Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Almajirai Ma 'Ya'ya Ne by Habiba Maina

GODIYA

Bismillahirrahmanirrahim!

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su tabbata ga Manzon Allah Annabi Muhammad (S.A.W) ina godiya ga Ubangiji da ya bani dama na rubuta wannan labari har na wallafa, godiya ta a gare shi, babu missaltuwa.

DOMIN MAHAIFIYA TA DA YAN’UWA NA

Ina alfahari da ke Mahaifiya ta, bani da kamarki, dukkan abinda zan samu a duniynnan dalilin addu’ar ki ne, kin yi mini komai, Allah ya biya ki da gidan aljanna! da ya yan’uwa na, waɗanda suka bani goyon baya suka karfafa min gwiwa, ina matuƙar godiya Allah ya saka muku da mafificin alkhairi.

INA YABA MUKU MUTANE NA

Ban manta da ku ba abokan arziki waɗanda nake tare da su da waɗanda Allah ya haɗa Ni da su ta social media, da ma waɗanda ban san su ba amma sun kasance masu karanta littattafai na, babu shakka kun zame min kamar yan’uwa na jini domin, na sami kwarin gwiwa da shawararwari da Soyayya a gurinku wajen rubuta littafi, ina son in sanar da ku cewa ina matuƙar alfahari da ku, domin sai da goyon bayanku ne , zan iya kai wa wani mataki ,Allah ya bar zumunci.

GODIYA TA MUSAMMAN

Ina so in miƙa godiya ta musamman, ga wannan manhajar ta Bakandamiyahikaya, da ta bani daman zama ɗaya daga cikin membobin ta, ina matuƙar godiya Allah ya saka da alkhairi.

GARGAƊI

Ban yarda a yi anfani da wannan littafi ba, ko wani ɓangare, ko ta fannin film, ko wallafa shi a wata kafa ba tare da izini na ba. Yin hakan babban laifi ne kuma duk wanda ya saɓa dokar zai fuskanci hukunci mai zafi.

FAƊAKARWA

Wannan labarin na Almajirai Ma Ya’ya Ne, kageggen labari ne, ban rubuta shi don ɓatanci ko cin zarafin wani ba, dukkan abinda kuka karanta Ta kowacce siga, kagegge ne, ba da kai ake ba kuma kuskuren da nayi a ciki Allah ya yafe min.

SADAUKARWA

Na sadaukar da littafin nan ga dukkanin ɗaukacin musulmai ga dukkan wanda zai amfana.

TAKAITACCEN BAYANI AKAN LABARIN

Almajirai ma ‘ya’ya ne labari ne akan wasu yara biyu Sa’idu da Halliru wanda iyayen su suka kai su karatu tun suna ‘yan yara ƙanana, suka zubar da su ba tarare da sun nuna tausayi, da kulawa ba.

Kamar yarda iyayen Halliru suka kaishi karatu suka jefar, ba tare da sun sake zuwa duba shi ba tun yana ɗan shekara biyar, har ya kai saurayi. sanadiyar haka ne yasa ya shiga halin sace-sace.

Haka kuma Sa’idu wanda yake Maraya ne ƙanin mahaifin shi ne yake riƙe da su amma tsabar rashin tausayi ya kaishi almajiranci, ya watsar da shi, da yan’uwansa.

gashi shi Sa’idu yaro ne da bai wuce shekara bakwai ba sanadiyar haka ne ya faɗa mugun hannu sakamakon yaudarar sa da wani mutum ya yi da sadaka, ya ja shi ya yi masa fyaɗe.

Sannan kuma dangane da yarda wasu jama’a ke nuna halin ko in kula ga almajirai, wai a cewarsu,

“iyayen sune suka wulaƙanta su da suka kawo su almajiranci.”

Daga karshe dai Hajiya Maryam wacce ta nuna tausayi ga yaran nan biyu ta tallafa, ta nuna wa jama’a yarda idan aka taimaka, rayuwar su zata inganta.

Babi Na Daya

Wani ihu ne da ya bige min kunne, cikin barci na kamar sarewa.

ihu ne na ɗan ƙaramin yaro, da yake cike da tsoro.

wani razana nayi da yasa na miƙe daga barcin, ba tare da na sani ba, domin ihun, ya cike duk wani sashi na ɗaki na kamar sabuwar ganga.

babu shakka, duk mai barci cikin hayyaci bazai gagara ji ba.

Nan take gumi ya yanko mini da yasa na jiƙe kamar wacce aka tsoma a kogi, ƙafafuwana kuwa sun ƙasa riƙe Ni, domin dukkan sassan jiki na rawa suke, tsabar bugun da zuciya ta keyi.

wani dishi-dishi, nake gani domin zuciya ta na Bugunda ke taɓa jijiyar, da ke haɗe, da idanuna. sai dai ban sake jin ihun ba, daga nan, sai wani tsoro ne ya mamaye Ni.

