Salatai kala-kala Adam ya ke ta ambata cike da ruɗewa da tashin hankali kaman wanda ya samu taɓuwa. Da sauri Najib ya yi gurin Haura yana taro ta amma ina har ta dangane da ƙasa. Juyowa ya yi ya na kallon Adam da ya ke ta faman salati harda hawaye kaman wanda ya zauce. Da ƙarfi ya kira sunan sa ganin yana neman zare wa “Adam samo mana ruwa please? Adam ya ƙara so gurin yana faɗin “Shikenan ta kashe ta, wallahi ta kashe mata uwa. Jin abun da yake faɗa ne ya sa Najib saurin toshe masa baki, ya miƙe ya taɓo mazauna kusa da su da suma suke cikin damuwar tasu jinyar, ya amshi ruwa ya fara yayyafawa Haura wanda sai da yayi sau biyar kafin ta saki ajiyar zuciya sannan ta fara magana da yaran su. “Cut kut kici-kici ƙuf zam gut vicce akuƙu fut tati, (Ma’ana ita dai a kaita gurin Amminta Amminta take son gani a kaita)Jin basu gane me take cewa ba ne yasa suka sake ta ai kuwa ta shige daɗin da taga an shigar da Amminta.
Tana shiga ta ganta kwance an rufe fuskarta da mayafi, da sauri ta buɗe tana kallon ta. Sai a lokacin ta ƙara fashewa da sabon kuka tana rungume uwar tata. Sosai Haura ke kuka harda hawayen jini wanda har aka fita da Ammin bata daina kukan ba.
Haka aka kwantar da ita a tsakiyar palon gidan nasu Adam da Najib suka yi jugun-jugun yayin da Haura take ta faman ihu ta na ta magana da yaran su. Da sauri Adam ya miƙe ya nufi ɗakin da ya kulle Ameera, yana zuwa ya buɗe ransa a mugun ɓace. Yana shiga ita kuma ta taso tayo kansa wanda tana zuwa ya ɗauke ta da mari sannan ya turata baya. Ita kuwa Ameera tun lokacin da ya kulleta ya tafi taci kuka har ta gode wa Allah, ta zageshi yafi cikin carbi. Da ƙarfi ta ƙwallara wani irin ihu domin marin ya shigeta yadda ya kamata, Adam ya fara magana cikin faɗa da masifa.
“Burin ki ya cika kin kashe ta yanzu sai hankalinki ya kwanta ko? Ya faɗa ya na ƙare mata kallo yadda ta fita a haiyacin ta duk ta rame tsabar masifa da ta ɗorawa kanta. Lokaci ɗaya Ameera ta ji gabanta ya bada wani rass! Saboda abun da taji. Adam na faɗa ya juya ya fita ya koma Palo ya kalli Najib ya ce “Wai yanzu yaya zamu yi da gawarta kaga su ba musulmai ba ne? Najib cike da mamaki ya ce “Bangane ba musulmai ba ne? To su wa ye?
“Irin arnan dajin nan fa suka samu damar shigowa gari. Sosai Najib yayi mamaki hakan yasa ya ce “Ai ni har zan kira Abba domin ai mata sutura a kaita makwanci. Suna cikin haka suka tsinkayo muryar Haura tana faɗin “Karku taɓa ta yanzu za’a zo a tafi da ita a binne ta a garin mu. Adam da Najib suka Kalli juna kafin Adam ya ce
“Waye zai tafi da ita ɗin?
“Mutanen garin namu ne sune zasu ɗauke ta. Haura ta ba shi amsa tana nufar gurin da Adam ɗin ke zaune.
Tana zuwa ta ce “Mun gode da taimakon ku a garemu Allah ya saka da alkairi zan bi yan garinmu mu tafi gida lokaci ya yi da zan je gida na amshi hukuncin laifin da muka yi. Shi dai Najib yana ta zuba ido yaga masu zuwa ɗaukar gawar. Adam ya ce “Ba zaki tafi ba kina nan damu har abada, yanzu kin zama ƴar gida ba yar aiki ba, idan za ki iya zama damu anan to zan ɗauke ki kamar ƙanwata har tsawon rayuwar mu. Haura ta fashe da kuka ta na faɗin “Ba zasu barni ba nima dole tare da ni zasu tafi. Ganin yadda take kuka yasa Adam matsowa kusa da ita ya kamo hannunta ya fara bata baki.
Sosai Ameera ke mamakin wai ta kashe ta, to wa ta kashe, sai a lokacin ta tuna da cewar ta naushi wannan tsohuwar maiyar matar da ta tsana. Tabbas a ranta taji mutuwar domin bata yi tsammanin faruwar hakan ba, amma ta wani bangaren taji daɗi kunga kenan yanzu sai su bar musu gida . A haka ta fito ta riski Adam riƙe da hannun Haura. Lokaci ɗaya wani irin abu na kishi ya ratsa zuciyarta, take taji wani irin tuƙuƙi na ƙunci ya dirar mata, hakan yasa ta nufo gurin cikin tsananin ɓacin rai mafi ƙololuwa a rayuwar ta.
