Skip to content
Part 45 of 52 in the Series Alkalamin Kaddara by Lubna Sufyan

Abuja

Kan gado ya koma ya kwanta, har lokacin yana jin muryar Nuri da yanayin tuhumar da take mishi tare da bashi rashin gaskiya kan abinda yayi ma Tasneem, gaba ɗaya zuciyar shi na ƙara jagulewa fiye da yadda take kafin ya buɗe ma su Fawzan ƙofar. Aroob ce zaune kusa da shi daga gefen gadon, don har lokacin hannun shi na dumtse da nata. Ita kaɗai ce bata yi judging ɗinshi ba, bata bashi gaskiya ko rashin gaskiya ba. Kawai ta nuna mishi tana tare da shi a kowanne daga cikin biyun.

Zafira da Fawzan wajen ƙafafuwan shi suke zaune, su duka sun zuba mishi idanuwa kamar suna son yin rami a jikin shi su shiga su hango abinda yake tunani. Kafin Fawzan cikin siririyar murya ya kira sunan shi.

“Yaya…”

Yadda yai maganar na sa Rafiq ɗin runtsa idanuwa, ba tare da ya buɗe su ba ya ce,

“Sai da kuka min alƙawari ba za ku dame ni ba kafin in buɗe ƙofa. Da kanka ka ce zama za ku yi kawai…”

Kafin Fawzan ya buɗe baki, Zafira ta amsa da,

“Eh haka muka ce, kafin mu san me ya faru…musan me ka yi.”

Aroob sake dumtsa hannun Rafiq ta yi.

“Don Allah ku ƙyale shi.”

“Aroob…”

Fawzan ya kira cike da kashedi yana ɗorawa da,

“Ba ka kyauta ba Yaya. Na san ka sani, wannan ne karo na farko tun tasowar mu da ka so kanka, son kai ba tsarinka ba ne ba, in ba ka duba ta ba ya kamata ka duba yaron da ke jikin ta.”

A hankali Rafiq ya buɗe idanuwan shi da suka rine saboda tashin hankali da kuma kukan da ya yi. Ga kanshi da bayan ciwon da yake mishi a cunkushe yake jinshi, kamar iska na kaikawo a ciki, yanzun kuma komai yayi tsaye cik, sam bayajin wani sarari a cikin kan nashi. Maganganun Fawzan ɗin na ƙara mishi zafi.

“Zan je gobe In sha Allah in dawo da ita, ko ni da Nuri.”

Can ƙasan maƙoshi Rafiq ya ce,

“Kabar maganar nan Fawzan. Don Allah ka barta.”

Zafira ce take girgiza mishi kai. Da gaske ne su dukkan su suna son shi, ƙaunar shi abu ce da basu da kalaman misaltata, amma bata rufe musu ido har basa ganin kuskuren shi ba. Wannan karon kam ya yi kuskure, yana buɗe bakin shi da kalaman Tasneem na gida tasan ya yi kuskure babba, kuskuren da take addu’ar a yi sauri a gyara kafin lokaci ya ƙure mishi. Ba zata fara misalta yadda rayuwarshi take a hargitse ba yanzun, shi yasa ba zata barshi ya ƙara hargitsata ba, nan da yan kwanaki zai gane babban kuskuren da ya yi na korar Tasneem ɗin, kuma bata jin zai yafe musu in yasan basu yi ƙoƙarin hanashi ba.

“Yayaa karka yi haka, lokaci zai ƙure maka, karka ƙara hargitsa komai.”

Zafira ta faɗi muryata na karyewa. Hannun shi Rafiq ya zame daga na Aroob yana miƙewa zaune tare da jingina bayanshi da jikin gadon ɗakin.

“Komai ya daɗe da hargitsewa in dai tsakanina da Neem ne, don Allah ku ƙyale ni.”

