Skip to content
Part 1 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Sadaukarwa ga marubuciyar Arziƙi. Yau na cika alƙawarin da na ɗauka. Wannan page ɗin naki ne ke ɗaya, Kahdija Candy.

Bismillahir Rahamanin Rahim!

Babi Na Daya

Ƙarar homm ɗin mutar da ta ƙara ji a karo na babu adadi ne ya sa ta bar naiman abun da da take yi ta nufo hanyar waje har ta na haɗawa da sassarfa. Zaune ta same shi a cikin motar ya na kallon hanyar fitowa da ga cikin gidan ya cika ya yi fam kamar zai fashe. Fuskarsa ta ƙara kalla a karo na biyu taga yanda ya haɗa rai kaman haɗuwar gaggarumin hadari a cikin watan ogosta. Da sauri ta buɗe ƙofar mai zaman banza ta shiga tana cigaba da satar kallonsa. “I’m sorry honey wayata na ke ta naima tun ɗazu bansan inda na jefata ba ne shi yasa na daɗe. Ameera ta faɗa ta na gyara zamanta a cikin motar. Ko kallonta bai yi ba yaja mota mai gadi ya buɗe musu get suka ɗauki hanya. Har suka iso babban asbintin babu wanda ya ƙara magana acikinsu. Kallonta ya yi a karon farko tun bayan shigarta cikin motar ya ce “Shiga ki fito ina jiranki idan kinje ki tsaya naiman wayarki karki fito da wuri.Ya faɗa ya na kawar da kansa daga gareta ganin ta kafeshi da banyan idanunta. Kallonsa ta yi ganin har yanzu fuskarsa a haɗe ta ke da ga ɗan abun da ya faru. “Wai wannan haɗe fuskar na meye dan Allah? Na baka uzuri nafa, please dan Allah muje tare wallhi ni kunya zuwa ni ɗaya nake yi please honey. Ta faɗa ta na kamo hannun angon nata cikin shagwaɓe murya. Kallonta ya yi ganin yanda ta ƙara haske ga y’ar rama da yagani a jikinta. Sosai ya ke lura da yanayinta kwana biyu ganin duk ta canja, hakan ne ya sa ya ce dole sai sunzo asibiti domin yanayin nata ya na bashi mamaki. Yana son matarsa sosai kaman yadda yasan itama tana sonsa, sai dai ya lura saboda zuwa asbintin nan da bata so ne yasa take son ɓata masa rai! Badan shine ya matsu da zuwa asbintin nan ba da ba zai shiga ciki ba. Kuma yasan tunda har ta fara haka tofa ko ya barta ita kaɗai ba zuwa zatayi ba. “Fito muje” shine abun da ya ce ya na cire hannunta a jikinsa sannan ya fita itama ta fito suka jera izuwa cikin asbintin.

Kasancewar likitan abokinsane ya sa tun kafin su isa cikin asbintin ya kirasa ya na sanar da shi isowarsu. Koda suka isa gaban likitan bayan sun gaisa Adam ya fara masa maganar abun da ya kawo su. “Ta yi fari ga wani irin taurin kai da takeyi yanzu ga rama idan na tambayeta ta ce wai ita lafiya ta ke, abun da yafi bani mamaki ma shine yanzu abu kad’an za’a mata ta fara masifa, ƙunci kamar ba itaba, to tun ba yau ba nake mata maganar muzu asibiti taƙi, sai yanzu na samu ta yarda, inaso a dubata idan ma ta kama gado za’a bamu to. Likitan yayi dariya ya na faɗin babu batun bada gado in sha Allah abun arziƙi ne. Koda likitan ya sa tayi fitsari domin ya gwada ko ciki ne gareta domin abun da ya fara zuwar masa kenan lokacin da ya haɗa ido da ita. Ita kuwa Ameera tashi ta yi ta nufi toilet ɗin dake cikin ofecc ɗin domin kuwo fitsarin. Gwajin farko ya nuna tana ɗauki da ciki. Tsabar murna Adam bai san lokacin da ya rungume likintan ba. Ita kanta Ameera abun yazo mata a bazata domin bata taɓa kawo ciki gareta ba. Sosai farincikin ta ya fito fili ta na kallon Adam kamar wanda ya fita daga haiyacinsa tsabar farin ciki. Kamota yayi a gaban likitan ya fara surfa mata addu’a ya na shafa cikin kamar ya samu kan motarsa. Sosai yake cikin farin ciki kana ganinsa zaka gane hakan. Riƙo hannuta ya yi suka fito bayan likitan ya gama sanar dasu yanda zasu kula da cikin ɗan wata guda, harda sanar da Adam cewa har yanzu cikin bai bar lokacin laulayi ba sai yayi haƙuri . Adam kuwa ji yake ba ma laulayi ba koma me ye zai jure a kan wannan cikin.