Tana zuwa ta kama Haura ta finciketa daga cikin Adam da sauri cikin masifa ta fara faɗin “Shigiya karuwa mara mutunci wallhi sai kin bar gidan nan munafuka. Kai kuma wallahi kaji kunya Adam! Kafin ta rufe baki ya fara faɗin “Kinsan Allah Daga yau Haura ta bar ƴar aiki ta zama yar gida, kuma bari kiji na faɗa miki koda kuskure kar hannunki ya ƙara sauka a jikinta in ba haka ba zaki gane kuran ki. Ganin haka yasa Najib saurin zuwa gurin ya riƙe Adam yana faɗin haba kai kuwa Adam ba kaji me na ce maka ba ne? Dan Allah kayi hakuri har su zo su tafi da gawar nan Please.
Ai take Ameera ta fara magana da faɗa “kai Adam har ka isa na yi magana ka ce min ba haka ba, to wallhi baka isa ba, ita kuma naga uban da zai hanani dukanta. Kuma sai… Kafin ta ƙarasa suka ji wata iska mai haifar da kasala wanda take ya saka su barci. Sun kai minti talatin kafin suka farka suka tarar babu Haura babu gawar uwar tata. Lokaci ɗaya suka fahimci an tafi da ita ne. Ita kuwa Ameera daga haka barcin wahala yayi gaba da ita. Najib kuma ya shiga kwantarwa da Adam hankali akan dan Allah kar ya biyewa Ameera ita ba lafiya gareta ba. Haka dai Najib ya fita ya bar gidan cikin alhini da wannan abun.
Kallon gurin da take kwance ya yi yaji kamar ya rufe ta da duka, tsaki yaja ya nufi ɗakin sa domin yin wanka. Bayan Najib ya koma gida ya sanar da Khadija duk abun da ya faru. Ai kuwa itama abun ya ƙara bata tsoron lamarin Ameera. Ta kalli Najib ta ce “Wai shin anya kuwa ba wani abun ne ya samu cikin Ameera ɗin ba, nifa sai naga nata abun kamar ya yi yawa wallahi, har da kisa? Sannan ni abun da nake tsoro anya mutanann zasu haƙura da kashe musu ƴar uwa da a ka yi kuwa? Najib ya ce “Nima tunanin da nake ta yi kenan, sannan maganar ki gaskiya ce nima na fara tunanin a kwai matsala a cikin Ameera Allah dai yasa kar ya tabbata. “Amin dai! Amma lamarin a kwai ayar tambaya.
Kwance yake ya ƙurawa fanka ido kai ka rantse ita ya ke kallo, amma hankalin sa ya yi nisan zango ga wannan gurin. Tunanin halin da Haura ta ke ciki kawai yake yi, shin zasu kashe ta ɗin ne ko dai yaya, shin yanzu a ina zata zauna. To shin wai yanzu ta tafi kenan bazata dawo ba, Allah yasa ta dawo ta karɓi Addininmu addinin Musulunci Addinin gaskiya da gaskiya. Ta shi yayi zaune ya na tunanin makomar cikin jikin Ameera kawai asibiti zasu a cire shi in dai zata dawo yadda ta ke. Sai yanzu ya samu mafita, ai kuwa da saurin sa ya tashi ya nufi Palo gunda ya barta a kwance tun ɗazu, tana nan yadda ya barta. Ya na zuwa ya kira sunanta da ƙarfi wanda tayi saurin tashi a ɗan firkice. Tana tashi taji wata azabbiyar yunwa wanda cikinta har wani ƙullewa yake yi. “Kije ki shirya zamu tafi asibiti yanzu, kuma karki ɓata mini lokaci. Ya na faɗa ya juya zai tafi. Cikin ƙarfin hali ta yunƙura ta miƙe ta ce “Honey yunwa fa nake ji ka sayo mana abinci ne? Ta faɗa ta na ɓata fuska cike da zaƙuwa.
Adam ya ce “Nima banci abincin ba, ba dai kin kori masu taimakon ki ba, kin san Allah daga yau kullum ke zaki dinga mana girki koda yaushe ko da kuwa cikin duniya ne ke jikinki, kuma yanzu ki tashi mu tafi idan mun dawo sai ki girka mana abinci.
Wani irin tuƙukin masifa da bala’ine suka zo mata wanda yunwar da take cin ta hanata cewa komai, sai kallon sa take yi cike da madarar mamaki.
Ganin zai juya ya tafi ne yasa ta faɗin “Wallahi babu inda zanje ƙara ma kasani” Cike da ƙuluwa ya ce “Ai kuwa wallhi dole sai kinje. “To sai naga uban da zai saka ni naje.