Wannan karon Fawzan ne yake girgiza mishi kai yana faɗin,

“Yayaa…”

Rafiq da ya sauke ƙafafuwan shi daga kan gadon yana sauka daga kai gaba ɗaya na saka sauran kalaman Fawzan ɗin maƙalewa, ƙofa Rafiq ya ƙarasa yana buɗe ta gaba ɗaya tare da miƙa hannun shi cikin yi musu alamu da su fitar mishi daga ɗaki. Kanshi yake ji kamar zai tarwatse, baya so kuma ya yi koma menene a gabansu. Ganin su duka sun zuba mishi idanuwa yasa shi faɗin,

“Ku fitar min daga ɗaki…”

Wasu hawaye ne masu zafi suka zubo ma Aroob, gaba ɗaya cikin kwana biyu rayuwar su ta hargitse, bata taɓa zaton zata kai ranar da Rafiq zai buɗe musu ƙofa yana nuna musu hanya da hannun shi ba, sosai abin ya mata wani iri, yadda ya nuna gaba ɗaya sun takura mishi. Tashi ta yi tana zuwa ta wuce ta gabanshi ba tare da ta kalle shi ba.

“Control ɗina na gab da ƙwacewa, don Allah ku fita, bana so in muku ihu, ku fita ku barni…”

Matsawa Fawzan ya yi sosai kan gadon yana jan pillow guda ɗaya ya matsa ya jingina bayan shi da kan gadon ya rungume pillow ɗin a jikin shi. Ba ihu ba, ko gaba ɗaya Abuja da maƙotanta za su taru baya jin za su iya fitar da shi daga ɗakin Rafiq, duk abinda zai yi sai dai ya yi. Ba zai yi kuskure kuma ya ce ba za’a faɗa mishi gaskiya ba. Shi ya koya musu ganin kuskuren junansu, kuma shiya koya musu gyarama juna kuskure ba tare da tunanin banbancin shekaru ba indai za su yi hakan da babu raini a ciki. Babu abinda zai canza don koyarwarshi ta biyo ta kanshi yau.

“Fawzan…”

Rafiq ya sake kira yana jin yadda har jikinshi ke ɓari saboda ɓacin rai.

“Da ka dawo ka zauna Yaya. Babu inda zanje wallahi.”

Fawzan ɗin ya faɗi yana ƙara gyara zaman shi. Zafira ya kalla ta kauda kanta, idanuwan ta cike taf da hawaye, bata son tashin hankali a rayuwar ta, ko kaɗan bata son tashin hankali, bata kuma son ta ga ran wani ya ɓaci ta sanadinta, takan yi ƙoƙarin kauce ma hakan daidai iyawarta. Ganin da gaske ba zasu fitan ba yasa Rafiq ƙarasawa ya ɗauki pillow guda ɗaya yana saka takalma a ƙafafuwan shi kafin ya juya yana ficewa daga ɗakin.

“Oh Allah na…”

Zafira ta furta tana miƙewa kawai itama ta fita. Pillow ɗin da yake rungume jikin Fawzan ya sauke yana ajiyewa kan gadon ya miƙe, sai dai shi ba fita yayi daga ɗakin ba, banɗakin Rafiq ɗin ya shiga ya watsa ruwa ya fito ɗaure da towel, ɗakin canza kayan Rafiq ya shiga ya zaɓi wanda sukai mishi ya saka. Duk da yasan babu abinda Rafiq ya tsana banda ya saka mishi kaya, baya so, ko dai inya saka karya dawo da su ya ajiye a wajen shi, ko kuma ya bashi kuɗi ya siya irin su. Idan yana jin neman tsokana ne yake zuwa ya ɗaukar mishi agogo, amma kayan sakawa kuwa baya yi, yana gudun faɗan Rafiq ɗin.

Yau ɗin ma a sama yake jinshi shi ma, shi yasa ya ɗauki kayan ya saka, har ya hau gado ya kwanta, ya sake saukowa ya je ya ɗauki socks ɗin Rafiq ɗin ya saka a kafafuwanshi, ya kuma ɗauko agogon da Rafiq ya fi so duk cikin tarin agogunan da yake da su ya ɗaura a hannun shi, don Nuri ce ta siya mishi na murnar zagayowar ranar haihuwarshi, agogon ya fi shekara takwas, amma yana nan, ya ma fi saka shi akan kowanne, don kusan ko yaushe shi yake sakawa. Tukunna ya koma ya kwanta, in Rafiq ɗin ya zo ya sa wuka ya yanka shi. Juye-juye yake ta yi akan gadon kawai, don ko kaɗan ba ya jin bacci, ya ma rasa kalan tunanin da yake yi.

