Skip to content
Part 10 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

Ɗauke da mamaki Ameera ke kallon Nana jin abun da ta ke faɗa a kan ta wai baƙin ciki. Cikin sanyin murya ta ce “Yanzu Nana nice ke miki baƙin ciki!? Nana ta gyara zama da kyau domin kuwa ranta ya ɓaci da irin cin mutuncin da yayar tata kewa Nasiru. “To idan ba baƙin ciki ba meme ne wannan? Mutum ya yi abun burgewa amma baza’a ya ba masa ba sai kuma cin mutunci ya biyo baya, haba Anty Meera ni ban san yaushe kika zama haka ba dan Allah ki dawo yadda kike please ki bar wannan halin hassadar da kika ɗauko wallahi bata ɓullewa. Nana ta ƙarasa ta na ƙoƙarin barin tashi ta bar ɗakin. Ameera da har wani kumfar masifa ne ke fita a bakinta ta miƙe ta janyota ta rufe ta da duka tana faɗin.

“Wallahi Nana kin yi kaɗan ki rainani har haka, daga faɗa miki gaskiya sai ki fara zagina harda kirana da munafuka magulmaciya, ke ɗin banza yaushe har kika girma kika san daɗin saurayin da zakimin rashin Kunya a kansa. Sosai take jibgarta babu ƙaƙƙautawa. Nana kuwa jin Ameera na ƙoƙarin sumar da itane ya sa itama ta fara mayar mata da martani bata duba ƙaton cikin dake jikinta ba.

Cikin ƙan-ƙanin lokaci Ameera ta fara ihun waiyoo cikinta. Sosai ta ke kuka ta na riƙe da ciki. Hakan yasa Umma saurin shigowa ɗakin tana tambayar ba’asi. Amma idonta ya sauƙa a kan Nana ta danne Ameera sai duka ta ke Kamar Allah ya aikota. Da sauri Umma ta rafka doguwar salati ta na isa gurin ta kama Nana ta wanka mata mari sannan ta jefar da ita kefe ɗaya ta yi kan Ameera wacce izuwa yanzu ta ma daina ihun sai numfashi da take saukewa a hankali.

Ganin haka yasa kafin Umma ta dawo gurin Nana har ta fita daga ɗakin. Nana na fita Haura ta shigo ɗakin tana tambayar lafiya. Umma da zuwa yanzu duk ta rikice ta ce “Kin iya tuƙa Mota? Haura ta amsa da “A’a ban iya ba. Umma ta ajiye Ameera da take kan cinyarta tun ɗazu ta nufi ɗakinta domin ɗaukar waya ta kira Abban su. Tana dawowa taga Ameera na sauke ajiyar zuciya Haura na mata sannu tana cigaba da rike cikinta. “Waiyoo Allah Umma cikina zan mutu! Ameera ta faɗa tana kallon Umma da take mamakin ganin lokaci ɗaya Ameera ɗin ta magantu.

Umma cikin faɗa ta fara faɗin “Wallahi kin bani mamaki Ameera, tsabar rashin sanin ciwon kai ki tsaya kina faɗa da ƙanwarki kina ɗauke da wannan tsohon cikin! Koma me zata miki bazaki haƙura ki barta albarkacin wannan cikin da ke jikinki ba, yanzu idan yazo da tsau-tsayi cikin ya samu wani matsalar fa? Ana cikin haka Adam ya ƙara so gidan dalilin kiran da Umma tai masa. Yana zuwa cikin tashin hankali ya sunkuceta izuwa Mota Haura tabi bayansu suka nufi asibiti. Suna fita Umma ta shiga kiran sunan Nana cikin wata iriyar murya wacce kana ji kasan ranta a mugun ɓace ya ke. Sosai ta ke kiran Nana ta ko ta ina amma babu Nana babu dalilin ta, lungu da saƙo na gidan babu inda bata duba ba amma babu Nana hakan yasa ran Umma ƙara ɓaci tana jin yau sai ta kusa sumar da yarinyar nan idan ta ganta.