“Haka kika ce?
“Eh haka na ce, naga wanda zai kaini asibiti yau.
Adam ya ce “Dan Allah ki tsaya har na shirya na fito na sameki. Yana faɗa ya koma ɗaki yana jin wallahi yau ko me zai faru sai an zubar da wannan cikin kowa ya huta, koda kuwa shi da kan sa zai zubar mata shi da duka. Sauri-sauri yake komai domin jikin sa har wani rawa ya ke yi kamar wanda zai shiga filin dambe.
Itama Ameera ganin kamar da gaske yake ne yasa ta tashi da gyar ta shiga kicin ta ɗauko sauran abincin jiya ta ɗumama tsabar yunwa ta haɗo da shayin ta mai karo sannan ta nufi ɗakinta. Sosai ta ci ta sha shayin ta yi gyatsa, domin ita cikin ta baya mata zaɓen abinci ko kuma ta ce ita abu kaza take so, ita duk wani abu da take ci a baya to yanzu ma tsaf zata ci, hakan yasa bata da wata matsala ta ɓangaren abinci. Wanka ta shiga tana cikin toilet ɗin taji shigowar sa ɗakin, sai kuma taji ya fita ba tare da yace komai ba. Tana wankan tana tunanin rainin hankalin sa. A haka ta fito ta shirya cikin duguwar riga ta zaman gida, ta ɗauko wayarta ta shiga karatun littafin ta da ta ke yi. Tana cikin karatun taji shigowar sa sai tashin ƙamshi yake yi, sosai ƙamshin nasa ya tafi da hankalinta har sai da ta ɗago ta kalli angon nata. Sosai ta ke kallonsa ganin wani irin kyau da yayi kamar ba nata Adam ɗin ba.
“Ta shi mu tafi” Adam ya faɗa babu alamar wasa.
Sai a lokacin ta dawo daga kallon sa ta ce “Babu inda zanje, yanzu ma so nake na kiraka kamin karatun littafin Addininmu, Please matso kusa kaji rikici tsakanin A J da Laɗifa da kuma Abdullah da Zainab. Ta ƙara sa tana murmushi haɗi da miƙo masa wayar.
Cikin zafin rai Adam ya fizge wayar ya ɗaga ta ya raɗa ta a kan yayiss ɗin ɗakin wanda nan take ta wargaje, yaci gaba da faɗin “Ke kin ɗauka wasa nake miki da har zaki wani bani waya nai miki karatu, to wallahi baki isa ba, bari na faɗa miki na rantse da Allah asibiti zamu je yanzu a cire wannan cikin na gaji da masifu iri-iri akan wannan cikin, idan ban cire ba bansan mai zai haifar zuwa gaba ba. Saboda haka tun kafin rayuka su ɓaci ta shi mu tafi. Adam ya ƙara sa yana nuna mata hanyar tafiya.
Wai Hausawa suke “Mai neman kuka ne aka jefe sa da kashin awaki! Sosai Ameera take bin wayarta da kallo ganinta a wargaje. Tana cikin haka taji batun wai za’a cire ciki ɗan wata bakwai da wani abu. Tun kafin ta yi magana take jin abun faɗa har wani turarreniya suke wajan fitowa daga bakin ta
Sai da ta miƙe tazo har gaban sa kafin ta fara magana har tana wani zaro ido tsabar masifa “Idan rayukan basu ɓaci ba Allah ya tsine musu! Na ce Allah ya tsine musu! Sannan na faɗa bazan je asibitin ba, wato ma cikin da ke wata bakwai kake batun azubar saboda a garin gaɓa-gaɓa muke ko? kuma wayata da ka fasa min Allah ya”…”Kafin ta ƙara sa ya ɗauke fuskar ta da mari sannan ya turata kan gadon ya shaƙe mata wuya bakinsa har rawa yake “Wallhi sai na kashe ki daga ke har cikin dake jikinki ke har kin isa ina magana kina magana a gaba na ko shakkar idona ba kya ji. Sosai ya sha ƙeta yana jin wani haushin ta kamar ma ya danne ta da filo. Cikin a zaba ta yi sa’a ta mai naushin guwar ƙafa a gaban sa, wanda yasa Adam ƙamewa na wuccin gadi a kanta. Ai kuwa sai gashi ya faɗo kanta kamar babu rai a jikin sa. Da sauri ta miƙe tana tari kamar zata yi amai. Tana cikin haka Adam ya farfaɗo ya ƙara kamo ta tayi saurin make masa hannu amma ya miƙe da sauri ya kamota ya ƙara wanke mata fuska da mari itama ta ɗaga hannu ta sauke masa mari kafin ta fara magana cikin ihu wanda shi kuma Adam har yanzu gaban sa na masa wani irin zafi.