A cikin motama dai da hannu ɗaya yake tuƙi hannu ɗaya kuma ya rike hannunta kamar wacce zata gudu. Saida suka tsaya suka sayi magani kafin suka wuce gida. Suna isa gida ya fito da sauri ya buɗe mata ƙofa ta fito ta na jinta kamar wata sarauniya, ga mukuma yanayin ƙuncin da take yawan tsintar kanta a cikin kwana biyun nan. Haka ya rike hannunta suna tafiya a hankali har suka isa cikin ƙaton falon nasu. Zaunar da ita ya yi a kan kujera sannan ya nufi kicin ya ɗauko rowa mai sanyi ya buɗe ya kafa mata tana sha ya na kallon yanda ruwan ke shigewa ta maƙogaronta, yana ji a ransa yanzu wannan ruwan zai dangana ga yaronsa dake wannan cikin, sosai murmushi ya samu mahalli a kan fuskarsa. Bayan ta gama sha ya zauna kusa da ita ya ce “Jikina yana faɗa mini ba lafiya kike ba ashe dai rabone mai girma a tere da ke. Dariya ta yi tana jin barci na son kamata. Wayarsa ya ciro ya fara kiran ƙanwarsa kasancewar mahaifiyarsu ta rasu daga shi sai ƙanwar tasa ka ɗai suka rage, mahaifinsu kuwa tun ƙanwar tasa na ƙarama ya rasu. Ta na ɗagawa ya ce

“Kadija albishirin ki?

“Goro fari tas-tas” ta faɗa cike da zumud’in son jin mai yayan nata zai ce mata domin tasan da jin haka to abune mai daɗi. “

Ameera na dau’ke da ciki har na wata guda.

Da ƙkarfi kadija ta kwaɗa wani uban ihu ta na cewa “Da gaske Yaya?

Bai ko bata amsa ba ya kashe wayar yana kallon Ameera da har barci ya fara tafiya da ita. Afili ya ce “A she ba a banza ba wannan saurin fushin naki da kikeyi na kwana biyu. Ganin haka yasa ya ɗauketa gaba ɗaya ya nufi kicin ɗaki da ita ya kwantar da ita sannan ya fita yana mai ci gaba da kiran ƴan uwa da abokan arziƙi.

Da misalin ƙarfe biyar na yamma Amerra ta faraka, ko da ta farka sai ta farka da wani irin ciwon kai, ga kuma wani ɓacin rai da mai barci ke tashi da shi musamman barcin yamma. Ta na fitowa falo ta ganshi sanye da kananan kaya na adides masu ruwa kore sosai kayan suka zauna a jikinsa, kana kallonsa kasan yana cikin farin ciki, ga kuma falon wani ƙamshine ke tashi shima dai a’lamar ya gyara ko ina. Ya na ganinta ya nufo gurin yana sakin murmushi haɗi da kiran sunanta. “Honey kin tashi? Muje ki yi wanka kafin a fara kiran salla saura kaɗan na gama abinci, ina fatan barccin ya isheki ko? Tun lokacin da ya fara magana take jin ɓacinran da ta tashi dashi yana ƙaruwa, haka kawai taji bata son yin mgn, sosai take daurewa karta ce komai domin tasan ba magana mai daɗi zatayi ba, hakan ya sa ta kasa cewa komai sai yatsine fuska da takeyi. Shi kuwa ganin haka yasa ya nufota yana dariya.