*****

Ba zai ce ga lokacin da bacci ya ɗauke shi ba, lokacin da ya buɗe ido har an fara sallah, da wani irin sauri ya diro daga kan gadon Fawzan, don a ɗakin ya kwana. Banɗaki ya shiga, da sauri-sauri yake ɗaura alwala, rabon da ya rasa sallar asuba cikin jam’i har ya manta. Idan bai tashi ba, Fawzan zai ƙwanƙwasa mishi ƙofa, ko da ya yi aure ma wanda duk ya riga tashi a cikinsu ya ke kiran lambar ɗayar. Har su Aroob ma sukan tashe shi idan sun ga bai buga musu ƙofa ba. Yana fitowa bai jira lalubar wayarshi ba, don baya tunanin ma ya taho da ita jiyan, da gudu ya fito daga ɗakin yana haɗa kafar benen bibbiyu a wajen sauka.

Amman kafin ma ya ƙarasa sauka an sallame sallah, ranshi ya ji ya ƙara dugunzuma, komai na dawo mishi da wani irin yanayi mai wahala. Tsaye yake a wajen, yana shawarar ya koma ɗaki kawai yai sallah, ko kuma ya je masallacin ko nutsuwar mintina ce ya samu. Ya hango Fawzan yana takowa, da jallabiyar shi da yakan saka idan zai fita sallar asuba lokutta da dama a jikin Fawzan ɗin. Idanuwan shi suka sauka cikin na Fawzan ɗin, kallon da Fawzan ya ke mishi ya tabbatar mishi da gangan ya ƙi tashin shi.

“Ina kwana…”

Fawzan ya faɗi don duk yadda ya so ya share Rafiq ɗin ya kasa, yana hango shi tsaye kan kafar benen ya gama tsara yadda zai raɓa shi ya wuce ba tare da ko kallon shi yayi ba, amma ba zai iya ba, tarbiyar da ya basu ta ci ƙarfin fushin da yake ma Rafiq ɗin.

Don da ƙyar ya wuce masallaci ba tare da ya duba ya ga ko Rafiq ɗin ya tashi ba, yana faɗa ma zuciyar shi cewar Rafiq na masallaci, bai tashe shi ba don baya so su takura mishi kamar yanda ya nuna musu jiya. Yana shiga masallaci ya fara dube-dube ko zai ga Rafiq ɗin, da na sanin ƙin tashin shi da bai yi ba yana lulluɓe shi.

“Fawzan ba ka tashe ni ba. Na rasa Subhi, ba ka tashe ni ba, me yasa?”

Rafiq ɗin ya tambaya, yanayin sanyin muryar shi na kashe ma Fawzan ɗin jiki. Amma hakan bai hana shi kallon ƙwayar idanuwan Rafiq yana faɗin,

“Bana so in takura maka ne Yaya…”

Numfashi Rafiq ɗin ya ja a hankali, yana fitar da shi, bai ga laifin Fawzan ba, yana shiga ɗakin shi ya kulle ya kwanta fuskokin su da yadda yai hurting ɗinsu na dawo mishi. Ba don kanshi da ke sarawa ba, kuma da gaske yana buƙatar shirun don ba ya so ya sauke musu abinda yake ji, da tun a daren jiyan zai koma wajen su ya basu haƙuri. Ƙaunar shi ce ta sa su damuwa haka ya sani. Amma ko me yayi musu baya son raini, sun fi kowa sanin wannan. Magana Fawzan ya faɗa mishi, cikin idanuwan shi Fawzan ya kalla yau yake mishi baƙar magana.

“Ka maimata min me ka ce…”

Ya buƙata yana tsayar da idanuwan shi cikin na Fawzan ɗin da dole ya sadda kanshi ƙasa. Girgiza kai Rafiq ɗin ya yi.

