Skip to content
Part 14 of 20 in the Series Ameera Da Adam by Salis M. Reza

“Cikin wata bakwai da kwanaki ne ka ke tunanin za ka zubar wai ka haƙura da shi, uban waye ya yi cikin? Idan har kasan ba ka so mai yasa ka yi? To wallahi babu wanda ya isa ya zubar mini da ciki domin ina son kaya na, kuma asbinti ne na faɗa na ƙara faɗa ba zanje ba. Ameera na gama faɗa ta fita daga cikin ɗakin ta koma ɗakinsa har lokacin shaƙan da ya yi mata na sa wuyan ta zafi. Adam kuwa shiru ya yi yana sauraron ta har lokacin gaban sa na masa wani irin zugi kamar tafiyar tsutsa, ya ɗauke wuta sosai yana jin duk abun da take faɗa amma ya kasa ko kallonta bare ya tamka. Har sai da ya kwashe mintina ashirin a kwance ruf da ciki a kan gadon kafin ya iya tashi ya zauna. Hannu ya kai ya shafo gurin ya ji ko suna nan, jin sun koma ƙanana ne yasa shi saurin leƙawa domin ganewa idonsa, ganin akwai su kawai sun daku ne yasa suka koma ciki sai ya saki ajiyar zuciya yana ƙoƙarin miƙewa tsaye.

Tana shiga ɗakin taji kamar motsin mutum hakan yasa ta tsaya tana jiran ganin ko waye domin ita yanzu ba tsoron komai ta ke ba dan uban mutum! Sosai Ameera ta ke ta nazarin maganar Adam wai zai zubar da cikin ta. To ma in banda wawa a ina a ke zubar da ciki ɗan wata bakwai, cikin da za a iya haifarsa a kowani lokaci.

Kallon cikin nata ta yi sai taga kamar ya na motsi hakan yasa ta shafa kansa tana tuno watarana kafin ta samu wannan cikin abun da Adam ya ce idan har ta samu ciki.

Waya ce a hannunsa yana ta ƙoƙarin tura saƙo izuwa email ɗin Najib cikin gaggawa domin ana buƙatar aiki da shine amma abin ya ƙi tafiya, hakan yasa yake ta sakin tsaki babu ƙaƙƙautawa. Yana cikin wannan halin Ameera ta fito daga ɗakin cikin shigar barci. Tana zuwa ta zauna kusa da shi ta ce “Please kabar wannan aikin ka taso mu kwanta zuwa gobe sai ka tura masa Honey ka ji?. Ta yi maganar cikin muryar shaƙwaɓa. Adam ya ce “Wallhi cikin daran nan ake buƙatar aikin ne idan ban tura masa ba a kwai matsala ne. Jin haka Ameera ƙara lanƙwaɓe murya kamar zata yi kuka ta ce “Uhun Uhun ni dai ni dai Allah ina bukatar mijina a kusa dani yanzu na kasa barci. Jin haka yasa jikinsa mutuwa ya kamota ya kwantar kan cinyarsa ya ce “Ki fara barci a nan kafin na ƙara gwadawa ko Allah zai sa a dace. Tana kwanciya ta tura kanta cikin girjin sa kamar zata shige ciki. Ai kuwa tana kwanciya sakon na shiga hakan yasa ya ɗan saki karar murna yana godewa Allah sannan ya ɗago da ita yana faɗin “Gaskiya Ameera ke alkairi ce a rayuwata, kuma ke ɗin mai sa’a ce, duba daga zuwanki har saƙon da tun ɗazu nake ta fama da shi ya shiga.