Bakinsa ya kai da niyar sakar mata kiss a kuncinta amma ta ja fuskarta ta na had’e fuskar harda tsartar da yawun bakita kamar wanda yayi mata kiss ɗin. Da mamaki Adam yake kallonta ganin abun da ta yi. “Lafiya kuwa kike honey? Ya faɗa ya na kallonta domin yasan abun da tafi so kenan a duk lokacin da zai fita daga gida ko idan ya dawo Koda ya dawo da ɓacin rai ne to ita zata masa, amma yanzu tun kafin yai mata tana kawar da kai. Bata ce komai ba ta nufi ɗakin ta domin ɗazu a ɗakinsa ya kwantar da ita, tana shiga ta faɗa toilet ta yi buroshe sannan ta yi wanka tana jin har lokacin ɓacin ran bai bar kantaba. Shikowa Adam uzuri ya yi mata ganin daga barci ta tashi gashi Kuma bata da lafiya. Sauri ya yi ya gama gyara komai kafin shima ya sake wanka sannan ya ɗaura alaula ya fito sanye da jallabiya. ‘Dakinta ya nufa ganin bai ganta a Palo ba. Yana shiga ya ganta a kwance tana kallon sama ba barci take ba. Kallonta ya keyi yana jin tausayinta sosai ganin yanda ramarta ke sake fitowa fili.

“Honey kiyi alaula kiyi salla kafin na dawo na yi mana girki mai daɗi yau na hutar dake Kuma…Tun kafin ya ƙarasa ta tsayar dashi domin ya kaita bango, shi bai san bata son yin magana bane. Cikin ɗan ɓacin rai ta ce “Dan Allah ya isa! ni nace maka yinwa nake ji ne? Fisabililahi kazo sai surutu kake mini wai kayi girki, to ni nasakaka, ko nace Adam kayi kirki ne, dan Allah kaje Kaci kayanka ni bama abinci zanci ba yau a ƙoshe nake. Ta na gama faɗa ta bar masa ɗakin ta fito Palo ta zauna tana jin wani haushi wanda bata san daga ina yake zuwa ba. Adam kuwa mutuwar tsaye ya yi ya saki baki da hanci yana kallonta har ta bar palon. Shi dai baiga abun da yayi ba, kuma Ameera da ko musu bata iya masa idan ya yi maga amma take masa irin wannan magana da ihu harda kiransa da Adam!. Shima fitowa yayi daga ɗakin domin an fara kiran sallah. Kallonta yayi ganin yanda ta haɗe rai ka rantse wani abu a kai mata. Ita kuwa ta na ganinsa ta kawar da kai ta tashi domin barin gurin. Adam kuwa bai karaya ba ya ce “Sorry honey nasan duk barcin yamma ne, dama ana magar cewar babu kyau barcin yamma, yanzu dai ki daure kiyi alaula kiyi sallah kinji. Kallonsa tayi tana jin magana a bakinta amma ta daure har ya fita daga gidan.

Ba domin maganarsa ba itama ta nufi toilet ta ɗaura alaula ta fara gabatar da sallar la’asar (Asar) kafin ta fara gabatar da magrib. Tana idarwa ta koma ɗaki ta sake kwantawa domin wani sabon barcin take ji. Adam kuwa yana dawowa ya nufi kicin saida ya gama fitowa da komai kafin ya shiga
ɗakinta domin kiranta suci abinci. Cikin mamaki yake kallonta ganin tayi shigar barci ta kwanta abunta harma barci ya fara mata nisa. Cikin kwantar da murya ya fara kiran sunanta haɗi da bubbuga mata gadon duk dan karya ɓata mata rai. “Honey honey honey hone…”Inna’ilai wa inna’ilaihi raju’un! Wannan wani irin masifane, yanzu dan Allah barcin ma bazaka barni nayi ba fisabililahi, wannan wani irin shiga haƙƙin mutum ne, ko ka manta zunubin da mutum yake samu idan ya tashi wani yana barcci ne, ni nace maka yau bazanci abinci ba, ko ana dole ne cin abincin. Cikin sanyi murya ya ce “Haba honey ya za’ayi ki kwanta bakici abinci ba Kuma gashi ba kya da lafiya, ai ko kaɗan kici sai kisha magani ko?
“To wallhi bazanci ba idan kuma dolene sai naga wanda zai sakani na ci, na ce maka na ƙoshi-naƙoshi ko dolene. Ta ƙarasa tana fashewa da kukan takaici Kai ka rantse da Allah dukanta a kayi. Sosai take jin barcin kuma harga Allah bata jin yunwa hasalima bata son ganin kowa a kusa da ita, yanzu haka ji take kamar dukanta ya keyi. Shi kuwa Adam gurin yin gwaninta zai rarrasheta harda kamota zai kwantar da ita a jikinsa amma ta wani ƙwace jikinta ta miƙe tsaye ta ƙara fashewa da wani sabon kukan ta na kiran sunan Umma tana ihu! “Wai ni dolene sai mutum yaci abincin ne? na ce maka na ƙoshi-naƙoshi Kuma barci nake ji dan Allah ka rabu dani waiyoo Umma! Ta na faɗa ta yi waje tana cigaba da kukan kamar wacce a ka sanar mata cewar unman ce ta mutu. Shima bayan ta yabi yana kallon wani sabon salo daga wajan matar tasa. Wai to mai ya ke damunta ko dai har yanzu barcin yamman ne bai saketa ba. Ganin ta zauna a palon ne yasa ya ɗauko kulan abinci gaba ɗaya ya nufo gurin ta ya na faɗin “kinga ko cokali uku kikayi sai kisha magani ki kwanta in ba hakaba zakisha wahala kodan cikin dake jikinki please honey ki daure.
Yana ajiye abincin Ameera da har yanzu bata daina kukanba ta ɗaga kulan abincin ta buga da ƙasa tayi booll da kulan ta na faɗin. “Idan ma wannan abincin na maitane to wallhi bazanci ba,ni barci nake ji na ce maka na koshi bazan ci ba. Ta na faɗa ta koma gurin daining tebul ɗin ta kwaso sauran abincin da abun sha da ya haɗa musu suma tayi watsi da su tana gamawa ta koma ɗaki tayi kwanciyarta abunta, cikin minti kaɗan barci yayi awun gaba da ita.