“Ka ɗago idanuwan ka Fawzan, ka maimaita min me ka ce …”

Leɓen shi na ƙasa Fawzan ya ɗan ciza yana sauke numfashi, a hankali ya raɓa ta gefen Rafiq ɗin yana wucewa da sauri, duk da Rafiq bai juya ba, yanajin sautin hawan da Fawzan yake ma benen, ya kuma san da gudu yake hawan shi. Juyawa ya yi yana komawa ɗakin Fawzan ɗin ya gabatar da sallar da ya rasa, Qur’ani ya ɗauka yayi karatu sosai, don har wajen shida da wani abu yana nan zaune yana karatu, tun bayajin nutsuwa harta fara saukar mishi. Yana idar da Surar da yake karantawa ya rufe Qur’anin. Hannuwan shi ya buɗe sai dai laɓɓanshi sun rasa da wacce buƙata zai fara.

Gajiyar da yake ji ya sa shi roƙar sauƙi da ƙarfin zuciya, haka yaita maimaitawa har sai da ya ji hannuwan shi sun fara mishi nauyi da alamar gajiya tukunna ya sauke hannuwan na shi. Tashi ya yi yana komawa kan gado ya kwanta, wannan karon da ya rufe idanuwan shi baya ganin komai sai hoton Imaan, sosai ya buɗe zuciyar shi yana neman inda take, don yasan tana can wani waje boye a zuciyar shi, wajen ya mishi nisan da zai gano ta ne. Inda zai tuna su, ko na rana ɗaya, ya tuna yin rayuwa da Samira, raɗaɗin rashin su zai ɗauke mishi hankali daga wannan tashin hankalin da baya jin yana da ƙarfin ɗauka.

*****

Zafira kuwa tana idar da addu’o’in safenta, wanka ta yi tana saka riga da zani na atamfa a jikinta, ko powder bata murza ba, hula ta samu fara tana sakawa akanta ta wuce kitchen. Tunda masu musu aiki, in sukai share-share da goge-gogen su, ɓangaren su suke wucewa, Nuri tun suna yara ita take dafa musu abincin da za su ci da hannunta. Idan aiki ya mata yawa ne ‘yan aiki sukan kama mata wasu abubuwan, sai kuma wanke-wanke. Ko da suka taso tare suke shiga kitchen ɗin da ita su kama mata aiki a madadin ‘yan aiki.

Tana jinjina ma Nuri don Aroob kan ce idan ita take da matsayin Nuri, tana auren mai kuɗi kamar Daddy, babu abinda zata shiga kitchen ta yi. Dariya Zafira takan yi kawai, don ita rayuwar gaba ɗayan ta ma bata ɗauke ta da zafi ba, shi yasa yanzun ma ta zo don ta haɗa musu abinda za su yi kari da shi. Yanayin gidan babu daɗi, bata kuma yi mamaki da ta ga kitchen ɗin babu alamun an ɗora wani abu a cikin shi ba. Hakan ya tabbatar mata da Nuri bata fito ba. Daddy ma tun jiya bata ga giccin shi ba, bata kuma tunanin yana gidan ma, don da dole sai sun sauka sun ci abincin dare gaba ɗayan su a tare.

Fridge ta buɗe, akwai farfesu a ciki kala-kala, don haka ta ɗauko na kayan ciki don ta sake ɗumama shi. Yanke shawara ta yi ta soya musu dankali sai su haɗa da farfesun da shayi . Tana ta fere dankali Fawzan ya shigo kitchen ɗin da sallama. Amsa mishi ta yi tana ɗorawa da,

“Ina kwana…”

“Zaf…”

Fawzan ya faɗi a madadin amsa gaisuwar da tai mishi.

“Me kika dafa? Yunwa nake ji.”

Ɗan murmushi Zafira ta yi mishi, dole su ji yunwa, rabon cikinsu da wani abin kirki tun shekaranjiya.

“Dankali zan soya…”

Shagwaɓe fuska Fawzan ɗin yayi, yana saka ta yin dariya.