Ameera ta yi dariya tana faɗin ba wai zuwana ba ne kawai fa ikon Allah ne. Adam ya yi charaf ya ɗauƙeta sai cikin ɗakinsa kan makeken gadonsu. Yana kwantar da ita ta ce “Wannan irin ɗauka da kake min ko jinjira ma ƙare kenan, har na matsu na samu ciki ka daina daukana irin haka domin nasan zanyi nauyi. Adam ya yi murmushi ya ce “Honey wallhi kullum addu’a na ke a ce yau kina ɗauke da cikina da daga wannan ranar kin daina komai har sai kin haife min shi ko ita ko su. Idan zaki je kicin zan goya ki, idan za ki shiga toilet zan goya ki, ke koma me zaki yi to kina baya na. Ni fa da sai na kafa tarihin da ba’a taɓa samun mijin da yayi shi ba, domin haihuwar ma tare zamuyi. Ameera ta yi dariya domin ta saba jin irin waɗannan maganganun a kan cikin da ba’a ma riga an samu ba.

Ta ce “Ni dai zan so naga ranar da za’a dinga koya ni ko ina na ce zan je. Adam ya ce to ki dage ki ɗauki ciki ko yau ne kiga aiki da cikawa daga bakin masu abun, yana faɗa ya na kamota suka shige bargo ya na ƙara cewa, da Kinga yadda maza ke naƙuda suna taya matansu aihuwa.

Kalmar taya matansu haihuwa ce ke ta yawo a kan Ameera lokacin da ta dawo daga tunanin. A fili ta ce “Gashi ba’a tayani haifa ba za’a tayani zubarwa. Sai ma yanzu take ƙara tunano irin alƙawarin da yayi akan ta muddin ta samu ciki. Hannu ta kai ta shafo wuyan ta ta ce “Allah ya isa mugu wallahi kashe ni yaso yi, wai ma yaushe Adam ya koma haka, ko dan mutuwar da wannan matar ta yi ne, to ai naga ba nice na kashe ta ba, kuma ma ni matar sam ban yarda da itaba ƙara ma da ta mutu. Tana cikin haka taji ana ƙoƙarin buɗe dakin nata, hakan yasa ta dawo da kallonta izuwa gurin. Adam ne ya shigo yana tafiya a gwale kamar ɗan kaciya hakan yasa Ameera kafe shi da ido tana son yin dariya, ganin yadda ya haɗe fuska ne yasa ta ƙara jin dariya ya zo mata, ai kuwa take ta saki kayar ta harda tafa hannu tana nuna shi. Adam kuwa ganin irin dariya da take yine yasa ya ƙara jin wani mugun haushin ta, haka ya shige toilet ba tare da ya tanka mata ba. Yana shiga ta bishi ciki tana dariya. Bai ce mata komai ba ya shiga cire kayan jikinsa ya juya mata baya amma da dawo ta gabansa tana kallon yadda suka koma kamar ta yara. Lokaci ɗaya ta ƙara sakin dariya harda faɗuwa.

Sosai Adam ya kai chan sama mutuƙar ƙuluwa, amma azabar da ya ke ji ba zai biye mata ba, shi dai hukuncin da ya yanke kawai shi zai aiwatar. Haka Ameera ta ke ta faman dariya har ya yi wankansa bata damu da jiƙata da yayi ba, ganin ya kusa gama wankan ne yasa itama ta fara nata wankan ba tare da ta cire doguwar rigar jikinta ba.

Adam na fitowa ya saka doguwar jallabiya ba tare da ya saka wando ba, ya kwanta yana kallon sama yana addu’ar Allah yasa dai abun nasa su tashi kar su samu matsala. Yana cikin haka yaji fitowar ta. Rintse ido ya yi yana jin wani faduwar gaba lokaci ɗaya, hakan yasa ya riƙe gefen zuciyarsa yana salati. Ameera kuwa tun a cikin toilet ta gama shirya irin muguntar da zata masa badan komai ba sai domin taga yadda zai yi. Tana fitowa daga ita sai tawul wanda girman cikinta bai sa ya ɗauru sosai ba. Ta na fitowa tazo gabansa ta ce “Malam ina bukatar haƙkina a gurin ka yanzu.