Shiru Adam yayi yana kallon ta batare da ya hanta komai ba har ta maba zubar da komai na abincin, shi kan Adam izuwa yanzu yasan ba wai barcin yamma bane yasa ta wannan haukan, anya kuwa Ameera ƙalau take, daga yau ɗaya kawai ta canja daga Ameeran da yasani izuwa zuwa wata aba da ban. Shi yanzu damuwarsa rashin cin abinci da batayi ba ne, rabonta da cin wani abun tun rana kafin su fita asibiti. Haka ya zauna saida ya gyara ko ina da ta ɓata kafin ya shiga ɗakin ganin har tayi barci yasa ya ja mata bargo ya fita izuwa masallaci domin yin sallar isha. Zuciyarsa yana jin izuwa gobe in sha Allah zata daina wannan ƙuncin. Har ya dawo daga masallaci barci takeyi, yaso ya koma ɗakinsa ya kwanta amma yayi tunanin kar Kuma ta tashi cikin dare tana neman abinci. Hakan yasa ya kwanta yana buƙatarta amma yana tsoran masifa, haka ya kwanta yana ta tunanin kyautar da Ubangi yayi musu a wannan lokacin da suke buƙata, kaman ya rungumota amma ya haƙura har shima barci ya ɗaukeshi. Da asuba shine ya fara tashi tun kafin yayi mata magana motsin sa ya tasheta, domin dama wani lokaci ma ita ke tashin su sallar Asubahi. Ko kallonsa batayi ba ta shiga toilet ta ɗaura alaula Koda ta fito bata ganshi ba, ta hau kan dadduma ta tada sallah. Tana idarwa ta koma barci ba tare da ta cire hijab ɗin jikinta bama,ga yunwa ta na ji amma barci ya hanata tashi.

Haka tana kwance har ya dawo. Ganin ko daddumar bata naɗe bane yasa ya naɗe yana kallon irin kwanciyar da tayi. “Good morning honey” ya faɗa yana hawa kan gadon domin komawa barcin. Jin shiru yasa ya kai kallonsa fuskarta ya ga ashe har ta koma barci. Da mamaki yake kallonta , iKon Allah wannan barcin dai anya kuwa na lafiya ne Ameera. Kasancewar safiyar litinin ce yasa bai so komawa barci ba amma baccin ya sa ce shi.

