mishi ya wuce banɗaki. Gefen gado Muneeb ya ƙarasa ya zauna, yana tunanin duk yadda akai Rafiq yasan maganar su Samira. Shi kaɗai ne abinda yasan zai hargitsa shi haka, wayar Rafiq ɗin ce ta fara ƙara, hakan yasa shi dubawa, Fawzan ya gani shi yasa ya ɗaga. 

“Yaya kana ina?”

Shi ne maganar farko da Fawzan ɗin yayi.

“Muneeb ne, muna tare Fawzan.”

“A ina?”

Fawzan ya sake buƙata. Ɗan jim Muneeb yayi, yasan Rafiq na da buƙatar zama shi kaɗai ne in har ya taho wajen shi. 

“Ka ga Fawzan ku ɗan bashi lokaci ya…”

Fawzan bai bari ya ƙarasa ba ya katse shi da, 

“Mun gode sosai Yaya Muneeb, na san Yayana, nasan in yana buƙatar mu bashi lokaci ne ko yana buƙatar mu…” 

Kafin Muneeb ya amsa shi Fawzan ta katse wayar daga ɗayan ɓangaren. Numfashi mai nauyi Muneeb ya sauke yana ajiye wayar ya fice daga ɗakin, kitchen ɗinshi ya nufa ya ɗauko yoghurt roba ɗaya da ruwa ya dawo, Rafiq har ya fito wanka, yana zaune a gefen gadon shi da wani nisantaccen yanayi a fuskarshi, ruwan Muneeb ya fara bashi tukunna ya zauna shi ma, karɓa Rafiq yayi ya sha tukunna cikin disasshiyar murya ya ce, 

“Na gode…”

Kai kawai Muneeb ya iya ɗaga mishi, yana miƙa mishi yoghurt ɗin da ya bita da kallo ya girgiza kai. 

“Jikinka na buƙatar abinci…ka yarda da ni za kai rashin lafiya in baka ci wani abu ba.” 

Karɓa Rafiq yayi ya buɗe yana kafa kai, shanye yoghurt ɗin yayi tas yana jin kamar zai yi amansa. Robar ya miƙa ma Muneeb yana jan ƙafafuwan shi kan gadon ya kwanta sosai. A ƙasa Muneeb ya ajiye robar ya gyara zaman shi. Wayarshi ya ɗauko da ke tare da earpiece a maƙale jiki, ya kama wayoyin yana zurawa a kunnen shi, in bashi da aiki da yawa yakan yi kallo da wayar shi dama, yanzun ɗin ma fim ɗin ya kunna yana ci gaba da kallo ko. Ba maganar shi Rafiq yake buƙata ba, zai bashi shirun da yake so tare da tabbatar mishi yana nan in yana buƙatar yin magana. 

Da yake maganar ba ƙureta yayi ba. Hakan yasa shi jin kamar ana kwaɗa sallama da kiran sunan shi, zare earpiece ɗin yayi babu shiri yana miƙewa, Rafiq ya kalla, idanshi biyu, amma da alama sam baisan me akeyi ba ma, ya tafi duniyar tunani, wucewa falon Muneeb yayi, yana jin gwiwoyin shi sunyi sanyi don idanuwan shi kan Zafira suka fara sauka, bai bari ya ƙare mata kallo ba saboda haramcin da ke cikin hakan, zuciyar shi na mishi wani iri ya mayar da hankalin shi kan Fawzan. 

“Yana ina?”

Numfashi Muneeb ya sauke

“Fawzan…”

Fawzan bai bari ya ƙarasa ba ya taka yana nufar ɗakin da ya ga Muneeb ɗin ya fito, Zafira da Aroob na bin bayanshi. Wani numfashin Muneeb ya ja yana fitar da shi da sauti, kan kujerar falon ya zauna kawai, don suna buƙatar privacy su da ɗan uwansu, zai basu hakan. Ɗakin suka nufa su dukkan su. 

“Yayaaa!”

Aroob ta kira da alamar kuka a muryata, hakan yasa Rafiq kallon su, yana jin yadda ya shaƙi numfashi mai sauƙi a tare da hakan. Tashi zaune yayi yana jingina bayanshi da kan gadon, ƙafafuwanshi na miƙe. Ƙarasawa sukai sosai, Aroob na cire takalmanta ta hau kan gadon ta ɗayan ɓangaren. Sosai ta matsa tana zama gefen Rafiq ta jingina duka jikinta a gefenshi tana kwantar da kanta a kafaɗarshi. 

“Aroob…”

Ya kira sunanta muryarshi a karye. 

“Ba sai ka ce komai ba Yaya…”

Gefen ƙafafuwan shi Fawzan ya zauna, Zafira na kan locker ɗin gefen gadon ta miƙa hannunta ta kamo na Rafiq ta dumtsa tana tabbatar mishi da suna tare da shi a kowanne yanayi. 

“In baka buƙatar mu, muna buƙatar ka Yaya…baka san kamar mota muke ba mu dukkan mu, kai ne injin….wallahi kai ne injin.” 

Fawzan ya ƙarasa idanuwan shi cike taf da hawaye. 

“Bamu da wani amfani in babu kai Yaya, bamu san ya za mu yi rayuwa babu kai ba.” 

Zafira ta faɗi, kai Aroob ta jinjina, tana saka hannu ta goge hawayen da ke fuskarta. 

“Yaya mota babu injinta bata da wani amfani…Ka sani kuma, karka sake barin mu…karka sake.” 

Kai kawai Rafiq ya iya ɗagawa, saboda kukan da ya ci ƙarfin shi, da gaske yana buƙatar su, da jini ko akasin hakan, ƙannen shi ne, duniya duka zata hargitse mishi, rayuwa zata buga shi ta ko ina, yana jin zai yi numfashi da sauƙi in dai suna tare da shi. Sa’adda ya fito daga gida baisan ta inda zai fara dai-daita rayuwarshi ba, zuwan su ya nuna mishi hanya, yana buƙatar riƙe hannayen su a duk takun da zai yi, baida tabbas kan hanyar da zai bi, amma yana da tabbacin zai samu sauƙin tafiyar in yana riƙe da hannayen su.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 39Alkalamin Kaddara 41  >>

1 thought on “Alkalamin Kaddara 40”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.