Ita kanta da ta yi maganar taso ta yi dariya domin ganin irin kallon da yayi mata, amma ta dake tana ƙoƙarin ɗaga rigarsa. Adam da ko magana baya jin zai iya yi ya ce “Idan kika taɓa ni Allah ya isa ban yafe ba. Adam ya faɗa kamar zai yi kuka tsabar takaice. Ameera ta ce “Ban gane Allah ya isa ni da hakkina ba, yo ta ina Allah ya isarka zata bi ni bayan Allah bai hana ba, kawai ka tashi ko na kwata da ƙarfi na. Ta ƙarasa tana ɗaga rigar tasa. Idan da tasan irin azabar da yake ciki da tai masa uzuri amma ganin da gaske take yasa Adam faɗin. “Dan Allah kiyi haƙuri. Ameera kuwa cike da mugunta ta ɗage rigar tana ƙara kallonsu tasa hannu ta taɓa, sai kuma ta kama da niyar jansu ko zasu tashi. Ai kuwa Adam ya kurma ihuu wanda yasa Ameera saurin sakinsu tana kallon sa. Ganin haka yasa Ameera ƙara dawo da shi ta ce “Malam Allah fa sai na karbi hakkina. Ta ƙara kwantar da shi zata ƙara kamawa jin tana son kashe shi ne yasa Adam faɗin. Idan kika ƙara taɓawa wallahi a bakin auranki!. Kina karawa na sakeki. Yana faɗa hawaye na zubowa daga idanun sa.

Da sauri Ameera ta miƙe tsaye ta saki dariya tana faɗin, ai ko baka faɗa haka ba ma ba yi zan yi ba, to ina abun ya ke, dama ina so ne kawai na gani ko zasu iya tashi. Tana faɗa ta nufi gurin kayanta ta ɗauko wata doguwar rigar irin ta jikinsa ta saka bata ko shafa komai ba sai turare, ta zo kusa da shi ta ce “Honey dan Allah ka ƙara ɗauko mana wata mai aikin please ni ba zan iya komai na gidan nan ba, idan yaso wannan karan ka samo mana tsohuwa kaji? Adam ya lumshe ido ya buɗe ya ce “Tom” Ameera ta rungumo shi ta na kantar da kan ta a kan ƙirjinsa ta ce “Na gode Honey sannu Allah ya baka lafiya ka ji. Ta faɗa cikin seriously.

Jin ta yi barci a jikinsa ne yasa ya tashi ya zauna yana kallonta. Lokaci ɗaya hawaye suka wanke masa idanu idan ya tuno da cewar wai Ameera ta Adam ɗin sa ce ta dawo haka, Ameera da bata ko iya ɗaga sautinta a kan nasa, Ameera da take son abin da yake so fiye da shi, Ameera da bata son ko damuwarsa amma wai ita ce yau take son kashe shi. Shi dai har yanzu bai yarda laulayin ciki ba ne wannan, wallahi wannan yafi ƙarfin laulayin ciki domin idan ya tuno abubuwan da ta yi sai ya ƙara tabbatar da cewar ba laulayin ciki be. Azuciyarsa ya ce “To me kenan? Sai kuma ya yi shiru yana tunani. Shi dai yasan babu komai kuma babu alamar komai a tare da ita.

Tashi ya yi ya koma waccen ɗakin ya ɗauki wayarsa ya kira Najib a kan yazo gidan yanzu, amma Najib ya sheda masa cewar baya gida yanzu kuma ba zai dawo ba sai dare ya bari kawai su haɗu gobe. Yana sauke wayar tunanin Haura ya faɗo masa. Ya ce “Yarinyar kirki mai haƙuri Allah yasa ki dawo muna kewarki. Yana faɗa ya tashi ya cire wannan doguwar rigar ya saka ƙananan kaya da wando gajere so yake ya kai karar Ameera gurin iyayenta domin susan halin da ake ciki. Ya ‘na gama shiryawa ya fita daga gidan, amma ganin irin tafiyar da ya ke yi ne yasa dole ya dawo domin yasa tabbas kallo ɗaya za’a ai masa a gano a kwai wata damuwar. Khadija ya kira amma bata amsa ba sai kawai ya tura mata da saƙo akan ta saka shi a cikin addu’a.