“Yaushe dankali zai yi? Don Allah ki bani wani abu, ina Nuri? Na san ta dafa ma Yaya wani abu…”

Sai da ta kashe fanfon da yake zubar ruwa tukunna ta ci gaba da fere dankalin tana amsa Fawzan ɗin da faɗin,

“Nuri fa bata sauko ba, banga alamar anyi amfani da kitchen ɗin nan ba yau…”

Fawzan bai yarda ba, yasan babu yadda za’a yi Nuri bata ajiye ma Rafiq abinda zai karya ba, ko da ba zai ci ba. Da auren shi ma sai ya kira waya ya ce abincin ta yake jin ci, kuma haka zata shiga kitchen ɗin ta dafa mishi, sam abin baya musu wani iri, don sunsan kusancin da yake tsakanin Nuri da Rafiq ɗin. Don haka ya ci gaba da bincike a kitchen ɗin, aikam ya ɗauko wata kular abinci mai guda biyu na silver, buɗewa yayi, ƙamshi na cika mishi hanci. Couscous ne ya ji kayan haɗi a cikin guda ɗaya, ɗayan kuma babu komai, ta saka a cikine don tasan hankalin su ba zai kai nan ba.

Zafira ya kalla yana dariya.

“Me nace miki?”

Itama dariyar take tana faɗin

“Innalillahi… Yaya Fawzan anya Nuri ba tsintomu ta yi ba? Wallahi ɗanta kawai ta sani…”

Kafin ya amsa ta, Aroob ta bangaje shi tana jan kular gabanta. Hannu tasa zata ɗauki nama Fawzan ya buge mata hannun yana janye kular.

“Ya za ki tsoma hannu a abinci haka? Me yasa baki da hankali ne Aroob. Zafira wanne irin kaya ne a jikin yarinyar nan dln Allah?”

Sai lokacin Zafira ta kalleta, rigar wanka ce a jikinta, ta towel mai kauri sosai, da ta tsaya iya kuwaurinta, irin mai igiyar nan a ƙugun. Pink ce rigar har shiga ido take yi, sai takalmanta masu kan kaza a jiki, da wani irin gashi buzu-buzu. Kanta ma irin shigen hular takalmin ce, dukkansu pink ne. Girgiza kai Zafira ta yi.

“Kuma fa tana ɗinka kaya a hakan…”

Juya idanuwa Aroob ta yi.

“Kayan da kike roƙona in ɗinka miki. Yaa Fawzan don Allah ka bari in ɗauka, ƙamshin na ta cika min hanci, yunwa nake ji. Ina nawa?”

Haɗa idanuwa Zafira ta yi da Fawzan suna kwashewa da dariya.

“Abincin Yaya ne wallahi. Nuri zata kashe ku biyun.”

Cewar Zafira da take kwashe ɓawon dankalin da ta gama ferewa tana zubawa a abin sharar da ke cikin kitchen ɗin. Numfashi Aroob ta sauke 

“Duk wannan shakuwar tasu a cemun Yaya bai fito daga cikin Nuri ba. Yazan fara yarda da maganar nan…”

Aroob ɗin ta ƙarasa tana sakawa dukkansu jikinsu yayi sanyi. Murfin kular Fawzan ya ɗauka yana mayarwa ya rufe, har ranshi kafin maganar Aroob ɗin ya yi niyyar cin abincin, amma yanzun kam ba zai iya ba, Rafiq na buƙatar dukkan wani tabbaci da zai samu. Wani irin shiru kitchen ɗin ya yi, banda Zafira da ke yayyanka dankalinta ba ka jin kowanne sauti, ganin hakanne yasa Fawzan faɗin,

“Ba wata wuƙar ne in taya ki yankawa?”

Basu ji zuwan Rafiq ba, ko takun tafiyar shi basu ji ba, sai sautin muryar shi da ya ce,

“Na san likita ne kai, ka iya ɗinki da su komai haka, amma bana son ganin jini ko kaɗan ka sani. Kuma ina son yatsuna duka, bazan iya baka ko ɗaya a ciki ba…”

Aroob kallon shi take yi, fushi take mishi sosai, amma ganin shi da ta yi yanzun ta nemi fushin da take mishi ta rasa. Musamman maganar da yayi, akwai ban haƙuri a yanayin muryarshi. A shagwaɓe ta ce,

“Yayaa….”

Tana ƙarasawa kusa da shi, da sauri ya matsa baya.