Sosai likitan ya hau Adam da faɗa bayan ceto cikin da suka samu suka yi da ƙyar. Faɗa sosai ya yi masa akan wai a daina wasa da cikin domin wannan da ƙarfi aka mawa cikin wanda hakan yasa sai da ɗan cikin ya juya daga yanda ya ke. Sosai Adam ya shiga amsawa da za’a kiyaye wannan ma baya gida ne shine yasa. Likitan ya ƙara ɗorasa a kan sharuɗa irin na masu tsohon ciki. Ya ce “Kar a barta ta yi wani aiki mai wahala koda shara ko wanki da sauransu. Sannan banda yawo ta zauna guri ɗaya domin ɗan cikinta ya jigata sosai yin wani babban abun zai haifar da damuwa. Sai da yamma aka sallamo su wanda kafin wannan lokacin sai da Haura ta je gida ta dafo musu abinci. A hanya ne Adam yake tambayar ta me ya sameta. Ameera ta yi shiru ta na kallon gefe ɗaya zuciyarta cike da saƙe-saƙe. Adam ya dawo da tambayar kan Haura ita kuma ta ce bata sani ba. Har suka isa gida bata ce komai ba sai hawaye da ke zubowa a idonta. Sosai ranta ke mata suya zuciyarta na mata zafi tana jin kamar a kwai wani abun da ya kamata ta yi domin taji daɗi. Sai ta ke jin duk duniyar ma ta tsani kowa, kaman babu wanda yake sonta a duniyar. A hankali take tuno komai da ya faru tsakanin ta da Nana. Shi kansa Adam tausayi ta ne ya rufe shi ganin yanda ta riƙe cikin ta ga kuma hawaye da yake zubowa ba tare da tayi kuka ba. Sai yanzu ya ƙara jin tausayin ta ganin ita kuma irin nata laulayin kenan. Itama Haura kaman tai mata kuka tsabar tausayi domin har ta rame sosai. Haka suka iso gidan mai gadi ya buɗe musu get. Kafin ma Adam ya ƙara sa tsayawa Ameera ta buɗe ƙofa ta fito ta nufi cikin gida da sauri. Bata son ganin kowa a kusa da ita, ta gaji da wannan duniyar bata san mai taiwa kowa ya tsaneta har haka ba.

Ganin haka yasa shima bai gama saita motar ba ya kashe ta ya fita yabi bayanta yana sanar da Haura da ta rufe motar. Ya na shiga ya sameta ta ƙifa kanta a bakin gado tana shesheƙar kuka. A hankali ya ƙara so kusa da ita ya fara mata magana a hankali “Honey dan Allah ki yi haƙuri wannan kukan ma zai iya kara haifar miki da damuwa keda ɗan cikin ki, please I’m so sorry kinji. Jin bata daina kukan bane kuma bata ɗago ta kalleshi ba ne yasa ya matso kusa da ita ya sa hannu zai ɗagota. Yana ɗora hannunsa a jikinta ta yi zumbur ta meƙe kamar mai jiran hakan. Wallahi babu wata-wata ta ɗauke fuskarsa da mari, ta cakumi rigarsa ta fara zaiyano komai da take jin ya tsaya mata wanda tun ɗazu take jin idan bata amayar ba zata iya mutuwa “Na tsane ku bana son ganin kowa ku fita a sabga ta wallahi bana son ganin kowa mutuwa ma kawai zanyi mai nai muku ina kuke so naje. Ta na faɗa tana cigaba da dukan Adam a ƙirjin sa. Ganin haka yasa Adam ƙoƙarin kwantar da ita a ƙirjin nasa amma ta ƙwace jikinta ta nufi gurin kayan kwalliya ta kwaso su ta watsar a ƙasa, ta ɗauki kwalbar turare ta wurgowa adam wanda yayi saurin kaucewa, ta ɗauko kwalbar mai shima ta wurgo masa tana kuka tana fasa duk abinda ta gani a cikin ɗakin harda madubin da ke gurin kwalliyar saida ta tarwatsa shi, sosai ta koma kamar mahaukaciya , Adam dai da abun nata yayi mugu-mugun bashi tausayi da mamaki ya tsaya yana kallonta har ta yi ta gaji ta zube a gurin tun tana jan numfashi har barci yayi gaba da ita.

Sai da ya bari barcin ya fara mata nisa kafin ya ɗauke ta ya kaita ɗakinsa ya kwantar da ita ya nufi ɗakin Haura da nufin kiranta ta gyara waccen ɗakin. Tun kafin ya tura dakin yauma yaji kamar ba Muryar mutun ɗaya yake ji a ɗakin ba hakan yasa shi saurin tura ƙofar ɗakin yana mai kai kallonsa izuwa cikin ɗakin. Cikin tsananin mamaki Adam yake kallon wannan tsohuwar matar mai yin bara nan wato mamar Haura. Zaune ya same su a gefen gadon ga soyayen naman kaza a gaban tsohuwar tana ci tana surutu. Gefe ɗaya kuma Haura ce zaune itama tana cin naman suna ta fara’a da yaransu. Kafin Adam ya ce komai Haura ta ce “Ammi ta ce tazo yanzu ina so idan ka fito na faɗa maka ne.

