“Haka kawai bayan yarinya ta gama sanar da kai labarin ta ce wa su ba musulamai ba ne amma har kana iya ce wa zasu zauna a cikin wannan gidan, to wallahi ba zata saɓu ba. Ameera ta faɗa ta na ƙarasowa gurin ranta a mugun ɓace. Kafin Adam ya yi magana ta ci gaba da faɗin “Kasan Allah wannan yarinyar zamanta ya ƙare a wannan gidan dan ubanta, mai za’ayi da dangin tsafi da rashin yin Sallah! Ta na faɗa ta fara kamo Haura da ke ɗuke ta na kuka. Cikin kwantar da murya Adam ya fara faɗin “Honey mana! Wallahi wannan yarinyar abar tausayi ce, kuma ba wai ƴar tsafi ba ce, ha ka itama ta tsinci kanta da abun amma in sha Allah zata daina, please dan Allah ki yi haƙuri su zauna na ɗan wani lokaci please Ameera ta Adam. Ya ƙarasa da tsokana a muryar ta sa.
Lokaci ɗaya Amera ta fashe da kuka ta na faɗin “Wannan yarinyar tsinaniya ce wallahi! Ba na son ko ganinta a kusa da ni, ba ta taimako na, jiya fa a gabanta Nana tai min dukan tsiya amma ko ta taimaka mini, idan ma kashe ni za’ayi babu ruwanta. Cike da mamaki Adam ya ce “Dukan tsiya! Kuma Nana? To a garin ya ya?
Ameera ta ja ƙwafa ta ci gaba da faɗin “Ai kawai ka bar wannan yarinyar Allah inaga ni ce ajalinta ita da tsinannen saurayin nan nata. Adam cikin tsananin ɓacin rai ya ce “Na ce mai kika mata da zata dake ki? Bata ganin abun da ke jikinki ne, ko Umma bata gidan ne? Wai ma yaushe har Nana ta iya dukan ki? Wai me ke faruwa ne? Sai ma a lokacin Ameera ta ƙara jin taikaicin abun da ya faru ɗin. Ta ke Amera ta kwashe komai ta faɗawa Adam sannan ta ɗora da ce wa “Allah da zarar na aihu ita zan fara tunkara koda kuwa ta na gidan mijinta ne, bazan taɓa yafe wannan cin fuskar ba. Ta na faɗa ta koma ciki ta bar Adam riƙe da baki a sake yana mamaki.
Afili ya furta zanje gidan na samu Nana akan wannan maganar, bata da hankali ne zata daki Mace mai tsohon ciki har irin wannan dukan. “Ta shi ki tafi zuwa gobe sai muje azo da Ammin ta ki ko? Haura ta miƙe ta shige ɗakinta yayin da Adam ya tashi ya bi bayan matar sa.
Bayan kwana uku Ammin Haura ta tadowo gidan kaman yanda Adam ya faɗa. Sannan babu abun da ya rage daga ɓangaren Ameera domin har yanzu duk abinda ta ce shi ake yi.
“Haura..! Haura..! Haura..! Da ƙarfin cin tuwonta ta ke kiran Haura ɗin duka da cewar ta na amsa amma hakan baisa ta daina kiran sunan ba har sai da ta ganta a gaban ta. Ta na zuwa ta ɗauke ta da mari ta na faɗin “Uban me kike yi da zan ta kiranki bazaki zo da sauri ba, tun ɗazu kin barni sai faman ihuu na ke yi kamar zaucecce yi ko? Haura ta yi ƙasa da kai ta na faɗin ki yi haƙuri. Waya ta miƙa mata game da faɗin “Gashi karatun wannan littafin zaki min kuma da sauri domin ba na son ana tsayawa, kuma dan Allah ki mayar da shi wani abun da ban kinji? Haura ta karɓa sannan ta fara karatun. Sosai ta ke karatun kamar wacce ta yi haddar sa, ko tsawa bata yi sai zubo karatu ta ke yi. Daidai anzo wani guri a cikin littafin Mai suna Addininmu Ameera ta tsayar da ita ta na faɗin. Yanzu ke a tunanin ki idan kece yaya zakiyi a gurin? Ace mamarki ta auri abokin yayanki, kuma matsiyaci ɗan matsiyata wanda bashi da ko sisi, sannan kuma ɗan ƙaramin yaro wanda bai fi ashirin da biyar ba. Haura ta ce “Shikenan sai kawai na ce masa Baba.
Ameera ta maka mata ashariya ta na faɗin. Uwar da ta haifeki mai shekaru da dama ta auri wanda kika fi tsana a duniya, wanda kuka ɗauko a matsayin mai aiki bayan kun gama hanata aure a baya sai kawai ta aure shi amma kice wai zaki kira shi da Baba. Haura dai ta yi shiru jin zagin da a kai mata. Ameera ta ce littafin Addininmu ya haɗu ta ko ina, bari gobe zamuci gaba in sha Allah! Haura ta ta shi zata tafi Ameera ta ce “Yawwa zo.