Da yamma da kansa ya shiga Kitchen domin yasan ita kam ba shiga zata yi ba, shi kuma yunwa ya ke ji, hakan yasa ya shiga ya haɗa musu abinci mai sauƙi. Bai gama abincin ba har kusan an fara kiran magariba hakan yasa ya na jere abincin ya yayi wanka ya fita Masallaci. Kafin ya dawo itama ta ta shi ta kara yin wanka ta fito palo tana hamma. Ganin abinci a jere yasa ta ja tsaki ta nufo gurin abincin ranta duk a jagule. Ta buɗe ta ga abin da ke ciki sai taji ita kawai ɗan wake take son ci ba taliya ba, komawa ta yi ta daura alwala ta fara Sallah.

Bai dawo ba sai da ya tsaya a ka idar da sallar isha. Yana shigowa ya sameta zaune tana jiransa. Ba tare da ya ce mata komai ba ya zauna ya buɗe abincin ya fara zubawa, ganin bai ce mata komai ba ne ta ce “Honey ya jikin naka?

Adam kaman yayi kuka dan takaici, yaushe ya ce mata bai da lafiya, idan ma abun da take nufi ne ai ita ce sila. Bai ce komai ba ya ci gaba da zuba abincin sa. Sai ta ƙara ce wa “Honey ni me zan ci ne? Ta yi tambayar domin shima yasan ba ta son taliya.

Adam ya ɗaga kai ya mata kallo ɗaya sai yaga kamar ba fuskar Amearan sa ba tsabar haushin ta da yake ji. Ganin dai bai tamka mata zai yi ba ne ya sa ta ce “Wai ina ta magana ka min shiru, kai kasan ni ba wani damuwa na yi da wannan taliyar ba, kuma ka dafa duda kasan bana so, na zo ina maka magana kuma ka yi shiru?

Adam ya ce “Abun da nake so na dafa kema zaki iya zuwa ki dafa abun da kike so. Ameera ta kalleshi ta ce..

“Ok tanan ka ɓullo kuma? To ni ɗan wake nake so ka dafa mini, please shi nake son ci. Ta faɗa cike da bada umarni. Adam ya ci ga ba da zuba abincin sa ba tare da ya ce komai ba. Ta ce “Ba ka ce komai ba fa?

Ya ce “Ba zan iya ba”

“To me ka ke nufi da ba za ka iya ba? Kenan haka zan kwanta banci komai ba?

Cikin tsananin bacin rai da wannan taƙura shi da ta yi Adam ya ce “Na ce ba zan iya dafa miki ɗan wake ba, idan kina so ki tashi ki yi kayan ki na gama magana. Ya faɗa cike da ƙunci da takaicin ta. Jin haka yasa Ameera faɗin…

“To wallahi ba ka isa ni na kwana banci abinci ba kai kuma ka ci, sai dai duk mu kwana a haka. Tana faɗa ta ture kulan abincin ƙasa ta ɗauki wanda ya zuba a fleet ta ɓarar da wannan ɗin shima, sannan ta ce “Sai dai kowa ya kwana bai ci abinci ba a cikin gidan nan wallahi. Adam da rabonsa da abinci tun safe, tsabar yunwa har wani jiri-jiri yake ji. Kallonn kulan abincin ya yi ganin duk ya zube babu komai sai yaji kamar an cire masa duk wata laka ta jikinsa, lokaci ɗaya ya ji wani irin abu na ɓacin rai da bai taɓa jin irin ba.

<< Ameera Da Adam 12Ameera Da Adam 14 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×