Misalin karfe shida daidai na safe Ameera ta farka tana jin wata a zababbiyar yunwa kaman an mata sata a cikinta,ɓangare ɗaya kuma ga wani irin ƙunci da yafi na jiya da ta tashi da shi! Kallon gurin da yake kwance tayi sai taji bata son ganinsa a kwance, haka kawai taji barcin da yakeyi ɓata mata rai yake. Wayarsa ta ɗauko ta duba lokaci ganin shida saura yasa ta ajiye wayar ta na tunani. Tashi ta yi ta na kallonsa kamar ta rufeshi da duka ganin yana barci. Kicin ta shiga ta haɗa tii (shayi) mai kauri da zafi ta ɗauki kick ta fito falo ta zauna tana ci. Zumbur ta miƙe kamar wacce aka tsurkula ta shiga d’akin domin ita har yanzu barcin da yakeyi ya tsaya mata a rai haka kawai. Ta na shiga ta nufi gurin da yake, ta ɗauki filo ta fara buga masa ta na cewa “Malam ka tashi ka tafi aiki, ko wani Namiji yana gurin aiki amma kai sai barcin a sara kakeyi tun jiya dadadare kake barci kamar wani mace malam wallahi sai ka tashi ka tafi aiki, yana ƙokarin tashi amma taƙi ba shi damar hakan sai cigaba da buga masa fulo takeyi. Shi kuwa Adam cikin barci yaji ana dukansa yana son tashi amma sai ƙara danneshi a keyi Kuma ba’a daina dukansa ba. Da ƙyar ya iya tashi zaune yana kallonta sai ajiyar zuciya takeyi kamar wacce tayi gudu. Sosai yake kallonta ganin ta kafeshi da ido tana jiran yace wani abu. Wayarsa ya lalubo ya duba lokaci ganin shida da minti biyu ne yasa ya d’ago kai ya kalleta ya ce “Yanzu ƙarfe shida shine kike cewa kowani Namijin arziƙi yana gurin aiki? Ƙarfe shida fa Ameera? wai lafiya kike kuwa. Cikin masifa dake cinta ta fara magana bilhaƙƙi da gaskiyarta “Eh wallahi sai ka tashi, wani irin barcine haka tun dare har yanzu ana yinsa sai kace barcin a sara, ni dai wallhi sai ka tashi ka tafi aiki yanzu nake so kuma. Adam ya ce “Wai honey me ke damunki ne, yanzu ko mai gadin gurin aikin namu bai tashi ba amma ni zan tafi gurin aiki, Ko wanka banyi ba banci abinciba haka kikeso na tafi gurin aikin?

“Su sauran ma’aikatan an faɗa maka abinci sukeci suke zuwa? ko wankanma dolene sai kayi, Malam wallahi ka tashi ka fita dun kafin raina ya ƙara baci.

Cikin karaya ya ce “To kisamamin wani abun kafin nayi wanka. “Babu abunda zan girka kuma bazakayi wankan ba,ni dai kawai kabar gidan koma ina zakaje kaje bana son ganinka ne a gidan gaba ɗaya.

Haka Adam ya miƙe ya ɗauki doguwar rigarsa ya saka, ita Kuma ta na biye dashi a baya riƙe da filo ta na cigaba da maganganu “Ni bana son Namiji rago kullum barci-barci sai kace mace, kawai ka fita gurin aiki. Sai da ta kaishi har ƙofar falon fita kafin ya ce “Kinci abincin ne ke? Cikin tsiwa da matsuwa da ganin yabar gidan ta ce “Ina ruwanka da naci ko banci ba. Tana faɗa ta tura shi waje ta rufe gidan tana Jan tsaki.

Tsaye Adam yayi a waje daga shi sai doguwar riga sai yanzu ya kula da ko takalmi ma babu a ƙafarsa wayarsa ma a ciki ya baro ta, afili ya ce “Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raju’un! Wai me ke damun honey ne, anya kuwa ba sauyamin ita a kayi a asibiti ba, to idan ba haka ba menene matsalar daga jiya zuwa yau na kasa sakewa a gidana babu damar nayi gwaninta. Ya na laluba aljihunsa yaji babu makullin mota, sannan babu ko sisi da zai hau mashi izuwa gidan ƙkanwar sa, kasancewar babban abokinsa take aure. Ko da yazo mai gadi barci yake yi abunshi haka ya buɗe get ɗin ya fita yana kallon titin tsit sai ɗai-ɗaikun mutane masu tafiya a ƙasa. Sai da ya daɗe kafin ya samu mai mashi ya hau izuwa gidan su Najib. Koda suka isa ya tsaya a bakin get d’in gidan yana bugawa, amma sun kai minti biyar babu wanda ya amsa harma mai mashin ɗin ya fara magana, suna cikin haka mai gadi ya buɗe get ɗin da masifar katse masa barci da a kayi, domin yasan dai masu gidan suna ciki. Amma ganin Adam yasa ya saki fara’a yana masa barka da safiya.