“Shin kunne na ne ya jiyo min ihun? Ko kuma dai da aljan, nayi gamo?” Wannan, tambayar nayi Wa kaina.

“Subuhanallah! Ni kuwa me zai sa in yi tunanin aljan, ne? to idan ɗan adam ne, me zai sa ya fito cikin wannan daren?”

Cikin tambayoyinnan ne, na motsa domin duba agogo na ƙarfe nawa? da lalume na isa ga kofar, har sai da nayi tuntuɓe na buge ƙafata domin duhu, da ya rufe mini gani. don kuwa, bana iya banbance gabar da yamma, balle kuma kudu, da Arewa.

Wani ɗan ƙara nayi domin zafin bugunda na ji. take na kuma rufa baki na Saboda tsoro, na manta cewa, gida na gida ne da yake da mai gadi.

Cikin wannan, saƙe-saƙen, na tsoro ne ya sake zuwa mini, amma haka na daure na laluma jikin ɗakinnan, nayi Sa’a na taɓo inda makunnin, wutan yake. garin kunnawa kuwa, sai wani kakkausar ihun, nasa na sake ji kamar wanda ake yankawa, wani firgita na yi da hannu na ya kunna wutan, ba tare da umurnin hannu na ba, sannan na buge flower pot ɗinda ke kusa da makunnin wutan. sai fash…! Kake ji ya fashe.

Ya Allah! Wannan yanayin ya zame mini kamar wanda aka tsare kan laifin kisa, ban san sanda hawaye, suka zubo mini ba.

Juyawa na yi na dubi ‘ya’ya na da ke barci kan gado, Ummi da Amir. naji tsoro matuƙa da faɗiwar flower pot ɗinnan, saboda gudun tashin su daga barci, domin rana ce ranar lahadi, ranar da kowane bil’adama ke kwanciya da wuri domin gudun makara wajen zuwa makaranta, da aiki. sai dai babu wanda ya motsa, da alamu dai sunyi nisa a barci.

Ajiyar zuciya nayi na kuma hanzarta kallon lokaci, domin hankali na ya kasa kwanciya. saboda babu wata uwa a duniya da zata ji ihun yaro, kuma hankalin ta ya kwanta.

Zabura nayi, na fice ba tare da na sake jin ko ɗigon tsoro ba, na nufi ɗakin Alhaji.

ƙofar sa na ƙwanƙwasa, kuma na ƙara, amma sai naji shiru…!, cikin yunƙurin ƙarawa da zan yi ne ya buɗe ƙofar.

Fitowa ya yi cikin gigin barci, sai dai hawaye da ya gani a idanuna, yasa ya wats’tsake ba tare da ya shirya ba. ya tambaye ni na fayyace masa komai, ina cikin yi masa bayani kuwa, sai ihun muka sake ji ya yi me ƙarfin gaske, tabbas idan maƙogoron sa igiya ce, to ta tsinke, ko da kuwa igiyar ƙarfe ce.

Razana mukayi daga ni har Alhaji. wani juyawa da baya Alhaji ya yi kamar zai koma tsabar firgita, daga bisani kuma, ya nutsu a matsayin shi na magidanci, ya tsaya da cewa,

“Innalillahi wa innailairraju’un! Babu shakka, maryam Yaronnan, yana buƙatar taimako….!”

Mai gadi ne da ya zo kusa a sa’inda ya jiyo ihun yaron, shima ya goyi bayan maganar Alhaji. ya kuma bada shawara Akira jami’an, tsaro. sai dai Alhaji ya ce, Yakamata a kama mai laifin kafin a ƙira su, domin idan ka taimaki rai guda, kaman ka taimaki ran al’umma ne baki ɗaya.

Wani farin ciki ne ya turniƙe Ni da jin wannan, batun nasu. saboda ina matuƙar son taimaka wa jama’a, kuma ina son mai taimakon jama’a!

Daga nan kuwa, suka ɗauki hanya suna ta dube-dube, amma shiru…!, babu alama kuma unguwar, ita ma shiru…!, babu motsin kowa, gashi lokaci, ya soma ƙurewa.

ƙarfe biyu da rabi na asuba, daga nan sukayi shawaran komawa, don basuyi dacen wurin ba. Cikin wannan, tunanin ne kwatsam! suka ji gurnanin yaron, a wani kango da ke gefen su. razana sukayi sannan ila mai gadi Ya ce,

“Babu shakka…! gurnanin nan na yaronnan, ne, don haka, muyi gaggawar ɗaukan mataki.”

Daga nan, suka laɓe a jikin garu, sukayi nasarar shiga, sannan sukayi nasarar kama shi dumu-dumu, yana yi wa yaron fyaɗe, Daga nan suka ƙira jami’an tsaro.