Adam dai bai ce komai ba sai bin tsohuwar da ido yake yi, itama tsohuwar sai kallonsa cikin ido take yi. Ganin haka yasa ya ce “Ok kizo yanzu. Yana faɗa ya saki ƙofar ya fita da mamaki. Shi dai bai yarda cewar yanzu wannan matar tazo ba, to idan ma zuwa zata yi sai kawai ta shigo kan ta tsaye, to shi yasan ma mai gadi ba zai barta ta shigo kai tsaye ba, hakan yasa Adam cewar sai ya tamba yi mai gadi ko shine ya barta ta shiga. Yana tsaye a Palo ta ƙaraso kanta a ƙasa. Kallonta ya ƙara yi sai yaga kamar ta ƙara zama yarinya. Sai da ya sauƙe ajiyar zuciya aɓoye kafin ya ce “Kije ɗakin Ameera ki gyara komai, a kwai kwalabe ki yi a hankali. Haura ta amsa da “Tom za’a gyara yanzu ” Adam na faɗa ya nufi gurin mai gadi. Yana zuwa bai bi ta kansa da ya fara wasu zantukan daban ba ko gaisuwar ma bai amsa ba ya ce “Amm bayan mu wani ya shigo gidan nan yanzu ne? Baba mai gadi cike da mamaki ya ce “Ranka shi daɗe gaskiya babu wanda ya shiga gidan nan bayan ku ukun da kuka shiga yanzu, kuma yau kasancewar ba kwa gida yasa ban je ko ina ba, abinci ma Haura ce da ta dawo ɗazu ta kawo min har nan, ai Allah ya sakawa wannan yarinyar bata gajiya kamar a gogo. Adam bai ce komai ba ya bar gurin yana girgiza kai alamun nazari.

Koda ya koma ciki yana shiga sai yaga kamar ƙiftawar mutum, amma bai ga kowa ba hakan yasa ya nufi ɗakin da yasa Haura aiki ɗin domin yaga ko ta fara. Yana shiga yaga ɗakin tsaf-tsaf a gyare komai an mayar da shi mazaunin sa kamar ma ba’a komai a ciki ba. Cikin wani sabon mamakin yake bin ɗakin da kallo ganin Haura ɗin bata ciki. Afili ya furta “Hasbinallahu wa ni’imal wakil! Haka yake ta furta wa yana bin ɗakin da kallo! Sosai izuwa yanzu ya fara tsorata da lamarin Haura. Da sauri ya fito ya koma ɗakin da Ameera ke ciki. Har yanzu barci take yi tana kwance a yadda ya barta. Juyawa yayi ya fito yana son zuwa ɗakin Haura amma yana tsoro hakan yasa ya ƙolla mata kira daga gurin da yake.

Ɗan nesa da shi ta tsaya kanta a sunkuye kanta babu dan kwalli ya ce “Inna Ammin na ki?

Haura ta ce “Ai ta tafi dama sauri take yi, wai tazo ne kawai ta ganni ko lafiya nake. Adam ya ce “To ta ganki lafiyar kike? Ya faɗa cike da takaici da mamaki. Itama Haura ɗin ɗagowa ta yi sai kuma suka haɗa ido tayi saurin kawar da nata.

Adam yayi saurin kallonta a karo na biyu yana ƙara jin shkkar ta. “Suwa ye ku? Mai kuka zo nema a gurin mu? Mai kuke nufi damu?

Da sauri Haura ta ɗago ta kalleshi jin abun da ya ce. “Haura ce da Ammi, kuma mu babu abun da muke nema gurinku sannan mu ba cutarku mukazo yi ba. Haura ta faɗa tana satar kallonsa again.

Afili ya ce “Faɗi min yanda a kayi Ammin ta ki ta shigo wannan gidan domin kuwa bata get ta shiga ba.

Cikin tsabar mamaki take kallon sa. A zuci ta ce “Wannan fa ya cika tambaya.

Take Haura ta sanar da shi abun da ta faɗa wa Ameera cewar su ba Musulmai ba ne, kuma ba Hausawa ba ne, sannan su suna yin wasu abubuwan ne ba irin na mutane ba kasancewar suna da tsfface-tsffce.

Da ƙarfi Adam ya ce “What! Auzu billahi! tsafi! Kuma ku ba musulmai ba ne? To wani gari kenan kuke. Haura ta ce “A garin Garuk muke kuma yaran Garuk muke ji, yanzu haka muna son komawa amma babu dama ƙaddara ce ta fito damu daga cikin garin wacce kuma bamu da damar koma , hakan yasa muka fara barace-barace- a nan har Allah yayi ka kirani aiki. Adam yayi shiru yana kallonta ganin tana kuka a hankali ya ce “Mai kuka aikata da yasa kuka bar garin naku, sannan yaya a kayi kuka iya yin Hausa? Haura ta yi shiru ta na kallon sa. Sai cen ta ce “Hausa mun koya ne, sannan abun da ya fito da mu daga Garuk labari ne mai tsayin gaske. Adam ya ce “Yanzu abun da nake so da ke shine Ammin ki zata dawo nan gidan da zama , amma ke da ita duk zaku koma wancen sashin. Ya faɗa yana nuna mata wani ƙaramin sashe dake gefe da nasu. Haura ta yi godiya ta miƙe zata tafi amma suka tsinkayo muryar Ameera ta na faɗin “Babu inda zasu zauna wallahi bazamu zauna da ar’na da kafurai a gida ba.

<< Ameera Da Adam 9Ameera Da Adam 11 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.