“Aroob tsaya nan. Tsaya nan…”

Daga Zafira har Fawzan dariya suke yi, don kowa yasan yadda Aroob take runguma, inta matseka sai ka ji kamar haƙarƙarinka za su karye, ba zaka kirata siririya ba, don ba kalar jikinsu ɗaya da Zafira ba, amma in ta riƙe ka za ka yi mamakin ƙarfinta. Dariyar take itama duk da idanuwanta cike suke da hawaye. Hannu Rafiq ɗin ya miƙa mata tana saka nata ciki, ɗan dumtse hannun nata yayi alamar ya fahimta tukunna ya saki yana faɗin,

“Ni kaɗai nake jin yunwa ne?”

Ba wai don yana jin yunwar ba, sai don yanayin su ya nuna mishi su suna buƙatar abincin, kuma suna buƙatar kulawar shi fiye da kowanne lokaci.

“Nuri ta dafa maka abinci. Mu ne dai kawai.”

Dariya yayi yana ƙarasawa inda Fawzan yake tsaye, plate ya ɗauko ya ja kular yana juye couscous ɗin a ciki, cokali ya saka, kafin ya ɗauko wani Aroob ta ƙaraso ta ɗauki wannan ta ɗibo ta saka a bakinta, lumshe idanuwanta ta yi abincin ya mata daɗi sosai.

“Allah Nuri tana yin son kai da yawa…”

Ta faɗi tana sake ɗibowa, wannan karon ta ciko cokalin taf. Su uku suka ci, don couscous ba abincin Zafira ba ne, dankalin ta fara soyawa. Tana kallon drama ɗin da suke yi, tana jinta kamar a mafarki har lokacin, ita ce a gida, ba tare da tunanin kowanne lokaci Omeed zai shigo ba, kowanne lokaci zata iya abu kaɗan da zai ja mata dukan da saita kwana da zazzaɓi. Sai dai duk da kwanciyar hankalin da ta samu ta wannan ɓangaren bai hanata jin nauyin auren Omeed har cikin zuciyarta ba, ko da za su fita su je gidan Muneeb wajen Rafiq ɗin tana jin yadda take ɗaure da igiyoyin auren shi, da yadda zunuban da ta ɗiba na rashin neman izinin shi kafin ta fitan ke danne ta.

Taɓa mata kafaɗa ta ji an yi, hakan na katse mata tunanin da take yi.

“Dankalin ki zai ƙone…”

Rafiq ya faɗi yana mata murmushi, tana ganin yadda bai kai cikin idanuwan shi ba. Kai ta jinjina mishi tana kwashewa ta zuba wani, a kitchen ɗin suka tsaitsaya su dukansu, duk da babbane, don har da wajen cin abinci na mutane shida a ciki, ba su yi niyyar zaman ba ne ba, asalima Fawzan ya ɗaga waya yana kiran Naadir daya amsa kamar zai yi kuka, a kuagauce ya faɗa musu ba zai samu zuwa ba sai ƙarshen satin, zai yi magana da su sosai yana abune. Zafira na gamawa anan kitchen ɗin suka zauna, su dukkan su duka suka haɗu suna karyawa tare a wajen cin abincin da ke kitchen ɗin. Tukunna suka fito babban falon gidan suka zauna, hira suke suna ƙoƙarin rage damuwar da su dujkansu suke cikinta.

Nan su kai zamansu a falon, don wani Indian film (Raabta) ne da aka saka a bollywood suka nutsu su duka suna kallo, ya ja hankalin su sosai, baka jin komai sai maganar su in sun taso ma Aroob da faɗa, sam ita bata so ana kallo ayi shiru ba’a magana, duk abinda aka gani a tatttauna akai, bata ƙi a saka pause a yi magana ba, tukunna a ci gaba da kallo, amma su sai su ce dole sai dai ayi shiru, sam ba zata iya ba.

“Nifa na hango kashe shi za’ayi…kuma nama fi sonta da wancen guy ɗin…”

Harara Fawzan ya watsa ma Aroob.