Haura ta dawo ta zauna ta na sauraron ta. Anjima zaki rakani wani guri, so ki zauna cikin shiri kar sai nazo ina famam kiranki.
Yau sosai Haura ta yi mamakin ganin sai hira ake ta yi da Ameera babu masifa, sosai ta ke mamaki. Haura ta amsa da “Ok tom.
Bayan ta ta fi itama ta shiga ɗaki ta kwanta ta na mamakin yanda yau cikinta sai motsi ya ke mata, a haka har bacci ya yi gaba da ita.
A hankali ya buɗe murfin motar ya fito ya na dariya yana mamakin abokin nasa. Adam ne ya fara faɗin “Kai dai Allah yasa naka cikin kar yazo da irin nawa, domin na sha wahala ko kuma na ce ina sha. Najib yayi dariya ya ƙara cewa “A’a ai bama iri ɗaya bane, ni dai nawa cikin ƙwaɗayi da barci ne kawai yake saka Madam, domin ita komai ta gani sai ta ce zata ci, kaidai bari wallahi idan Mace nada ciki to mijinta ya fita wahala da shi, ita wahalar kawai na haifeshi ne, amma bayan shi komai Maza ne ke yi. Adam ya ce “Kaɗan ma ka gani mu ai irinmu acikin masa tamkar muke ɗauke da cikin ne. Adam ya faɗa ya na dariya. “Kasan fa ba zan shiga ciki ba ina jiranka a nan ka kawo min na tafi kar Madam ta naimi wani abun bana gida. Najib ya faɗa ya na dariyar zolaya. Adam ya ce “Wa ai wallahi ko baka so sai ka shiga kun gaisa da Ameera, yanzu ta rage wannan fushin, domin tun jiya rabonta da ta yi faɗa da kowa, ai inaga shikenan ta dawo Ameeran da na sani.
Haka dai Najib ya amince suka nufi cikin gidan suna hira irin ta abokai, suna shiga Najib ya samu guri ya zauna shikuma ya nufi ɗaki yana kiranta.
Sosai ta sha barci wanda hakan ya haifar mata da ciwon kai, ga kuma har yanzu ɗan cikinta na motsa mata sosai, sai taji kamar yawo yake mata hakan ya ƙara haifar mata da zafin kai, sai ta zauna a gefen gadon ta kasa tashi sai zubar da hawaye take yi tana riƙe da cikin nata. Tana cikin wannan halin Adam ya shigo ɗakin ya na kiran sunanta. Da sauri ya ƙara so yana ƙoƙarin roƙota amma jin irin tsawar da ta daka masa ne yasa shi saurin ja baya yana kallonta kamar ba ita ta yi maganar ba. Lokaci ɗaya cikin nata ya ƙara hautsinewa wanda yasa ta kurma ihun. Adam ya ƙara matsowa ta ƙara faɗin “Karka taɓa ni. Amma Adam ya yi banza da ita ya kamota. Ai kuwa ta gantsara masa cizon da yasa sai da ya sake ta. Sai kuma ta fara kuka da ƙarfi tana riƙe cikin nata, sai kuma ta fara zagin Adam a kan ya bar ɗakin bata son ganin sa. Sosai ta ke sarfa masa zagi uwa ta uba, harda kai masa duka tana ya tashi ya fita bata son ganin sa. Shi dai Adam bai fita ba sai kallon yanda take kuka ta na riƙe ciki yake yi, duk ta haɗa zufa ta fita a haiyacin ta, bai san lokacin da hawaye ya zubo masa ba, yana tausayin matar tasa sosai, yana jin ba zai iya fita ya barta a haka ba dukda kuwa haka ta ke buƙata. Ameera kuwa wani irin juyi ta ji ana yi mata a cikin ta, ga zafi da kanta ya ɗauka ga ciwon kai, ga kuma wani irin ƙadaici da take ji.
Ihunta ya karaɗe gidan hakan yasa Haura da Ammi suka fito zuwa sashin nasu, wanda shima Najib ihun nata ne yasa shi nufar dakin yana kiran Adam. Sosai Ameera ta ke jin a zaba wanda yasa bata iya gane komai, sai zage-zage zage-zage take yi ta na juyi. A haka Najib ya shigo ya na tambayar lafiya? Suma Ammi da Haura suka ƙara so. “Lafiya mai kai mata? Najib ya tambayi Adam da hawaye ke zubo masa.
“Wallhi nima haka na shigo na same ta kuma ta hana na taɓa ta. Najib ya kalli Haura da Ammi ya ce “Kuje ku riketa sai muje asibiti bamu sani ba ko aihuwar ce tazo. Suna isa kusa da ita Ameera ta daka musu tsawa ta na faɗin “Kufita min da ga ɗaki bana son ganinku dukkanku karku matso kusa dani! Ammi ta roƙo hannunta da niyar janyota, amma Ameera ta fisge hannunta ta ware iya ƙarfinta ta dunƙulawa Ammi naushi a ciki, ta yi saurin ƙara mata a haƙarƙarinta wanda yasa ta sumewa nan ta ke. Ganin haka yasa Ameera ƙoƙarin sauƙa daga kan gadon ta na nufo gurin su idanunta duk ruwan hawaye. “Na ce kubar min ɗaki bana son ganin ku tsinannu. Da sauri Haura ta yi kan mahaifiyarta tana kiran sunanta, ganin haka yasa Najib ɗaukerta su ka yi waje.