Cikin jin kunyar ganinsa a haka da mai gadin yayi ya ce “Kamin mgn da Najib yanzu please. Ko da Najib yaji cewar Adam ne da sauri ya fito yana mamakin zuwansa da sassafennan dama jiya kadija ke sanar masa da cewar Ameera tanada ciki kodai ba lafiya bane. Kafin Najib yace komai Adam ya ce “Please sallami mai mashin ɗin nan yana faɗa ya shige gidan ya bar Najib da mamaki ganinsa a birkice.

Ameera kuwa bayan fitan Adam palo ta koma ta zauna ta ɗauki shayinta ta fara sha, jin yayi sanyi yasa ta koma kicin ɗin, ta ƙara haɗa wani, zata ɗauki keck amma taga ya ƙare, ita kaɗai sai kumbure-kumbure takeyi, tana jin haushin komai ma shi kanshi gurin da a ke ajiye Keck ɗin ganin babu saida ta rufe gurin da ƙarfi har yana tsagewa. Firiza ta buɗe ko zata samu super commando domin shine drink dinta shima ganin babu yasa ta ture firiza ɗin da ƙarfi har yana faɗuwa ko ta kansa bata biba ta duba bredi shi Kuma taga saura kaɗan Kuma ya d’an bushe hakan yasa tayi wurgi dashi ta shiga ɗaki ta ɗauko kuɗi ta nufo gurin mai gadi.

Tsabar masifa na cinta ma ko sallama bata yi ba ta fara buga ƙofar ɗakin kamar ɗakin ne yayi mata laifi. “Baba mai gad…Baba mai gadi!… Da sauri baba mai gadi ya fito yana amsawa domin ya gane muryarta.

“Na’am hajiya lafiya dai ko?

“Saboda nazo kiranka shine kake tambayar lafiya? Ok idan da lafiya ban isa kiranka ba kenan ko? Na ce ban isa kiranka ba kenan ko?

Jin yayi shiru yasa ta harareshi sannan ta ce “Aikenka zanyi kuma saura kamin shirme kuma wallahi ka dawo yanzu! Tabna faɗa ta jefa masa dubu ɗaya ta ce “Abu mai laushi zaka sayomin yanzunan karka ɓata mini lokaci. Ta na faɗa ta juya ta fara tafiya ta bar baba mai gadi da buɗe bakin ganin sabon lamari daga matar gidan nasu. Matar da ko ɗaga ido ta kalleshi bata yi, bare har tai masa ihu barema aike, shi dai tun da yake a gidannan bata taɓa zuwa ta aikeshi ba, wani lokacin dai Adam ke turota ta ce inji Adam ka sayo abu kaza. Ganin zata shige be kuma gane aiken ba ne ya ce

“Hajiya wani abune mai laushi bansan wanda zan sayoba?

Tun daga gurin da take ta nufoshi cikin masifa kai ka rantse zaginta yayi, har tana haɗawa da gudu ta iso gurinsa ta ce “Kai baka da ilimi ne baka san abu mai laushi ba har sai ka tambaya to kaje ka sayo goriba ko rake tunda baka da lissafi, yanzu abu mai laushi har sai an faɗa maka in banda samun guri, to wallhi kaje ka sayo min yanzu ina jiranka. Ta na faɗa ta juya fuuu ta nufi ciki ta bar baba mai gadi tsaye yana juya kuɗin yana nazari to meye abu mai laushi! Kuma da sassafe haka, anya kuwa hajiya lafiya taka. Haka dai ya fita badan yasan me zai sayo ɗin ba.

Ita kuwa Ameera bayan ta koma ta nufi gurin da firizan da tafaɗar tana son ta ɗaga amma ta kasa, tati-tayi amma ko motsashi ta kasa, haka ta dawo ta zauna tana jiran baba mai gadi domin taga mai zai kawo mata, domin ita kanta bata san me takeson ci ba, ita dai tasan Abu mai laushi take marmari, idan da za’a yankata bata san me take son ci ba, kuma bata son cin bredi hakan yasa bata ce masa bredi ba.

Najib da kadija cikin mamaki suke tambayar Adam lafiya dai yazo a haka. Cikin rashin sanin abun yi ya ce “Wallahi babu lafiya gidana tun jiya ba lafiya. Da sauri kadija ta ce “Mai ya samu Ameera ɗin Yaya? Wani abun ne ya samu cikin nata?