Bayan kammala komai ta ɓangaren jami’an, tsaro da likitoci, duk sunyi iya ƙoƙarin su ta fanin aikin su. kasancewar ina gida ban san yarda ake ciki ba, yasa ila ya zo ya taho da ni. Ai kuwa, ya faiyyace min komai…, cikin tausayawa na ce, muje. amma abun mamaki shine, sai taro muka gani da ya tare hanyar wucewa, Samari sunyi dandazo…! wasu na cewa, “Barawo ne ku kashe shi mu huta…!, domin ya gallabe mu da sata a unguwar.”

Da jin haka kuwa, na hanzarta, na shiga tsakani, na basu haƙuri sosai…,
sannan na basu shawara da idan haka ta faru, su daina ɗaukan doka a hannun su. sun kuwa ɗauki shawara ta, domin kasancewata mai kirki a gare su a unguwar, da taimako ga masu bukata. bayan haka, na ɗauki saurayinnan, na kai asibiti.

Bayan farkawar yaron, jami’an tsaro sukayi masa tambayoyi kamar haka,

“Mene ne sunanka? a ina iyayen ka suke? shekarun ka nawa? sannan ya akayi ka shiga hannun wannan, mugun mutumin?”
Sai dai abun tausayi, yaronnan ya shaida musu cewa,

“Sunana Sa’idu shekaruna bakwai, ni Maraya ne iyayena duk sun mutu, kanin mahaifinmu ne ke riƙe da mu, shine ya kawo mu almajiranci, da ni da ‘yan’uwana biyu.

Wannan, mutumin kuma ya kasance mai bani sadaka, shine ya ce, da Ni idan dare tayi in zo in karɓi abinci, da naje karɓa, sai Kuma ya ce, mini in rakashi sayan abu, a nan ne ya kaini ya ɗaure ni. amma sai dai, malaminmu bai san duk abunnan da ke faruwa ba.”

Ta ɓari ɗaya kuwa, Ni nake kula da saurayin nan da aka daka, kan sata. tambayoyi nayi masa akan halinda ya tsinci kansa. sai dai abun mamaki, shima ya sanar da ni cewa,

“Sunana Halliru ni almajiri, ne an kawo Ni karatu ina ɗan shekara biyar, daga nan iyayena basu sake waiwayo Ni ba, har na kawo i’yau. kuma ban san garinmu ba, balle in nemi su. shima malamin namu da kansa ya ce, bai san inda garimu yake ba, balle iyayena. domin an kawo ni ne ta hannun, wani malami. kuma shi malamin yanzu, ya rasu. rashin sana’a, ne ya sa ni cikin halin sace-sace.”

Bayanan Halliru sun ɗaga mini hankali matuƙa! domin kullum in zani aiki, sai na haɗu da yara ‘yan shekaru, uku, huɗu, biyar…., suna Bara akan titi, cikin rashin kulawa. shin me ya kawo haka?

Sanadiyar haka ne yasa na buɗe gidauniyar taimakon almajirai, don haka, na tara mata iyaye domin basu shawara akan taimako, musamman almajirai. nayi musu bayani kamar haka,

“Almajirai ma ‘ya’ya ne kamar ‘ya’yan kowa. suna da iyaye da ma dangi. sai dai rashin iyaye ingantattu ne, ya jefa su cikin irin wannan, halin….

Wasu marayu ne babu mai kula da su, wasu kuma iyayen ne da kansu, suke kawo su. babu shakka, neman ilimi ko wane iri ne yana da matuƙar muhimmanci. amma kawo yara ƙanana, cin zarafin yara ne. Wa’yanda suke da wayo ma, yana da kyau, ana basu kula. malaman kuma, yana da kyau, suna fahimtar da ɗaliban nasu yarda za suyi mu’amala, da masu basu sadaka. Sannan magana ta ta karshe, na buɗe gidauniyar nan ne saboda almajirai, zanyi iya kokari na wajen kula da su fisabilillahi!

Ina Kuma bamu shawara iyaye, mu taimaka musu, mu nuna musu so, tamkar ‘ya’yan mu. ba kamar yarda wasu ke cewa,
“Ba zasu taimaka ba, ai ba su suka kawo su ba, iyayen su ne suka wulakanta su…..”

Hakan, sam! ba daidai bane, muma suna bukatar taimakon mu. kada kuma Musa ido akan gwamnati ita kaɗai, matuƙar muna neman gyaruwar al’ummar mu, idan muka haɗa ƙarfi da ƙarfe, zamu kawo ƙarshen dukkan matsalolin mu.”

Na dakata da faɗin haka, na kuma ƙare magana ta da cewa,
“idan, ka taimaki wani, kaima Allah zai taimake ka.”

Bayan wasu shekaru kuwa, gidauniyar tawa tayi tasiri matuƙa acikin al’umma, mutane da dama, sun bani haɗin kai. yanayin karatun yara kuwa ya yi kyau…! ana karantar da su hatta boko.

Daga ƙarshe dai, bayan karatun addini, Halliru ya zama babban jami’in tsaro, mai kare hakkin jama’a da tsaron su. yayinda kuma shi Sa’idu, yana jami’a, inda yake karatu ta fannin ilimin zamantakewa, da na laifuka.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×