Ruwa ya zuba mata amma bata farka ba, hakan yasa ya ɗauke ta suka wuce asibiti Haura sai kuka ta ke yi. Sosai Ameera ta fita a haiyacin ta, wallhi idan ka kalleta sai ka tausaya mata, ta tsagi Adam uwa ta uba amma yaƙi barin ɗakin, shi dai dole sai ya kaita asibiti ita kuma taƙi yarda. Sosai ta ke dukansa ta ko ta ina a dakin kamar mahaukaciya. Ganin dai kamar bazata daina bane kuma izuwa yanzu dukan ya fara shigarsa domin da ƙarfi take dukan hakan yasa ya shiga ƙoƙarin ƙwace jikin sa amma ta riƙe shi da ƙarfi. Da gyar ya ƙwace jikin sa ya jefata a kan gado ya rufo ɗakin ya fita. Ya fara kiran Najib ya na tambayar sa wani asibiti suke. Najib ya sanar masa sannan ya nufi asibitin ya na tunanin lamarin Ameera. Ya na isa asbintin ya tarar da Haura sai kuka ta ke suna zaune a harabar asbintin suna jiran sakamako daga gurin likitocin. Najib ya ce “Ina ita Ameera ɗin?
Adam ya amsa cikin fushi da ƙosawa da komai “Ta na gida taƙi yarda musu asbintin, kuma da dukkan alamu ba haihuwa bace, babu yadda banyi da itaba wallhi ta ƙi! Ni na gaji, wannan cikin ko cikin aljannune iyakaci kenan, haba dan Allah, to ni gaskiya na gaji ba zan iyaba, ni ban taɓa ganin inda ciki yake mayar da mace mahaukaciya ba, yanzu dubi abun da tai wa wannan matar fisabililahi! Adam ya ƙara sa ransa a mugun ɓace. Najib ya ce “Ka yi hakuri wallahi irin wannan abubuwan duk suna faru ga mace mai ciki, kai dai dan Allah ka cigaba da hakuri har Allah ya sauƙeta lafiya. Cikin tsananin masifa da baisan yanada itaba shima ya ce “Wallahi is okay! Na gaji bazan jura ba, idan haka ne kawai aje a zubar da cikin na hakura da shi bana so, haba dan Allah ita kaɗai ce mace mai ciki, ita baza’azo kusa da itaba wallhi wannan duk ƙarya take yi kawai iya shege ne ba cikin bane ya ke saka ta wasu abun. Haka fa ranar wai taje gida ta nemi faɗa da ƙanaarta Nana tai mata dukan tsiya saura kadan cikin ya zube, bayan naje gidan wai Nanar da yake itama shegiyar ce take sanar dani cewar wai saurayin ta ma ya taɓa marin ta, haba Najib wani yaro ya daki mamata dan Allah wannan wani irin cin mutumci ne. Najib dai sai hakuri yake bashi yana tausarsa akan ya bar maganar zubar da ciki. Suna cikin haka likitocin suka fito fuskokinsu cike da alhini!
“Ganin likitocin suna ta sunkuyar da kai ne yasa Najib faɗin”Dr lafiya dai ko? Sauran suka tafi suna girgiza kai. Babban likitan da shine ya tsaya a gaban su ya ce “Ƴaƴanta ne ku? Da sauri Najib ya ce “Eh Dr me ya faru ta farfaɗo ne? Dr da bai kula da Haura da ta kafa masa ido tana son jin mai zai ce ba, tun kafin ya fito jikinta ya bata a kwai matsala domin kuwa taji wata jijiya dake riƙe da ragamar rayuwata ta tsanke, tabbas taji bangwan da da ta jingina a jiki yana zaizayewa, taji ƙofar da makullin rayuwata ke jiki ya karye a ciki. Tabbas taji!
“Sai haƙuri Allah ya yi mata cikawa sakamakon haƙarƙarinta ya bugu kuma dama ta na fama da gurin. Likitan na faɗa ya share hawayensa ya bar gurin. Inna’ilaihi wa inna’ilaihi raju’un! Adam da Najib suka haɗa baki wanda yayi daidai da subewar Haura a gurin.
Inada tabbacin yanzu kun gama gane ina muka dosa. Saƙone mai wahala fahimta wanda sai mutum ya natsu zai fahimta, ba a cika samun marubuta suna rubutu a kan irin wannan matsalar ba, hakan yasa na tsaɓi wannan bangaren. Ina fatan kuna nan tare da Ni?.