Shi Adam har ga Allah harma ya manta da cewar cikene gareta. Cikin su’butar baki ya ce “Au wai dama ciki gare ta?

Da mamaki Najib da kadija suka Kalli juna jin abun da ya ce.

“Yaya ina ce kai da kanka jiya ka kirani kace Ameera nada ciki ko dama tsokana ta ka keyi? Kallonsu yayi ganin sun kafeshi da ido sai ya sunkuyarda kai ya ce

“Eh gaskene kawai sha’afa na yi.

“Ban gane ka sha’afa ne ba, wai wani abu ne yake faruwa ka fito ko takalmi babu ga shi ko kayan arziƙi babu a jikin ka, yanzu kuma wai kace ka sha’afa ne lafiya kuwa? Najib ya faɗa yana ƙara nazarin abokin nasa.

Cikin murya tausayi Adam ya fara cewa “Wallhi tun jiya da muka dawo daga asibiti Amerra ta sauya, dana tun kafin jiyan ta zama abu kaɗan fushi da masifa, to daga jiya kuma abun ya ƙaru komai nayi masifa, idan nace taci abinci masifa,idan na tasheta a barci faɗa, yanzu haka itace tace wai na tashi na tafi gurin aiki, nace mata lokaci baiyi ba wai wallhi sai na fita, ta barni na sake kaya ko naci abinci ma wallhi taƙi, harfa waje ta rakoni tana dukana da filo. Ya ƙarasa kamar zaiyi kuka.

Dariya kadija ta yi tana cewa “IKon Allah ita Ameeran ce harda dukanka? To ko dai nata cikin ne yazo mata da ƙunci da ɓacin rai?

“To Kuma sai tayi ɓacin ran harda ni mijinta? Adam ya tambaya cikin rashin yarda.

Kadija ta ce “Ta to wallhi yaya in dai irin wannan cikin ne to mutum koma waye sai ta masa, wani lokaci ma idan bata samu abokin yi ba to kuka zata fara ita kaɗai ko kuma ta samu wani abu a gidan ta huce a kansa, irin wannan yanayin mata da yawa na shiga irin sa, Kuma suna shan wahala sosai dole sai kayi haƙuri, dama ai Yaya ka sha faɗin cewar idan Ameera ta samu ciki zaka tarairayeta kamar ƙwai, to kaga haka zaka daure.

Cikin mamaki Adam ya ce “Wai dama cikinne yasa wannan abun? Nifa duk inace barcin yamma da tayi ne yasa ta haka, yanzu dan mace nada ciki sai ta fara masifa Fisabililahi! Najib ya ce

“Ai kawai abokina haka zaka daure, yanzu dai ka shiga kayi wanka ka fito muci abinci anjima kadija sai taje gurinta kar a barta ita ɗaya a gida kaga babu daɗi. Adam ya tashi ya tafi ɗakin da suka nuna masa yana tafiya yana mamakin wannan lamari, yanzu kawai sai mace ta fara masifa saboda ciki, shi bai ta’ba jin wannan labarin ba.

Tana zaune idonta ƙurr a ƙofar falon Mai gadi ya turo ƙofar falon hannusa riƙe da leda, idonta a kan ledar domin ganin mai ya kwaso mata. Shi kuwa baba mai gadi jikinsa har rawa yake domin yasan dole sai ya she masifa barin ma yanzu da ya ƙara haɗa ido da ita ganin yadda ta kafe ledar da ido. A zuciyarsa ya ce “Yanzu fisabililahi ki aiki mutum ba tare da kin sanar da shi abun da zai sayoba, fatan kawai ki wahalar dani, yanzu nasan dole sai na koma. Jin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin ƙarasawa gabanta ya miƙa mata ledar kamar zai faɗi. Karɓar ledar ta yi ta na ƙoƙarin buɗewa, ganin ledar na mata gardama ne yasa ta yaga ledar tana jin ƙamshin abun da ke cikin ledar, cikin mamaki take kallon abun da ke ciki. Ɗagowa tayi ta kalleshi kafin ta Kara kallon abin da ke ciki ta ce…

Kubi S-REZA a hankali kusan bai saba baku kunya ba.

Rate, share, comment.

S. Reza

First Class Writers’ Association

Ameera Da Adam 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×