“Wai don Allah ki koma ɗakinki ki kalla acan mana…”

Runtsa idanuwa Rafiq yayi ya gaji da faɗan da suke yi tun ɗazun, don da gaske kallon yake yi, sosai kuma ya ɗauke mishi hankali daga damuwar da yake ciki.

“Wallahi ku dukkanku kun kusan barin falon nan, kowa zai koma ɗakin shi tunda ba za ku yi mana shiru…”

Shirun suka yi, Fawzan na watsa mata harara, ita kuma ta juya mishi idanuwanta. Magana zai yi sallamar Daddy ta sa shi yin shiru, su dukkansu suka amsa sallamar a tare, amma idanuwan Daddy kan Zafira suka sauka, bai kuma kula da sannu da zuwan da suke mishi ba, takowa yayi yana shigowa cikin falon, tare da saka hannu a cikin aljihunshi ya zaro wata takarda yana miƙa ma Zafira da ta sa hannunta ta karɓa tana kallon shi cike da rashin fahimta.

“Aurenki ya ƙare da Omeed. Takardar sakinki ce Zafira…”

Jikinta ko ina ɓari yake, batasan asalin yanda zata fassara abinda take ji ba. Bata kuma san lokacin da ta miƙe tsaye ba, sai jinta ta yi ta zagaya hannunta tana riƙe Daddy tare da fashewa da wani irin kuka. Duk wani tsoro da rashin tabbaci na rayuwa da ta shiga daga aurenta zuwa yanzun yana dawo mata sabo. Riƙe ta Daddy yayi a jikin shi sosai yana jin girman kuskuren da yayi ma rayuwarta da yai alƙawarin yin amfani da duk wata dama da Allah zai ara mishi tare da ita a nan gaba wajen gyara mata wannan kuskuren.

“Daddy na gode… Na gode sosai.”

Take fadi tana ɗagowa daga jikin shi, fuskarta ta goge duk da hawayenta bai daina zubowa ba. Tana miƙa ma Rafiq takardar da ke hannunta, karɓa yayi ya buɗe, ya ga saki ɗaya ne, amma baisan lokacin daya sauke wani irin numfashi mai nauyi ba. Inda Daddy bai raba auren nan ba, da kanshi zai san yadda yayi ya yanke shi, don zuciyarshi zata daina bugawa kafin ya bari Zafira ta koma zaman aure da Omeed.

Da murmushi a fuskar Rafiq ɗin ya kalli Daddy yana ɗan ɗaga mishi kai, saboda ba shi da wasu kalamai da zai yi amfani da su. Daddy murmushin da Rafiq yai mishi ya mayar mai yana mayar da hankalin shi kan Zafira da faɗin,

“Ki ɗauki dukkan lokacin da kike buƙata Zafira, nasan yayi kusa in miki maganar aure, amma ina so kisan kowa za ki aura zai zama zaɓinki ne, in har na tabbatar zai riƙe min ke da daraja zan bashi wallahi.”

“Daddy…”

Zafira ta faɗi kukan farin ciki na sake ƙwace mata. Kai ya ɗaga mata yana sake tabbatar mata da maganar da yayi. Hawaye na zubar mata take jinjina mishi kai, tana jin kamar an sauke mata wani irin nauyi da yake danne da ƙirjinta.

“Rafiq komai zai yi daidai, ka yarda da ni, zan gyara muku duk abinda zan iya da yardar Allah…”

Daddy ya faɗi yana son su ga kalar ƙaunar da yake musu, da yadda zai iya yin komai akan abinda zai same su zai fara bi takan shi kafin ya bar hakan ya faru. Har cikin ranshi bai taɓa haɗa ƙaunarsu da komai ba, don su ɗin har cikin ƙasusuwan jikin shi yake jinsu. Musamman Rafiq, tabbas bai fito daga jikin shi da Nuri ba, amma yana jinshi a ko ina na zuciyarshi, yana jinshi kamar yadda yake jin su Fawzan, ko ya ce fiye da haka ma, don a ko ina nashi Rafiq ya fara samu kafin su, shi ya fara shayar da shi abinda yake tattare da kyauta ta samun yara.

Haka takardun shi da abubuwa da dama Rafiq ɗinne akai, baisan me kowa zai ce ba, bai kuma damu ba, Yafindo zata iya kiran Rafiq ya fito daga cikinta, amma za’ai yaƙin duniya kafin wani ya ce zai karɓi Rafiq daga wajen shi. Wannan abu ne da baya tunanin ma, don ba zai yiwu ba. Ganin sunyi shiru suna kallon shi yasa shi faɗin,

“Ina matata?”

Hakan na saka su dariya su dukkan su.

“Daddy…”

Aroob ta faɗi tana dariya.

“Da gaske nake ina kuka kai min mata?”

Daddy ya sake tambaya yana ƙwala mata kira.

“Hafsatu!”

Tare da wuce su Rafiq ɗin, don ba zai iya jira ta fito ba, yana buƙatar sauke idanuwan shi kan matarshi, duk yadda bai haɗa su da komai ba, wajen ta daban ne, har abada babu abinda zai zo ko kusa da inda take ballantana ya kwatantasu, in tana waje ko yaran baya gani, idanuwanshi akanta kawai suke. Ƙaunar da yake ma matarshi ta dabance.

Waje Zafira ta samu ta zauna, sun ma manta da fim suke kallo, don Daddy na yin sallama Rafiq ya tsayar da film ɗin, su dukkan su Zafira suke kallo.

“Yaya gani nake kamar mafarki, ka ce min ba mafarki nake ba.”

Zafira ta buƙata, muryarta na sake karyewa. Gyara zama Rafiq yayi kan kujerar yana miƙa mata hannun shi, ƙarasawa ta yi ta riƙe tana zama ƙasa kan kafet ɗin, takardar da ke hannun shi ya ajiye gefe yana kama ɗayan hannun nata.

“Ba mafarki kike ba, kina jina? Auren ki da Omeed ya ƙare Zafira, ki yi bacci ba tare da tunanin shi ba. Bana so ki sake bashi wannan muhimmanci don bai cancanta ba…”

Kai Fawzan ya jinjina.

“Amman ina son dukan shi har yanzun wallahi.”

“Jiba Yaya Fawzan fa. Hmm zuwa ɗaya zai maka duk shekarar nan babu likitan da zai gano matsalarka”

Haɗe fuska Rafiq yayi, sosai yake ƙoƙarin ganin dariya bata kubce mishi ba, Aroob ta ɗora da,

“Banda haƙoranka da za kai sallama da wasu, kai kanka saika rasa gane meye asalin matsalarka…”

Runtsa idanuwan shi Rafiq yayi, Fawzan na faɗin,

“Ke banza marar hankali. Abin aiba a girman jiki yake ba…”

Wannan karon Zafira ce tai magana bayan ta goge fuskarka.

“Nizan baka labari Yaya…”

Kai Fawzan ya jinjina

“Yawwa Zafira, ita wannan mahaukaciyar ba zata gane ba a jiki abin yake ba…”

Kai Zafira take girgiza ma Fawzan ɗin don ta ga alamar bai gane me take nufi ba.

“Baka gane ba Yaa Fawzan, wallahi in ya riƙe ka har asthma ɗinka sai ta gudu ta barka…”

Wata irin dariya Rafiq ya kwashe da ita, kafin Aroob ta tayashi, sosai suke dariya, Zafira kuwa ta kasa, don ba za su gane ba, basu taɓa zuwa hannun Omeed ba da sun fahimci abinda take nufi, Fawzan kuwa ya gyara zamane kawai ya turo laɓɓanshi, sam abin bai bashi dariya ba. Don har ranshi yake jin yadda tsaf zai iya dukan Omeed, don ƙarfi a zuciya yake. Amma su dukkan su ba za su yarda da hakan ba. Miƙewa Rafiq yayi har lokacin yana dariya, dan ya ga lokacin sallah ya gabato, bashi da tabbas akan abinda yake faruwa da shi ko wanda zai faru da shi, amma yana da tabbas in suna tare da shi zai gano farin ciki a duk inda ya shiga, za su bashi dalilin da zai ji sauƙi a cikin kowanne ƙunci.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Alkalamin Kaddara 44Alkalamin Kaddara 46 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×